MASARAUTAR MU

16/17

by @3166321120319264



FREE FAGE





.....................✍🏼 Prince Zaid ne zaune a cikin jirgin da zai maidasu gida Niger, Hibbullah da ke ta zumud'in zuwa ya ga sahibarsa Iffah dan ya yi missing d'in ta sosai. So ya ke suyi hira kafin su isa amma ganin gogan na ku sarautar ce ta motsa,yasa ya koma gefe ya sa masa ido.





"Wai kallon me kake min ne sai ka ce maye" Prince ya tambayi Hibbu.

Dama kad'an Hibbu ya ke jira ya ce" kai da wana idon kasan ina kallonka ka ji mutum?"

Tsaki Prince Zaid ya yi, ya d'auke kansa.

Dariya Hibbullah ya shek"e da ita ya na cewa" yau sai da dogarai an koma gidan tsaro".



Abin da Prince Zaid ya tsana kenan wannan tsaron na masifa,ba dama ka fito daga d'akin ka sai an bika a baya duk in da zakaje.

"Ka na wani abu sai kace mahaukaci mtsww" Prince Zaid ya fad'a ya na k'ara k'ullewa.

"Daga fad'ar gaskiya sai a kira ni mahaukaci, to ai shikenan" daga haka kowa ya yi shiru su na ci gaba da addu'ar Allah ya sauke su lafiya.






Jakadiya ganin inuwar mutane ana isowa wajen da ta ke tai saurin sakin jikin ta, ta nufi hanya da sauri kamar shigowar ta kenan, ganin Fulani babba ce yasa ta kama kirari " taka warki lafiya babbar gwiwa a shigo lafiya  matar sarki uwa ga sarkin gobe inshaallah " . A haka su ka k'arasa har bakin k'ofar d'akin Fulani Hafsa baiwar ta ce ta k'on k'wasa.



Lukman ne ya ba da izinin a shigo bud'e k'ofar baiwar ta yi, Fulani ta shiga d'akin ganin mai martaba a tsaye ya na shirin barin d'akin.

"Allah k'ara lafiya da Nisan kwana ya mai jikin" Fulani da ta ke gaban mijin nasu sarki Abdrrahman ta fad'a. 





'Daga kai kawai ya yi sannan ya amsa"Alhamdulillah,ta samu bacci ma" 

"Allah ya k'ara sauk'i" tace.

Lukman ya gaishe ta cikin girmamawa tamkar mahaifiyarsa haka ya ke bala'in yi wa Fulani biyayya.

Ya mai jiki tai masa ya amsa.sannan su ka fito gaba d'ayan su, Fulani da Lukman su na ta ke wa sarki bayansa, su na fitowa Jakadiya da sadiya baiwar Hafsa da baiwar Fulani su ka ta ke mu su baya.






Suna fita fadawan sarki su ka koma ba kin aikin su, Fulani da bayin su su ka wuce part d'in su, Lukman ya koma part d'in sa. Dama so ya ke ya keb'e ya kira Likita dan me zai ce sai gobe bayan gobe ake sa ran dawowar bak'in shegen nan da wannan d'an sa idon munafukin abokin nasa, kiran likitan ya yi dan ya ji meyasa ya yi hakan? 





Likita ya na gidan sa ya na ta farin cikin arzikin da ya samu rana d'aya, ya ji kiran Lukman da rawar jiki ya amsa duk da lokacin k'arfe 12:30am na dare ne.

Cikin fad'a - fad'a yace "damme za ka ce sai gobe result zai fito?".





Murmushi Dr.Abdallah ya yi yace" ranka ya dad'e k'a'ida ne sai anyi hakan, kuma gobe inshaallah zan kawo result d'in kamar yadda ka ke so, a yi min afuwa yallab'ai".

"Okay to nagane ba matsala, sai goben"

Katse wayar ya yi sannan ya kwanta baccin asara.






Hidima a ke ta yi a cikin masarauta dan tun da aka ce Prince Zaid zai dawo kullum cikin hidima ake, yau ne a ke sa ran dawowar su Prince Zaid da Hibbullah, tun safe airport d'in Yemen ya ke cike da magoya bayan prince Zaid, a Polo duk da an hanasu shiga amma k'ofar a cike ta ke da matasa.





Zeenat tun kafin asuba ta tashi, ta sha kwalliyarta, Allah - Allah ta ke a ce a je taron yarima.

'Daukin da ta ke har mamaki ya bawa umman ta, "umma wai da k'arfe nawa jirgin na su zai iso ne?" Zeenat da ta gaji da jira ta ke tambaya.

"Ni ina zan sa ni Zeenat da kin tambayi babanki ai".

Cuno baki gaba ta yi ai kamata ya yi ace tun asuban nan su ka iso saboda Allah". Umma ta ce" tun da har yan zu bai iso ba, ga wanke -wanken cen ki yimin kafin mu je tarb'ar shi".




Dafe k'irji ta yi kamar angayamata abun tashin hankali tace"nashiga uku umma, wana wanke - wanke kuma bayan na gama shiryawa dan Allah ki bari sai mundawo please umma na"

Ta fad'a ta na had'e hannuwanta irin na indiyawa.





Tun wajen goma na safe Dr. Abdallah ya iso cikin masarautar, sai murmushi ya ke ta faman dokawa, iso aka yi masa har cikin falon Fulani ta uku, kowa ya hallara a wajen Lukman,Prince Safwan,Fulani da Fulani ta biyu wato Samira. 

Fulani ta uku kuwa,ji ta ke kamar da gaske cikin za'ace ta na da shi.





Sai yatsina ta ke yi, 

Likita ya iso fuskar sa tar da murna, "Assalamu Alaikum" 

Zubewa ya yi gaban Fulani babba ya d'ibi gaisuwa, sanna ya had'a ya yi wa sauran a tare, hakan da ya yi, ya k'ara rura wutar k'iyayyar ta a zuciyar Samira.





Likita ya gyara coat d'in jikinsa yace"Alhamdulillah sakamakon gwaji ya fito ranka yadad'e"

Farar paper ya zaro daga aljihunsa ya mik'awa Lukman dan a mik'awa mai martaba, idan ya fito. Cikin zak'uwa Lukman ya ce" Doctor (likita) me ya sa me ta ne? "




Mummushi ya yi yace"ranku ya dad'e, ina ta ya ku murna, ai ta na d'auke ne da juna biyu"  

Wani murmushi Fulani Hafsa ta yi, yadda planning ya ke tafiya dai dai.

"Alhamdulillah,Allah mungode maka" Fulani babba da farin ciki kwance a fuskarta ta fad'a, mungode da wannan kyakkyawan albishir d'in likita"





Fulani Samira kuwa kallon likitan kawai ta ke yi ta na mamakin cikin da Hafsat d'in ta ke da shi, daure kishin da ya taso mata ta yi tace, "mashaallah muna ta ya ki murna, Allah ya inganta, likita akwai kyauta da za ta zo yan zu daga gareni"

Zubewa k'asa likita ya yi ya na ta godiya kamar ya aro baki.






Prince Safwan kuwa cewa ya ke"ni zan fara yiwa mai martaba albishir d'in nan" Lukman ma cikin farin ciki yace "tab ka ma isa, ni ne zan fara yi masa wannan albishir d'in ai"

Gaba d'aya su, su ka yi murmushi. Fatan alkhairi su ka yi mata sannan su ka tashi kowa ta koma part d'in ta.





Likita na shiga office d'in sa ya ji alert ya shigo 10 millions sun fad'a

Hannun sa har rawa ya ke ya d'auko ya duba. "Wow ni ne da wannan kud'in wayyo arziki na ya zo, dare d'aya Allah kanyi bature, bari in sanar da yallab'ai sun shigo".

Kiran Lukman ya shiga yi,amma ba'a d'aga ba,hak'ura ya yi anjima ya k'ara kira, amma kafin nan text (sak'o) ya tura ma sa ta wayar ya Samar da shi kud'in ya shigo, sannan ya rufe office d'in ya fice daga asibitin gaba d'aya.






Lukman ne zaune gaban mai martaba ya mik'a masa result ya na ta murmushi, " Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana likita ya zo d'azun, ya kawo sakamakon".

"To mashaallah" ya fad'a ya na karb'ar takardar da Lukman ya mik'a masa.

Bud'ewa ya yi ya fara karanta wa da kansa tun da a cikin turakarsa ne, ganin abin da sakamakon ya nuna ne ya sa sarki y...............





Hamza da tawagar 'yan JIHAD DA'AWAH FOUNDATION, su ka sauka a kasar Morocco, domin d'aukaka kalmar Allah. Sun sauka a bayan wani gari Wanda su ke rayuwa kamar dabbobi, ba su da wani addini haka nan su ke rayuwa.





Sultana ce gaban mahaifiyarta kuka ta ke kamar ranta zai fita "mommy ki sa daddy ya gayawa sheik Usman ni Sudees na ke so na aura, idan ba haka ba Wallahi sai na shiga duniya" shiru mommyn na ta tayi ta rasa meyasa Sultana ta nace sai wannan ustaz d'in ta ke so, ga ta da masoya tun daga 'ya'yan sarakuna da masu muk'amai manyan mutane dai,amma duk tak'i sai ita sai Sudees.




"Sultana ni bazan iya wannan abun naki ba, ki je ki same shi da kan ki,ki gayamasa ni nagaji da ganin wannan yaron ya na wulak'anta ki. ke kad'ai Allah ya ba mu, idan mijinki ne Wallahi dole sai ya aure ki,komai girman kansa, sai ya yi miki biyayya kuwa.




"Sultana ba abinda za ki nema, a duniyan nan ban yi miki shi ba Wallahi Tallahi sai kin mallaki yaron nan a hannunki dan ubansa" ambassador...




Boka Gannami yace wa mesar nan "zan aike ki wajen wasu mutane, na aiki bayi na har biyu ma su had'ari amma sun gagaresu, nasan ke za ki iya hallakamin su ki je ki nemosu duk in da su ke a fad'in duniyar nan ki hallakamin su, barin su na iya zama had'ari ga MASARAUTAR MU, da rayuwar mu gaba d'aya" ta ke mesar ta bud'e bakinta wani ruwa mai zafi ta ke fesarwa, wan da in dai ya tab'a mutum ko dabba sai ya k'one. Ta ke ta nitse cikin k'asa ta b'ace.






Hazid ne ya ce "ya shugaban bokaye, su waye wannan mutanen da ka ke tsoron shugowarsu MASARAUTAR MU?" 

Sarki Gannami yace" Hazid boka 'Daundumi ya ce su na da hatsari sosai, ni da kaina na so ya barsu su shigo, mu ba wa K'ainina jinin su, ko da sun kai girman runduna na wa amma yace ba su da yawa sai dai k'arfin wani abu da ke tare da su, wan da ba tsafi ba ne".





Hazid ya bushe da dariya yace " hahhh hahhhh amma boka 'Dundumi ka ban kunya akan wasu tsirarun mutane ka aika musu, wannan mesar ai kuwa ka ban kunya"

Boka 'Dundumi yace" ya shugaba na nayi - nayi na gane lagunsu amma abun yacitura,tabbas in dai ban dakatar da zuwan su wannan MASARAUTAR ba to kuwa mulkin kuma sai ya k'are".

Takobi Hazid ya zare ya na nufo boka 'Dundumi ya na cewa "k'arya ne boka ina rantsuwa da k'arfin tsafin baba na ba wanda ya isa ya karya mana MASARAUTAR MU zan so su zo, kuga yadda zan musu kisan gillah da kaifin takobina".





Boka 'Dundumi ya bushe da dariya me firgitarwa cikin muryar yara yace" Yarima tun da k'arfin tsafina bai nunamin abin da su ke tak'ama da shi ba to kuwa na rantse da girman K'ainina ba mahaluk'in da ya isa ya gani, nasara d'aya da za ka samu shine su na da maganin da zai warkar da kai kuma warkar da kai dai - dai ya ke da karyewar MASARAUTAR MU kuma na yi alk'awarin ni da kaina zan samo maganin da za ka warke".







Hazid ne yace " k'arya ka ke tsoho, ni da kai na nasan yadda zan yi da su, tun da kai ka kasa"

Sarki Gannami da ya gaji da wannan zancen na su yace" Hazid zaka warke tabbas nasan K'ainani zai warkar da kai ka k'yale zancen boka 'Dundumi ni nasan k'arya ya ke". Boka da ya ke murmushin mugunta ya na sak'a musu mugun nufi a ransa, yadda su ke k'aryata shi a yanzu, ya san duk abin da ya fad'a musu to kuwa sai ya tabbata amma sun manta da waye 'Dundumi akan buk'atar kansu.





Shiwu da ta ke cikin keji ta na jin abin da su ke fad'a ta ce"ni nasan Hazid zai warke ya shugabana ka fitar da ni daga cikin kejin nan dan furfurar kan kakanka Hauno na tuba ya shugaba"

Sarki Gannami ya ce "tun da ki ke son ganin bayan MASARAUTAR MU anan za ki ta zama Shiwu". Hazid yace " Ya babana, kar ka manta uwace a gare ni, in dai ana son ayi bikin shekara cikin albarkar K'ainina to ka kwance Shiwu idan ba haka ba zanyi b'arnar da kowa sai ta ja masa tsinuwar K'ainina.





Sanin halin Hazid ya sa sarki Gannami nu na kejin da sandar sarautarsa ta ke kejin ya b'ace Shiwu ta fito, rungume d'an nata Hazid ta yi ta na masa kirarin da ta ke masa acikin kunnensa, soyayyar d'a da uwa sai Allah. 






Obi ganin anfito da Shiwu ya sa ta je fa mata wa ni abu kamar k'onar wuta da idon ta, kafin abin ya je ga jikin Shiwu,Hazid ya rik'e shi ido kawai ya k'urawa Obi, ta ke jikin ta ya fara rawa, dan tasan waye Hazid ya sha Jamata kunne akan Shiwu amma ba ta ji. Je fa tsafin ya yi a jikin Obi ta ke ta hau ihu ta na rok'on Hazid, boka da ya ga abin da ya ke faruwa ya sa ya bushe da dariya yace "ba'abin da ke sa in nishad'i irin rama cuta ga macuci ka yi dai - dai yarima Hazid"  




Take jikin Obi ya yi burd'in - burd'in kamar k'una, sai d'aukan ta akai,aka mai da ita d'aki, sai ihu ta ke tasan tun da Hazid ya rama to kuwa ba zai warkar da ita ta dad'in rai ba.





Yau ne bikin shekara kowa ya sha ado cikin sabon walkinsa, mata sai tuk'a tuwon accan su suke, domin ci da miyar naman hadaya.

Rona ce ta fito cikin shirinta Lamma na cewa" Rona ki tawo mana da miyar hadaya ko K'ainina ya ba mu daman fita kamar kowa".

Bisi ne ya shigo cikin sabon walkinsa,dogon mutum k'akk'arfa damtsen hannunsa d'aure da guru kalar walkinsa fuskar sa d'auke da murmushi

Jikinsa luf - luf kamar ba mai sana'ar faskara ice ba.






Hantsi ce ta fara ganin shigowarsa d'akin, Lu'u da ya fito shima cikin shirinsa na janwalki, ganin Bisi a gidansa ya razanar da shi,dan bai tab'a sanin yana zuwa gidan ba, tsoron tonuwar asirinsu ne ya sa yace" Samari lafiya?"

Bisi ya sakar masa murmushi sannan yace "lafiya lau,na zo ne in ga su Lamma kafin in tafi wajen bauta".






Lu'u cikin razani yace" anan g....

Rona ce ta katse shi da cewa"Bisi shigo mana yan zu nake tunanin ko ka wuce wajen bauta"

Lu'u da mamakin ya akayi su ka san shi ya kamashi. Lu'u yace "Rona waye wannan?" Bayani tai masa sannan shi ma ya ji hankalinsa ya nutsu da Bisi.





Haka su ka tafi wajen bauta a tare akabar su Hantsi da Lamma a d'akin su duk gari an tafi wajen bauta.

Cike wajen bautar ya ke da mutanen garin Duhuwa ga hadaya an rataye su a jikin dogon gini, wani k'aton mutum ne rik'e da mashi Wanda za'a tsire hadaya K'ainina ya sha jini,sannan a yanka a yi miyar shekara da namansu.

Bisi da ya ke jin rashin dad'i a ransa ganin za'a yanka hadaya haka zuciyarsa ta ke jin, wannan ba dai - dai ba ne, ba yan da zaiyi haka shima ya kama rawar da suke yi a wajen ya na tayasu farin ciki.





Fitowar sarkin Gannami da Hazid da Shiwu ne yasa kowa ya nutsu a ka hau gaisuwa sarki Gannami na hard'e akan kujerar azurfa wa su bayi sun d'auko shi akan kafad'arsu.

Haka Hazid da Shiwu duk d'auko su a ka yi. 

Bayan angama rawa da gaisuwa aka tsire hadaya k'ok'on tsafi a ka Tara a ka yanka su jinin ya taru a k'ok'on boka 'Dundumi ne ya ke tsafin sa ta ke jinin ya b'ace ihu gaba d'aya gurin ake ambawa K'ainina jini. Naman a ka yanka wuta sosai a ka hura, ana ta miyar da kowa a hannu ake ba shi domin samun albarka, samarin gurin sai neman matar da zasu aura su ke, dan duk shekara ake aure a wajen,in dai ki ka bari saurayi ya rike ki to shikenan kin zama matarsa. 







Bisi na gefe a tsaye abokan sa matasa ne su ka zo su ka ce "Bisi ka zo muje samo mata a wajen 

Layin 'yanmata mana".

Yatsina fuska ya yi yace" Ni ba aure zanyi ba ku je ku kuyi"

Timi ne yace"ba na gaya muku ba, baisan me ya ke masa ciwo ba"

Haka su ka bar shi su ka tafi.




Hazid neman budurwarsa ta madubi kawai ya ke,amma ba ita haka ya ji bayason kama ko wacce mace a wajen dan budurwar kawai ya ke buk'ata, sarki Gannami ya ga k'asa ta na girgiza ta na t.........








*    *    *    *    


Misalin k'arfe 12:45 jirgin Prince Zaid da Hibbullah ya sauka, dogarai da fadawa ne kawai su ke kai kawo a airport d'in, matasa kuwa sai ihu da murnar dawowar fitaccen d'an wasan Polo kuma Prince d'in su Zaid Abdurrahman Abdul'azeez su ke.





Fitowa ya yi sanye da kayan sarauta bak'ar alkibba ce a jikinsa da glass bak'i Wanda ya b'oye ainahin idanunsa. Tun da ya fito ake ta faman d'aukar sa a camera ko ta ina, sai ka re shi ake yi ana ba shi tsaro, Hibbu na gefensa cikin shigar coat brown ya sha stoking. 





Mota aka bud'e masa sabuwa dal musamman mai martaba ya tanadeta saboda dawowarsu Prince Zaid da Hibbullahi Waziri Usman.






Mai martaba ya na ganin abin da result ya nu na ya yi farin ciki dan ba k'aramin tausayi Fulani Hafsa ta ke ba shi ba, ganin ita Allah bai bata haihuwa ba, a ta ke yace wa Lukman "an bawa Likita kujerar Hajji guda uku saboda wannan kyakkyawan result d'in.

Lukman ya saki murmushin gefen baki yace" godiya ya ke ranka ya dad'e,Allah ya sa a gama lafiya".

Mai martaba ya amsa da "Amin Lukman.

Me ka ke so na baka a matsayin tukwici?"

Murmushi Lukman ya yi yace"ba abin da na ke so, komai ina samu raka ya dad'e".

Fitowa ya yi yana fito dan nasara kawai ya ke gani cikin kwanciyar hankali. Jakadiya ya gani ta na kallonsa ta na dariya,zuwa ta yi tace"ranka ya dad'e "Alhamdulillah yarima babba ya iso lafiya,su na hanya yan zu haka".







Da sauri Lukman ya ce "dama yau ne ko, okay ai namanta shap da ni da kai na zan d'akko abokina kuma d'an uwana ai,amma yan zu ma ba ta b'aci ba"

Jakadiya cikin bugar cikinsa tace"ranka ya dad'e ina ta ya ka murna,Fulani an samu rabo, Allah ya inganta, fatan mu samu takwaye" kallonsa ta yi ko ya zai yi, fito ya ci gaba dayi ya wuce part d'in Auntyn na sa, dan sanar da ita kyautar da akayiwa likita.

Shigar sa d'akin kenan ya same ta a.................