4
by @zeety
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*_
_wannan page din naka ne *ABBAS KAROFI* A.K.A Voncaxee A.K.A bobosky A.K.A angon Mardiyya ne ko Farida🤣 bari dai inyi shuru kar crushes dinka su kamani, dukda dai naji readers suna baka mardiyya har yau banga en team din farida ba🌝 kuma da halamu itace twinny ka tunda gashi har kama kukeyi😅. nevertheless, just want you to know that anty zee loves you much, keep on pepper🔥🔥🔥 them bro❣️_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
4📚
Mardiyya, zeezee da farida tare suka tashi anguwan su d'aya, saidai tun suna yara dama zeezee da mardiyya hankalin su yafi zuwa d'aya, amma dai duk da haka suna a shiri da farida, rashin shirin su ya samo asali ne lokacin da suka fara girma, farida da zeezee sun kasance masu son gaye sosai saidai duk da haka zeezee tafi farida class kuma komai tayi sai yafi na farida kyau, wannan abun shi ya fara rabasu saboda farida mutun ce me kishi batason wani ya iso ta balle har ya wuce ta, ta fison duk inda tashiga tazamo itace madubi kowa ita yake kallo, sai ya kasance mutukar zeezee na wajen to babu me bi takanta wannan abun sai yasa tatsani zeezee sosai, ita kuma dama bata cika hidima da ita ba don haka ta ebeta ta tawatsar….
Mardiyya kuma saida suka shigo jami’a dalilin hasib tadaina kulata kuma dama tanadan jin haushin ganinta da zeezee , Hasib farko farida yafara gani kuma da ita suka fara soyayya, amma bai tab'a zuwa gidansu ba kullum acikin skul yake samun ta, shima kuma sai hakan yafi mishi dad'i… don yasamu kanta kullum yazo zasuyi hira a mota dan kiss da hug da sauran touch touch duka yana samu a wajenta saidai taki yadda yaakaita gidan shi … kullum sai yayi kokarin shan kanta amma fir saitaki wataran harsai tayi kamar zata yadda amma inta tuno da baban ta sai taki, don duk iskanci farida tanajin tsoron baban ta, ana cikin hakane wani rana idon shi ya kyalla kan mardiyya bakad'an ba kyanta ya fisgeshi, amma ganin yanayin nutsuwar ta ne yasashi monitoring d'inta har saida yagane gidan su, yaki tunkaran ta acikin makaranta saboda yasan irinsu bazasu kula na miji akan hanya ba, bai tab'a sanin anguwan su daya da farida ba sai bayan yashawo kanta anfara soyayya, kuma dama tunda idon shi ya kyalla kan mardiyya ya manta da wata farida kota kirashi ma baya d'auka karshe ma blocking d'inta yayi (maza kenan ).
Wani rana yazo hira wajen mardiyya tarakoshi wajen gate saiga darida kuma ta dawo daga anguwa , daga farko ta mayar kamanni ne amma suna matsowa kusa ta tabbatar wa kanta lallai Hasib dinne… sa driver tayi ya tsaya a setin su… glass din motan ta saukar, saida sukayi ido hud'u sannan tace mishi suje…
Koda ta shiga mardiyya kallon tuhuma tabishi dashi tace kasanta ne…. girgiza kanshi yayi halamun a ah sannan yace ko kad'an, may b dai ina mata kama da wani wanda tasani ne.
washegari da sukaje skul acikin mutane farida tazo cikin izza ta nuna mardiyya da yatsa tace mata wallahi idan kina neman lafiya dani kifita a harakan Hasib in kuma ba haka mu zuba nida ke, take zeezee taji ranta ya b'aci rai a ta buge yatsan faiza da sauri mardiyya ta riketa fizgewa tayi tace da Allah mardiyya kyaleni bazaiyu tayitayiwa mutane rainin wayo ba, kankance ido zeezee tayi tareda nunawa faiza yatsa tace bari kiji duk macen da ta isa mace bata fad'a akan na miji, kuma idan har saurayi nasonki bazai bi wata ba, watakila ma karya kikeyi baisanki ba kece kikeson shi baima san kinayi ba, take zuciyan farida yahau tafasa… nan fa cacar baki ya kaure saida kawayen su suka rabasu da kyar, tun ranan suka daina magana, kullum tagansu sai bakar magana su kuma kobi takanta ma basayi, wannan sune dalilan gaban su.
Tana wucewa da kawarta mardiyya tace yauwa ni zeezee dama farida tanada yayane? Kad'a kai tayi tareda nuna ko inkula tace gaskiya bana tunanin tanada shi... wani nake gani a gidansu kamanin shi da farida harya b'aci… zeezee d'aukan jakanta tayi tareda tab'e baki tace halan d'an uwan ta ne, tashi mutafi lokaci ya kure ni banason tad'in yarinyan nan… murmushi mardiyya tayi tareda jinjina d'aukan zafi irin na zeezee aranta, ita dai gani take komai yawuce kuma ma ko kad'an bata rike farida a ranta ba.
Yana ajiye nabil yawuce office dayake yayi reporting, take aka turashi office d'in manager da zaiyi aiki, yaje office d'in yayi knocking izini akaba shi ya shiga wani babban mutun me fara’a shi kadai yagani a cikin tangamemen office d'in da halamu dai shine manger, gaisawa sukayi mutumin yace mishi kaine corper da aka kawo ko? Yace eh, yace munyi magana da dad d'inka shiyasa nace akawoka office d'ina… mutumin ashe abokin dad d'inshi ne, nan yafara tambayan shi a ina yake da zama kwatanta mishi anguwan yayi , mutumin yad'ago kai yace gidan Alhaji hanif? kai ya kad'a mishi sannan yace eh… barin rubutun da yakeyi ya d'ago kanshi duka yace ai neighbor nane meye halakan ku dashi? Abbas yace mishi brother mama nane… nan dai haka sukayi ta tad'i yinin ranan babu aikin da yayi sai washegari yafara aiki.
Satin shi guda kenan da fara service a office d'in Abban Mardiyya, a wannan satin duk yadda farida takeson tasamu time d'in shi abun ya gagara, kullum sassafe yake tafiya kuma sai yamma yake dawowa,baifi sau biyu suka hadu da safe ba, nan ma yana sauri gaisawa kawai sukeyi yafita , in yadawo da yamma kuma yashiga d'akin shi baya fitowa sai sallah sai kuma 10 na dare nan ma ruwa yake zuwa d'auka a fridge, sau d'aya tasamu tayi timing d'inshi don kin shiga d'aki tayi ta zauna a falo, ko da ya fito direct kitchen yawuce, taso ta mishi magana amma sai yamata kwarjini, ganinta ita kad'ai a falo yasa har zai tambaye ta sai kuma ya kwab'i zuciyar shi da sauri, yace meya kaika yiwa wannan er rawan kan magana kalen ta likema ka banu, haka yawuce tanaji tana gani tsabar bakin ciki saida tayi hawaye.
Yau Saturday kamar yadda mukasani ba makaranta kuma ba aiki… don haka yana kwance a d'akin shi yana kallon wani American series mai suna blindspot, singlet me irin karamin hannun nan ne a jikinshi da wando three quarter, kwance yake rufda ciki, ji yayi ana knocking kofan shi, rage muryan kallon yayi, sannan ya tashi ya zauna kafun yabada izini shigowa, bud'e kofan tayi a hankali tareda sallama, doguwar riga tasa irin straight fitted d'in nan wuyan rigan irin open shoulder nanne, fuskan ta kuwa tasha makeup irin na zamani, ba laifi tayi kyau sosai kamar wata er tsana,tsayawa tayi ajikin kofan, hannu ta d'auke da takaddu… saida ta kare mishi kallo sannan tace ya Abbas Assignment nazo katayani please… cikin wani irin yanayi na yanga da shagwaba tayi maganan…
Mikewa yayi batareda ya kalleta ba, yace wane course ne, ya tambaye ta tareda daukan wani long slip me anini ya na daura wa akan rigan shi batareda da yasa aninayen ba, chemistry tace, yace mata alright muje falo gaba tayi ya biyo ta abaya…
Dinning side sukaje suka zauna, fara duba assignment d'inta yayi, a hankali ya fara mata bayani dalla dalla sosai take ganewa duk hankalin ta baya kan assignment d'in sosai, tafi bada hankalin ta wajen kallon dan karamin bakin shi da yake magana da kuma manyan idanun shi da gashin kanshi na fulani wanda yasha gyara sosai sai sheqi yakeyi… a hankali idonta har ya sauko kan broad shoulder shi.. take taji tanason fita a hayyacin ta tsikar jikinta har wani zubawa yakeyi…
Wayan shine yafara kara wanda yayi sanadiyyan dawo da ita cikin hayyacin ta, d'auka yayi tareda yin sallama, Abban Mardiyya ne a d'ayan bangaren yace dan Allah Abbas idan baka wani abu kazo mana… yace ba matsala gani nan zuwa, kallon faiza yayi yace oga na yana kirana saina dawo mu karisa, kodon ma kad'an ne yasaura kuma duk procedure dayane in kikabisu da kyau zaki iyayi, take ta shagwabe fuska tana cewa a ah nikam bazan iya ba idan ka dawo d'in kawai sai muyi tare… kai kawai ya girgiza mata sannan yawuce d'akin shi, daya rufe kofan jingina yayi da kofan yana sauke numfashi bakaramin dad'in kiran ogan shi yaji ba, dama yana sane da irin kallon da take mishi… a fili yace wannan wace irin yarinya ce ba kamun kai.
Toilet ya fad'a ya watsa ruwa sharp sharp a gurguje yasa kaya, blue pencil jeans yasa da white shirt anyi blue rubutu a gaban ta an rubuta "THAT GUY", taje kanshi yayi sama sama duk cikin hanzari yakeyi ya fesa body spray na black oud sannan ya fita, farida na leken shi ta window d'akinta taga yafita bai d'auki mota ba, aranta tace yau kuma adaidaita za’a shiga kenan.
Knocking gate d'in yayi me gadi ya bud'e mishi karamin kofa shi ya mishi iso har kofan falon Abba… har zaiyi sallama yaji Abban na cewa inason in tuntubi yaron nan ya turo iyayen shi naji sunyi yayi shuru, yanzu kam ma sam nadaina ganin shi, bansan meyake nufi ba, antyn ta ne tayi ajiyan zuciya sannan tace da dai kafara kiran Mardiyya kaji ko wani abune yafaru, girgiza kai yayi sannan yace kamar kin manta waye Mardiyya ko zanyi yaya bazata tab'a gayamin ba saidai ke ki tambaye ta wannan aikin kine, toh shikenan zan tambaye ta muji bari inkawo ma fruits.Jin motsinta halamun tana fitowa yasa Abbas yin sallama, ansa mishi sukayi sannan abba yace yauwa malam Abbas kariso, shigowa yayi saida suka gaisa da anty sannan ta fita, bayan sun gaisa ne Abba yace sorry na d'agoka kana hutawa, dama Assignment ne zaka taya kanwar ka, idan har baka wani aiki, kanshi ya sosa sannan yace a ah Abba banayin komai, yace to shikenan, wayan shi ya d'auka ya kira mardiyya, cikin mintu biyu sai gata, da sallama ta shigo kanta a kasa, d'ago kai yayi yana kallon ta take fuskanta ya fad'o mishi, don sunsha clashing…
doguwar rigane purple ajikinta saman rigan yasha stone har zuwa hannu rigan, harta karisa gefen Abba ta zauna bata d'ago idon ta ba, Abba ne yace mata ganan Abbas zai tayaki Assignment d'in yayanki ne daga yau kinji, sai lokacin tad'ago narkakkun idanun ta ta sauke akanshi, shima d'in ita yake kallo take idanun su suka sarke dawuri ta sunkuyar dakanta tareda cewa sannu da zuwa, bugun zuciyan tane taji yana tsanan ta, Abba yace to kikaishi falo reading side dinku. toh tace tareda mikewa , Abba yana murmushi yace mishi suje..
Reading side d'in takaishi sannan tajawo mishi kujera tace bismillah, thank you yace mata tareda zama, takaddun ta ta d'auko sannan taje kitchen ta kawo mishi abun motsa baki… bud'e Assignment d'in yayi yaga exactly irin na farida d'agowa yayi yace mata course d'inku daya ne da farida? girgiza kai tayi sannan tace a ah, saidai akwai courses d'in da mukeyi tare ne ok yace, sannan yakara cewa wane level kuke, sai lokacin tad'ago ta kalleshi da mamaki, don tasha mamaki ace baisan ajin farida nawa ba, ganin ita yake kallo da sauri ta sauke idanun ta kasa sannan tace 300level.
Take yafara nuna mata taji dad'i sosai don tanaganewa fiye da na aji ma, tunda yafara ko sau d'aya bata bari sun had'a ido ba, suka gama saida ya tabbatar tagane tas sannan yace shikenan ni zan wuce. Mikewa tayi da sauri tace dan Allah kabari kaci abinci gashi ko ruwa ma baka sha ba, shuru tayi tana wasa da yatsun hannun ta, murmushi yayi sannan yace mata a ah babu wani abu nagode, da abunda dazanyi ne, bata kara cewa komai ba sai kad'a kai datayi irin na gamsuwa, rakashi tayi falon Abba suka tarar baya nan, yace mata badamuwa inya dawo tace mishi yawuce kawai, daganan tabarshi ta koma ciki shikuma yafita, a bakin gate su kusan cin karo da zeezee da sauri tace mishi dan Allah kayi hakuri ban lura ba, shima ce mata yayi sorry ni na taho da sauri ai, murmushi kawai yayi mata ya rab'a ta gefe yawuce..
(kumin afuwa zan d'an kwana biyu kafun inyi post saboda en wasu dalilai🙏🏻)
*ZEETY DELIGHT*💖