๐ซ๐จ๐ต๐ฎ๐ฐ๐ต ๐ผ๐ฉ๐จ๐ต๐จ
๐ฌ๐๐๐๐๐ ๐ 5&6
by @milhart
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
5 and 6
WASHE GARI
Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam.
Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?"
Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa.
Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta.
Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday ne Babu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti"
"Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje."
Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta.
Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka?"
"Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta"
Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma"
"Eh Mummy"
"Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka"
Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa.
Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?"
Murya na rawa yace "Tana.....tana.... d'aaaa ki"
Murmushi Mummy tayi tace "To ka kaimu mu ganta ko?"
Jiki na rawa ya shige d'aki Suma suka Mara Masa baya, Ma'isha kuwa sai Murmushi take har cikin ranta take jin dad'in ganin mahaifiyar Haisam na raye, suna had'a da Haisam kuwa kallon tuhuma yake mata,tana ganin haka sai ta Fara dariya kasa kasa.
Banda tari babu abinda mahaifiyar Haisam keyi, cike da tausayi yace "Ki kimsa ta ku fito" hannun Haisam ya riko, sannan ya cewa Ma'isha "Daughter zo mu jira su a mota" ba musu ta bi bayansu,suna isa inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya.
Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba.
Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida.
Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa"
"Ina sauraron ki"
"Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba, sannan Ina so a biya wa Haisam WAEC"
Murmushi yayi ya riko hannun ta yace "Madallah da samun mace kamar ki a rayuwa, tabbas ke d'in rayuwa tace, Maryam Allah ya Miki Albarka, a irin Rayuwar da muke ciki yanzu kowa kansa ya sani Amma ke kullum cikin taimakawa na kasa dake kike"
Murmushi tayi Tace "To mijina mene ne amfanin Kud'in namu? Idan baza mu taimakawa na kasa damu ba,Kuma na lura Ma'isha tana so a taimaka musu ne kuma ina matukar son farin cikin ta,nasan idan taji Haisam zai dawo gidan nan kuma taji za a biya Masa WAEC zatayi matukar farin ciki"
" Hakane Yar Albarka,Halin ki ta d'auko tana da tausayi sosai,ga son mutane"
"Kaji ka da wani zance kai ta d'auko dai"
"Zancen kike so,yanzu dai naji dukkanin maganar ki, Kuma zanyi yanda kike ce, Kuma Insha Allah zan rike Haisam tamkar d'ana, da niyata gidan nasu nake so a gyara musu"
"A a tun da ga nan Kuma gidan ya mana girma mu kad'ai, su dawo Nan kawai"
"To ba matsala, idan Allah ya Kai mu gobe zanje makarantar tasu na biya Masa, sannan ina so kije gidan ki d'auko mahaifiyar Haisam d'in, ban yarda ta 'dauko komai ba, Zan tura miki Dubu d'ari biyu, ki saya mata kaya, idan na nadawo zamu fita da Haisam d'in Shima na Masa sayayya"
Farin ciki da Murna yasa ta rungumi mijinta had'e da yi masa godiya, a haka sukayi bacci.
Washe Gari
Daddy Kan yaje gun aiki ya biya ta makarantar su Haisam ya biya masa Kud'in WAEC harda NECO.
Mummy na fad'a wa Ma'isha maganar da suka tattauna Akan Haisam da Umma tayi farin ciki sosai harda tsalle, tayi ta musu godiya da musu addu'a Wanda ya dace d'a yayiwa iyayen sa.
Tana Isa school a kusa sit d'in Haisam ta zauna, tunda ta lura shi d'in ba mai son magana bane Hakan yasa sai ya kulata take kulashi.
Principal ne ya shigo yana Kiran sunan wa'anda basu biya Kud'in WAEC d'in su ba, ga mamakin Haisam har aka gama ba a kira sunan sa ba, hannu ya d'aga yace "Excuse me sir!!!
Yace "Yes"
Mikewa yayi yace "I haven't paid and you didn't call my name"
Cike da mamaki yace "You didn't pay? What's your name?"
"Haisam Ahmad Umar"
Ya shiga dubawa Bai ga sunan Haisam ba Yana duba list d'in wa'anda suka biya yaga sunan Haisam yace "Mr Man you already payed"
Cike da mamaki yace "I payed? But sir please can you check the date of the payment for me?"
"Sure"
Yana dubawa ya Maida kallon sa ga Haisam yace "It was payed today"Yana Kai Nan ya sa wa'anda basu biya ba a gaba har Saida ya kai su bakin gate ya jaddada wa Mai gadi Akan Kar ya bari su shigo ya koma ciki.
Haisam mamakine ya rufe, a zuciyar sa yake fad'in "Wa ya biya min Kud'in nan?" Da sauri ya d'ago kansa ya kalli Ma'isha ita ma kallon sa take, murya kasa kasa "kin San wani abu Akan haka ko?"
Kai ta girgiza Tace "Ni ban sani ba" ta karasa maganar tana rufe bakin ta alamun dariya take son yi.
Cikin sanyin murya yace "Ma'isha Please"
Tace "Daddy ne ya biya"
"Dan Allah dagaske?"
"Uhmn gashi ka gani"
"Amma....... "
Shigowar malamin sune ya Hana shi karasa maganar da yayi niya, suna fita break ya Shiga neman ta bai ganta ba, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah Allah na gode maka, yau Dole. Naje gidan su Ma'isha da Umma muyi musu godiya"
Ma'isha da tun d'azu take tsaye a bayan sa tayi gyaran murya Tace "Anya zuwa gidan mu zakuyi ko Kuma Zaku koma gidan mu?"
"Hmm zuwa Zamuyi dai"
"Za dai ku koma gidan mu"
"Ban fahimce ki ba?"
"zaka fahimta idan driver yazo sannan ko ka gudu zamuje har gida mu d'auko ka" tana kainan ta ruga a guje, Yana Kiran ta Amma ina tayi nisa.
_____________________________
Please comment and Share ๐๐ป๐๐ป
Milhat ce
Yar Terawa