KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka 1

by @kyautadagaallah10

Kai ka jawa kanka 1


Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah


Page 01


Wayyo Allah na yazanyi gashi hadari ya hadu Ni Fatima cikin tsanin kaduwa take magana.


Tsawar da akai daga sama yakara firgitata ta cure gefe daya tana kyarma jin anyi hor agabanta yasa ta dago jajayen idanunta da suka kada yanayin wacce take gab da sakin kuka.


Baiwar Allah lafiya naganki cikin wannan hadarin da ake ko gidan naku ba anan kusa yake ba.


Kada Kai tayi Masa alamun eh

Shigo daciki in rage Miki hanya hartai tunanin tace aa bazata shiga gani ankara kece da sabon hadari me karfin gaske tabude murfi gaba tashiga sai kyarma jikinta yake


,kallon ta yayi ya fuskanceta wani unguwa kike inkaiki harzatai Masa halin nata na tsiwa saita tuna kartayi toMasa batasan koshi wani irin mutum bane yai maganin ta tunda gasu amota yakasa tafiya sbd ruwan da akeyi me karfin gaske ne .


Maimaita tambayarsa yadawo da ita cikin hayyacinta .

tabashi amsa da

Sunan unguwar tamu sabon layi Dan Allah muje ka kaini Kar aga nadade ban dawo ba .


To ko inbude Miki kofa ne ki tafi in sauri kike Danni bazan iya bin cikin ruwan Nan ba ,

Kiciniyar bude murfin kofar take


Ke Ina zakije kike kokarin fita ya daka mata tsawa ,be Ankara ba sai ganin yayi harta fita tana buga sauri , sha gabanta yayi da motar sa .yace haba yan Mata daga Ina Miki wasa saiki fita.


Ko kallon inda yake batai ba cigaba da tafiyar ta ,tayi yanabin abaya cikin saurin da take saide tajita tafadi akasa tasaki uban wani Kara wani katon dutse ne ya buge ta Bata kula ba .


Khalid yaso yayi dariya amma saiya dake yace wayyo muga kafar

Sannu kinji .

Taso muje inkaiki asibiti ko yafada cike da kulawa.


No basai munje ba nidai tunda hadarin yadan tsagaita nakarasa dakaina

Cikin yanayin rarrashi yasoma magana pls taso wlh bazan taba cutar dake ba.

Dakyar ta amince da bukatar sa.

Bayan tashiga motar tafara masa kwatancen gidan nasu tafiya befi minti shabiyar ba suka iso bude murfin kofar tayi tafita zata shige gida.


Haba kekuwa daga saukeki.babu godiya saiki wuce

Furucin sa ya Bata ran ta

Au Ashe badan Allah ka kawoni ba tunda kake neman godiya daga gareni.

Kaga tafiya ta! Yasha gaban ta haba ko sunan ki aikin fada mun .

Suna na fatima ta fada cike da gajiyawa da damuwar sa.


Nikuma khaleed Sani Yaro

Ki taimaka min da lambar wayar ki

Yana kokarin Mika Mata wayar sa.


Naso in hanaka amma mutunci da kamin yasa zanbaka ,miko wayar ka ,Yana mika mata tasa masa nomba ta Mika masa wayar sa batareda tajira Mai zai ce ba .

Ta wuce Kai tsaye gida tashiga bakin ta dauke da sallama bala mai gadi yace gimbiya hankalin kowa yatashi yanzu alhaji yadawo daga neman ki .


Tsaki taja tafara fada daidai da fitowan alhaji ,maman ta n'a biye dashi abayan sa , cikin Isa tafara fadin nidai wlh bakwa kyautamin akan me zakaje nema n'a saikace na goye , momi ta daga hannu zata wanke ta da mari , alhaji yarike rike mata hannu cikin matukar bacin rai yake kallon Mommy.


Yace koda wasa Kika mari fatima wlh banyafe Miki ba.

Ya juyo ya fuskanci fatima tana kunkuni

wlh Daddy da kabarta ta mareni nasan dayau zamanta yakare agidan nan . Thanks

Momi ta fashe da kuka yanzu fatima nikike cewa haka , karki manta Nina dau cikin ki wata tara n'a shayar dake ,naci kashin ki da fitsarin ki ,amma kikemin wannan kalamin ,

Ran alhaji inyayi dubu ya baci yace to saime aikema iyayenki sunmiki dawainiyyar dayafi Nata duniya haka take tafiya akan me Zaki ringa bata mata rai .

ke Kika jawa kanki taimiki wannan furucin .

Bala mai gadi dake kallon abunda ke faruwa yace ikon Allah wai ya kesa uwar ta kuka ,

Wannan wani irin uba ne da yadau son duniya yadaura mata kodan ita kadai ce yar shi ,sai kada Kai yake Yana jinjina al'amarin gidan nasu.

********************************

Bangaren Khalid yana barin gidan su Fatima kai tsaye gidan su ya nufa cike da zumudi.


Khaleed na isowa mai gadi ya bude masa gate yashiga ransa fal da farin ciki n'a aiyyana wa azuciyan sa yasamu matar aure ,shigowan gidan su keda wuya Kenan ya iske kowa a falo a'ladar gidan su tare ake cin abinci ,mahaifiyar sa wacce suke Kira da umma tace ,ya naga Khaled tun shigowan ka da magana abakin ka .

kuma nasan me dadin sauraro ne Abban sa ya gyara zama ya fuskance sa zonan Dana zauna kabamu lbr mana .


Aisha kanwar sai darawa take uhmm.mudai mun kosa muji ko menene pls yaya Kai muke saurare.


Ajiyan zuciya yasauke ya dauko lemun kwali exotic ya zuba akofi tangaran yasha ,Yana wani lumshe idanu ,

Umma tayi tsaki tace kwarai Saboda Kaga mun

kosa muji labari shine kake wani ja mana rai.


Khalid yace Haba umma lallabani zakiyi ba fushi ba Yana murmushi

Dama bawani labari bane

Yau dai Allah yahadani da wata yarinya mai suna Fatima in Allah ya daidaita mu ita zan aura.


jikake kake tasss

Umma ta wankesa da mari what Kana hankali kuwa koka mance

yau duka ba'ai wata biyu , ba da rasuwar matar ka ,ta goma sha Daya tare da drever shamsu takarashe zancen tana nuna sa da yatsa cikin fushi .


Abba cikin bacin rai yace ke wace irin uwa ce da baki damu!

Da damuwar danki ba ,ni in Khalid yace yanason duka matar duniyar Nan indai ya halatta zan aura Masa.


Abba da ace ba gaban ka aka haifeni ba dasai ince wanna ba uwata bace. wlh haba kana ganin Marin datamin idanuna Sun ciko da kwalla.


Aisha kanwar Khalid tace yaya dan Allah Kai hakuri Amma maganar umma gaskiya ce mutane zasu fara zargin me yakashe mata goma shadaya da suka mutu ,ni da za'a bi shawara ta ,

Dan Allah kabar zancen auren nan sainan da shekaru ,

Tsawar da taji andaka mata daga Abba yasa jikin ta yafara rawa har tana neman faduwa .


Abba ya ce "Sha-sha-sha mai kika sani a kan rayuwan duniya nawa kike cefanen kunu Get out yace mata ransa abace a sukwane tawuce daki .


Kekuma nadawo kanki ki fita harkan Dana wlh inbazaki sa idanuba to dan Allah kibar shiga harkan mu .


Khalid ya kalli umma cikin huci sama sama yace wlh badan ke mahaifiya ta bace marin da Kika min saina rama .


Cikin daga murya umma tace to khalid kazo karama Marin mana gsk bazan fasa fada muku zalinci baya dorewa kaida uban naka Allah Yana jiranku a madakata.


*************************

Bayan kwana biyu Khalid yashirya yaje gidan su Fatima yana cikin motar ya lura da wasu Mata guda biyu a napep sanye da nikaf shi suke kallo

Kiran Fatima yai tai ring harta gaji tana gani bata daga ba

Fitowa yai yaje gun Bala Mai gadi ,yabuga gate yabude ,Bala yace mallam daga ina cikin tabe baki kamar shi akewa tambayar nosens ,Fatima zaka kiramin , sai tsintar muryan ta yai tana fadin me zatai maka

Murmushi ya fadada yafara Mata kirari ranki yadade gimbiyar Mata nakira baki daga ba.

Banga dama bane fadi me yakawo ka gidan namu, cikin kosawa da tsayuwar .

Khalid yace tun ranar Dana barki dake nake kwana dake nake tashi in takaita miki.

Dakata ! ya isa haka kafadi Abunda yakawoka tana yatsine fuska ko in shige gida

Fatima bazan boye miki ba tunda kinki bani damar yimiki dogon bayani inasonki inason ki inasonki zan mutu akanki

Jikake tass ta wanke shi da mari

Kai dan gidan uban waye ka aro mota zakazo kaimana burga ' takara taku biyu tazo daf dashi har suna jin numfashin juna kalleni dakyau ni FATIMA AUWAL nafi karfin yaro saide baban yaro .

Khalid rike da kuncin sa umma ta maresa yau kuma babyn roba ce cikin ayyanawa aransa ko zaa mutu adawo saiya auri fatima marin datai masa saiya fanshe shi , kakalo murmushin dole yai daman haka hannun ki keda taushi kaman auduga inzaki kwana marina niko zankwana miki godiya .

wannnan kai yadama tashiga kwalawa bala mai gadi dake gyangyadi kan kujera ya taso a firgice ranki ya dade gani yana kokarin durkusawa.

cikin tsawa fatima ke magana daga yau banda kawata safiyya wani ko wata yazo nema kabude musu gate abakin aikin ka , horn din motar DADDY yasa ta daka dashiga ciki ganin mahaifin ta yai parkin motar sa yai gun khalid dayai mutuwar tsaye saboda takaicin rainin hankali irin na fatima

Daddy yace ranka yadade aida kace inzo har gida zanje kaban umarni .

Fatima batasan sanda wayar hannun ta yafadi


KHALID WANNAN KANA NUFIN YARKA CE

yana murmushin mugunta eh ranka yadade diyata ce Fatima itakadai na mallaka DADDY YA KALLI FATIMA cikin bacin rai kina ganin nagaida oga na ,bazaki gaishe shi , cikin fadin rai tace inawuni , inba kanada kunne ba bazaka ji abunda take fadi ba.

Lfy lau kanwa ta kuma amarya ta,

Daddy sai washe baki yake yace daman kasan fatima ne , no alhaji ran ne muka hadu , yau nasake dawowa amma taki kulani kokai mata miji ne

Ranka yadade batada saurayi kaine farko ,dan nabaka fatima duk sanda kk so ganin ta namaka izini kashigo gida .

Bala bala yana kiran mai gadi ,duk sanda ranka yadade yazo aringa kaishi dakin baki ,

Bala yace angama ranka yadade tareda juyawa komawa bakin aikin sa .

Dadddy yashige gida yabar fatima da khalid.

Kallon kallo sukewa juna kowa da abunda yake ayyanawa aransa ,

Ya katse musu tunani ta hanyar cewa yau dai kinga ikon ALLAH ko ,nanda sati biyu daurin aurena dake umarni ne zanba mahaifinki ,

Kutumar uba saikace auren awaki , to bari kaji ni bazan aure ka ba , mahaifina kake iko dashi banida.,

Khalid yace kwarai kuwa da ubanki nake da iko ,shikuma yanada iko dake .

Wayarsa daya fara ring a scren din wayar abba yafito ,ya daga wayar tareda sa hans free , abba yace my son kana ina bakazo office ba kasan munada meeting gqggawa ina kiran manager auwal baya dagawa ,sorry dady ina babyn roban dana baka labari ai diyar manager auwal ce , ataikace nasa ranar bikin nanda sati biyu

Abba ce mashaALLAH TAZO GIDAN SAUKI KAMA SAMU KAGAMA, KIRASHI KUZO tare ku kadai ake jira ,yana murmushin mugunta ya katse wayar , kanwata jeki kiramin daddyn ki , tsaki taja tawuce ciki tana gayawa mahaifin sako tai dakin ta aguje tafada gado tareda rushewa da kuka .

Khalid na tuki ya lura da wayannan yan matan masu sanye da nikaf ,shi suke bi ,murmushi yai azuciyar sa yace yanzu zanci ubanku ,shan gaban su dayai ,hankalin me napep din yatashi yai reverse aguje khalid ya...

hankalin me napep din yatashi yai reverse a guje , khalid yamusu horn da mota yana kokarin fitowa , dayan me sanye da nikaf tace wa drever dan ALLAH KA KARA GUDUN napep karka bari asirin mu yatonu hankalin su a tashe ,duk yanda khalid yaso ya cin musu saida suka bace da ganin sa.

Me napep ya tsaya kunga dai mun sha da kyar ,tun safe muke ta bibiyar sa , kudin ku na karuwa , dayan tace salamatu karamai dubu biyar , to anty ta amsa tareda mika masa kudi , godiya yaimusu tareda tambayar ina zekai su salamatu tace ,kaimu gidan da khalid yafito zance , to ya amsa tareda dokan hanya sunsha tafiya kafun su iso , me napep ya ajiye su ya juya , salamatu tace anti banso kika fito ba wallahi ni kinga ,khalid besanni kekuwa ganinki ze lalata komi duk shirin mu ya tafi abanza domin duk inda kike tunanin khalid yawuce ki , next time KARKI KARA BIYO MU , wai ma ya zamu tunkari yarinyar gidan dan nalura yar zafin kai ce , itama .

Anty maryam , pls menene mafita

Bangaren fatima taci kuka harta godewa ALLAH ,momyn ta tashigo bakinta dauke da sallama , zama kusa da ita tai pls daughter me yake damun ki ,nalura ranki abace yake , gyara zaman ta tai tareda , dauko ribbon tai parkn gashin kanta , har mom ta fidda ran zatai magana cen taji ,tace momi wannan yaron danace miki yadawo dani gida ana ruwan sama, ashe DAN SANI YARO NE ,yau ma yasake dawowa taba mom labarin abunda yafaru , tirkashi hauka yake zece nanda sati biyu ze aure ki shiya haifa mana ke kenan ,kibari alh yadawo bazeyu ba wlh shege da hauka dan sunada arziki ai ubanki ma yanadashi dan dai sune uban gidan shi, kwantar da ita tai akan cinyar ta tana rarrashin ahaka barci yai gaba da ita ,gyara mata kwanciya tafito dakin ,tana mamakin karfin halin khalid .

Jin karan buga gate yasa bala bude gida safiyya kawar fatima ce tazo sanye take da habaya pink takalmin ta da jakarta gold ce ta yafa dan karamin gyale simple makeup tai ita kanta tasan tayi kyau , BALA yace sannu dazuwa ranki yadade ,yawwa tare da mikamai dubu biyar ,sai washe baki yake yana fadin ALLAH YAKARA MIKI LFY ,MAKIYANKI FADAWAN KI ,BUDE MATE GATE YAI tashigo da motar ta , ko minti biyu baai da rufewa ,

Yakara jin buga gate waye yafada , yaji ance mune , kune wa , baki ne suka amsa , bala yace wa kuke nema ,sukace to bude gate din mu gayamaka ,,

Yana bude wa yaga mata biyu sanye da nikaf ,shan kunu yai waiku dan ALLAH bakuda aiki sai maula to megidan bayanan ,

Salamatu tace ba maula yakawo mu ba aiki kanwata take nema ko shara da wanke wanke , bama bukata tareda rufe gate ya barsu a tsaye ,

Anty maryam tace kinga nacemiki bazamuyi nasara ki kalla ki me gadi kenan yai mana haka , inaga masu gidan ne nasu saiyafi nashi muni mu hakura da taimakon yarinyar gidan akan khalid bazamuyi nasara ba, horn din da suka ji ne ya katse musu zance ganin motar da yai parkin gaban su ,hankalin su atashe.

ganin dattijo ne fari dogo sanye yake da farar shadda ,tsananin kamannin dasukaga yanayi da fatima su tabbatar mahaifinta ne.

Ajiyar zuciya suka sauke .

Daddy yace lafiya kuke tsaye kofar gidan fuskan sa ba yabo ba fallasa , duk kucire nikaf dinku , suna cirewa Daddy yanata kallon anty maryam kaman yaso yasan fuskan a wani wuri , meke tafe daku ?

Salamatu tasoma kuka ranka yadade dan Allah kataimaka kadauke ni aiki agidan , mahaifin mu yarasu , maifiyata nakwance ba lafiya ga kannena hudu dani suka dogara yara ne dukan su , abuna zamuci yana gagarar mu .

Daddy yace calm down zandauke ki aiki amma na sameki da rashin gaskiya zakibar aiki , inshAllah zaka same ni da gaskiya da rikon amana .

Daddy yai horn bala mai gadi yabude masa gate , yashiga da motar sa , kiran bala yai yace masa wasu mata nawaje yashigo dasu .

Safiyya da fatima abinci sukeci amma talura walwalar kawarta yarage , waini fatima tunda nashigo naganki sai ahankali , kukan da take kokarin dannewa yataho mata idanunta suka ciko da kwalla , hankalin safiyya yatashi haba fatima yanzu akwai abunda ke damun ki da bazaki fadamin ba ,

Cikin shekekar kuka , lbr khalid danabaki rannan yau yadawo tana kaiwa safiyya karshen labarin , ai wannan ba abun kuka bane kokin ,manta waye khalid sani yaro, sunada arzikin har jikokin su bazasuyi taulaci ba ,ke intaikata miki ,ninan wallahi har adua nake ALLAH YABAN DAN gidan SANI YARO amma ke kinsamu kina kuka to wlh babban dama ce ALLAH yabaki , kiyi wasa da kudi yanda zancen baki sonsa ajiye shi ,ahankali zaki soshi, bayan kudin ga kyaun sura dan inba ancemaka bahaushe bane saikince yahada iri da larabawa maybe hakane mune dai bamu sani ba.

Daddy yafito daga dakin yazauna kujerar dake face fatima , yata na saudakar da komi dan farin cikin ki tun kina karama kikai rashin mai tsanani kaman bazaki rayu ba akace sai ansamiki koda , ban yarda aka samiki nakowa sbd tsabar son danake nawa nabayar aka samiki , alfarma daya nakeson kimun ki amince da zancen auren ,khalid nahango alkhairi acikiin auren ,sallamar bala maigadi ya katse DADDY ,ranka yadade gata nan tashigo dayar tawuce ,bismillah zauna cen inazuwa , yadawo da duban sa ga fatima ,pls karki ban kunya .momyn tashigo tana bata rai nidai Alhaji abi komai a hankali saboda nalura bataso , aure ba bincike shine ma me yanke ranar auren , Daddy yace to shine me?

Ni dai wallahi ban aminta ba , daddy au daman yardan ki nake nema ina daurata ahanya kinason rusawa to wlh akan auren banki in tsinke igiyoyin auren ki ,cikin kuka fatima tace yanzu duk akaina ake haka .

DAddy na amince ta fuskan ci momyn ta datai mutuwar tsaye , ku iyaye na banason rabuwar ku shiyasa na amince .

salamatu dake zaune cen gefe tana kallon Al'ajabi .

safiyya takama hannun fatima sukai daki .

daddy yacewa salamatu nadawo gareki akwai wata yar aikin sunanta asabaru , ya kwada mata kira tazo tareda durkusawa .

gani ranka yadade

gyaran murya yai tareda nuna mata salamatu taje ta nuna mata dakin su ta amsa da angama,

momy tace ya sunanki tace salamatu to sannunki dazuwa tace yawwa.

khalid zaune da babban aminin sa suna hira yace amma kai dan iska yaro dakai aure na goma sha biyu baka ajiye da ba

idan har kana da kudi wasu matan babu ruwan su da haihuwa

wallahi karyane kodan suci gado sunso hada zuri,a dakai hakane kuma

barin inkirata dalling nombar fatima yai tanada dagawa yace amaryata ,cen kasan makoshin taji ranta ya sosu saboda kwarewa da karatun da safiyya tai mata tace ango na yakake mamaki ne yacika shi yace kalau ne ,

ki fara shirye shrye bikin mu duk abunda kuke bukata,

ki sanar mun , ta amsa da to_ tareda katse wayar dan cikin su babu wanda ya iya soyayya.


Abokin khalid ,mai suna aminu yace khalid kasan matar ka bata dade da rasuwa ba , yan jarida wani amsa zaka basu yanzu zargin ka akeyi da kashe sauran matan ka,

tashi tsaye khalid yasa hannayensa biyu abaya , nasan da haka wace hanya kake ganin zamu bi dan kauda hankalin al,umma akanmu . mafita daya ce saide daga kan fatima ka kulle ina nufin kabarta tazauna zama na har abada


Mu haɗu a Chapter 2 don jin cigaban wannan ƙayataccen labari

Daga Marubuciya

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah