KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka Chapter 3

by @kyautadagaallah10

Kai ka jawa kanka 3

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah


Page 3


Bayan sallah ishai Khalid yadawo ,yana yatsaya bangaren su umma Dan cin abinci 'abba na gefen sa cikin jin dadin ganin sa yace Dana wai ina amarya ne banta ganin tazo anci abinci tare ba kodai Khalid laifinka ne

Aisha dake cikin cin abinci tace Abba kila tanajin kunyar surukan tane dauko ruwan faro tai ta siyaya a Kofi tareda tashi

Umma ta kalle ta tace ita Fatima tacemiki kunyar mu take tunda aka kawo ta banyi tozali da ita kekuma ina Zaki naga hanyar waje Kika fuskanta

Eh umma isma'il ne yazo yana waje . Khalid yace ke dawo nan banason shashancin kin dauke mu mutanen banza bazaki gayamana isowar shi ba saide kija kafa kaman angulu zaki tafi ke gaki mai saurayi stupid dake

Umma tace haba Khalid Naga aiba bako bane bare ace ta gabatar dashi ba gyaran murya Abba yai tareda yin tsaki nidai kina ban mamaki ya zaai

Shida kanwar sa be isa ya tsawata Mata ba umma hakuri tabashi tareda bin hanyar dakin ta Nan tabarsu sai Abba dake ta zuba ruwan masifa tareda Koran aisha ta koma daki

Fatima ce dake saukowa daga sama duk abunda suke idanunta nakai isowa tai kusa da Abba tace gaishe shi a ladabce ya amsa da yana Mai fadada faraar shi

Fatima tace badan kada kace n'ai maka karanbani ba naso dan Allah abar aisha taje taga isma'il tunda kunsan da shi kallon ta KHALID yai alamun ina ruwan ta yai mata da hannun sa

Cikin girmamawa tace my husband nasan kaji haushi ko Amma ai...

Dakatar da ita yace haushin me zanji Dan kin nuna kulawa akan kanwa ta yanzu dai muje ki gaisa da umma atare suka tafi ABBA yai ficewar sa

Ganinsu atare bakaramin dadi yaiwa umma ba.

Bismillah zauna diyata

Gaisheta fatima ta amsa fuska a sake , aisha dake gefen umma tai Mata sannu dazuwa

Fatima tace umma aringa barin aisha tana zuwa min hira fuskantar Aisha tai tace tashi ki tafi isma'il na jiranki

Kallon khalid tai taga ko inda suke be kallo tashi tai tana sanda sanda ta fita .

Umma

Zanje inkwanta

Tun yanzu Fatima Amma plz kitaimaka kiringa cin abinci cikin mu

Khalid yace to ai inaga daga gobe Zaki fara ganin ta

Tare suka fito shida fatima

Suna Shiga dakin ya fada gadon fatima sai mirgina yake cikin muryan shi datai kama da me jin barci yace

Yace haba wife zoki ragemin kayan jikina Kara gudun AC dakin ki

Kallon shi take da mamaki meyake nufi a dakin ta zekwana

Ganin batada niyan yin abunda yasa yatashi yacire Kayan jikin sa agabanta

Innalilahi yaji ta furta tana neman hanyar guduwa .

Tana neman hanyar guduwa.

Ke ina Zaki kike neman fita!

Cikin inda inda tana kallon kofa tace zanje dakin umma ne,

Riko hannunta dayai yasa hankalin tashi hawaye shar

A idanunta

Ki nutsu babu Abunda zanmiki Amma kisani wataran hakan saita kasance jawo ta yai tafada jikin sa yana shakar kamshin jikin ta

Tunani yashiga yi mai murfi inda fatima ta sabule daga jikin sa batareda yasani ba

Daukar wayarsa yai ya danna lambar Aminu bayan andaga

Khalid yace aminu inaganin kamar nafara samun lafiya fa

Aminu ya katse shi yace yabari su hadu Dan maganan bata waya bace



Kashe gari

Mommy sun hada kayan cin cin da dubulan alkaki da donot , cake zaa kaiwa Fatima 'salamatu dasu Inna khadija wannan Karan harda asabe .

Bala Mai gadi yabude masu gate aringa daukan kaya ana zubawa a boot din motar

Duk abunda ake hankalin salamatu baa kwance yake ba gashi zataje gidan khalid batasan hanyar dazatabi musu ta gudu ba

Wata dabara ce tafado mata

Zata zaga ta bayan gidan su tafita cen daga nesa ta hango wasu kattai da alama yaran Khalid ne cikin karkarwa da jikin ta yasoma yi

Ta d'au waya takira anty Maryam cikin yanayin tsoro da fargaba take sanar Mata

Maryam ta nisa a tunani cen saita ce mata tabi masu Kai Kayan daga cen zaa samu mafita

Mommy tafara ihun Kiran salamatu katse wayar tai taje gun ta

Haba salamatu kin shanya mutane anajiranki maza kije Ku tafi banson kuyi dare


Mommy tabisu da Allah yatsare ta juyo cikin gida

Bangaren su Maryam

Shamsu ne yazauna cikin kaduwa da halin da salamatu ke ciki

Yace Maryam yarinyar nan tana ban tausayi inhar Khalid yai nasarar kamata to duk yanda zeyi saiyasan wacece ita maganar danake Miki yanzu kawai hasashe yake kinsan mutum marasa gaskiya be yarda da kowa

Ummu dake zaune tace gaskiya kafada shamsu Abu daya zaai inhar taje gidan alh sani yaro to me zehana Kai kaje a napep ka daukota, Maryam tace haba ummu wannan aikin saide mashin duk inda gudu ykama dawuya akamasu 'cikin yanayin kuka ummu tace yanzu ace da Raina iyayena na raye Amma babu damar in gansu sbd Khalid wallahi

Khalid me mukai maka ne sbd mun kasance talakawa marasa galibu ne kokuma sbd bamuda yancin kanmu

Shamsu ne yakatse ta yace pls

Hakuri mukeyi dukan mu baa son ran mu muke jejin Nan ba Kuma muka sake akasan Muna raye to karyanmu yakare

Aisha keta zuba uban sauri a hanya kasancewa yau bata fita da mota ba Kuma baa zo daukar ta ba ,wasu gayu ne su biyu Kana ganinsu kaga kalan Yan shaye shaye Shan gabanta sukai tareda dakata mata tsawa

Cikin bacin rai tace ku wani irin yan iska ne kullum kuyita bibiya n'a

Dayan me suna hamza yace ai ki gode ma Allah da kikai kasuwa

Horn din mota sukaji

Khalid ne yafito ransa abace yace

Ke indo mekikeyi da Yan iskan nan

Hamza zeyi magana saide yaji saukan.maruka lafiyyu guda uku Wanda yasa yaringa ganin taurari rike da kuncin sa yace Nika Mara

To wlh zakasan ka mareni

Kekuma wlh inde kere na yawo zabo na yawo wataran zamu hade

Shiga muje yace Mata tareda Jan motar hankalin na gida yasan duk inda akai salamatu nacen

Salamatu tace Fatima inason muyi magana dake me muhimmancin

Fatima tace to inajinki tana latsa wayar ta yayinda sauran sunacen anata Mata gyare gyara jin salamatu tace magana ce akan khalid yasa Fatima dago kanta daga kallon wayar ta tashi tazauna ta fuskance

Inajinki Fadi ..

Salamatu tace teema ba aiki bane yakaini gidan ku ba

Illah naje ne dan Allah da kyakyawar niyar samoki daga rijiya ko ince halaka

Nan take annurin dake shinfide fuskar Fatima yadauke ta daure fuska kamar Bata taba dariya ba arayuwar ta cikin kosawa da zancen tace Fadi Amma kisani kikaiwa mijina karya kotu ce zata raba mu

Nan take salamatu tashi tsaye tai hannayenta duka biyun goye abaya taku daya tayi ta isa wajen window dakin ta cikin muryan dagaji tasan ba wasa ciki tace

Fatima ninan yar babban gida ne ba Alfahari ba nasan bakifini jin dadi ba saide a halin yanzu kinfini yanci tunda nalura da rayuwata nason Shiga hadari 'kokinsan Khalid kece mace ta goma sha biyu daya aura ,cikin su harda antina Maryam wacce muke uwa daya uba daya

Nayi tunanin taimaka miki zaiyi sauki ne amma saina lura nayi gangancin da bansan ta inda zanfara gyrota ba BAZAN BAKI DUKA LBR BA HARSAI KINGANO ABUNDA ZESA KINEME NI AMMA KAFUN NAN WANNAN ITACE NOMBAR WAYATA INHAR KIKA BARI MIJINKI YASAN WANNAN HIRAR DAMUKAI NIDAKE TO KAMAR KIN DAUKI WUKA NE KIN SOKA WA CIKIN KI ,DALILIN DAYASA NATSYA WAJEN WINDOWS NAN SBD INASON INGA SHIGOWAR KHALID


KUMA NAGA YANZU YASHIGO ZANSHIGA WATA TSABARGA DAN Allah karkiyi abunda zesa ya fahimci wani abu harsai nabar gidan Nan

Jikin Fatima da babu Abunda yake sai bari da zufa dake sar sarfo Mata duk gudun ac dakin behana gumi keto mata ba

Cikin yanayin damuwa da tace

Amma salamatu ,sallamar khalid ne ya katse Mata zancen datake Shirin furtawa ,cikin wayance wa kada yai zargin wani abu


Tai murmushi yake tace haba salamatu kowa na aiki bazaki tayasu ba


Tareda Mika Mata wayar ta tana Mata alamu da idanu Dan karta mance bata sama ta nombar ta ba 'fahimtar haka yasa salamatu danna nombobin ta tareda Mika Mata waya

Cikin girmama wa tace Yaya khalid sannu da zuwa gabanshi ne ya tsanan ta bugawa cikin dakiya yace yawwa my sista fita tai tabarsu adakin

Fatima tace haba my husband kazauna man ,zauna man tashi tai taje kitchen tadauko ruwan sanyi hade da lemun kwali exotic a tray Dan Abunda yafi bugata kenan daya yadawo

Ta ajiye gaban sa kofin glas tadauka ta zubamai tareda kokarin bashi abaki 'cikin tsananin mamaki sabon salon ta

Yace wife waya koyamiki iya tarban miji kode su Inna khadija ne naga kin sauya yau dinnan

Kakalo mirmushin dole tai tace aikasan Inde Kana tare da manyan wataran zaka iya

Kararsa wayarce tasa shi saka hannu aljihun wayar sa kan screen din wayar zahradeen aka rubuta daga wayar yai tareda sa Hans free Dan lemun dayake Sha beson ya ajiye '

Sallama yai yana murmushi

Daga cen bangaren cikin murya me nuna zallan shagwaba yace haba Yaya khalid Ashe ka sakeyin wani auren shine baka sanar mun Aiko banzo ba zanyi adua 'kallon Fatima yai yaga shi take saurare cikin wayance wa yace to kanina Naga baka gari banson karatun ka yaita baya shiyasa ban gayyace kaba 'amma ga amarya zaku gaisa 'mika wa Fatima waya yai


Cikin sanyin murya kaman Mara lfy suka gaisa daga cen bangaren yace ina fatan dai Zaki rike mana yaya'na amana

Amsa masa tai da inshAllah bakada matsala Mika wa khalid waya tai ganin yatashi yabar dakin yanufi dakin sa tabishi abaya ,rufe kofar sa yai ta kasa kunne amma batajin abunda yake Fadi .


Yana shiga yace deen Dan Allah inason kabaro sudan a satin. Nan daga cen dayan bangaren yace Yaya Allah yasa lafiya

Eh lfykalau khalid yabashi amsa ataikace inde kazo zan sanar dakai katse wayar yai

Sai yanzu hankalin sa yadawo da tunanin salamatu karfa ta gudu ,cikin azama yafito yanata buga uban sauri saura kadan ya buge umma '

Cikin mamaki umma tace kaiko kanka daya kuwa ko ta kanta be bi ba

Harabar gidan yafito yanata kalle kalle ,Mai gadin su mallam isa yace ranka yadade lfy kuwa

Khalid yace mallam isa bakaga wata yarinya tafita agidan nan ba

Mallam isa yace aiko yanzu tafita inaga ko nisa batai ba

Shiga motar sa yai yafito yanabin layi cen ya hango salamatu sai gudu take akasa

Kafun yakaraso gun ta wani me mashin yarufe fuskar da fask Mask yasha gaban saWuce shi yai tareda pakawa gaban salamatu aikuwa saita haye aguje yaba mashin dinsa wuta tareda barin wajen

Khalid Kara gudun motar sa yai tareda

Me mashin din daya dau salamatu yanata bin lunguna tareda Kara gudun mashin dinsa

Salamatu sai waige waige take tana cewa dan Allah kara gudu gashi cen yakusa cinmana

Karki damu inshAllah zamu bace wa ganin sa sunyi gudun dayakai kilomita 16 ,salamatu cikin tashin hankali ganin mashin dinsu.ya tsya alamun mai ne yakare tace waini shamsu yau dubun mu yacika gashi mun bar cikin gari

Sauka induba matsalar tana sauka yahau dubawa cikin azama

Waiko incigaba da gudu ne acikin jejin kallon ta yai alamun bakida hankali tada mashin din yai Allah yataimaka saiya tashi

Hango motar Khalid yakusa kamosu yasa yajata a mashin din tareda ba mashin din wuta

Cikin tafiyarsu suka iske go slow din tireloli ,shamsu ya kutsa cikin su ko duba gabansa baya yi

Koda khalid ya iso ganin go slow din Nan yasa yabuga sitiyarin motar da karfi yasa huci sama sama

Cikin bacin rai da kunan rai yace Yan iskan nan ya akai suka bace min .

Jin karar wayarsa yana duba wa yaga sunan Abba yadaga

Dagacen bangaren yace khalid kanada hankali kuwa Jami,an tsaro sunce sunga motar ka sai tsula gudu kakeyi har kana kokarin buge mutane ,waima Ina kaje duk inda kake kadawo gida yanzu ina nemanka


Kasa magana yai cikin bacin rai

Yace ganinan tafe



******

Suna isa SALAMATU tafada jikin Antin ta maryam tana kukan murnan sake haduwan su ,zaunar da ita tai tace Alhamdulillah kin tsallake rijiya da baya , tsohuwar dake tare dasu tace waini yaushe zakuban labarin rayuwar ku ne


Watan Ku uku amma kunkasa gayamin tarihin rayuwar ku


Shamsu dayake haki dan gajiyar hanya dasuka yasha yatashi daga ringine dayai yace


Inna l'ami.idan lokacin sani.yai Zaki sani aikin wuce jin komai daga garemu keda Kika bamu wurin kwana keda mallam ado

Allah ne kadai zebiyaku

Ummu ta kalli salamatu cikin halin tausayawa tace salamatu duk halin da ake ciki gobe kibar kasar nan Zaman ki anan kokuma komawan ki gida tamkar barazana ne ga rayuwar mahaifiyar Ku kinga dai haryanzu itama batasan Maryam n'a raye ba ,SHAMSU YACE zancen ki.haka yake

UMMUL KHAIRI amaryan khalid zance ne ko uwargida cikin bata rai n'a wasa take kallon sa kaide ka iya tsokana wai Kana nufin haryanzu ina matsayin matar sa ne .

Maryam tace aikuwa haryanzu dukan mu matan sa ne saide matan da baa san suna raye ba

Ajiyar zuciya salamatu ta sauke tace anti wlh mijin ki shu'umin gaske ne wannan dawuya muyi nasara Akan sa

Shamsu yace akul. Kada insake ji kina fadin Haka ai inshAllah sai ya girbe abinda ya shuka Amma fa zamu sha wuya a jejin Nan abinci ma sai mallam ado yafita yake siyo mana

Ga rashin samun wadattacen muhalli

Duban salamatu yai cike da zallar.kaunar da yake mata yace bamu labari yana janyo kwanun abinci dan tun safe rabon sa da abinci

Nan tashiga bamu labari Abunda yafaru gidan su

Khalid


Shamsu yace lallai salamatu ke jaruma ce gobe kiyi kokari kibar kasar nan kamar yanda ummu tace , mallam ado ze rakaki airport

Allah yakaimu nima aina fison inkoma cen incigaba da kasuwancina mahaifiyar mu Daman batasan nazo ba .



*****

Sai safa da marwa Abba yaketa yi cikin daki 'yana ganin SHIGOWAR KHALID yai gun sa

Yana duba jikin sa koba abunda yasame shi hamdala yai tareda kamo hannun sa suka shiga daga ciki zaunar da khalid yace

Gaskiya Abunda bakaso shi zanmaka bodyguard dinka duk zasu dawo aiki Ina tsoron wani abu yasameka

Abba bakomai fa kawai nafita neman wani saiwar magani ne

Haba son daman saboda saiwar magani kake son kashe kanka aida n'a maka visa kaje USA kasamoshi. Jin muryan umma sukai tana cewa maimakon ka nuna Masa kuskuren sa da gangan cin da tafka akan titi inda yayan mutane ya buge shikenan ya buge banza kenan

Tsawa taji khalid ya buga Mata saida hantar cikin ta ya kada

Taku uku yai ya iso gabanta ganin yana dab da ita harsuna jin numfashi juna yasa umma jin baya da baya yana Kara kusantota sai jitai ya shake Mata wuya

Idanunta suka kada sukai jajir kalmar da take kokarin furtawa takasa Fadi cikin zazzare idanu da neman taimako

Abba na tsaye yana kallon su sai murmushi yake yana kallon irin shakkae dayake Mata

Jin an bankado kofa Yusuf yai tsallen kura kaman wani kumurcin zaki yai kan khalid gadan gadan .

cikin zafin nama ya fisgo shi tare da bashi naushi abaki zekara yaji sautin Abba nacewa inka Kara Yusuf zan tsine maka Albarka


Kin sakin khalid yai saida yakara nausa masa akaro nabiyu yaci gaba da bugun sa


Khalid ya aro jarumtar cikin Wanda ya jigata ga bakin shi dake jini ya rike hannu Yusuf


Idanun sa dasuka kada tamkar garwashi suke kallon juna shida Yusuf

Kalaman Abba sukaji yana Fadi Yusuf Allah ya tsine maka

Aikuwa cak Yusuf ya tsaya

Kalaman Abba yasa shi shekewa da dariya yayin da yake takowa izuwa gaban sa

Cikin kallon irin n'a tsana ya tsaya gaban Abban sa

Dan katsine mun s'aime ai Babu biyayya agun sabawa Allah

Kin hukunta Yaya khalid kamar haramci ne kakeson n'a aikata cikin nuna halin ko in kula da abunda Abba yayi

Yakara da cewa karkai tunanin nazo ne dan sbd dakai mahaifiya ta nazo gani

Tsuki yaja yabar Abba tsororo sake da baki yana kallon Yusuf dayai gun mahaifiyar sa

Umma sannu nace miki kizo muta fi gidana kinki wayannan marasa imanin saisun kasheki

Mikar da ita yai Yana goge mata fuska, raka ta har daki ya kwantar da ita

Tareda daukar waya yakira personal docto dinsu Hamza

Docto yace gashinan tafe .

Umma tace Yusuf Allah yaimaka albarka badan kaiba dayau khalid yakashe Ni ,daga fadamusu gaskiya tana mgn cikin sanyin murya Wanda Mai sauraro yasan tana jin jik

Dauko ruwa Yusuf yai a cup tareda siyaya mata , yabata abaki Tasha tana ajiyar zuciya take Nan barcin wuya yai awon gaba da ita .


ABBA

Kama Khalid yai yazaunar dashi Akan babban lallausan kujerar dakin tareda kwantar dashi yana jera masa sannan

Zaro wayarsa yai tareda danna lambar personnel docto dinsu hamsa

Hamza na dagawa yace ai gani daf dazuwa gidan naku yanzu Yusuf yakirani tsuki yaja tareda katse wayar yace waini yaron Nan bana sallama shi bane me yakawo shi gidana Dan iska me shegen taurin Kai kamar uwar sa .

Tarin da khalid yasoma yasa yakira sabuwar yar aikin da khalid yadauko wa Fatima mai suna Balaraba

Cike da ladabi ta sunkuyar da Kai tana jiran umarnin sa

Kije ki Kira uwar dakin ki Fatima mijin ta ba lfy


Cikin azama ta isar da sako sai gasu sun dawo tareda cikin tsananin damuwa Fatima takaraso gaban khalid ganin jini a bakin sa .

Lafiya meya sameka cikin ihu take magana a gigice kakalo mirmushi khalid yai cikin dakiya yace ahshh ashhh Fatima kaina ze fashe Nan take yanayin ta ya sauya ta manta Abba yana wajen tallafo kansa tai

Tana adu'oi tana shafa Masa a Kai sai Kara narke Mata yakeyi cikin zallan shagwaba yana wayyo wayyo teema bani ruwa .

Siyayo Masa ruwa tai tana bashi abaki Abba dake gefe yana kallon tsageran rashin kunyar su .

Sallamar docto Hamza ne yasa Abba ya tunkare shi maza kaduba mun Khalid .

Cikin kwarewa da sanin makaman aikin sa yahau duba akarshe dai yarubuta masa magunguna tareda basu shawaran abarshi ya huta

Docto yai hanyar dakin umma

Fatima tace docto wa zakaje dubawa aciki .

Rau rau da idanu sukai khalid da abban sa

Likita yace au bakisan hajiya batada lafiya ba wajen ta n'ai

Zata mike tabi bayan likita


Khalid yarike Mata hannun cikin yanayin Wanda ke jin barci yace wife kaini daki .

Bataso haka ba Amma haka ta hakura da niyyan data kaishi tadawo Dan duba lafiya umma


Docto Hamza yace gaskiya kiyi hankali hajiya jinin ki.kadan yarage be buga ba, kirage yawan tunani da damuwa

Magunguna yarubuta Mata ya mika wa Yusuf tareda Masa bayanin in ansiya yanda zata sha su godiya Yusuf yai Masa

Saka hannun sa yai aljihu ya zaro dubu 30 yana kokarin mika Masa ,Hamza yace haba yallabai nima uwata ce banzo dan abiyani baNima inaga sojan Nan zanfara bakaga yanda Kai kyau acikin kakin ku ba ga babban mukami kasamu ,aikin ku aikin sadaukarwa ne , Yusuf yace ai Kuma aikin naku na ceton ran Al'umma ne gashi kazo kataimaka mana ba


Sallamar aisha yai daidai da fitan docto hamza daga dakin ,cikin firgici tace

Umma meya faru ne

Yaya Yusuf meke damun ta kalau nabarta nafita tana magana cikin yanayin tsoron karta rasa uwarta

Umma tace aisha babu komai naji sauki ,ajiyar zuciya tasauke tareda fuskantar Yaya Yusuf cikin jin dadin ganin sa

Sai kare Masa kallo take sama da kasa Yaya kagan ka kuwa wlh kahadu cikin kakin nan ko shugan sojoji baze nuna maka komai ba ,

Dariya yasaki har fararen hakoransa suka bayyana


Indo haryanzu kinanan da halin naki ko tare da tsakale Mata hanci

Ashh Yaya da zafi fa wai ma daga fadin gaskiya yar Kara ta saki yayin da murza yatsun hannun ta


Umma sai murmushi take tana tuno rayuwan su na baya

Mike wa Yusuf yai tareda kusanto umma Dan Allah kisha magungunan ki zanba indo kudi taje tasiyo sannan Daman nazo in sanar miki aiki amun transfer maiduguri gobe zamu tafi nazo Inga kyakyawar fuskar ki tareda albarkar ki mahaifiya ta yayin da ya durkusa gwuiwoyin sa akasa ya sunkuyar da kansa

Dafa kan tai tace ya Allah kataimaki Dana Yusuf kasa masa Albarka ,barin dakin yai tareda aisha .

Yayi daidai da saukowar fatima daga sama sama tsayawa kallon Yusuf daya bata baya ne

Yana kokarin barin falon

A hanzarce t'ai bayan sa burin ta taga fuskan Yusuf din Dan aisha tai Mata text yazo

Kai jimana !

Tsyawa Yusuf yai cikin son ganin dashi ake be waigo ba yaci gaba da tafiya

Yusuf sani yaro Dan tsaya Mana tana kokarin karaso wa inda yake

Muryan Abba taji daga bangaren sa yafito.yana cewa ke wannan ba dana bane karki sake hada zuriar mu da wannan tsinannen

Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo daga idanun Yusuf batareda ya waigo ya fita daga gidan tareda aisha Dan siyan magunguna

Aisha tace haba Yaya na mahaifiya itace kan gaba kana tareda da albarkan ta

Abba mutum ne mai son kansa ni tunda inna Farida da sumayya sukaje hutu da rashin ka da zahradeen naji gidan yaimin girma

Gobe zahradeen zedawo

What mekike nufi be shekara da komawa ba


Cikin zuciyarsa dake tafasa yadau waya zekira Deeen

Zekira deen ,cikin isa sa da bacin rai yace haba zahradeen me zakazo yi Nigeria da dagacen bangaren yace am sorry Yaya na .

Khalid ne ya nemi inzo yace taimakon gaggawa zanmasa ,nikuma kasan ban iya bijire wa umarnin sa.


Yusuf yace tunda umarnin Allah ne saikaita bi nidai nagayamaka banson Kana Wasa da karatun ka soyake kazo Ku shiriri ce kaman shi kaje Kai nazari in zuwan ka yafi to Allah yatsare katse wayar yai batareda yaji amsar daze bashi ba.

Aisha tace haba Yaya Yusuf nida nake farin ciki zezo Dan nasamu abokin hira ,kallon kishiga taitayin ki ya watso Mata batareda ta sakeyin magana ba ta tsuke bakin ta tai shiru .

******

Fatima tai hanyar zuwa dubo surukar ta da sallama bakin ta


Tashiga dakin azaune ta sameta tana ganin Fatima ta fadada murmushin ta zauna diyata tareda nuna mata bakin gadon nata.

Cikin yin kasa da murya tace sannu umma yajikin naki ,bansan bakida lfy ba saida naga docto yazo dubaku ,

Umma tace karki damu ainaji sauki Dan ma sonake inje kitchen ma

Haba umma kibari nida balaraba mun dafa cikin gamsuwa da bayanan ta


Ta gyada Kai


Fatima inason in rokeki wata Alfarma


Inajin ki umma umarni zakiban incika .


Tareda rufe idanunta tana sauraren ta .


Umma tace inason ki sa Khalid ya sake ki

Firgit teema tabude idanun ta cikin kaduwa dajin zancen kamar saukar aradu daga sama

Kallon umma takeyi tanason ta tabbatar da zancen da taji

Karkiyi mamaki kidaibi Abunda nace Kuma karki tambayeni dalili .

Cikin kaduwa da zancen nata Fatima tace umma kozan iya sanin dalilin ,kokuma kina ganin bandace da inzama matar khalid bane duba da irin arzikin gidan Nan ,rike hannun umma tai

Pls umma gayamin dalilin ki karki sa zuciyata taita mun sake sake har infara zargin anya kuwa kece mahaifiyar khalid .

Ajiyar zuciya umma tasauke tana fuskantar ta yata karki Bari soyayya ta rufe miki idanu tun randa kikasa kafa agidan Nan naji Ina kaunar ki kin kwantamin araina banson inga zaki fada halaka ban tsamoki ba , sannan kimun alkawari bazaki fadawa kowa wannan maganar ba.

Hawayen dake cike a idanun ta suka fara kwaranya cikin zafi da kunan rai tabar dakin aguje


Tabi gaban surukin ta tana sheshekar kuka ,wayar dayake yi besa ya fahimci halin da take ciki ba

Direct dakin ta tanufa inda ta murzawa dakin Nata ke


Tana shiga daki tai hanyar toilet wani irin gudawa na tashin hankali yataso Mata tashiga toilet yakai sau biyar ,bayan tagama ne ta sakawar kanta ruwa Kaya na jikinta kasa ciresu tai tanajin saukar ruwa akanta zuciyarta na dada sanyi Nan take nutsuwa yafara saukar Mata , zallan mamaki yakamata lura datai Kaya n'a jikin ta ,maganganun umma suka fara dawo mata cikin kwanyar kanta barin toilet din tai tareda canja wasu kayan


Mai tadan shafa tareda daukar wata meterial pink color dinki rariya akai wa rigar

Cikin hanzari tafara hada kayan ta cikin akwati , ring din wayarta kan screen din wayar mommy ta gani da sauri ta daga wayar

Cikin sanyi take maganar

Mommy tace meyake damun kine naji muryanki sai a slow

Bakomai mommy cewar Fatima

Yau dai zanzo gida surprise naso inmuku daddy dake zaune kusa da ita ya amshi wayar yace

Haba Fatima nine fa daddyn ki ko nemana bakya yi aure yai dadi Kenan

Murmushi t'ai Wanda ya bayyana zallah kyawunta da nipple dinta dayan losa

Tace waceni Abba kudai kujirani ai yanzu zan iso inshAllah daddy wai ina salamatu ne

Ajiyar zuciya yasauke yace muma nan nemanta muke ta tafi ko kudin aikin ta bata karba ba

Tom Allah yakyauta daddy saide nazo ku tanadamun Abunda nafiso

Daddy yace bakida matsala bayan ta katse wayar tazauna cikin zuciyarta ta nanata salamatu tabar gida kodai dagaske take bayannan datai inko hakane yakamata in samo inda salamatu take cikin gaggawa.

Karar buga kofa ne yadawo da ita cikin tunanin datai zurfi


Muryan Khalid taji yana Fadi wai mekikeyine da bazaki bude kofa ba .

Tashi tai jiki a sanyaye ta bude Masa kofa ,idanu ya zuba Mata yakasa dauke su akanta tunda tashigo gidan bata taba burgesa ba irin na yau gani yai Takoma irin kaman balarabiya wani kwarjini tai Masa da kyau

Fatima tace mallam lfy wannan kallon haka , sai a lokacin yadawo duniyar tunanin daya shiga

Murmushi ya sakar Mata yace babu komai idanun sa caraf suka sauka kan akwati da tazubawa Kaya .


Khalid yace ina Zaki Kai Kayan nan ,


Tuno mata da bacin Ran da takeciki tai, tai tsaki ta ja tareda cewa gidan mu zani fuskan ta daure tamau.


Me akai miki Zaki gidan naku sannan da izinin wa Zaki fita


Abunda da takeyi.tabari tazo Daf dashi takaraso matsowa kusa dashi kaman zata shige jikin shi .

Yatsar hannun ta nakusa da babban yatsa ta dangwali kansa dashi tace da izinin Allah zan tafi


Kuma Bari kaji in gayamaka auren ka ban karu da komai ciki ba sai tashin hankali

Mamaki yakama khalid yace todan matsa baya man kin tsareni kaman zaki bugeni Anya kanki daya kuwa .


Murmushi tai tareda komawa window dakin ta tsya hannun ta goye abaya tace


Khalid inason ka rubuta min takardan saki yanzu nan inbakso nan gaba in maka abunda yafi wannan.


Firgici da tsorone yakamashi cikin tashin hankali da baa samishi rana yace


Ai bazan taba iya sakin ki nagane dalilin neman sakin Nan sbd tunda mukayi aure bantaba koda kusantar ki shine damuwar ki.

Sororo.fatima ke kallon shi dariya yaso ya kubuce Mata Amma tadaure ,tace wannan Kai ya dama

To.inbashi bane to me zesa kice a sakeki babu laifi tskanin mu ke in mafarki kike kidaina babu saki a aurena dake wlh

Kuka ta soma cikin sheshekar kukan tana fadin kataima khalid Dan Allah Ni karatu nakeson in koma daga baya innagama zaa maida auren .

Murmushi yai Wanda yafi kama Dana ciwo zuciyarsa n'a tafasa yace zauna muyi magana

Zama tai suna fuskantar juna .

Gayamin meyasa kikeson mu rabu

Fatima tace Dan Allah inason ka gayamin gaskiya

Gyada mata Kai yai

Yace inajinki

Dan numfasa t'ai sannan tace

Lokacin dazaka aureni a dangin ka akwai wayanda basu amince maka bane .

Khalid yace kowa ya amince sossai ma meyasa kike min tambayar Nan


Fatima tace ina nufin kamar iyayenka ,umma da Abba sunso aure n'a dakai su ma

Umma da Abba sunfi kowa son aurena dake 'jimm tai kafun tace to taya zan tabbatar da hakan in gaskiya ne


Cikin tsananin mamaki yace

Yace anjima.zan tabbatar miki .

Cikin wayance wa tace ko zaka je kasiyomin chocolat Dina yakare

To.kibari indawo daga massalaci yafita jiki ba kwari

Tana ganin yafita ta maida akwatin nata cikin data yar kamar Jakarta tadauka tareda wayar ta tafito dakin tana tafiya ahankali batason aga fitowar ta , Mai gadi baya nan yaje sallah Haka yabata damar fita daga gidan batareda tadau motar ta ba .

Napep ta tara inda taimasa kwantance gidan nasu (tudun wada) .


Umma ta idar sallah sai adu'oi take jerawa tanawa Allah kirari cikin azkar dinta .

Fatima ce tafado mata Arai

Nan take ta tashi da niyar yau zataje sashin ta , akaro na farko duk matan da Khalid ya auro bata taba leka dakin su amma gashi yau zataje ta leka n'a Fatima


Take wasu hawaye suka fara zubo Mata Allah yasani tanason Fatima ta jinta kamar jinin ta sau da dama ta kalle ta sai taga suna kama , adua take ya Allah yasa taga mahaifiyar ta da yan uwanta tasan su bazata iya gane su ba shekaru sun ja

Amma tabbas zata iya gane mahaifiyar ta .

Tafito dakin zatai hanyar dakin fatima daidai da shigowan aisha da.khalid atare ita tadawo daga school shikuma khalid yafito daga sallah .

Oyoyo indo na saiyanzu kika dawo , murmushi kwance akan fuskarta tace wlh umma kinganmu jarabawa mukeyi ne

To maza kije kiyi sallah kici abinci ganinan zuwa yanzu zanje sashin fatima .

Indo tace Yaya khalid inawuni amsa mata yai ba yabo ba fallasa yakama hanyar hawa benen gidan su .kusan atare suka hau shida umma .

Bawanda yai wa wani magana cikin su tsyawa yai yaga inda zata ganin ta kwankwasa kofar dakin matarsa yasa yaja tsuki

Fatima.kibude yau nice dakaina jin shiru baa bude ba yasa , khalid bin ta gabanta ya bude kofar ya leka ko Ina dakin har toilet babu ita babu labarin ta


Cikin kaduwa yace umma ai bata ciki still itama dakin tashiga ta leka babu kowa


Cikin zuciyar ta tace kodai maganar da mukai dazun ne yasa tabar gidan




Wata zuciyar tace to ai dazun tace zasuyi girki itada Balaraba kotana cen ne.




Kusan atare suka sauko daga itada Khalid hanyar kitchen ta nufa taga Balaraba tareda.dayar me aikin su ne suke girki batareda Sun ganta taba tajuyo hankalin ta atashe azuciyar ta fadi take Allah yasani Fatima kaunar ki nake shiyasa nagayamikki taya zan gyaro al'amarin Dan ta lura khalid yashiga cikin matsanan cin damuwa tausayin sa yakamata

Kusan uwa da da sai Allah

Aisha yace umma tunanin me kikeyi ne wai ina anty fatima taje naje daki batanan tasan yau zahradeen zedawo zamuje tareda tarbosa airport muka shirya

Khalid dake dafe da kansa dake sarawa gefe ya kalleta yace

Ni kadai zanje indaukoshi airport


Sallama da akai ne yasa su zazzare idanu wayanda sukagani yasa....



Umma umma ga su Inna Farida sundawo da sumayya tareda kama jakar hannun su .

Suna biye da ita abaya suka shigo falon fuskarsu dauke da murmushi lale lale da zuwan K


Daga hutu kamar bazaku dawo ba kuzauna ga waje nan

Inna Farida tace khalid meyasamu bakin ka ne Naga ya kumbura gyara zaman sa yai

Yace sannun ku dazuwa inna ta

Nadan buge ne amma dasauki ma


Sumayya tace yaya khalid inawuni lafiya ya amsa Mata fuska asake ,tashi yai yadau key din motar sa , saina dawo yace musu.

Inna Farida ta kalleshi tace haba Dana daga zuwana bazaka zauna mudan Yi hiran yaushe gamo ba .


Murmushi yai yace kedai Bari inje indawo sbd zanzo kwance jaka ,yana fadin Haka yai ficewar sa daga gidan

Indo zubo musu lemu tai a kofofi ta tsiyaya musu ta kalli sumayya tace kinga yanda kikai kiba kuwa da alama kin dadin garin .

Dariya sumayya take Mata

Umma tace gsk yau gidan Nan cike da baki yake yau fa

Zahradeen zedawo.shima

Inna Farida tace lallai yau zanga maza agidan nan

Wai Ina amaryan khalid take naji ance yai aure ko tana sashin ta ne

Umma tai jugum.tace yanzu Nan tafita batasan da zuwan naki ba data jira kun gaisa Amma nasan bazata dade ba

Balaraba ce dauke da kwanun abinci ta jera a dinner table tareda yiwa baki sannu da zuwa

Sossai sukaci abinci sbd Sun kwaso hanya ga rashin cin abinci .


***

Me napep yace Malama ai gamu tudun wada inane layin naku


Sorry Dan Allah ba tudun wada bane sabon layi ne kaini konawa ne zan biya juya akalar napep dinsa yai

Basu wani dade ba sai gasu kofar gidan nasu .

Kudade ta fiddo rafan dubu ita kanta batasan adadin kudin da ta bashi ba

Sai washe baki yake yanata fadin Allah yakara daukaka hajiya ameen tace.tareda

Kwankwansa kofar gidan nasu

Bala dake kwance yana barci yataso cikin magagin barci yana waye ne Dan Allah da rana tsaka zaku dame mu.

Jin muryan ta yai tana fadin Kai Dan rainin wayo.nice

Aguje yabude yana washe baki


Barkanki. Da zuwa hajiya ashe kece yi hakuri ya gajiya ya hanya

Lafiya lau tace Mai a gajarce ta wuce ciki

Bala yakama baki yace ita wannan yarinyar tai aure ashe har yanzu batai hankali ba


Jibi yanda take tafiya kaman zata taka mutane Allah yashirye ta.

Ita ko. Yar tsaraban Nan bata kawowa saide fadin rai yana magana yana tauna cingam abakin sa.


Oyoyo.oyoyo fatima kece yau agidan namu ,daddy sai washe baki.yake yace zauna daughter na zama tai cikin tsananin farin cikin ganin iyayenta

Daddy yace Ina khalid yake inace tare zaku zo

Fatima tai shiru tana nazarin amsar dazata bashi

Daddy shiya saukeni yaje yadawo yanzu zaku gansa


Asabe ce tazo fuskanta dauke da murmushi ta durkusa har kasa tace sannu da zuwa shugaba ta


Amsa Mata tai cike da kewar su tace ya aiki


Ta amsa Mata da lafiya tareda ajiye Mata kayan ciye ciye agabanta


Ta ficewar ta

Fatima tace daddy nidai yau gidan Nan zan kwna pls

Dariya tabasu mommy tace in mijin naki ya yarda Amma kwana daya kacal inkuma yaki agaida gida

Bata fuska tai tace nidai ku rokamin shi mommy

Daddy ya kalleta cikin so da kauna da begen yar tasa yace

A'a fatima bazaai Haka ba kar ya dauke mu mutanen banza kece dai zaki Masa magana

Sallamar khalid ne ya katse musu hiran cikin mamaki take kallon sa , iya bariki cike acikin fatima

Ta kalli Khalid tace au harka dawo daga ajiyeni kofar gida.

kace bawani uzuri gareka ba


Murmushi yai ya fahimci batasanar musu komi ba yace ai Wanda naje nema ne banganshi ba shiyasa nadawo


Daddy yace Bismillah shigo neman wuri yai yazauna suka gaisa cikin mutuntawa ,bayan sunci sunsha har Khalid yace


To zamu tafi


Ganin Fatima taki tashi ta noke Tace pls yau Nan nakeso zankwana ganin idanun iyayen nata akansu yasoma sosa

Keyar kansa


To ai Babu matsala yau da gobe ai duk dayane ,daddy yace bazaai hakaba ke tashi kibishi

Nokewa tai taki tashi tanata zuba kukan shagwaba ita tayi kewar gida abarta badan ransa yasoba yace wa iyayenta subarta goben zezo.yadauketa

Rakoshi tai har kofar gida ya kalleta cikin bacin rai yace ke yanzu kin kyauta Abunda kikai

Abunda nai shine daidai.tabashi amsa ai kamar yanda nace maka inaso ka tabbatar mun lalle iyayen ka sunso aurena dakai ko Basu so ba

Khalid yace yanzu kina nufin saina kawosu Nan gidan kenan

Tace kwarai kuwa inhar sunzo ze tabbatar mun suna son auren mu .

In gani afuskar su

Wayarsa ce tafara rinng yaduba wa yaga zahradeen ne .

Naji abunda kikace zantafi airport dauko deen saide goben innazo .

Shiga motar yai tareda barin kofar gidan direct aiport yawuce.

Fatima shiga dakinsu asabe tai tace Mata ta nuna mata kayan da salamtu tabari

Asabe ta nuna Mata

Daukar jakar kayan tai taje dakin ta dashi tareda zazzage su akasa tanabin kowani.kaya daya bayan daya

Idanunta sukai caraf akan I'd card din salamatu dauka tai tasaka cikin Jakarta tareda maida sauran Kayan yanda suke ,maida jakar t'ai dakin su asabe .


**

Deen na hango khalid aguje yaje ya rungumesa rataye yake da jakarsa cikin farin cikin ganin sa yace gaskiya yaya khalid Kai kiba Kai kyau kodai duk amaryar ta mu ce

Ta gyara ka murmushi yai masa yace shiga muje.


Suna cikin tafiya 'Deen yadau waya sai kiraye kirayen abokan sa yake ,ciki harda buduewar sa Karima

Khalid yace kaide suda saika shelanta zuwa ' dariya yasaki

Yace gwamma susani barima in Kira yaya Yusuf.

Nan take ran khalid yabaci take yafara tuno irin naushin da Yusuf yaimasa da bakin sa begama warke wa ba

Yace deen kabari inmun sauka saika kirashi cikin gamsuwa da maganar sa batareda da ya fahimci komai ba

Suna shiga falon yatafi aguje ya rugumi umma


Kukan farin ciki tafara yi daidai da shigowan Abba cikeda farin ciki yake kallon kanwar sa

Farida tareda yarta yace sannun ku dazuwa kallon deen dake makale jikin umma yai .


Yace cingam din mamar sa andawo lafiya ,cikin shagwaba yace nifa Abba ai super glue ne ni

Khalid yai gyaran murya yace deen kaje Kai wanka Kai sallah abinci n'a jira ya kalli su aisha da sumayya yace indo kibarsu su huta kinsasu agaba yana maganar ne da dan bacin rai

Tashi sukai atare sukai dakin aisha 'inna Farida data fahimci

Khalid nason ganawa da iyayensa ne t'ai hamman gajiya tace nidai zanje indan kwanta tareda mikewa ta ciki.


Abba yace khalid Naga yanayinka ya canza tunda nashigo

Cikeda tsananin damuwa kwance afuskar sa

Khalid yace abba fatima ce take zargin wai bada amincewar ku na aurota ba shine tabar gidan.

Cikin kaduwa umma tazare idanu tana tsoron kar su gano itace tace waye ya fada mata hakan ai mune kam mukeson auren ku, babu Wanda zeki Fatima tazama surukar sa

Yarinya mai hankali da hangen nesa,

Abba yace ai zancen banza take bayan nida mamata kullum Muna nuna Mata kulawa saidai inhar wani ne cen daga waje ya zugata .

Ajiyar zuciya umma tai dabe zargeta ba tace Kuma hakane fa to yanzu meye mafita .

Nan khalid yabasu labarin yanda sukai da ita

Abba yace me sauki ne gobe

Ki shirya inzamu office sai mubiya tare harda khalid din

Murmushi yai tareda rungume Abba yace gsk Abba samun ka saa ne arayuwata .

Ya. Kalli umma yace uwa uwa ce amma.bakowa ke amsa sunan ba

Murmushi tai tace Amma kasan cewa Albasa batai halin ruwa ba

Abba sai kallon su yake sannan yatashi cikin muryan wanda ke jin barci yace

Khalid dagani zanshiga daga ciki

Tashin sa yai daidai da fitowan Khalid ya shirya tsaf cikin kananan kaya ba karamin kyau yai ba

Direct dinner table yai yana gama cin abinci yahau kan kujerar falo ya kwanta tareda dauko wayarsa yana chattin yana kallo


Shi Khalid ke kallo yace anjima kasameni adaki da to ya amsa masa.


Washe gari


Karfe shadaya momyn ta shirya tana jiran Khalid da abbansa suzo su tafi . Kusan atare suka fito shida uban nasa Basu tsya bata lokaci ba .

Suna kokarin fita daga gidan

Inna Farida ce takira umma gefe daya

Tace gsk ki fadawa yarinyar nan gaskiya inhar bazaki iyaba nizan iya ,umma tace kidai Bari indawo zamu yi magana.

Shiga motar sukai khalid yajasu mallam isa yabude musu gate tareda musu fatan adawo lafiya

Direct sabon layi sukai katafaren gidan su Fatima gidane tsadadde Wanda duk Wanda yagansa yasan an narka nairori tsarin gidan zamani ne shuke shuken flower ne kofar gidan


Horn sukai Bala Mai gadi yabude musu gida

Kai tsaye ya kusa hancin motar acikin farfajiyar gidan

Sallama abakin su suka shiga daga ciki

Daddy yafito.cikeda farin ciki yace yau inada manyan baki oga dakanka

Dariya sukai tareda gaigasawa cikin mutuntaka momy tashigo fuskarta dauke da faraa tareda Kiran sunan fatima .


Tana isowa ta durkusa ta gaishe da iyayen mijin nata

Fatima tace to Bari inje kitchen indauko muku abun tabawa

Kai tsaye kitchen ta nufa.


Umma tai dariya tace Bari inje intaimaka Mata .

Momy tace dakan ki ai asabe na Nan tace aa aini nafison inga Ina motsa jinina bare Kuma ga yata a kitchen.

Direct kitchen taje inda ta tsya bakin kofar shiga kitchen tana kallon Fatima data juya Mata baya

tana kokarin daukan kayan dake gabanta Dan kaiwa falo.

Ji tai an dafata ta baya ,waigowa tai, taga kowaye ganin umma dauke da murmushi a fuskar ta

Riko hannayen Fatima tai ,kallo kallo sukewa juna ,kowanne da abunda yake ,tunani a zuciyar sa.


Mu haɗu a Chapter 4 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah