KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka Chapter 4

by @kyautadagaallah10

Kai ka jawa kanka 4

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah


Nazo Nan ne dan in rokeki daki koma gidan ki naga damuwa a cikin kwayar idanun khalid '




Fatima tace umma meya canja miki raayi daga jiya zuwa yau




Uhmm ta Dan numfasa tai murmushi yata .


Daman nace miki hk saboda naga Khalid haryanzu yana cike


Da kewar matar sa ,maryam data rasu ,har hoton ta yake adakin sa yakasa cire ta aransa




Ina gudun kada Haka ya cutar dake yata kasancewa kina bukatan kulawa agun mijin ki




Ajiyar zuciya Fatima tai tareda sakin murmushi


Umma indai saboda wannan ne


Karki damu namiki alkawari zan kula da khalid zemance baya .


Dan Allah umma kisamun Albarka kirikeni kamar Maryam din naga kema kina kewanta umma .




Rungume umma fatima t'ai sunajin numfashinn juna.




a,a fatima ba kewarta bane yasa nace hk ba tabbas mun zauna da ita lfykalau




Yanzu de abunda nakeso kije kishirya kutaho keda Khalid tare gidan kinji n'a rokeki kuma nagode da rufamin asiri da kikai




Zatai magana,umma ta rufe mata kedai diyata muje intayaki daukan Kayan nan .




Atare suka fito .




Mommy sai dariya takeyi tace Kai umma kina fa ji Dan wannan yar taki , dariya umma tai tace aikuwa dai babu ruwanku tsakanina da yata.




Abba ne ke kallon umma data fahimci kallon dayake mata ne ta dagamai.gira alamun komai ya tafi daidai .




Daddy yace Alh sani yazakuce bazaku ci ba kufa ba baki bane Yan gida ne .




Dakyar sukaci kadan , wayar abba ce tafara ring , dubawa yai


Yaga inna Farida ce ,ke Kira


Yana daga wayar yace kanwata


Yadai, daga cen bangaren banji me tace ba . Yace Mata gamu Nan zuwa yanzu yanayin sa ya canja .




Umma tace lfy kuwa , murmushin yake yai yace bakomai ,tashi muje Kai Khalid in Fatima ta shirya ku taho tare yanzu ,




Daddy yace oga dafatan dai bawata matsala ,




No babu komai yabashi amsa a gajarce rakosu har bakin mota sukai ,tareda musu adua Allah yakaisu ,lfy




Bala Mai gadi ya wangale gate yana fita da motar gidan aguje yake ,tuki .


Da mamaki umma ke kallon sa






Tace inafatan bawani abu yafaru ba.




Ajiyar zuciya yasauke cikin bacin rai yace ,yan iskan Yan jaridun kasar nan sunacen sunyi sansani wai sunji lbr ance fatima tayi yaji.




Allah yakyauta shine amsar da umma tabashi takara da cewa gsk bekamata suzo gidan babban mutum kaman ka ba babu izini ba .




Abba yace aiyanzu bodyguard duk zasu dawo aiki hatta ke kanki inzaki fita sai dasu.




Basu wani dade ba sai gasu cikin farfajiyar kerarren gidan nasu dayafi kama da gidan shugaban kasa Dan gidane dashi kadai ne ya zarra a unguwar kasancewa kusan layi daya na unguwar nashi ne .




Yana faka motar ,kokarin sauke kafafun sa yake dan fitowa , gabadaya Yan jaridu suka kewaye su .




Murmushin yai Wanda yafi kama da ciwo yakama hannu ,umma suka Shiga gidan ,suna biye dashi abaya .




Inna Farida tace gwamma daka dawo yanzu sun tsareni da tambayoyi .




Zama yai yana nazarin su ,sannan yatashi tsaye ,lasifikokin hannun su duk suka tsaita shi gaban shi ,dayan cikin su yace ranka yadade anata yada jita jitan wai Dan ka yasaki amaryar sa ,wasu kuma sunce yaji tayi ,munason muji gaskiyan Lamari dan kauda zancen da aketayi .




Gyaran murya Abba yai yace , family sani yaro akasar Nan yana cikin manyan family da ake ji dasu a jahar dama kasar gabadayan ta ,da akace abunda kike Fadi gsk ne akan mu ,bazamu damu ba .




Amma kiris kuke jira kuje kuyita jada jita jitan banza ,kiris nake jira duk Dan jaridan daya Kara karya Akan ahlin gidana kotu ce zata raba mu , tareda tara mai tsanani .




Yan jarida kowanne yafara kallon dan uwan sa ,suna jinjina maganar sa,




Alh sani yaro ko zaka iya gayamana gaskiya lamarin.




Umma ta amsa zancen da cewa Khalid be saki amaryar sa ba.




Kowa nada sirrin sa ,mu shikenan bamuda sirrin kan mu duk motsin mu ,ido nakai. Cikin Yan jaridu wata me suna aisha ,tace ranki yadade wai ya labarin ,matar khalid Maryam ko ansamu gawanta .




Abba najin hk ya amsa zance yace anakan bincike dai


Har Allah yasa agano Wanda yai aika aikan .




Yar jarida aisha tana maganar zuci tace in wannan Karan ka kubucewa tambaya ta ,


N'a gaba bazaka tsira ba, tana murmushi da ita kadai tasan fassaran shi.




Abba yace Kuna iya tafiya ko.


Sallama Khalid da Fatima ne ,yasa abba jin wani sanyi a ranshi tun kararsu yai yacewa yan jarida ,wannan Dana ne KHALID SANI YARO , tareda amaryar sa FATIMA AUWAL wato surukata inafatan kun gane , kaman jira suke suka fara musu tambaya fatima ta rungumi Khalid tace ba saki aurena da khalid Kuma ni banyi yaji ba .




Khalid da yarasa amsar daze Basu kama hannun fatima yai suka shiga daga ciki.






Kashe gari






Fatima ce ke wanke Kayan ta a washing machine ,tana rera karatun alku'ani muryan tai mai dadin sauraro ,Inde take karanta suratul A'ala , sallama taji daga bakin kofa bada izinin shigowa tai ,aisha da sumaiyya ce tareda wata yar karamar yarin wacce ake Kira da nusy .




Sumayya tace au anti aiki kikeyi Ina Balaraba take , murmushi Fatima tai tace yau da kaina nakeson yi ,aisha tace to bara mu tayaki Amma kafun Nan ,munason magana dake.




Muje falo tace musu tareda wanke hannunta da kumfar omo ya bata , dukansu sun zauna sunyi tagumi .




Fatima tace inafatan lafiya kuke Naga kaman kunada damuwa atare daku.




Aisha tace ba dole kiga hakan ataredamu ba ,kinyi yaji kin tafi meyasa bazaki dauke mu a matsayin kannen ki ba nida sumayya , nasan zakiyi kewan gidan ku Nan bakida abokin shwara to mu ki daukemu amatsayin kannen ki uwa daya ,uba man .




Dan Allah karki sake tafiya kibarmu ,cikin shesheka kuka dukansu harda kwalla .




Jikin Fatima ne yai sanyi tarungume su suka hada Kai waje daya ,itama stil kukan take .




Tace namuku alkawari bankara tafiya ,inma inada damuwa zan sanar muku tana dariyan farin ciki.




Tsalle sukai sumayya da aisha suka tafa hannu .




Fatima sai dariya take tanajin sonsu da kaunar su na Karuwa acikin zuciyarta




Kamo hannun karamar yarinyar t'ai nusy tareda daurata Akan kafafun ta .






Fatima tace waini dan Allah in tambayeku




Suka amsa da muna jinki




Tace wannan yarinyar wai ina mahaifiyar tane .




Kowacce daga cikin su sai kallon junan su suke.




Aisha cikin sanyi murya tace wannan ai diyar Khalid ce ,sunan maman ta


Maryam






Azabure fatima ta Mike tsaye tace 'wai daman wannan diyar Khalid ce shine be taba fadamin


Shiru dukansu sukai tareda dukar da kansu kasa .




Sallamar khalid ne yasa dukansu suka dago Kai .




Cikin girmamawa sukace masa ina wuni ya amsa a gajarce .




Aisha tace to anty zamu je saimun dawo ,kama hannun nusy sukai zasu raba ta gefen sa , su wuce .




Nokewa t'ai tana fadin ga dadddy ga dadddy tana tsalle ,


Dariya ya sakar mata tareda durkusa ya shafa kanta yace




Nusy nakawo miki chocolate da ceeze kibisu kije gun umma tabaki.




Nusy ta kalli Khalid tace yee yee daddy n'a inason ka ,tareda ficewa adakin tabi bayan su aisha.




Kallon kallon sukewa juna shida fatima ,cikin dakiya da aro jarumta tareda danne fushin ta .




Tace sannu da zuwa .




Dafatan kadawo lfy , murmushi ya sakar mata tareda bude hannayen sa alamar tazo ta rungume shi.




Kasa zuwa tai inda shida kansa ne yajawota ya rungume ,acikin kunnenta yake mata rada .




Yace fatima inasonki , inasonki komai kikeso aduniya zanbaki ,karki guje ni .




Nasan ban cancanta da zama mijin ki ba




Rufe masa baki t'ai da hannayenta tace pls kadaina irin maganganun nan ,Ada bantaba jin Sonka ba amma daga baya naji kashige min araina ,nabaka amanar kaina Khalid cikin sanyin murna take


Magana.




Tace amma meyasa baka taba gayamin kayi aure acen baya ba


Harda haihuwa .




Zaunar dasu yai kan kujerar dakin suna face din juna .




Yace my wife dogon labarine


Nayi tunanin idan nafada miki '


Bazaki aureni ba ,yana 'matso kwallan karya .




Zuciyar ta ya karaya tace babu komai yawuce amma inason kaban labari komai.




Shafa bayan ta yai yace Bari zanbaki labari ,amma karki kara yimin mgn ni zangayamiki dakaina.






Aisha da sumayya ne suka saukowa daga saman bene rike da hannun nusy






Sumayya ta kalli aisha tace


To meysa yaya khalid be fadamata yanada ya ba.




Boyayyiyar azuciya indo ta sauke tace kinsan shi mutum ne miskili kuma sam shi kullum


Rayuwa yake kamar n'a fir'auna




Tuntsirewa da dariya sukai atare ' sumayya tace kinga zo bar nan dan wlh yaji mu .




Bazamu Kai labari ba .






Umma ta hange su ,sai dariya suke' tace kudai Allah yashirye


Da sumayya bata nan ,kindawo kalan tausayi yanzu tadawo sai zuba iskanci kuke.




Indo tace ,haba umma wai me kikaga munayi ne kawai ba daman mu dara sai a tsargu.




Rike baki ,umma t'ai tace iyeeh watau ma tsarguwa n'ai kaniyar ki indo ! Nace kaniyar ki.




Inna Farida ce data fito daga dakin ta tarako mai gidan ta alh nura ,babban sumayya dariya ,take musu inda suka gaisawa da 'umma.




Alh nura yace umma gsk yarannan aure Zaki musu ki huta ,




kaidin Bari ai hk zanyi kar nan gaba akasa gane waye uwar wacece yar acewar umma




Indo da sumayya kama hanyar dakinsu sukai suna cewa 'amana auren man agani ko bazamu zauna ba.




Rike da baki umma take kallon su tana dariya .




Inna Farida ta dawo daga rakiyan mijinta , tace zauna umma




Samun wuri sukai inda bbu me jin abunda suke fadi .




Inna Farida tace waiko inntambeki yakukai dakikaje gidan fatima.




Nan take annurin fuskar umma ta dauke , cikin murya me nuna tsananin damuwa tace ,nacanja abunda nai niya ne kasancewa naga damuwa Akan idanun khalid alamu Sun nuna yanason fatima so mai tsanani.




Inna Farida tace haba kekuwa nasan raunin ki zehana ki fada mata gsk amma meysa ni bazaki Bari in gayamata ,




Umma tashi tsaye t'ai cikin muryan ta dake nuna alamun babu Wasa ciki tace .




Shekaru talatin ina cikin gidan nan babu abunda nasani arayuwa ta sai bin umarni da cutarwa da azabatar dani akai '




Nayi kokarin ceto FATIMA saina lura itama ta kamu da son Khalid ,matsamata Akan tayi abunda nakeso ,barazana ce ga rayuwa kema kinsan haka'........................Amma taya zanbar zalunci taci gaba da dorewa ina ganin ,inna mutu da wani hujja zanje gaban Allah .zance wa Allah ne saboda Khalid Dana ne shiyasa ban dau mataki ba.




Dafa Inna Farida t'ai tace kinfini sanin halin SANI YARO yayan ki ne.


Uwar Ku 'daya uban Ku daya.






Ajiyar zuciya Inna Farida tasauke tace nidai zanyi kokari in fada mata gsk '




Umma tace no yanzu ba lokacin yin hakabane karki kuskura




Adua zamusa agaba ze taimake mu.




inshAllah .




Kai Inna Farida ta gyada alamun gamsuwa amma azuciyar tadau niyar tunkaar fatima .




Sallama zahradeen ne yadawo dasu cikin duniyar tunanin dasuka shiga




Wai umma ina kika shiga ne sai nemanki nakeyi.


Murmushi ta sakar masa,


Tace to dan mama ,me zan baka ne ,sosa keya yai yace au




Inna Farida ashe kina kusa dariya t'ai tace Kai daman bakaganni sbd kazo Kana zubawaa umman ka shagwaba




Deen yace nidai yunwa nakeji naga baa jera abinci dinner table ba yana marairaice fuska




Umma tace to acici mala'ikun tauna muje yanzu zaka ci .






Kowa yasauko kamar yanda akasaba , suna cin abinci babu abunda kakeji sai karar cokali '




Deen dake kokarin tsiyaya lemu a kofin glass dake gaban shi ya kalli Fatima yace Kai matar yaya naga bakaman bakya cin abinci sossai ,.




Fatima dariya ta saki .


Ran khalid ya baci jin abunda deen yace, cikin kosawa da abincin




Yace ,umma mudai zamu fita nida fatima zamuje dan shakatawa zazzaga ,cikin gari tareda ziyarar asibiti , kinsan shekara ta zagayo dan hk tareda ita zamu je .




Tashi yai ,itama tabiyo bayan sa'


Umma tace ai baku wani ci abinci ba ,




Abba sai kallon shi Khalid yake yace to saide kadawo dana Allah yatsare.




Deeen ne yatashi a hanzarce yabi bayan Khalid yace




Wai yaushe ne m'a zamuyi maganar dakace shine dalilin dawowata gida.




Khalid kallon fatima yai yace dan bamu waje zamu yi magana .




Kamo hannun denn yai yace




Aikine ne mai tsauri amma nasan bazakaban kunya ba.




Murmushi Deen yai yace haba yaya kaide fadamin aizanyi .




Boyayyen ajiyar zuciya Khalid yasauke tareda duba tsintsiyar dake daure hannun sa yana duba lokaci .




Khalid ya dubi Khalid cikin maganar dake nuna tsantsar gaskiyar sa yace .




Deen inason Karinga kwana dakin fatima daga yau .






Cikin son yakara maimaita masa abunda yace ne




Yace banjiba dan maimaita.



Khalid yace ina nufin karinga zuwa dakin ta a madadina




Dummmmm Deen yaji zancen har cikin kokon zuciyar shi , idanun sa da suka kada sukai jajir ya yajuyo.ya kalle shi .




Muryan sa arauna ne yace A'a khalid bazan iyaba bazan iyaba nace yana runtse idanunsa ,zuciyar n'a harbawa da karfi




Khalid ya dafa bayan shi,cikin tausasa murya yace yanzu deen har akwai Abunda zance kamin aduniya kanada halin yinsa ,kaki mun .




Kwarai kuwa banda sabon Allah deen yabashi amsa , inbaka son ta ka saké ta , yafi Kai wannan tunanin Akan ta ,ina ganin yarda da mu da t'ai.a family mu.




Muzo muci amanar ta sam A'a badaniba ,ya juya zefice.




Khalid yace dakata ,tsayawa yai batareda ya waigo ba.




Khalid yakaraso inda yake ,yafara zubda hawaye , cikin kunan rai yace ashe daman Deeen wannan rana zata zo ka bijire ,kaman ce .




Ni.khalid nina raineka ,har gadon bayana nake goya ka '




Nasaka.kai karatu mai zurfi Wanda koni banyi ba ,ajiyar


Zuciya yasauke yace inhar bakai min abunda nace ba .




Tabbas zan mutu da bakin cikin ka.




Sannan babu ni babu Kai .




Kaje Kai tunani nabaka sati daya




Yna gama fadin hk yajuya tareda Kiran ,fatima suka fice daga gidan.




Deeen' yakasa motsi daga inda khalid yabar shi rike yake da satin kan shi dake sarawa.




Umma ta hango shi.aguje.taje tasameshi.tareda kamoshi suka shigo da ciki.




Deen meke damun ka , ko asma dinka ne yatashi girgiza mata Kai yai alamun A'a .




To meyake damun ka tana mgn arude ,dakyar ya iya furta kaina ke ciwo.




Balaraba takira tabada kudi taje pharmacy tasiyo magungu n'a.




*




Khalid tuki yake amma yana tuna tattaunawar su da Deen yana murmushi ,a zuciyar.fadi Yake , nasan halin ka deen zaka yarda ne .




Fatima t'ai murmushi tace wai


Dariya me kake ne Kai kadai




No natuna abokina ne daya taba karyewa gun wasan kwallon kafa .


Shine abun yake ban dariya dan yasha kuka kamar karamin yaro.




Fatima darawa t'ai.tace ah lallai dole Kai dariya ,a ga kato n'a kuka daban dariya gsk.




Dan aramun wayar.ka.inkira.safiyya narabu da jin .




Mika.mata.wayar yai kan screen din wayar hotunan mata tagani kowacce Macé ansa lamba kan hoton ta .




Hoton ta ne nakarshe me dauke da nomba 12 , cikin zallan mamaki tace wayannan hotunan fa ,






Kwata kwata yamance da hoton screen din daya hanata waya ,cikin basar wa yace.




Anjima zamuyi mgn , binshi da kallo take da alaman tuhuma , barin duk wata tunani t'ai .




Tareda cewa ko zaka kaini gidan safiyya kaga batada nombata Dana canja yanzu karatu be barin ta sakat




Kamar baze amsa ba yace in zamu dawo gida zamu biya.




Shiru kakeji babu mai mgn acikin su.






Suna.iso.babban restaurant aguje aka bude msu Gate kasancewar ansa da zuwan 'nasa ,barka da zuwa.ma'aikatan wajen suke masu


.


Bayan Sun zaune ne ,Aka jera masu dring agbansu tareda tambayar su ,me zasu ci




Khalid yai murmushi yana kallon fatima ya lura idanun mutane akansu , yace wife .


Me.zakici .




Murmushi t'ai tace banda zabi .




Kallon mutumin dake gaban su


Khalid yace akawo musu fruid salad da peppe su ,




Angama ranka yadade tareda tafiya dan kawo musu .




Assalam alaikum.


Wasu yan jaridu guda uku ,Macé daya cikin su.


Ya sallam khalid yafada acikin zuciyar sa.




Wannan dalilin yasa Bana zuwa populaire waje , sbd yan jarida nan.




Cikin Yan jaridu daya daga ciki




Yace ranka yadade kozamu iyayi maka wasu. Yan tambayoyi






Khalid yace Aa bazan amsa kowani tambaya sbd nazo da amaryata kyakyawar sahibata ,


Me kyaun hali da nagarta shakatawa .




Murmushi fatima t'ai batareda tace uffan ba.




Yar jarida tace wa fatima inama ace zanzama kamar ke 'kina tareda namijin mafarkin ko wace Macé.




Fatima.ta kalle tace nagode' acikin zuciyar ta sai fadi take




Kamar sunsan Zaman da akeyi acikin gidan ne.




Bazamu dade ba ,direct asibiti. .Suka nufa ,al'adar khalid ne taimakawa marasa karfi a asibiti,kuma duk shekara yake




Ziyartar ta marasa lafiya.




Bayan sun baro 'asibiti




Direct gidan safiyya suka nufa.




****




Aisha tafito makaranta sai jiran drever take taji shiru ,wani daga cikin student din ajin yace yace ah kowa yatashi kina nan ke kadai.




Eh wlh tabashi amsa a gajarce




Still sake kallon yai yace in babu damuwa zomuje a mashin Dina in rage miki hanya .






Shiru t'ai tana tunani cen tace ,to babu matsala ring din wayarta ne yasata bude jakar ta.




Ismail tagani, murmushi ta saki ,tareda daga wayar ,inawuni honey , kaga drever bezo yadaukeni ba ,




Wani student din ajinmu yace zesaukeni a mashin din sa .




Daga cen bangaren yace A'a wlh ban yarda ba ki tako akasa ,kinji nagayamiki cikin fada yake mgn.




Aisha tace wlh akwai wasu yan iska dasuke tareni ,




Isma'il yace kedai karki hau mashin din sa ,kuma Yan iska ko sunmiki mgn karki kulasu.




Student din daya fahimci firan su , ficewa yai abunsa batareda yabari ta bashi amsaba.






*




Oyoyo . maman mama zokiga fatima ,cewar safiyya






Mama tafito ahanzarce tace Ah ah yau manyan baki 'ne agidan'


Namu ,ga wuri kazauna surukina.




Safiyya tace sannu dazuwa khalid ya amsa mata fuska asake ,dring ta jera agaban su.




Sannun ku kunsha hanya, fatima ta bata rai cikin Wasa tace shikenan saikika dauke kafa,kindaina zuwa gida'na tana kallon khalid.




Murmushi yai yace nima dai hk zance to munzo biko.




Dariya mama t'ai tace Ayya ai kullum mgn ta agidan nan




Bewuce 'na fatima .




Fatima tace in hakane to meyasa bata zuwa ,




Khalid yadan sha drink din yamike tsaye .


Kallon mamaki , fatima tabishi




Dashi alamun ina zeje ,mama tace to tun yanzu zaku wuce ne .




Amsa mata yai A'a zanjirata awaje akwai wayar dazanyi ne.




Cikin gamsuwa da hk ta gyada Kai ,tace karka damu daka gama kashigo kuci abinci pls




Badamuwa yace tareda fita daga dakin.




Mama tashi t'ai tawuce kitchen dan karasa girkin ta .






Safiyya tace ,fatima naga aure n'a canja mata amma ke naga baki canjaba saide ,rama dakikai.




Badole in rame ba safiyya tunda n'ai aure wlh bansan dadin aure ba nan tabata labarin komi .




Sossai safiyya ta girgiza tace amma fatima kema akwai naki laifin ' keko yar kisisina n'a mata




Baki iyaba. Sai girman Kai




To Bari kiji Maza yanzu Yan iska ne ,sunfison macen da idanun ta suka bude wlh.




Nan tashiga bata shawarwari .


Game da yanda zata jawo hankali mijinta.




Ni cikin labarin ki ,aure 12 dakika ce mijin ki yayi ,shine yafi tadamun hankali ,kibi ahankali ,kuma id card din salamatu kimun hoton sa.




Ki turomun ta whsap ni zanmiki bincike akansa .


Fatima t'ai murmushi tace shiyasa kike burgeni akwai tunani irin n'a manya.






Khalid yashigo yana duba Time agogon hannun sa .




Yace fatima taso muje akwai inda zani


Safiyya da mama data fito kitchen dauke da wamers hannunta suka hada baki wajen cewa abinci fa ,mekuke nufi ne.




Fatima ta marairece fuska nidai mama kicemai yabarni yatafiyar sa.




Mama tace bazaai Haka ba ,saffiyya dauki abinci kisa.mata a mota nasan halin teema .




Rakosu safiyya tai tareda saka mata abincin a mota .




Fatima n'a gaban mota ,tace safiyya dan ban wayar in samiki


Nombata .




Mika mata t'ai tasa mata nombar.




Bye byee sukai mata inda Khalid ya figi ,mota aguje yabar gidan su ,safiyya.




**




Aisha ,gudu takeyi suna biye da ita abaya kara gudun takeyi iya karfin ta tana kuka ,


Wayyo mama nashiga uku






Bata fargaba sai gasu agabanta




Cikin razana da tsoro tace wai menai muku ne.




Dayan yace ai tunda yayanki ya mare ni nace miki saina rama kuma wlh fyade zamuyi miki ,


Mu ,uku , nan gaba zakiyi hankali.




Kuka mai tsuma zuciya tafara tace dan Allah kurufamun asiri




Karku keta min mutuncina




Dariya suka bushe dashi ,tareda daukar ta suka rufe mata baki.




Tana ihu muryan ta bé fita .




Jefa ta amota sukai .






Suna tukin ganganci a hanyar harsaida sukazo wajen gari.




Wani gida dan nesa da titi, suka nufa da ita tana musu musu tana zazzare idanu.




Suna shiga daga gidan suka kara bushewa da dariya ,




Ogan nasu yace kinga gadon amarcin ki ,gimbiya.




Yana kokarin..

rabata da Kayan jikin ta Ihu tasaki cikin muryan ta daya disashe saboda kuka, tace dan Allah karku rabani da budurcina .


Dariya ogan nasu yafara sannan ya hade fuska yace kedai yau dandani zumar ki.



Ni ikilima adam ban iya kallon irin abunda sukai wa aisha dan munin sa.


Wata kara tasake still yayin da wani me mota jeep yai parking


Wajen.




Bindigar dake ,cikin motar sa




Ya dauko tareda tareda kasa kunnen sa ,don yaji daga ina


Kukan Macé ke tashi.




Direct gidan yanufa '




Bankada kofar yai da kafafun , yashigo cikin gidan yanata waige waige ,hango su ''yai




Sunata aikata Masha da diyar


Mutane wadda tuni ta sume .




Jin karar bindiga yasa suka fara fita ta Windows.




Gabansa ne ya tsananta buga da firgici da tashin hankali.


Ya isa wajen aisha ,ta bata yai .




Yaji kamar bata numfashi


Ya ilahi ya furta nan take tsoro yakamashi gudun daga taimako ace shiya kashe ta.




Ruwan faro yadauko a motar sa


Tareda yayyafa mata ,


Numfashi taja me karfi ,ta barke da sabon kuka tana fadin nashiga ,uku n'a lala ce.




Mutumin sai kallon yake ,cikin son gane fuskarta amma ya rasa ina yasanta ,Ajiyar zuciya


Yasauke cikin tsananin tausayin ta ,




Yace ,baiwar Allah inane gidan 'naku ,kuma meye hadin Ku


Dan yan iskan nan da sukai


Miki ta'asa ,




Cikin sheshekar kuka tace wlh babu laifin danai musu '


Hanya ce tabi dani ta wajen su




Shine suka biyo , wayyo Allah umma ta shikenan tawa ta


kare.




Dan Allah karufa mun asiri gidan mu banson kowa yasani




Dan akwai matsala .




Da mamaki yake kallon yace kamar ya Kenan ,sokike akyalesu




Suci gaba da cutar da Al'umma




Fyade fa yai miki ,Toni inbaki sani nidin nan soja ne.




Nine zandau case dinki a hannun n'a ina fatan zakiban


Hadin Kai , kuma Zaki gane su




Gyada masa Kai alamun zata gane su , still kara marairaice fuska t'ai tace dan Allah dan girman ma'aikin Allah kabar zancen nan banson yafita




Fitar da maganan' nan kaman tonamun asiri ne.




Saurayi n'a , kawayena, Kai harma da gari zedauka




Musaamman yanda family mu


Yai kaurin suna a fadin Nigeria




Mutumin yace wani family kenan'




Sunkuyar dakai tai tace




Yaro house




Ni diyar SANI YARO ce




Azabure yatashi yace wat




Cikin sauri ya ciccibeta yai asibiti da ita.




Umergency Aka shiga da ita suka fara bata taimakon gaggawa .




Docto 'ne yafito ya kalli Wanda yakawo indo yace.yabishi offis dinsa.




Jiki.asanyaye yabita


Likita yace wannan aika aikan babban ne dan sunji mata rauni sossai .




Badan kai soja bane.bazamu karbeta saimun ga, iyayenta.




Sojan ya kalleshi yace nidai yanzu ya jikin Nata ,inafatan bawata matsala babba.




Eh to babu babban matsala amma dole sai wani.daga gidan su ,yazo yasa.hannu.






Sojan ajiyar zuciya yasauke yace ' nizan tafi inada aiki.




Kaban acct nomba ka insamaka


Kudin aikin .






Likita yarubuta masa acct nomba a pepper'


Sannan yarubuta mata ordonnance din magungunan




Tareda Mika masa.




***




Hankali umma atashe sai Safa da marfa takeyi ,kowa agidan babu mai sukuni , Deen yace wlh umma.bakiga yawon




DAMUKAI ba.a cikin gari bamu ganta ba.




Cikin kuka' umma tace iya shekarun Dana dauka da indo




Bata yawo ,dole akwai.mummunan abunda yafaru da ita.




Inna Farida cikin tsananin damuwa tace ,sumayya .


Ta bata lambar isma'il akirashi


Aji ko suna tare




Deen ne ya kalle ta ,tuni kwalla yacika idanun sa yace ai har


Gidan su isma'il naje naganshi


Basa tare yacemun dai sun yi '


Waya akan baazo daukan ta ba.




Cikin kuka' umma ta kalli ,sumayya tace jeki kiramun


Fatima .




Amsa mata da toh t'ai inda Kai tsaye dakin fatima ta nufa.




Iske ta kan darduma ta idar da sallah tana jan casbaha.




Fatima tace lfy sumayya naga


Kinfita hayyacinki lokaci daya.




Agajarce sumayya tace ,umma n'a Kiran ki .


Ta juya batareda bata wani amsa ba. Kusan atare suka.sauko daga saman bene itada sumayya.




Sallamar abba 'ne yasa 'umma


Karasowa kusa dashi tace .




Yadai ansamu labarin ta ,


numfashi ya fesar tareda rike kugun sa ,yace babu wani.


Labari ' amma khalid yatafi makaranta su shida alh nura.




******




Sojan Kai tsaye dakin da Aka kwantar da fatima yashigo ya shaida mata abunda docto yace nagason wani Nata yazo '




Magunguna ya Mika mata tareda nuna mata yanda zata sha kowan'e daga cikin su.




Wayarsa ce tafara ruri kan screen wayar sa ,sunan maigidan sa ,yusuf sani yaro.




Ahanzarce ya daga yasa wayar Hans free , inawuni sir ya aiki ya kokari ' daga c'en bangaren yace haba Ahmed wannan case din danabaka kafun intafi maiduguri haryanzu ka kasa kawo karshen ,




Gaban Aisha tsananta bugawa yai da taji muryan yayanta yusuf ' azuciyar tsoro da fargaba kada ya gayamai .


Tasan yusuf koda besan mutum


Ba to zebi masa hakkin sa in Aka cuce shi.




Sojan yace pls sir amun afuwa wani case nakara cin karo dashi


A hanyata ta dawowa wata matashiyar budurwa akaiwa fyade.




Yusuf mike wa yai tsaye jikin yadau rawa ,zuciyar sa 'na tsananta bugawa yarasa dalili.


Shidai ya tsani kalmar fyade




Da kisa 'fashi da makami.




Amma kuma ana fada masa wannan fyaden yaji abun har jinin jikinsa duk da besan wacece ba.




Ya sunan wacce akaiwa fyaden




Sojan yace..

sunanta Aish

Dumm yaji maganar ' nan take ya tuno da kanwar sa ,abun kaunar yace.




Yace Ahmed , inason abinciko min wayanda sukai mata fyaden ,sannan ita inkuna tare Kana iya hadani vidéo call da ita




Sbd akwai muhimman tambayoyi dazan mata.




Aisha duk ta gama kidime wa


Jin har vidéo call za'ai




Ahmed ya amsa to babu matsala ai muna tareda zan kunna data n'a yanzu 'suka kashe wayar.


Dubansa yakai ga Aisha wacce take kuka mai tsuma rai.




Ke ! Ina fatan bawani abu ke miki ciwo ba.


Kai ta girgiza masa alamun babu.




Amma kuma dazun kincemin ke diyar SANI YARO ne.




Ogan nawa dan gidan ne.




Batareda ta kalle shi ba tace


Nasan da Wanda kake mgn


Yaya yusuf ne dan Allah karka hadamu vidéo call




Kacemasa nagudu nabar asibiti


Wlh nasan halin sa .




Tsaf zece zedau mataki' Wanda hakan n'a iya Sawa narasa mafi soyuwa agareni saurayina ,pls kataimaka mun.




Ajiyar zuciya yasauke tare daukar wayarsa vidéo call ya dannawa yusuf Kira.




Tareda kallon ta yana nazartan ta 'cikin halin ko inkula da zancen nata dan shi ganin wautan yai ,duk wannan tsoron Akan saurayin ta , takeyi bata tunanin makomar ta.




Yusuf ya daga vidéo call din ,yace yww dan hadani da ita '


Zan mata wasu yan tambayoyi.




Jin Haka Aisha tarufe fuskan ta 'da kafafuwar ta .




Kallon ta yake ta yi yace baiwar Allah dago fuskar ki .




Dago kanta tayi ta kalli wayar idanun ta cike da kwalla.




Raza yai ,nan take yaji tsayuwa ta gagareshi yana neman faduwa , dafa bangon office ,din sa yai.


Innalilahi wa'inna ilai rajun kawai yaketa maimaita wa ,cikin karfin hali yace indo.




Why why why yana ihu idanun sa da suka kada sukai jajir nan take , yace Ahmed ya kashe vidéo call din .




Direct yakira wayar ta amma shiru kasancewa c'en ta bar wayar.




Kiran wayar sojan yai tareda bashi umarnin bata waya.




Aisha Takara fashewa da kuka tace yaya yusuf kaga yanda rayuwa t'ai dani.




Daga cen bangaren idanun sa ,cike da kwalla yace indo


Suwaye suka aikata miki wannan ta'asan .




wlh so da dama idan zanbi hanyar nan saisun tareni wai suna sona Bana kulasu.


Rana ta karshe Sun tareni , yaya khalid ya kwace ni hannun su .


Harda mari yai ma Wanda yaimin fyaden shine yace wlh saiya dau fansa ,tana Kai karshen labari ,tace dan Allah yaya n'a kozan rokeka wani' Alfarma kamin .


Inajinki fadi , tace dan Allah banson maganar nan kowa yasani yazama sirrine tsakanina dakai ,


Jimm yai yace indo bazan Bari maganar nan tafita ba amma dole n'a hukunta su, akarshe umma dole tasani mahaifiyar ki ce.


Cikin gamsuwa da bayanan sa tace naji n'a yarda amma kacewa wannan mutumin yabar case din saika dawo.




Haba indo ai yanzu da dumi duminta zaai komai shima Ahmed ze yi iya bakin kokarin sa ,batareda anbari maganar ta fita ba ,nima bazanso aji mummunar lbr akanki ya zagaye duniya ba.




Mikawa Ahmed wayar .




Sojan n'a karban wayar sarawa yai kaman yana ganin sa yace sir wannan case din kanwar nan tamu babba ce namaka alkawari wlh saina ga bayansu .


Daurin rai da rai inhar suka shigo hannu


Yusuf da duk ya gigice cike da tashin hankali yace ok yanzu ka kaita gida abunda zakace musu


Shine hatsarin mota t'ai.


Nikuma zankira umman ta'


In sanar mata komi .daga nan suka kashe wayar.






***




Abba ne yakalli agogon hannun sa karfe tara n'a dare ,cike da damuwa yace wai kodai kidnapping din yarinyar nan 'akai Denn jeka kiramun dreve Aisha amma kaji dan iska t


Ya akai beje yadaukota babu kwakwaran uzurin daya hanashi.


Kowa zazzaune yake Sun zuba uban tagumi'




Fatima ,ce tamike tsaye jin wayar ta n'a ruri daga sama.




Ahanzarce ta isa dakin ta ,


Kafun ta daga Kiran ya katse




Sabuwar nomba tagani .


Da mamaki cike ta kallon lambar ,danna nombar t'ai ring daya Aka dauka.


Sallama t'ai tace wayene? Dagacen bangaren yace sunana Ahmed lawal inuwa ,ni jami'in tsaro ne ,fatima najin Haka aguje tasauko daga dakin ta tazo tasamu su, abba akasa sa wayarta t'asa hansfree , gabadaya dakin kowa ya kewaye ta .




Fatima tace inajinka lfy kuwa


Yace ina fatan da FATIMA KHALID YARO nake magana?




Kallon kallon sukai itada khalid ,tace eh nice .




Daman akwai wata yarinya AISHA SANI YARO jin Haka abba ya amshe wayar hannun ,fatima cikin daga murya da dakamishi tsawa '


Kai dan Allah katsyaa batamana lokaci ,kafadi menene yasamu yata ,ransa matukar abace dan shi arayuwar shi beson aita jan zance yafison Kai tsaye afadi abunda zaa fadi .




Yi hakuri alhaji daman Aisha ce dazun mota ya kade ta yanzu Haka muna asibiti 'yana mgn yana kallon Aisha dake dan murmushi agefensa .




Innalilahi wa'inna ilai rajun abba yashiga maimaitawa gayamin asibitin da kuke.




Eh muna asibitin SAUKI CLINIC dake kan titin zaria road.


Daki mai lamba 12.


Daga fadin hk ya katse wayar.




Aisha tace nagode' yallabai ka rufamin asiri kaima Allah yarufa maka naka, ameen ya amsa mata yace wannan nayine dan oga yusuf babu abunda ze nema aduniyan nan bazan mishi ,kakin jikina alfarmar shi ce.




Ki dan gyara kwanciyar ki , kinga canja miki asibiti n'ai nakawo ki asibitin mu n'a sojoji .




Nan ne kadai zan iya fadin komai Akan ki su yarda batareda amsamu matsala ba.




****




Ahanzarce suka fito ,sumayya motar Deen suka Shiga itada Inna Farida ,




Khalid n'a kokarin budewa fatima murfin mota , wayar sa tadau ruri ,batareda ya kalli me kiransa 'ba .


Ya daga yace wayene cikin sauri sauri


Mutumin yace nasan bazaka ganeni ba shekaru Sun Ja




Nine Wanda kaba kwangilar kashe ummu khalid sani yaro




Arazane Khalid ya kalli wayar '


Gaban sa ya tsanan ta bugawa.


Katse wayar yai batareda yabashi amsa ba.


Dan yalura idanun FATIMA n'a kansa ,




Lfy kuwa naga yanayin ka ya canja ?




Bakomai ,kibi motar Deen ni akwai inda zani.




Bangane akwai inda zaka ba.




Tsawa ya daka mata saida hanjin cikin ta suka kada 'tass taji saukan mari a fuskar ta zekara mata, yaji anrike masa hannu.


da mamaki kwance akan fuskar sa


yake kallon DEEN daya rike masa hannu, yarfe hannun sa yai daga cikin nasa ransa a matukar bace .




YACE YAUSHE RAINI YASHIGA TSAKANINA DAKAI ZAKA SHIGA MIN LAMARIN IYALINA.




MURMUSHI DEEN YAI YACE AZUCIYAR YACE AH KAJI WAI IYALINSA .




AMMA YAKESON YATURANI DAKIN TA .






abayyane cewa yai yi hakuri yaya khalid naga mace ce karfin ku ba dayaba .




fatima rikeda kuncin ta da zugin marin daya saka mata ciwon kai nan take.


sai hawaye ke kwaranya daga idanunta dasuka kada , sukai jajir .




shatin hannun sa kwnce akan fuskar ta .




abba da fada yace khalid ya haka metai maka .


lura da yanayin dan sa yai .




nan da nan ya karanci damuwa .


afukarsa umartan su yai da su,shiga mota .




dakyar inna farida ta lallaba FATIMA tabisu.




shiko khalid hanya daban yabi tareda kiran layin




mutumin na dagawa ya bushe da dariya nasan zaka kirani!


bawani abu nake bukata ba face milion dari kacal asirinka arufe.




sai asannan khalid yai murmushi wanda shikadai yasan manufarsa ya maimaita million dari .


watau kudin danabaka kana nufin ka cinyesu millon dari biyu.


buga sitiyarin motar sa d karfi yai azuciyar sa yana tunanin irin hukunci daze masa ,




Gayamin inda kake in sameka.




Kasameni a bakori wajen gidan makama layin karshe.






*






Su umma suna shigowa asibiti .


Reception suka nuna aka nuna musu daki mai lamba 12 .


da dan saurin su suka shiga dakin .




umma naganin kan ido rufe da bandeji alamun jini ajiki .


gabadaya saida suka rikice .


ko sake kallon inda sojan yake basuyi ba.




kuka mai tsuma rai umma tafara tarungumi aisha .


Abba yace inafatan kin danji sauki .


Gayamin daidai inda akai hatsarin , zansa aje amun bincike.


Deen rike da hannun aisha sai jero mata sannu yakeyi.


Sumaiyy da inna farida kama indo sukai dan gyara mata kwanciya tareda daura kan ta.


Akan filo ,atare suka jero mata sannu sunata nan nan da ita tareda bata kyakkyawa kula




Deen yace gsk yakamata assalame mu.


Sai asannan sukakai dubansu akan soja AHMED wanda tun shigowar su yake kallon su. musamman tsatsan kamanni da yaga umma takeyi da yusuf .




Sai satar kallon sumaiyya yake yi yayin da taketa banka masa harara ta kasan ido.


Wow sarki ya tabbata wanda ya


hallici , kyawawa gata fara sol ,kaman balarabiya hancin ta kaman biro da dan karamin bakin ta ,




amma dai wancen tafi su kyau yana kallon fatima azuciyar sai fadi yake ,anya ba matar aure bace ,tunani barkatai sukai ta


zuwa masa




abba yada fashi arazane yajuyo kaiko lfy kalau kuwa sai magana muke maka amma katafi duniyar tunani.




aidole yatafi duniyar tunani tunda ya tsaya kalle matan dake dakin .




soja yalura sumayya mgn take babu wanda zeji abunda ta fada.


caraf acikin kunnen sa.


yajita murmushi yai tareda mikewa tsaye yana fuskantar abba




zaku iya tafiya an sallame ta .


takiyaye kanta daga dokar da likita ya kindaya mata. Godiya abba yai masa bisa namijin kokarin sa akan aisha tareda karban lambar wayarsa.




zahradeen suka kama aisha ,wacce dakyar take takawa ,atare suka fito harabar asibitin da mamaki ,umma ke kallon tafiyar aisha yanda kasan wacce akaiwa kaciya.




***






khalid ne yafaka mota yafito tareda danna nombar mutumin yasanar masa da zuwansa.




babu bata lokaci sai gashi ya iso yana tafiya irin na gogan gu yan daba .




yallabai harka iso nasan zakazo dan dole.




murmushi yai yace tunda mala'ikan mutuwa yai kira ai dole na amsa .


inason insanar dakai acikin aikina babu jeka kadawo ,makudan kudaden dana baka inada labari akan inda ka kaisu ,wannan ma bashine damuwata ba .


kudin da kakeson inbaka .


kudin menene su??




dariya yasaki hade tattare hannayen sa waje daya .


khalid dolen ka kabani kudi .


sbd inada komai na hujja akanka.


daze bata martaban gidan ku .


inkuma sa akulleka.......dakata atsawace yakaraso gaban sa cikin bacin rai yana huci.


dan matsiyata zanbaka kudin kaban nanda sati biyu.




bataeda yajira amsar daze bashi ba yashige motar sa yabar wajen agujee yake sharara uban gudu zuciyar sa .


na kuna.




daukar wayar sa yai yakira fatima yai mata miss call yakai biyar tana gani bata dagawa.




tsaki yaja yace shasha ko uban wa zata nunawa zuciya yarinya da shegen shishigi.


kiran abba yai .




abba yace haba dana ina kaje ne .




abba kuna asibitin ne ganinan zuwa ga.






abba yace har mun dawo gida.


ganinan zuwa yace tareda nufar hanyar gidansu.


marin dayai wa fatima dazun yaringa tunowa yana jero tsaki kadan kikagani indai zance ga abinda zakiyi .


kitsya mun shishigi.




..........




labari ya karade jahohin nijeria diyar SANi yaro tayi hatsari.




khalid kan hanyar sa .


tashiga unguwar yan jaridu yagani sun mamaye kofar gidan .suna neman shiga ,bodyguard sun hana.




ya sallam ya furta waini yau wace bakar rana ce gabadayan ta babu alkhairi .




afusace yafito daga motarsa.


ya nufo su.


yai daidai da isowar yusuf dan tun lokacin da yaji kanwr sa.


akaiwa fyaden .




a sittin saba'in yabaro maiduguri .




kallon khaled yakeyi yanda yaketa zuba ruwan bala'i akan yan jaridu.




tsakii yaja yafara horn mai gadi da bodyguard sukaga shine.




wangale masa babban gate


sukai kusan atare suka shigo


gidan shida khalid .




ahanzarce yafito ze shige babban falon gidan nasu.




daka ta!




Cak yusuf yatsaya batareda ya waiga ba.




Me yakawoka gidan ubana.




Waigowa yai yace nikuma ai gidan uwata ne..kuma ko ubanka be isa yahanani shiga ba.


Tareda nunashi da dan tsaya.


Sannan kuma karka tunanin na kyale ku ne kaida ubanka.


Koda nabar gida to inanan akan baka ta.




Wlh wlh wlh ni yusuf nine zan sawa ubanka ankwa in jefashi cikin cell , kaikuma saide yarana su samaka sbd sawun giwa ya take na rakumi saide baban ka.




Khalid mutuwar tsaye yai yana bin bakin yusuf d kallo yanda yake zaro zantuka .




Boye tsoron sa yai yace.




Ai dan tsinuwa be ALBARKA SANNAN




DAKA TA.




Muryan umma ta katse masa zancen sa karasowa tai gaban sa.


Kamar zata cemasa wani abu.


Saita fasa hannun yusuf takama suka shige ciki.




Khalid rike da baki yake kallon su har suka bace masa da gani.




Compoud din gidan nasu ya nufa , zama yai abun duniya yai masa yawa.




Abba sai neman sa yake yana hangoshi ya nufoshi.




Khalid wai meke damunka ne,


Gabadaya sai aslow ka......

gayamin wata matsalar ce takara kunno kai.




khalid yaba abba labarin mutumin da wanda sukai da yusuf yanzu.


dafashi abba yai cikin son kwantar masa da hankali .




meze dameka akan kacalle dan yanemi kudade hannun ka hukunci yakamata mu dauka na batar dashi a doran kasa, kaban nan da yan kwanaki saide uwar shi ta haifi wani .


murmushi khaleed yai yana kallon abba zuciyar sa wasai.




shikuma yusuf nashi me sauki ne wlh badan agabana hassana ta haifeshi ba cewa zanyi ba dana bane.




ni abu daya zanwa yusuf shine wannan kakin da yake ikirarin sbd mu yasashi zansa acire masa kuma nan bada dadewa ba .


karyan shi wlh yaga bayan mu wannan fada ne tsakanin da da uban sa buga kirjin sa cike da takaici wlh yusuf saina maida rayuwar sa mara amfani nidai bazan iya kashe shi dan akwai kauna ta da da mahaifin sa.




khalid yace to meze hana ni kabani daman kashe shi yana cije labban sa.




Aa khalid ban aminta da zancen kitsa ba amma duk wani mugun aiki na yarje maka.




.....




umma rike da hannun yusuf suka shige ciki .


sallama yaiwa mutan gidan inda yasamu yazauna kusa da inna farida :




cikeda kewansu yace inason kasancewa daku .


yanayin rayuwa da yanda iska ke kada yahana.




inna farida tace to ai ka guje mu tun lokacin da akasamu sabani.


murmushi yai tareda son kawar da zancen yace,


amma sumaiyya kin rainani dayawa bazaki gaisheni ba.




turo baki tai tace inawuni


bazan amsa ba saida na roka.


dariya ta saki wanda yasa fararen hakoran ta suka bayyana.




hakdai sukai ta hira yaushe gamo.


kama kunnen deen yai ,ya murda da dan karfi.




ihu yasaka wayyo Allah umma kitaimakeni allurar ta motsa .


umma tace karka cirewa dana kunne




au niba dan ki bane aisaida nace kada yazo nigeria sarkin yawo yazo babu abunda yake sai zaman kashe wando.




wlh yaya ba zaman kashe wando nake ba


kwanan nan aure ma zanyi .






yusuf ya dara sossai yace to ai ni sumayya zaa bani tuwona maina ko inna farida?




Murmushi sukai dukan su .inna farida tace azuciyarta ALLAH yasa wannan furucin mala'iku su amsa da ameen..




Yusuf kama hannun ,umma yai


suka shiga dakin ta.




inda aisha ke kwance hawaye shar a idanunta abunda akaimata ne take tariyoshi cikin kunan rai ta furta kalmar ALLAH YA ISA.




SHIGOWAR SU YUSUF NE TAFARA GOGE HAWAYEN TA .DUKAR DA KANTA KASA TAI TANA WASA DA YATSUN HANNUN TA.




Yusuf tun shigowar sa dakin duk wata annurin sa ya dauke .


Kallon umma yai yace .




Aisha ba hatsari tai ba saide kiyi hakuri .




Fyade akai mata .




Innalillahi yusuf bangane fyade ba dan ALLAH IN WASA KAKEYI KADAINA .


DA DAN DAGA MURYA TAKE MAGANA HAWAYE SAI KWARANYA SUKE DAGA IDANUN TA.




HABA UMMA KINA DAGA MURYA SAI KOWA YAJI BANASON MAGANAR TAFITA DAGA DAKIN .




Kece kika haifi aisha ina tabbaci baki kaini shiga damuwa ,umma kaddara tariga fata , da ace zan iya tariya wlh dana goge bakin fentin da akaimata.




Wasu hawaye masu zafi yake fitar wa , nifa bansan hukuncin dazanyi musu dazesa inji nahuce ba.




Daurin rai da rai shine kawai mafita juyowa yai yana fuskantar kanwar shi hannun sa yadaura bisa kanta tareda tallafota ya rungume ta ,kuka suke tayi har ita umma babu me lallashin wani.


duk abunda suke fadi




fatima tadade labe kofar dakin su taji komai kuka tasaki mai fidda sauti.




kukan fatima daga waje yasa yusuf dakatar da kukan dayakeyi ahanzar ce yabude kofan.




ganin fatima yai adurkushe tana kuka .




kallon umma yai wannan wacece anan take mana kuka .




baiwar Allah daga ina yana nuna mata hannu.




dago kai tai suka kalli juna kawar da kanta gefe tai tana kokarin wajen.




fatima fatima FATIMA




DA DAN DAGA MURYA UMMA TA KIRATA .




JIKI ASANYAYE TAZO DAKIN TANA KALLON INDO WANI SABON KUKA YAZO MATA.




UMMA TA KALLI YUSUF


KAGA WANNAN ITACE AMARYAN KHALID.




KALLON KALLON SUKEWA JUNA SHIDA FATIMA YACE OK




INAWUNI ANTY NA




TA AMSA MASA ASANYAYE DAN BABU ANNURI AFUSKARTA .




umma tace teema nasan kinji duka firan mu dan Allah banson maganar tafita.




sbd kare mutuncin aisha a idanun duniya.




haba umma ni me rufawa indo asiri ce ballatana kaddara ce tana kan kowa kama hannun aisha tai cikin kulawa yi hakuri ni fatima zan tayaki adua Allah ya bayyanasu ,sannan saita mike tana fuskanta umma da yusuf kasiyo mata maganin wanke mara yanada matukar amfani .




musamman virgin yawan cin wayanda akewa fyade da ciki ake samun su.






murmushi umma tai yabawa da hankalin fatima tace to yusuf kadai ji maza kaje yanzu dan Allah kasiyo.




yaji dadin bayanan ta da nutsuwar ta azuciyar sa sai fadi yake .




wannan yarinyar ai matar manya mutane ce masu hankali ba irin saunan mijin ta abayyane godiya yai mata kai tsaye yafito harabar gidan .






khalid ya hango shida uban nasa.




ahankali yake taku yana kokarin bude murfin motar sa.






abba yace .




ji mana




waigowa yai yace inawuni abu khaleed .




amsa masa yai tareda tsareshi da idanu yace .




wai yusuf waye gatan ka akasar nan .




Allah shine gatana.




dafashi yai cikin ransa daya soma baci.




nina haifeka




abu khaleed kaima muhammad ya haifeka harya mutu beji dadin ka ba.




kamatudin tudan .


baka tunanin ramuw....






stop abba yace atsawace.




yusuf uban ka .nace ubanka kai uban da ya haifi ubanka.






yusuf dariya yai irin na narainin sens yace .




zagin harda muhammad ayau kaji irinta nan shiyas...








khaleed a kufule ya iso yace abba wai meyasa kk damuwa da dan daka cire a jerin yayan ka.




kama hannu abba yai tareda jefawa yusuf mugun kallo tsaki yaja .




yusuf da ko ajikin sa .


abunda khaleed yai.


ficewar sa yai dan gabatar da uzurin sa.


****************




yau satin aisha daya inda tasamu cikakkiyar kulawa daga umma da fatima saida sukai gasa ta duk abunda sukasan yadace aimata nan da nan sukeyi .




yusuf yakoma bakin aikin sa tunda yadau duk bayanan dayakeso dauka daga bakin aisha .




khaleed dauke da nusy ahannun sa ahankali yake saukowa daga kan step .


direct dinner table ya zarce yasamu kowa ya halatta .


abunda fatima kemasa agidan tun ranar da ya mareta sai hau ha wa yakeyi.


kujerar ta itada deen kusa da juna .




barka da safiyya yace musu .abba yace yww dana ka iso .




Eh abba na iso ,umma ta kalli fatima da deen yanda suketa dariya suna hira cikin nishadi.


azuciyar ta sai fadi take Allah ya shiryaku .


ran khaleed ya gama baci dan abunda yatsana mutum ya nuna besan da zaman sa ba.




karfin hali yai yace fatima zubo min abinci tai kaman bataji ba saida ya maimaita na uku.




fatima tace indo pls zubawa yayan ki naga kunfi kusa ,aisha ta tashi ta zubamai .




deen ya kware ahanzarce fatima tadebo masa ruwa tabashi tana jero masa sannun tareda masa fifita .




Deen yai fuskar shagwaba yace anty nidai bankoshi ba.




am sorry bari kara maka janyo wamers tai tareda da zuba masa arish da plaintain ..




take khalid yaji abinci dayakeci yafita aransa tareda ajiye cokalin yana goge bakinsa da tissu .


ya mike yai hanyar dakin sa.


inna farida tace khaleed bakawani ci abinci ba.




agajarce ya amsa mata nakoshi ne.




itako fatima sai da dariya ke cin ta ganin abun khaleed keciki .




yana isa dakin isa sai safa da marwa yakeyi .


wayarsa yadauko ya danna lambar fatima jin karar wayar yai adakin ta .


watau ma suna cen ita da deen tabar waya adaki tsuki yaja.




sake fitowa again yai da saman bene yana kallon kasar falon gidan su kowa ya watse fatima da deeen kadai ne zaune.




inuwar sa tahango alamun yana kallon su .




aikuwa fillow tadauke tana jifan deen shiyama yana jefa mata sunata guje guje kaman kana nan yara.




afusace yasauko kasa :




deen na ganin sa aguje ya je yakamashi pls yaya boye ni karta sameni.




tsawar daya dakawa deen yasa hantar cikin su kadawa .banason shashan ci saikace wasu yan kananan yara .




kama hannun fatima yai suka haura sama direct dakin ta yakai ta yai jifa da ita kan gado .


yana ta huci sama sama .




ai kicemin maza kika fara bi bansani ba abunda kike yanunan haka.




kishirya gobe zamuje honeey mood .


kallon sa take nifa babu






inda zani indai deen baze je ba....






😨😨😨




ni ikiilima adam




nace fatima da deen suna wasa da rayuwar su.


sai dai inda deen zamuje.


hade rai yace kinga teema nasan fushi kike dan ban baki hakuri ba , nifa a al'adata ban iya neman yafiya amma inason ki sauke rawanin tsiyar dake kanki dan muzauna lafiya .




sannan kishirya yau zamuje gidan naku kiyi masu sallama .




tabe baki tai tana duban sa tare turo jajayen labban ta gaba .




oho dai kaikasani daman nace maka kaban hakuri , rike abunka .


nuna masa hanyar kofa da yatsar ta kaga hanyar fita ficemin daga daki.




ni babu inda zani tsaye tabar shi tana girgiza kugu tana wakar nan.




wakar mawakin nan .




dama dake nafara haduwa dani aure tuntuni. rabin raina .




tashige toilet tana rangwada khalid mutuwar tsaye yayi .dafa kansa yai lissafi ya kwance mishi to ita wannan yarinyar bata samu tarbiyya agidan nasu bane.




niko nace kaji manya kamar shidin tarbiyya gareshi.






haka yabar dakin direct company su


ya nufa.




wani tafassashen kamfani mai hawan bene sunkai bakwai gabadaya tayis ne jikin bango ma'aikatar inda.




jikin saman kofar shiga ma'aikatan an rubuta .




YARO ENTREPRISE NG LTD




Horn yai nan take me gadi ya wangale babban gate din daman tareda bodyguard yafito gida.




motoci uku ajere gabadaya maaikatan duk kowa yabar aikin sa akai layi ana jiran fitowar oga khalid.




ahankali yasauke kafafun sa yana gyra wuyar rigar gilashin dake kusa dashi yadauka yasa .




yana fitowa kowa ya dukai dakai ana gaishe shi barka barka da zuwa ranka yadade cikinsu harda Manager auwal , mahaifin fatima .




ya karaso gaban khalid tareda amsa takardun Hannun sa khalid yai gaba suna biye dashi abaya ma'aikatan.


yana shiga office din sa su bodyguard suka tsaya bakin kofa , ma'aikata suka shiga .


.zaune yake kan kujerar sa ta alfarma yanata juya wa kallon yakai ga manager yace bismillah zauna .




anatse tattare da kamalarsa yazauna yace sir yagida ya iyali .




amsa yace da lfy lau , akwai metin da zaai gobe ma da wani time ne?




karfe goma ne yabasa amsa ataikace .




inason asoke wannan metin sainan da sati daya .manager auwal yace amma yallabai wannan zaman da zamuyi yanada matukar muhimanci .


dan zamu gana ne da kamfanin jiragen ruwa daga zaman zekawo cikas a aikin mu.




kallon sa khalid yake yana nazartan shi sannan yace to anjima kasameni agida saimu tattauna .bayan shi babu wani abu ko yace sai tsare tsare da aikin da akai ga chief account ta zeyi maka lissafi yana fadin hk ya juya yabar office zuwa nasa office din.




zama yai yana juya zancen dasukai da khalid .barin wani tunani yai yakira yakira yar sa awaya tana daga kiran tai karya muryan ta tana masa shagwa daddy wai khalid tafiya yakeson muyi nikuma banson nayi nesa daku.




murmushi yai haba yata me aciki amma begayamin zeyi tafiya dan akwai metin da zamuyi gobe cewa yai adaga kenan wannan shine dalilin sa.




eh inaga hkne amma daddy meze hana ka koma harkan kasuwancin ka kaga khalid surukin ka ne banajin dadin yana saka aiki pls kaji .




abba yai dariya yace ai teema nakusa barin aiki kamfanin yaro




nawa kamfanin inacen ana aikin sa ankusa gamawa sunanki nasa.




FATI GLOBAL




wow daddy kace zankara fasowa gari ,dariya tai cikin murna tace Allah yakara arziki daga hk sukai sallama.




karfe daya daidai khalid yabaro ma'aikata direct gida ya nufa.




akofar shigowa ya jiyo muryan fatima da deen suna fira suna hango inuwar khalid sai sukafara yiwa juna kallo irin ta masoya yai daidai da karasowar falon dan atunanin sa basu gansa ba.




tsawa ya daka musu ransa abace yakara so wajen ku wani irin dakikai ne .


Deen yace afuwan yaya bara naje nai wanka lokacin sallah jumaa ta gabato tareda barin wajen.




fatima ta tsare mijin da da idanu tana maimaita kalmar dakikai ah lallai zata nuna masa dakikan ci, danma nayi sauki sanda nake gaban iyayena nawuce hk tana maganar zuci tsaki taja tace sorry ban lura da kashigoba amsar kayan hannun sa tai hanyar dakin sa yana biye da ita abaya.




hotunan dake makale jikin bangon dakin sa, ta zubawa idanu.


sun kai 11 a jere zuwa tai tana kare wa hotunan kallo .


khalid wayannan suwayene ? matan dana aura yabata amsa ataikace.




hankalin ta yai mugun tashi take taji zufa yana keto mata , kallonsa takara yi ,cikin son tabbatar da abunda kunnanta yaji.




kara maimaita mata yai yace fatima kaddara tace banson ace yaro dani nai aure aure haka duk rasa su nai badan raina yaso ba nan take yafara hawaye .




fatima komai kike so arayuwar duniyan nan zan baki ,kudi matsayi ina iya baki kudin da ahlin ki bazasuyi talauci ba ,amma karki gujeni nasani kina mamakin duk sanda kika shigo daki na ,kina iske narigaki barci .




saboda bazan iya kusantar ki bazaki iya daukan cikina ba.




ina nufin...