KAI KA JAWA KANKA

Ka ka jawa kanka Chapter 7

by @kyautadagaallah10

Kai ka jawa kanka 7

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah

Dayan yace wllh kaji tsoron Allah ishaq Kai kadai ne ' kai abunka babu 'ruwan mu saida muka hanaka kaki ji.

Ishaq din yace yallabai wallahi har..........saukan mari yaji Wanda yasa jin sa yadauke nawani second .

Naga kunason Ku rainin mun hankali 'amma idan nasa Aka casaku 'zansan wayanda ke wajen akai fyaden .

Cikin kuka' dukansu 'sukace wlh yallabai 'dukan mu 'muna wajen'

Amma banda wannan dan wlh tsautsayine da rashin jin maganar iyaye irin namu ya jamishi .

Yusuf yakalli 'wanda akace masa beda laifin yace 'kai ya sunan ka.

Cikin muryansa dake cike da tsoro 'da zufa da ya jikemai jiki yace sunana. Abdullahi ranka yadade .

Mike tsaye yusuf yace masa tareda Bada umarnin afita dashi akaishi office dinsa yajira sa.

Nagode Allah yasaka da Alkhairi hakika Kai adalin ma'aikacine kanayin aikin ka 'tsakani da Allah

Yafita cikin hanzari tareda bin sojojin .

Yusuf kallon su yake yace kunsan koni wanene.

Sukace a' a 

Ya dafa kansa yace 

Sunana Zaki !!

Dan Haka kun shigo hannuna kafun kotu ta yanke muku hunci ' zan muku nawa hukuncin ' 

Zazzare idanu suka 'soma yi.

Suna ranka yadade wlh sharrin shedan ne bazamu saké ba.

Beko bi takansu ba yafita tareda Bada umarnin a Kona wuta mai zafin gaske ko wanne a manna masa daidai mararsa hade hukuncin duka mai tsanani jin abunda yusuf yafada suka fara kuka mai tsuma rai '

Ishaq yace wlh nasan mutuwa zamuyi anan kanajin irin abunda yafada 'najawa kaina wajen ramuwa 'gashi ina girban abunda nashuka .

Begama rufe baki ba' kawai yaji 'saukan bulala akansu 'ihu suke da Dukan karfin su' anacikin Haka sai ga wukake nan sunyi jajir awuta .

Sun shigo dashi dan cika umarni' 

Niko kyauta daga Allah nace ban iya kallon wannan azabar tayi tsauri 

Amma kuma aisune suka jawa kansu.

.......

Yusuf nashiga office dinsa zama yayi kan kujerar da ke lilo dashi.

Coffe Aka kawo masa da zafi zafin sa 'kasancewa bai karya ba.

Yana Shan Coffe yana kallon abdullahi dake zaune kansa aduke.

Ahmad n'a tsaye 'alamun chattin yake murmushi nagani kwance Akan fuskar sa.

Gyaran murya yusuf yai Wanda yasa hankulan su yadawo kansa.

Kai meye hadinka da wayannan yan iskan 'da Aka kamaku tare 'ya tsaresa da idanu masu kwarjini.

cikin kuka yace wallahi rashin abun da zanci yasa nake binsu 'sune suke taimaka min kasancewa n'a rayu ne nikadai.

Kallon kallon yusuf sukai shida Ahmed tareda suka furta bamu gane ka rayu Kai kadai ba.

Eh to nidai sunana abdullahi amma wlh bansan iyayena ba' tun ina karami Haka nataso 'saide inje inyi bara in samu abunda zanci ' agarin kano nataso ' daga baya ne ' naji ina shaawar garin katsina shine dalilin dawowata.

Kallon sa 'yusuf yake yana nazartan kalaman sa.

Cikeda son jin komai yace.

To akanon wajen wa kazauna ko ince wace unguwa ne ka rabe kake zaune'. Cikin kuka' yace wlh a gwammaja tagwayen gida nan nake zama ' in dare yai 'ina kwana kofar shagon sadii mai cajin waya.

Cikeda gamsuwa da bayanan sa 'yusuf yasoma rubuce rubuce dago Kai yayi yana kallon sa .

Yace abdullahi kozaka iyayin aikin soja.

Wlh yallabai zan iya koba komai zan tsare mutunci n'a 'sannan aikin taimako ne.

Ok amma inkaga iyayenka zaka iya shaidasu kuwa duk da an dade .

Kwarai kuwa 'zangane su dan wlh inaganin kamanni mahaifiya ta a idanuna da mahaifina 'duk da anyi shekaru barkatai.

Cikeda da gamsuwa yusuf yace ok zan ajiye ka gidana kafun nan zamusan abunyi .

Godiya yai tayiwa yusuf hawaye shar a idanun sa.

*

***************************

Zazzare idanu khalid yai nan take mood dinsa ya canza.

Ahankali deen yajuyo tareda fuskantar ta 'jiki a sanyaye yace antina ya jikin naki dafatan babu inda ke miki ciwo'?

Kallon khalid t'ai taga idanun sa 'akansu 'murmushi ta sakalo 'tace deen Dina dasauki .

Dafatan dai Kaci abinci 

Yanzu zanje in ci bejira 'amsarta ba yafice cikin hanzari cike da mamakin 'sabon salon fatima.

Khalid da yakai wuya 'yace ke wallahi anyi sakarya banda asibiti'muke ba ,Dana babballaki 'kaman jira take yazo nan .

Harara tafara watsa masa' tareda kallon tsana 'tace akwai sakarai daya wuce ka Khalid 'nusarin namiji ' mata 'maza kawai tana n'a murguda masa baki.

Ni ai bansan Kai dakiki bane sai yau 'kuma wallahi rayuwa no control akanka daga yau .

Dan Haka kafice min daga daki 'juyawa yai ransa abace haryakai kofar fita!

Tace daka ta!

Cak yatsaya be waigo ba.

Wallahi ni fatima auwal saina koya maka hankali 'saina kawo karshen ta'addancin ka' bazan nemi saki daga wajen ka, ba awannan muran da muke ciki 'dan ina gudun bacin Ran mahaifina 'amma badan Haka ba 'dana take igiyar auren ka' shasha kawai gooo ta fadi cikin tsawa .

Aisha dake rike da Kayan brek itada sumayya 'sake baki sukai 'ganin Khalid fuskarsa babu digon rahma 'rabashi sukai 'suka shige dakin .

Inda yaja kansa yai gaba 'dakyar yake taka kafafun sa.

Umma ta hango wucewar sa 'rike baki sukai itada Inna farida' waiko yaron nan aljanu gareshi ne 'daga zuwa duba 'mara lafiya sai yafi to ahaka.

Inna Farida tace 'kila yanayin dayaga matarsa ba lfy ne shine ya firgita shi .

Balaraba tace aikuwa yana iya zama Haka .

.....

Aisha da sumayya Saïda suka taimaka mata t'ai brosh da makilin da suka siyo mata a asibitin ' tareda bata tea tasha kadan.

Murmushi ta sakar 'musu tana mejin kaunar su' azuciyar ta 'sai fadi take 'ina ma ace ba Khalid n'a aura ba ' Dana huta da matsala.

Wayar ta 'tasoma ring Aisha ta miko mata' ganin daddy ne 'ke Kira dasauri ta daga tareda jingina da bangon dakin.

Daddy yace ina kika shiga ne 'tun jiya sai neman layin ki'nake bakya dagawa ' shiru t'ai n'a wasu yan dakiku rasa amsar da zata bashi yasa tace.

Daddy ai bamu gaisa ba 'daga c'en bangaren yace yi hakuri yata damuwar Dana shiga Akan rashin samun ki 'shiya kawo Haka.

Gaisawa sukai 'tace ina mommy tana lafiya yace mata ,c'en sukai shiru ' daddy yace fatima akwai Abunda ke damun ki ne?

Aisha fisge wayar hannun fatima t'ai 'tace daddy ina wuni 'ya amsa da lfykalau wacece?

Sunana Aisha kanwar Khalid ' wallahi anti Fatima bata lafiya tun jiya muke asibiti' a sume Aka kawo ta 'amma dasauki gani n'ai ,bé kamata ta boye muku ba 'amatsayin Ku 'na iyayen ta.

Innalilahi wa'inna ilai rajun dadyn yashiga furtawa 'mommy dake gefen sa 'ta razana ince dai ba wani mummunan Abu bane yasamu yar mu?

Daddy be bata amsaba 'maida hankali kan wayar dayake yi 'yai yace wani asibitin kuke ne?

Aisha tabashi 'amsa da *Sauki*

Ok gamunan zuwa yace tareda katse Kiran.

Mommy fuskar ta 'cike da kwalla tace ni baka gayamin abunda yasa mu 'fatima ba.

Jimm yai cikin tausasa murya dan ya kwantar mata da hankali' yace kema fa, kinsan in Macé nada ciki toba ita babu lfy.sai ranar da akace ta haihu .

Cewa Akai ,suma t'ai amma dasauki 'tunda kinji harnayi waya da ita 'kira asabe ta hada mata hadaddan girki Mara nauyi Haka 'muje mata dashi.

Ajiyar zuciya 'mommy tasauke tace wlh bakaga yanda narikice ba ' yata guda daya tilo in rasa ta 'kamar yanda n rasa yayan ta.

Daddy yace inshAllah'muna tareda ita 'har jikokin mu ,saimun gani ' murmushi t'ai tareda tashi 'nidai bara inje kitchen inyi wa asabe 'magana 'pls kashirya dawuri , kafun mugama 'bara inkira kakarta 'insanar mata .

Mommy n'a shiga kitchen ta iske asabe na wanke wanke ' kallon ta t'ai cikin sanyin murya 'tareda bata umarnin t'ai maza ta hada mata délicieux girki 'fatima zaa kaiwa.

Dakin ta 'takoma tareda laluban inda ta ajiye wayar ta.

Tana ganin wayar.

Kira ta dannawa mahaifiyar ta wayar t'ai ring harta yanke baa daga ba.

Oh Allah nasan yanzu Haka wayar tana daki 'ita tana waje karasa me amfanin waya ahannun wannan tsohuwar.

Kara kiranta t'ai 'cikin saa ta daga ' haba Kaka sai aita kiranki baki dagawa 

Dagacen bangaren tace oh ni uwar laifi shikenan sai inta yawo da waya hannuna 'kamar wata Mara abunyi .

Uhmm mommy tace 'daman nakira insanar miki fatima ba lafiya tana asibiti ' 

Salati tasoma ganinan zuwa gidan Ku 'yanzu wlh inkika tafi bakijirani ba' Zaki sani ehee .

Tom saikin zo daga hk ta katse wayar.

Fatima ta kalli aisha cikin yanayin dake nuna bataji dadin fadamusu batada lafiya ba' tace indo daddy n'a 'nada hawan jini 'yanasa Abu aransa 'shiyasa banso 'sukaji ba.

Sumayya tace lallai 'anti indai Hakane kinfi mu 'gaskiya inshAllah bazamu kara ba 'kinji Antin mu 'tareda rike kunnen su 'itada aisha'.

Fatima batasan sanda dariya ya subuce mata ba' cikin sanyin murya tace bakuyi laifi ba 'kannena.

'.............

Yusuf n'a barin office direct gida 'ya nufa shida Ahmad da abdullahi .

Ahanzarce suka shigo 'kasancewa lokacin sallah ya gaba to 'ko takan su rukayya da suke kallo basu bi ba .

Yusuf direct dakin sa 'yanufa alwala yadauro 'tareda canza Kaya zuwa jallabiya 'baki sai shenin yake Kai daga gani kasan mai tsada ne.

Aisha tace'rukayya tashi muje muyi 'sallah kinga ko magana basuyi mana ba.

Rukayya tace nidai kije 'yau ina fashin sallah .

Ahakadai su yusuf sukaje masallaci ' suka dawo gidan .

Taku daya yai yakaraso kusa dasu 'kallon rukayya yai 'yace ina pepper' danace ki rubutamin inda kika sanni 'kallon ta yake babu ko kiftawa.

Lura da kallon da yake mata 'yasa ta dukar da kanta ' cikin nutsuwar ta 'tace ni bansamu papper ba.

Amma Kai hakuri mun gama hada kayan 'mu 'zamu wuce . Nasan ka 'ta daliin Aisha kanwar ka.

Saboda a lokacin n'a taba zuwa gidan Ku 'inda n'a iske Kana fada 'da abban Ku 'kace Kai zaka bar mishi gida,umma n'a kuka tana rike maka hannu ' jikina yai sanyi 'na tambayi Aisha meya hadaku da abba 'budan bakin ta 'sai tace Kai gaskiya ne bakason atake .

Tun lokacin data fadamin hk naji kashiga Raina'da Wasa Wasa tun ina daure wa 'harnakasa 'gidan mu 'kowa yasan da Haka ' dan mahaifiya ta 'zagina take da yar wahala.

Nazo maiduguri ne badan inkwana ba 'saidan in gayamaka sakon zuciyata in tafi 'koda muka zo ganin ka yai mana wahala sai jiya.

Ajiyar zuciya yasauke 'kana ahankali yake kallon kwayar idanun ta 'dasuka cika da kwalla '

Yace nagode da kauna.

Amma inason indan muku nasiha ' a matsayin Ku ' n'a yaya mata.

Barin gidan iyayen Ku 'dakuke yi da karyan unguwa ' har kusamu kuje wajen saurayi ba Abu bane mekyau 'dayawa wajen yawo akai musu fyade 'wasu akai kidnapping dinsu 'wasu kuma Aka kashe su. wasu akai zina dasu .

Inda wani mummunar Abu yafaru daku 'kuka mutu 'kuna tunanin Allah ze kalli hujjar kune'?

Gabadayan su suka girgiza Kai alamun 'a'a

To wallahi ina me tabbatar muku 'wuta zaku tafi direct '

N'a farko kunyi karya .

Nabiyu kunje neman saurayi.

Dan Haka Ku gaggauta gyara halayenku ' da duk me hali irin naku 'ya kiyaye kada yafada fushin ubangiji.

Naji bukatar ki 'rukayya 

Zanbaki nombar wayata 'zan amshi taki 'inhar kin isa zamu ringa waya.

Gabadaya suka zube kasa 'sunata masa godiya.

Yusuf yaba' Ahmed umarni su wuce katsina taredasu.

.....

Kaka 'ce agaba cikin saurin ta wai zata Riga 'su Shiga dakin da Aka kwantar da fatima .

Mommy da dadyy sai kallon ikon Allah suke.

Deen n'a ganinsu yai musu jagora yaimusu har dakin da fatima take.

Kaka 'cikin kuka ta rungumi fatima ina fatan babu inda ke miki ciwo' ko

Murmushi take mata 'taki magana.

Daddy yace haba Kaka 'kidan barta taga iyayen ta ,mana.

Iyeeeh 'kaka ta kwabe baki ' Kaci gidan ka' auwal nace Kaci gidan auwal .

Au ni daga sama n'a fado Kenan .

Banda dariya babu abunda kowa keyi adakin.

Daddy da mommy 'cikeda tausayawa sukaita nan nan da fatima '

Likita ne yashigo ya duba fatima yace 'naga jikin 'dasauki .

Ga wayannan magunguna zaku siye mata a asibiti'kuna iya tafiya gida inkun gama .

Cikeda jin dadi 'suka fara harhada Kayan su.

Kaka tace da 'ita zaa tafi gidan su 'fatiman.

....

KHALID ne yana kallon abba dake waya .

Abba yace *murhu* nabaka nan da zuwa gobe 'duk inda kacalle yake akashe mun shi 'kisa ta wulakanci

Abdullahi n'a fita office din ' Ahmed ya fuskanci yusuf kansa akasa yace yallabai' kozan iya fita Domin yunwa nakeji .

Ok saika dawo katafi tareda abdullahi duk abunda zakaci 'kuci tare .

Ok ranka yadade angama tareda barin office din

Wayar yusuf yafara ring kallon fuskar wayar yai'. Ganin Aisha yasashi daga wayar cikin hanzari.

Kanwata ina kwana dafatan kowa nagida n'a lfy' daga c'en bangaren tace kalau ne yaya 'saide muna asibiti tun jiya 'matar Khalid babu lafiya 'dan a sume muka kaita asibiti har yanzu bata farfado ba.

Zumbur yusuf yatashi tsaye tareda rike kugun sa' yana cije labbansa ' gayamin Aisha poisson Aka bata ne 'kokodai Ankara tafka n'a baya ne.

Aisha tace yaya bangane n'a baya ba 'likitoci sundai ce zuciyar ta bugu ne.

Ok ke bazaki gane abunda nake nufi ba' bani umma in tana kusa.

Mikawa umma wayar t'ai 'bayan Sun gaisa ne 'yusuf yace ' umma nasan kinsan komai 'kece kika haifi Khalid dan ....

Dakata umma tace cikin tsawa bangane nice n'a haifi Khalid' ba , wannan kalamin Aisha taimin jiya 'kunason Ku hade mun Kai.

Yi hakuri umma nifa ba laifin ki nake gani ba 'amma fa kuskure daya kike tafkawa umma 'sanya tsoron bayin Allah nan acikin zuciyar ki' shine kesa komai n'a tabar barewa ' 

Dan jimm umma t'ai 'cikin sanyi da hawaye dake silalowa ta idanunta 'tace 'yusuf ai ciwon fatima beda alaka da wancen matsalar dan Haka yanzu ba lokacin yin ta , bane yaushe zaka dawo ne 'dan fa inason a saida maganar aurenka kaida sumayya' Aisha a satin nan zaa zo neman auren ta 'tareda sa rana lokaci daya.

Gab gab gab Haka gaban sa ya dunga bugawa 'umma bangane aurena da sumayya yarinyar da magana bata iyaba 'zaku aura min?

To idan muka aura maka ita 'aisai ka koya mata magana .

Wallahi yusuf kafita idanuna kuma auren sumayya babu fashi sai anyi 'in Khalid yafi karfina 'kaide bakafi karfina ba.

Cikin sanyi yace Allah yasa Haka yafi zama alkhairi bejira cewan ta 'ya katse wayar.

Itako 'umma kallon wayar take da murmushi kwance a fuskarta.

Dago Kai dazatai ne taga khalid rike da hannun nusy sunshigo abba nabiye dasu abaya.

Balaraba ta hango dauke da brek cikin dan madaidanci kwando' .

Inakwana khalid yaimusu suka amsa fuska asake banda umma.

Inna Farida tace haba Khalid tun juya saiyanzu zaka zo'?

Soso kansa yasoma yi yana tunanin irin karyan daze mata' 

Yi hakuri Inna Farida motata ce babu mai 'ban lura ba Saïda nazo fita.

Allah yakyauta tace mishi dan tasan karya ce.

Abba ya kalli 'umma da kanta ke aduke yace hassana dago Kai tayi ta kalleshi ta amsa da naam.

Ina dakin da Aka kwantar da fatima'kuma ta farfado kuwa'?

Gaskiya bata farfado ba 'amma sunce kowani Time zata iya farkawa' ga dakin c'en 'ta nuna mai da yatsaya.

Balaraba a ladabce ta duka ta gaishe su' suka amsa da yawwa ya aiki ya kokari lfylau ta amsa musu.

Ga brek fast dinku 'tareda kokarin fiddo su cikin kwandon dan ta zuba musu.

Deen ne yashigo da alama tunda yaje sallah asuba ,barci barawo yai awon gaba dashi 'dan cikin Yan kwanakin nan 'beda sukuni 'baya samun barci .

A nutse tattare da kamalarsa yakaraso inda suke jiki a sanyaye 'caraf idanun sa ya'sauka kan abba da khalid.

Aladabce yagaida su'.suka amsa da lfylau.

Deen yace 'jiya munta jiran zuwan ka 'shiru dan har likita ya tambayi ina mijin nata?

Khalid yace saikace me?

Saina cemusu nine yabashi amsa batareda yakawo komi aransa ba.

Ran khalid yagama baci dannewa yai 'yace ai babu matsala tunda Kai kanina ne.

Kuzo muje dakin da Aka kwantar da fatima .

Dukansu mikewa sukai dan bin bayansu'babban burinsu bewuce ace ta Farka ba.

Suna isa dakin zaune suka iske ta.

Ta lumshe idanunta 'kamar me barci 'tana tuna abunda yafaru ajiya bakin ciki 'da danasanin auren khalid ne duk ya lullube ta' tanajin haushin kanta , kin sauraron salamatu da batai ba sanda taso fada mata gaskiya.

Tsayuwar mutane akanta ne' yasata dago Kai ,caraf idanun ta 'yasauka Akan 'aisha da 'umma dasu sumayya .

Umma takaraso gabanta cikeda da damuwa tace sannu yata yajin naki ' dasauki tabata amsa 'cikin sanyin murya

Inna Farida 'da su aisha da sumayya sunata jero mata sannu 'murmushi ta sakar musu alamun taji sauki .

Aisha tace antina yakamata 'ace kinci abinci koda tea ne 'kidan sha dan Allah pls karkice aa tana marairaice fuska.

Fatima ta gyada mata Kai alamun ta kawo .

Ahanzarce sukabar dakin 'itada 'sumayya dan hada mata brek .

Suna fita su Khalid suka samu damar shigowa tareda abba 'da deen.

Inna Farida naganin Haka 'tafita tabasu waje.

Tabar umma 

Abba yace FATIMA ya jikin ki 'lfy lau ne tabashi amsa .

Caraf idanun ta ya'sauka Akan khalid da Deen.

Ajiyar zuciya tasauke' umma mikewa t'ai ni zanje inyi brek 'abba yace to mu fita tare sauri nake zanje office.

Atare suka fita yaiwa fatima Allah yakara Sauki.

Khalid gaban fatima yace mata ta 'ya jikin naki fa' shiru kakeji banda karar fanka dake juyawa.

Kara maimaita abunda yace yai nanma banza t'ai dashi.

Deen ' da tsoro yagama kamashi cikin fargaban kar ta hada dashi harya juya zefita.

Yaji muryan ta 'ya Doki dodon kunnen sa.

Tace haba 'deen Dina ina zakaje ne 'ko ya jiki bakamin ba 

Zazzare idanu ka

Nan zan tsaya akwai n'a anjima inshAllah inde banda aiki

Tsawa yaji fatima ta dakamai nan take taci kwalar rigarsa tana ihu , deen amana ta zaka ci , ina matar yayar ,Kana neman keta min haddi 'idanun ta Sun kada sunyi jazir kaman wuta , Allah yasa isa tsakanina dakai ,.kuma wallahi saina Kai wajen Khalid yanzu 'tana kokarin jan sa 'yana Jan cikin sa.

Wallahi anti Fatima ki gafarceni banda niyyar akaita alfasha dake .

Tasss yaji saukan maruka guda uku lokaci daya , rike da kuncin sa 'ya dawo kalan tausayi .

Pls anti Fatima kowani irin hukunci kidauka akaina, amma banyarda kikaini wajen Khalid ba.

Shege dan iska, maci amana ,tanata Dukan sa ,da Dukan karfin ta.

Ganin bashine mafita ba 'tafita aguje a dakin ta kulle shi aciki , direct dakin khalid ta nufa.

Karar buga kofa da karfi ya farkar da khalid a razane ' waye ne ya furta cikin muryan me barci.

Daga cen wajen kofar ta amsa da fatima ce kabude kofa cikin ihu take magana .

Ahankali yasauko daga kan gadon sa, wutar dakin sa' ya kunna ' yana kallon agogon dakin ' karfe shibiyu n'a dare' tareda jan tsaki yace ' ita kuma wannan me takeso a daren nan.

Karar buga kofar yasa shi zira takalmin 'cikin dan hanzari yaje yabude kofar.

Kallon fatima yake da mamaki yanda hawaye shar a idanunta 'lfy meke faruwa.

Kasa , magana t'ai saidai ta kama hannun sa 'taringa jansa ,shikuma yana biye da ita abaya.

Fadamin meke faruwa ne 'wife 'kaide muje tabashi amsa tana sheshekar kuka mai tsuma rai.

Suna shiga dakin , Khalid yakai dubansa ,ga deen suna kallon juna.

Fatima tasaki hannun Khalid tareda zuwa gaban deen ' cikin muryan wacce Aka cuta 'tace Khalid kaga kanin sa ,fyade yakeson yamun inaga bayau bane yafara zuwamin ba , Allah ne yatona asirin sa.

Khalid yai shiru sai kallon deen yake 'deen da tuni kansa ke akasa banda hawaye babu abunda yakeyi.

Saké Kai Duban ta 'ga khalid t'ai tace ina gayamaka abunda kanin ka ,ke shirin aikatamin amma Kai shiru ka Gaza magana.

Buden bakin Khalid 'yace deen kafita kabamu waje nace cikin fada.

Sakaka fatima ke kallon sa 'hawayen ta 'yabushe kace yafita?

Eh nace yafita 'tareda rike hannun ta'.

Deen sanda 'sanda yafita dakin cike da tashin hankali da baa samishi rana.

Khalid yace pls fatima wannan abun dayafaru kidauke shi kuskure ne.

Tasss yaji saukan mari Wanda yasa yake ganin taurari ' ni kika Mara .

Eh kaina Mara 'inba dan iska ba 'ina matsayin matar ka 'inkama kwarto ,adakin ka.

Amma saika cemin wai yafita 'batareda kanunamai fushin ka ba.

Khalid tashi daga kan gadon fatima yai 'cikin daga murya yace .

Eh fatima Haka nace.

Abunda yasa banwa deen magana ba 'nine n'a turo da sanina da amince wa ta yazo dakin ki.

Wani shock jikin Fatima yai jin kalaman Khalid tana kallon da magana.

Cikin kuka' tace khalid meyasa Kai Haka.

Nayi hakane dan nasan bazan taba iya kusantar ki ba 'ina gudun kada sha'awa ta sa kifara 'fita neman namiji awaje 'amma banyi da niyar cutar wa Saidan in taimaka miki .

Cikin kukan dayaci karfin ta 'tace meyasa ka aureni Khalid .

Eh n'a aure ki ne saboda inason ki,inason ganin ki ,cikin gida n'a.

Fatima dake tsaye 'zuciya ta dibeta nan take ta yanke jiki ta fadi a sume.

Innalilahi wa'inna ilai rajun khalid yashiga furtawa yana jijjigata yana Kiran sunan ta' amma shiru yakeji'. Frij Din ta yabude ya dauko ruwan Goran mai sanyi yashafa mata 'stil dai shiru.

Tsoro yakamashi kada fa 'yarinyar nan ta mutu 'ne.

Aguje yasauko daga kan matakalan step yayo kasa.

Tsakiyar falo yasoma ihu yana fadin kowa n'a gidan nan yafito 'fatima ta suma .

Aguje kaman suna farke 'kowa yafito da Kayan barci ajikin , kowa ya tsassare shi da idanu sukai ina take ne ?.

Tana dakin ta yabasu amsa.

Dukansu matan gidan dakin fatima suka nufa aguje har suna tuntube .

Abba da alhaji nura, da khalid ne tsaye kowanne rike da kugun sa '.

Alh nura yace Khalid wai meyasa méta ne Haka .

Nima kawai Haka naganta a sume yabashi amsa 'tareda rike hannun abba , sukai dakin abba dan tattaunawa.

Umma rike da fatima Akan kafafun ta 'tace Inna Farida yarinyar nan Anya tana numfashi kuwa?

Eh tana numfashi 'karmu tsaya bata lokaci .

Aisha je Kira muna deen yazo yadauke mu 'yakaimu asibiti.

Aguje Aisha t'ai dakin deen ,ga mamakin ta 'ganin sa' t'ai yanata kuka.

Aisha tace yaya deen meke damun ka ne.

Idanun sa da suka kada kaman wuta 'yace 'indo wani abune yafadamun a idanuna .

Cemishi sannu t'ai 'tace yaya kazo dakin anti Fatima tana c'en a sume asibiti zaka kaimu.

Tashin hankali da baa samishi rana 'a kidime yabaro dakin yariga Aisha fita.

Deen n'a kallon fatima hawaye cike a idanun sa ya 'ciccibeta direct sai cikin motar.

Su umma suka take masa' baya.

Alh nura dake tsaye shikadai yabi su 'abaya yace to ai baa gayawa mijin ta ba.

Gashi yana dakin abban sa.

Deeen yace pls alh nura ka sanar musu mun tafi asibiti (Sauki) n'a docta Hassan.

Da to.ya amsa musu tareda musu fatan sauka lafiya .

Khalid adakin abba 'tagumi yai .

Abba yace wai khalid me yakawo suma acikin daren nan.

Bawa abba abunda yafaru yai cike da damuwa a fuskar sa.

Tikashi abba yafurta .

Ya kabari ta kwabe Maka 'hakane baa taba samun mistake ba 'sai akanta.

Wai wannan wace irin yarinya ce mai tsaurin idanu.

Khalid rike da kansa dake sarawa yace abba nidai bansan me 'mafita ba.

Abba ya dafashi yi hakuri.dana Bani nan dazuwa gobe zamu san yanda zaa yi inshAllah bazata baka matsala ba.

Tashi muje kasan tana daki

Fitowa sukai 'suka iske alh nura waya yake alamun yayi nisa awayar .

ganin su 'yasa yamike tsaye tareda cewa Bari dasafe zamuyi waya.

Murmushi ya sakalo yace 'aisun tafi asibiti sunce asanaar muku.

Khalid yace wani asibitin Kenan .

Yabashi amsa (Sauki.)

Ok Abba tunda dare yayi mubari dasafe munje kasan banson abunda zetaba lafiya ta.

Cikin gamsuwa da Haka abba ,da khalid sukai wa alh nura sallama 'saida safe 'kowa yanufi 'sashin sa.

......

Deen ,tuki yake 360 amma sai gani yake kaman besauri a hanzarce ya d'Anna hanci motarsa a' asibiti kasancewa me gadi yaji Horn dinsa ya wangale masa Gate.

Umergency umergency Haka yaketa furtawa cikin daga 'murya 'aguje Dukan ma'aikata asibiti suka taho da gado Aka daura fatima.

Su umma n'a biye dasu abaya ,akai urgemency block da ita.

Su 'umma 'inna Farida 'deen 'sumayya' Aisha babu abunda suke furtawa sai innalilahi wa'inna ilai rajun zuciyoyin su 'cike da rauni......

......

Aisha da rukayya' tabe baki sukai suna kallon juna' waishi wannan mutumin dan rainin hankali yatafi yabarmu 'anan ko ga ruwa be ,cemana ba. Céwar aisha.

Rukayya tace ' kiyi hakuri kila wani.uzurin gareshi aciki' hararta Aisha tayi tace wlh kedai kincika sauna wlh ace baki ganin laifin sa' saina nawa tana turo baki.

Yusuf dake saukowa daga sama 'ahankali yake taka matakalan step din .

Ya iso falon TV bangon dakin ya tsurawa idanu 'dasuke kallo 'rike bakin sa yai yace ' to su wayannan sakarkarun harda min karanbani 'azuci yake magana.

Asace yake kallon su' sai yanzu yake karewa rukayya kallo atsanake ' farace tass irin kyakyawa 'ga hanci kaman biro' bakinta dan daidai ,tsaki yaja yace to inci uban me da wannan agwagwan.

Kallon Aisha yake yace itakuma wannan yaukin da shegen tsiwa inama zan buge bakin Nata.

Yana ta maganar zuci.

Fuskantar su yai' cikin hade rai yace 'ga daki c'en yana nuna musu dakin kasa 'cen zaku kwana 'ku tabbatar kun share adaren nan 'kun goge kun wanke toilet .

Aisha sai kallon sa take 'zatai masifa kwarjin sa yarufe mata baki.

Rukayya tace inshAllah amma dan Allah yunwa 'muke ji.

Ai bakusanar dani.zuwan Ku 'ba sannan ni Bana girki 'in akwai wacce ta iya ga kitchen saikuje Ku dafa amma Ku tabbatar kuna gamawa Ku gyara wajen dan kuku n'a ba bawan Ku , bane.

Yana gama fadin Haka yai ficewar sa 'yakoma sama .

Aisha da rukayya sai kallon juna suke' ruky tace uhmmm kedai kinga mu hakura dacin 'abincin nan' saikace mayu girki adaren nan.

Zodai muje kitchen din 'suna Shiga sukaga bred 'da madar peak 'komai n'a buka ta' wow sukace yanda suke mamakin ganin komai' a kitchen din.

Shayi suka hada batareda Sun fito ba anan suka tsya Shan Kayan su.

..........

Acen asibiti sai Safa da marwa sukeyi 'basuda gindin zama.

Likita ne yafito daga umergency aguje suka nufe shi ' .

Likita yaya dai ' kayi shiru kaki magana.

Likita yace ina mijin ta yake.

Cikin zazzare idanu 'sai yanzu suka lura ashe khalid be biyosu ba.

Kunyi shiru 'sauri nake kuban amsa?

Deeen yace nine mijin ta.

Biyoni likita yace tareda zuwa office dinsa 'deen ya take masa baya.

Umma tace 'to baga irinta nan ace matarka n'a asibiti bakazo ba, saboda Allah abunda Khalid yakeyi yana kyautawa kuwa' yanzu da babu deen Kenan da ya zamuyi ,cikin bacin rai take magana, Aisha ta dafata yi hakuri 'umma kefa kika haifi Khalid 'kinfi kowa sanin halin danki 'kokuwa? tana kallon Inna Farida da sumayya.

Eh wlh tafi mu sanin halin sa Inna Farida ,da sumayya suka amsa mata.

Tokingani umma 'ki kyaleshi da halin sa'tunda ga yaya deen yatafi amatsayin sa.

Mudai jira abunda zaa fadamai ' 

Allah yasa muji alkhairi Dukan su,suka fada.

....

Deen gaban likita ,tsaye kikam 'likita ya kalleshi cikin tausasa murya 'yace zauna mana .

Zama yai yana fuskantar shi 'yace likita yimun bayani ,me ke samun ta?

Likita ya fuskance shi yace wannan yarinyar zuciyar ta ,ta kumbura 'kuma inhar ta buga akwai babban matsala ' ya amatsayin ta ,na matar ka, baka bata cikakkiyar kulawa da kwantar mata da hankali .

Yanzu dai 'mun samu mun shawo kan matsalar zaa bata gado' saide zuwa gobe 'dasafe zaku iya zuwa ganin ta ,dan yanzu sossai take bukatar hutu .

Akwai magunguna da zamu daurata akai inhar zamu sallame ta 'zata ringa Shan su zai taimaka 'mata .

Amma kuma duk da hk dan Allah aguji abunda ze bata mata rai.

Deen ya Mike tareda mikawa docto hannu 'sukai musabaha 'nagode sossai docto zaa kiyaye tareda barin offi ce din.

Jiki babu kwari 'yazo yasamu su 'umma da suka kagu 'suji bayanin likita ,nan ya zayyana musu komai .

Hankalin su 'yai matukar tashi 'aisha tace to akwai Abunda akewa anti Fatima n'a rashin jin dadi ne ,da bamu sani ba ?

Inna Farida tace 'keko Aisha ai ciki badan tuwo kadai akayishi ba,kila tanada damuwa ne 'fatan mu 'dai Allah yabata lafiya.

Da ameen suka amsa.

Daki suka nema Aka basu inda babu kowa dan anan zasu kwana.

Umma t'ai juyi Akan deen yaje gida dasafe yadawo amma fur yaki .

Washe gari.

Khalid 'da abba' da alh nura Sun fito massalaci 'kai tsaye gida 'suka ' cike da kosawa khalid yace .

Abba Allah yayi dare gari yawaye 'kaga yanzu ne daidai lokacin dazan je 'asibiti.

Gaskiya ne Dana ai bazan so 'akan wata ba' kafita tsakar dare ba' Alh nura yace abba bangane wata ba' mekake nufi?

Naga ai fatima tawuce acemata wata 'matar shi ta sunnah 'murmushi yai Wanda shikadai yasan ma'anar sa yana ayyana aransa 'kodai dagaske dai Khalid baya iya kusantar matan shi ne' inhaka yasan fatima abukace take 'zesan hanyar dazebi.

Abba ya katse masa tunani tareda cewa kaiko nura ban hanaka samun baki cikin hidimar gidana ba.

Tsaki khalid yaja yana mai hararan sa ' 

Afuwan abba namanta ne 'shiyasa n'a soma baki n'a 'ina ganin kamar yadace inyi magana ne.

Dan Allah gafara c'en 'khalid yace rai abace 'kai kazamin rayuwar da kakeyi Kana tunanin bansaniba ' wlh nura a tafin hannuna 'kake .

Abu nakarshe wlh inka kuskura kasake neman bata mana sunan gidan mu' uhmmm zaka kwashi tsummakaran ka 'kabar gidan nan.

Sadaf ! sadaf ! sadaf Haka alh nura yaja jikin shi yafice 'yabar su 'dan ya lura ,suna son su Kira masa ruwa.

Nusy ce ke saukowa daga matakalan step tana kuka.

Khalid tsareta da idanu yai ,danshi harga Allah ya mance da ita.

Kamo hannun ta yai suka zauna shida abba ' yace haba baby n'a meya sameki?

Cikin kuka' tace banga mama ba.

Kallon juna 'sukai shida abba ' oh nusy mama bata lfy ankaita asibiti jiya 'kinji zata dawo anjima ' kara fashewa da kuka t'ai 'tace nidai daddy ka kaini wajen ta.

Abba yace ' kuje tare man khalid kaga makaranta tabari gobe taje.

Cikin gamsuwa da hakan Khalid ya kwadawa Balaraba Kira 'tareda bata umarnin taje ta shirya nusy 'sannan ta hada brek zekai asibiti a ladabce ta amsa da to.

Tareda juyawa danyin abunda akasata.

.........

Shamsu ne gaban makaranta su 'nusy shiru bega zuwan ta' alamun Sun nuna yau batazoba' cikeda damuwa 'yace gun mai gadin makarantar.

Yace ranka ya dade barka da aiki 'amsa masa yai da barkadai.

Dan Allah tambaya nake' jikar sani yaro' tazo makaranta yau kuwa ?

Me gadi yace 'no batazoba '

Nagode yabashi amsa tareda juyawa .

........ 

Yusuf 'shida Ahmad Sun gama shirin su 'tsaf nazuwa aiki ' ahanzarce suka sauko kasa.

Ganin 'su rukayya zaune sunacin indomi da Kwaï yaji Kayan miya sai baza kamshi yake.

Lumshe idanun sa 'yai tareda kallon su 'a fakaice .

Ganin sa yasa dukansu suka rusuna 'suna inkwana ' lfykalau ya basu amsa 'ciki 'ciki.

Ahmad ya kwabe baki 'ni bazaku gaisheni ba yana kallon su' rukayya tace sorry ai harda Kai gaisuwan nan' banyarda yacemusu.

Yusuf ganin Sun cika shi da surutu gashi sauri yake 'sbd zeje yahada bayanan dazeyi Akan wayanda sukaiwa kanwarsa fyade .

Kallon su 'yai n'a minti daya 'cikin yanayin da beson magana da mata' yace wata jaha kuka fito.

Aisha tace katsina' da mamaki yake kallon su ya maimaita 'katsina 'sukace eh nan muka mufito.

Ina kuka sanni har kuka biyoni nan garin.

Zazzare idanu 'suka soma yi 'suna inda inda ' ganin zasu bata masa lokaci yace 'inason Ku dauki papper Ku rubuta inda kuka sanni 'zan dawo da azahar saiku ban . Sannan Ahmed zekoma anjima ze tattara mun Ku'yawuce daku katsina tunda c'en ya nufa.

Batareda yajira cewar su ba' yafice daga gidan Ahmed ya take masa baya.

Rukayya kinajin abunda ya fada kuwa wai ya tattara mu ' saikace Kayan wanki.

Uhmmm kasa magana rukayya t'ai 'tace ni Abunda yaban mamaki shine wai mu rubuta inda muka sanshi a pepper' inyazo abashi ya karanta.

Wannan rainin yai yawa cikin kuka' rukayya ke magana wlh Allah yasani inason shi Aisha duk abunda yakeyi bedameni ba' kuma dole yai mana kallon marasa kamun Kai 'tunda muka baro garin mu' muka biyo shi.

Amma wlh kema kinsan inada tarbiyyya Aisha 'badan munyi karya zamuje biki kauye bane ,da wlh bazaa barmu 'mu tafi ba.

Aisha jikinta yai sanyi 'ta dafa rukayya yi hakuri inshAllah inamiki fatan nasara akansa.rungume juna sukai .

....

Yusuf n'a isa Barack duka ma'aikatan subar Abunda suke 'suka jeru tareda Sara masa ' barka da isowa sir.

Yaww barka dai y amsa musu tareda kallon su' atsanake ' cikin tausasa murya yace 'bakin da sukazo da me laifi daga katsina inafatan Sun juya ' kuma kun musu tarba me kyau irin ta ma'aikata.

Eh yallabai anyi abunda yadace 'wani daga cikin su yabashi amsa a ladabce.

Ok good .

Kowa yakoma kan aikin sa.

Ina me tsaron cell yake 'kansa aduke yace gani ranka yadade'muje ka kaini inda Aka kawo masu 'laifin jiya da to ya masa tareda yin gaba.

Yusuf n'a biye dashi abaya yana tafiya kaman Zaki a dawa.

Bude masa cell din 'akai yashiga daga ciki sauran sojojin suna tsaye suna jiran umarnin ogan nasu dan har jikin su 'yafara rawa allurar su 'ta soja ta motsa.

 Yusuf cike da takunsa da fuskar sa tamau yashiga ciki' suna ganin sa 'hankalin su 'yatashi dan Sun shaida shi jiya.

Cikin kakkausar murya mai cikeda tsawa yace wanene acikin Ku 'yaiwa Aisha sani yaro fyade .

Cikin kasa da murya yace nine amma da taimakon su.

Dayan yace wllh kaji tsoron Allah ishaq Kai kadai ne 'kai abunka babu 'ruwan saida muka hanaka kaki ji.

Ishaq din yace yallabai wallahi har''''saukan mari yaji Wanda yasa jin sa yadauko nawani second .

Naga kunason Ku rainin mun hankali 'amma idan nasa Aka casaku 'zansan wayanda ke wajen akai fyaden .

Cikin kuka' dukansu 'sukace wlh yallabai 'dukan mu 'muna wajen'

Amma banda wannan dan wlh tsautsayine da rashin jin maganar iyaye irin namu ya jamishi .

Yusuf yakalli 'wanda akace masa beda laifin yace 'kai ya sunan ka.

Cikin muryansa dake cike da tsoro 'da zufa da ya jikemai jiki yace sunana. Abdullahi ranka yadade .

Mike tsaye yusuf yace masa tareda Bada umarnin afita dashi akaishi office dinsa yajira sa.

Nagode Allah yasaka da Alkhairi hakika Kai adalin ma'aikacine kanayin aikin ka 'tsakani da Allah

Yafita cikin hanzari tareda bin sojojin .

Yusuf kallon su yake yace kunsan koni wanene.

Sukace aa 

Ya dafa kansa yace 

Sunana Zaki !!

Dan Haka kun shigo hannuna kafun kotu ta yanke muku hunci ' zan muku nawa hukuncin ' 

Zazzare idanu suka 'soma yi.

Suna ranka yadade wlh sharrin shedan ne bazamu saké ba.

Beko bi takansu ba yafita tareda Bada umarnin a Kona wuta mai zafin gaske ko wanne a manna masa daidai mararsa hade hukuncin duka mai tsanani jin abunda yusuf yafada suka fara kuka mai tsuma rai '

Ishaq yace wlh nasan mutuwa zamuyi anan kanajin irin abunda yafada 'najawa kaina wajen ramuwa 'gashi ina girban abunda nashuka .

Begama rufe baki ba' kawai yaji 'saukan bulala akansu 'ihu suke da Dukan karfin su' anacikin Haka sai ga wukake nan sunyi jajir awuta .

Sun shigo dashi dan cika umarni' 

Niko kyauta daga Allah nace ban iya kallon wannan azabar tayi tsauri 

Amma kuma aisune suka jawa kansu.

.......

Yusuf nashiga office dinsa ' Maza yai kan kujerar da ke lilo dashi.

Coffe Aka kawo masa da zafi zafin sa 'kasancewa bai karya ba.

Yana Shan Coffe yana kallon abdullahi dake zaune kansa aduke.

Ahmad n'a tsaye 'alamun chattin yake murmushi nagani kwance Akan fuskar sa.

Gyaran murya yusuf yai Wanda yasa hankulan su yadawo kansa.

Kai meye hadinka da wayannan yan iskan 'da Aka kamaku tare 'cikin kuka yace wallahi rashin abun da zanci yasa nake binsu 'sune suke taimaka min kasancewa n'a rayu ne nikadai.

Kallon kallon yusuf sukai shida Ahmed tareda suka furta bamu gane ka rayu Kai kadai ba.

Eh to nidai sunana abdullahi amma wlh bansan iyayena ba' tun ina karami Haka nataso 'saide inje inyi bara in samu abunda zanci ' agarin kano nataso ' daga baya ne ' naji ina shaawar garin katsina shine dalilin dawowata.

Kallon sa 'yusuf yake yana nazartan kalaman sa.

Cikeda son jin komai yace.

To akanon wajen wa kazauna ko ince wace unguwa ne ka rabe kake zaune'. Cikin kuka' yace wlh a gwammaja tagwayen gida nan nake zama ' in dare yai 'inkwana kofar shagon sadii mai cajin waya.

Cikeda gamsuwa da bayanan sa 'yusuf yasoma rubuce rubuce dago Kai yai ya kallesa .

Yace abdullahi kozaka iyayin aikin soja.

Wlh yallabai zan iya koba komai zan tsare mutunci n'a 'sannan aikin taimako ne.

Ok amma inkaga iyayenka zaka iya shaidasu kuwa duk da an dade .

Kwarai kuwa 'zangane su dan wlh inaganin kamanni mahaifiya ta a idanuna da mahaifina 'duk da anyi shekaru barkatai.

Cikeda da gamsuwa yusuf yace ok zan ajiye ka gidana kafun nan zamusan abunyi .

Godiya yai tayiwa yusuf hawaye shar a idanun sa.

Abdullahi n'a fita office din ' Ahmed ya fuskanci yusuf kansa akasa yace yallabai' kozan iya fita Domin yunwa nakeji .

Ok saika dawo katafi tareda abdullahi duk abunda zakaci 'kuci tare .

Ok ranka yadade angama tareda barin office din

Wayar yusuf yafara ring kallon fuskar wayar yai'. Ganin Aisha yasashi daga wayar cikin hanzari.

Kanwata ina kwana dafatan kowa nagida n'a lfy' daga c'en bangaren tace kalau ne yaya 'saide muna asibiti tun jiya 'matar Khalid babu lafiya 'dan a sume muka kaita asibiti har yanzu bata farfado ba.

Zumbur yusuf yatashi tsaye tareda rike kugun sa' yana cije labbansa ' gayamin Aisha poisson Aka bata ne 'kokodai Ankara tafka n'a baya ne.

Aisha tace yaya bangane n'a baya ba 'likitoci sundai ce zuciyar ta bugu ne.

Ok ke bazaki gane abunda nake nufi ba' bani umma in tana kusa.

Mikawa umma wayar t'ai 'bayan Sun gaisa ne 'yusuf yace ' umma nasan kinsan komai 'kece kika haifi Khalid dan ....

Dakata umma tace cikin tsawa bangane nice n'a haifi Khalid' ba , wannan kalamin Aisha taimin jiya 'kunason Ku hade mun Kai.

Yi hakuri umma nifa ba laifin ki nake gani ba 'amma fa kuskure daya kike tafkawa umma 'sanya tsoron bayin Allah nan acikin zuciyar ki' shine kesa komai n'a tabar barewa ' 

Dan jimm umma t'ai 'cikin sanyi da hawaye dake silalowa ta idanunta 'tace 'yusuf ai ciwon fatima beda alaka da wancen matsalar dan Haka yanzu ba lokacin yin ta , bane yaushe zaka dawo ne 'dan fa inason a saida maganar aurenka kaida sumayya' Aisha a satin nan zaa zo neman auren ta 'tareda sa rana lokaci daya.

Gab gab gab Haka gaban sa ya dunga bugawa 'umma bangane aurena da sumayya yarinyar da magana bata iyaba 'zaku aura min?

To idan muka aura maka ita 'aisai ka koya mata magana .

Wallahi yusuf kafita idanuna kuma auren sumayya babu fashi sai anyi 'in Khalid yafi karfina 'kaide bakafi karfina ba.

Cikin sanyi yace Allah yasa Haka yafi zama alkhairi bejira cewan ta 'ya katse wayar.

Itako 'umma kallon wayar take da murmushi kwance a fuskarta.

Dago Kai dazatai ne taga khalid rike da hannun nusy sunshigo abba nabiye dasu abaya.

Balaraba ta hango dauke da brek cikin dan madaidanci kwando' .

Inakwana khalid yaimusu suka amsa fuska asake banda umma.

Inna Farida tace haba Khalid tun juya saiyanzu zaka zo'?

Soso kansa yasoma yi yana tunanin irin karyan daze mata' 

Yi hakuri Inna Farida motata ce babu mai 'ban lura ba Saïda nazo fita.

Allah yakyauta tace mishi dan tasan karya ce.

Abba ya kalli 'umma da kanta ke aduke yace hassana dago Kai tayi ta kalleshi ta amsa da naam.

Ina dakin da Aka kwantar da fatima'kuma ta farfado kuwa'?

Gaskiya bata farfado ba 'amma sunce kowani Time zata iya farkawa' ga dakin c'en 'ta nuna mai da yatsaya.

Balaraba a ladabce ta duka ta gaishe su' suka amsa da yawwa ya aiki ya kokari lfylau ta amsa musu.

Ga brek fast dinku 'tareda kokarin fiddo su cikin kwandon dan ta zuba musu.

Deen ne yashigo da alama tunda yaje sallah asuba ,barci barawo yai awon gaba dashi 'dan cikin Yan kwanakin nan 'beda sukuni 'baya samun barci .

A nutse tattare da kamalarsa yakaraso inda suke jiki a sanyaye 'caraf idanun sa ya'sauka kan abba da khalid.

Aladabce yagaida su'.suka amsa da lfylau.

Deen yace 'jiya munta jiran zuwan ka 'shiru dan har likita ya tambayi ina mijin nata?

Khalid yace saikace me?

Saina cemusu nine yabashi amsa batareda yakawo komi aransa ba.

Ran khalid yagama baci dannewa yai 'yace ai babu matsala tunda Kai kanina ne.

Kuzo muje dakin da Aka kwantar da fatima .

Dukansu mikewa sukai dan bin bayansu'babban burinsu bewuce ace ta Farka ba.

Suna isa dakin zaune suka iske ta.

Ta lumshe idanunta 'kamar me barci 'tana tuna abunda yafaru ajiya bakin ciki 'da danasanin auren khalid ne duk ya lullube ta' tanajin haushin kanta , kin sauraron salamatu da batai ba sanda taso fada mata gaskiya.

Tsayuwar mutane akanta ne' yasata dago Kai ,caraf idanun ta 'yasauka Akan 'aisha da 'umma dasu sumayya .

Umma takaraso gabanta cikeda da damuwa tace sannu yata yajin naki ' dasauki tabata amsa 'cikin sanyin murya

Inna Farida 'da su aisha da sumayya sunata jero mata sannu 'murmushi ta sakar musu alamun taji sauki .

Aisha tace antina yakamata 'ace kinci abinci koda tea ne 'kidan sha dan Allah pls karkice aa tana marairaice fuska.

Fatima ta gyada mata Kai alamun ta kawo .

Ahanzarce sukabar dakin 'itada 'sumayya dan hada mata brek .

Suna fita su Khalid suka samu damar shigowa tareda abba 'da deen.

Inna Farida naganin Haka 'tafita tabasu waje.

Tabar umma 

Abba yace FATIMA ya jikin ki 'lfy lau ne tabashi amsa .

Caraf idanun ta ya'sauka Akan khalid da Deen.

Ajiyar zuciya tasauke' umma mikewa t'ai ni zanje inyi brek 'abba yace to mu fita tare sauri nake zanje office.

Atare suka fita yaiwa fatima Allah yakara Sauki.

Khalid gaban fatima yace mata ta 'ya jikin naki fa' shiru kakeji banda karar fanka dake juyawa.

Kara maimaita abunda yace yai nanma banza t'ai dashi.

Deen ' da tsoro yagama kamashi cikin fargaban kar ta hada dashi harya juya zefita.

Yaji muryan ta 'ya Doki dodon kunnen sa.

Tace haba 'deen Dina ina zakaje ne 'ko ya jiki bakamin ba

Zazzare idanu ka

Zazzare idanu khalid yai nan take mood dinsa ya canza.

Ahankali deen yajuyo tareda fuskantar ta 'jiki a sanyaye yace antina ya jikin naki dafatan babu inda ke miki ciwo'?

Kallon khalid t'ai taga idanun sa 'akansu 'murmushi ta sakalo 'tace deen Dina dasauki .

Dafatan dai Kaci abinci

Yanzu zanje in ci bejira 'amsarta ba yafice cikin hanzari cike da mamakin 'sabon salon fatima.

Khalid da yakai wuya 'yace ke wallahi anyi sakarya banda asibiti'muke ba ,Dana babballaki 'kaman jira take yazo nan .

Harara tafara watsa masa' tareda kallon tsana 'tace akwai sakarai daya wuce kakuwa Khalid 'nusarin namiji ' mata 'maza kawai tana n'a murguda masa baki.

Ni ai bansan Kai dakiki bane sai yau 'kuma wallahi rayuwa no control akanka daga yau .

Dan Haka kafice min daga daki 'juyawa yai ransa abace haryakai kofar fita!

Tace daka ta!

Cak yatsaya be waigo ba.

Wallahi ni fatima auwal saina koya maka hankali 'saina kawo karshen ta'addancin ka' bazan nemi saki daga wajen ka, ba awannan muran da muke ciki 'dan ina gudun bacin Ran mahaifina 'amma badan Haka ba 'dana take igiyar auren ka' shasha kawai gooo ta fadi cikin tsawa .

Aisha dake rike da Kayan brek itada sumayya 'sake baki sukai 'ganin Khalid fuskarsa babu digon rahma 'rabashi sukai 'suka shige dakin .

Inda yaja kansa yai gaba 'dakyar yake taka kafafun sa.

Umma ta hango wucewar sa 'rike baki sukai itada Inna farida' waiko yaron nan aljanu gareshi ne 'daga zuwa duba 'mara lafiya sai yafi to ahaka.

Inna Farida tace 'kila yanayin dayaga matarsa ba lfy ne shine ya firgita shi .

Balaraba tace aikuwa yana iya zama Haka .

.....

Aisha da sumayya Saïda suka taimaka mata t'ai brosh da makilin da suka siyo mata a asibitin ' tareda bata tea tasha kadan.

Murmushi ta sakar 'musu tana mejin kaunar su' azuciyar ta 'sai fadi take 'ina ma ace ba Khalid n'a aura ba ' Dana huta da matsala.

Wayar ta 'tasoma ring Aisha ta miko mata' ganin daddy ne 'ke Kira dasauri ta daga tareda jingina da bangon dakin.

Daddy yace ina kika shiga ne 'tun jiya sai neman layin ki'nake bakya dagawa ' shiru t'ai n'a wasu yan dakiku rasa amsar da zata bashi yasa tace.

Daddy ai bamu gaisa ba 'daga c'en bangaren yace yi hakuri yata damuwar Dana shiga Akan rashin samun ki 'shiya kawo Haka.

Gaisawa sukai 'tace ina mommy tana lafiya yace mata ,c'en sukai shiru ' daddy yace fatima akwai Abunda ke damun ki ne?

Aisha fisge wayar hannun fatima t'ai 'tace daddy ina wuni 'ya amsa da lfykalau wacece?

Sunana Aisha kanwar Khalid ' wallahi anti Fatima bata lafiya tun jiya muke asibiti' a sume Aka kawo ta 'amma dasauki gani n'ai ,bé kamata ta boye muku ba 'amatsayin Ku 'na iyayen ta.

Innalilahi wa'inna ilai rajun dadyn yashiga furtawa 'mommy dake gefen sa 'ta razana ince dai ba wani mummunan Abu bane yasamu yar mu?

Daddy be bata amsaba 'maida hankali kan wayar dayake yi 'yai yace wani asibitin kuke ne?

Aisha tabashi 'amsa da *Sauki*

Ok gamunan zuwa yace tareda katse Kiran.

Mommy fuskar ta 'cike da kwalla tace ni baka gayamin abunda yasa mu 'fatima ba.

Jimm yai cikin tausasa murya dan ya kwantar mata da hankali' yace kema fa, kinsan in Macé nada ciki toba ita babu lfy.sai ranar da akace ta haihu .

Cewa Akai ,suma t'ai amma dasauki 'tunda kinji harnayi waya da ita 'kira asabe ta hada mata hadaddan girki Mara nauyi Haka 'muje mata dashi.

Ajiyar zuciya 'mommy tasauke tace wlh bakaga yanda narikice ba ' yata guda daya tilo in rasa ta 'kamar yanda n rasa yayan ta.

Daddy yace inshAllah'muna tareda ita 'har jikokin mu ,saimun gani ' murmushi t'ai tareda tashi 'nidai bara inje kitchen inyi wa asabe 'magana 'pls kashirya dawuri , kafun mugama 'bara inkira kakarta 'insanar mata .

Mommy n'a shiga kitchen ta iske asabe na wanke wanke ' kallon ta t'ai cikin sanyin murya 'tareda bata umarnin t'ai maza ta hada mata délicieux girki 'fatima zaa kaiwa.

Dakin ta 'takoma tareda laluban inda ta ajiye wayar ta.

Tana ganin wayar.

Kira ta dannawa mahaifiyar ta wayar t'ai ring harta yanke baa daga ba.

Oh Allah nasan yanzu Haka wayar tana daki 'ita tana waje karasa me amfanin waya ahannun wannan tsohuwar.

Kara kiranta t'ai 'cikin saa ta daga ' haba Kaka sai aita kiranki baki dagawa

Dagacen bangaren tace oh ni uwar laifi shikenan sai inta yawo da waya hannuna 'kamar wata Mara abunyi .

Uhmm mommy tace 'daman nakira insanar miki fatima ba lafiya tana asibiti '

Salati tasoma ganinan zuwa gidan Ku 'yanzu wlh inkika tafi bakijirani ba' Zaki sani ehee .

Tom saikin zo daga hk ta katse wayar.

Fatima ta kalli aisha cikin yanayin dake nuna bataji dadin fadamusu batada lafiya ba' tace indo daddy n'a 'nada hawan jini 'yanasa Abu aransa 'shiyasa banso 'sukaji ba.

Sumayya tace lallai 'anti indai Hakane kinfi mu 'gaskiya inshAllah bazamu kara ba 'kinji Antin mu 'tareda rike kunnen su 'itada aisha'.

Fatima batasan sanda dariya ya subuce mata ba' cikin sanyin murya tace bakuyi laifi ba 'kannena.

'.............

Yusuf n'a barin office direct gida 'ya nufa shida Ahmad da abdullahi .

Ahanzarce suka shigo 'kasancewa lokacin sallah ya gaba to 'ko takan su rukayya da suke kallo basu bi ba .

Yusuf direct dakin sa 'yanufa alwala yadauro 'tareda canza Kaya zuwa jallabiya 'baki sai shenin yake Kai daga gani kasan mai tsada ne.

Aisha tace'rukayya tashi muje muyi 'sallah kinga ko magana basuyi mana ba.

Rukayya tace nidai kije 'yau ina fashin sallah .

Ahakadai su yusuf sukaje masallaci ' suka dawo gidan .

Taku daya yai yakaraso kusa dasu 'kallon rukayya yai 'yace ina pepper' danace ki rubutamin inda kika sanni 'kallon ta yake babu ko kiftawa.

Lura da kallon da yake mata 'yasa ta dukar da kanta ' cikin nutsuwar ta 'tace ni bansamu papper ba.

Amma Kai hakuri mun gama hada kayan 'mu 'zamu wuce . Nasan ka 'ta daliin Aisha kanwar ka.

Saboda a lokacin n'a taba zuwa gidan Ku 'inda n'a iske Kana fada 'da abban Ku 'kace Kai zaka bar mishi gida,umma n'a kuka tana rike maka hannu ' jikina yai sanyi 'na tambayi Aisha meya hadaku da abba 'budan bakin ta 'sai tace Kai gaskiya ne bakason atake .

Tun lokacin data fadamin hk naji kashiga Raina'da Wasa Wasa tun ina daure wa 'harnakasa 'gidan mu 'kowa yasan da Haka ' dan mahaifiya ta 'zagina take da yar wahala.

Nazo maiduguri ne badan inkwana ba 'saidan in gayamaka sakon zuciyata in tafi 'koda muka zo ganin ka yai mana wahala sai jiya.

Ajiyar zuciya yasauke 'kana ahankali yake kallon kwayar idanun ta 'dasuka cika da kwalla '

Yace nagode da kauna.

Amma inason indan muku nasiha ' a matsayin Ku ' n'a yaya mata.

Barin gidan iyayen Ku 'dakuke yi da karyan unguwa ' har kusamu kuje wajen saurayi ba Abu bane mekyau 'dayawa wajen yawo akai musu fyade 'wasu akai kidnapping dinsu 'wasu kuma Aka kashe su. wasu akai zina dasu .

Inda wani mummunar Abu yafaru daku 'kuka mutu 'kuna tunanin Allah ze kalli hujjar kune'?

Gabadayan su suka girgiza Kai alamun 'a'a

To wallahi ina me tabbatar muku 'wuta zaku tafi direct '

N'a farko kunyi karya .

Nabiyu kunje neman saurayi.

Dan Haka Ku gaggauta gyara halayenku ' da duk me hali irin naku 'ya kiyaye kada yafada fushin ubangiji.

Naji bukatar ki 'rukayya

Zanbaki nombar wayata 'zan amshi taki 'inhar kin isa zamu ringa waya.

Gabadaya suka zube kasa 'sunata masa godiya.

Yusuf yaba' Ahmed umarni su wuce katsina taredasu.

.....

Kaka 'ce agaba cikin saurin ta wai zata Riga 'su Shiga dakin da Aka kwantar da fatima .

Mommy da dadyy sai kallon ikon Allah suke.

Deen n'a ganinsu yai musu jagora yaimusu har dakin da fatima take.

Kaka 'cikin kuka ta rungumi fatima ina fatan babu inda ke miki ciwo' ko

Murmushi take mata 'taki magana.

Daddy yace haba Kaka 'kidan barta taga iyayen ta ,mana.

Iyeeeh 'kaka ta kwabe baki ' Kaci gidan ka' auwal nace Kaci gidan auwal .

Au ni daga sama n'a fado Kenan .

Banda dariya babu abunda kowa keyi adakin.

Daddy da mommy 'cikeda tausayawa sukaita nan nan da fatima '

Likita ne yashigo ya duba fatima yace 'naga jikin 'dasauki .

Ga wayannan magunguna zaku siye mata a asibiti'kuna iya tafiya gida inkun gama .

Cikeda jin dadi 'suka fara harhada Kayan su.

Kaka tace da 'ita zaa tafi gidan su 'fatiman.

KHALID ne yana kallon abba dake waya .

Abba yace *murhu* nabaka nan da zuwa gobe 'duk inda kacalle yake akashe mun shi 'kisa ta wulakanci

Murmushi kwance Akan fuskar Khalid dayaji abba nace wa ,zebada millions 10 inhar Aka kawar da KACALLE.

Abba yai gyaran murya 'khalid wai fatima ta Farka ta ,ta gan ka kuwa ?

Ran khalid yasoma baci tuno cin fuskar datai masa ' tsaki yake ta jerowa akai akai tareda ciza labbansa ahankali 'cikin muryan sa 'dake nuna bakin cikin daya kunsa 'yakebawa abba labari Abunda akai a asibiti.

Abba 'yace 'yo Mèze dameka Khalid dan tamaka Haka ,kasan tana cikin bacin Ran 'abunda yafaru 'tunda kanason ta 'kai hakuri da abunda taimaka .

Khalid zumbur ya Mike ' cikin dagawa yace' au abba hakuri 'zakace awannan abun da akemin ' ?

Abba cikin saisaita muryan sa, tareda ban hakuri yace ,dana ba hk nake nufi 'akwai abunda nalura gameda fatima kaida kake auren ta ,ma bakasani ba

Cikin kosawa dajin zancen 'khalid yace kaman me Kenan 'tareda zama kujera yana fuskantar abba.

Wlh khalid fatima da kake gani in kai Wasa , sai ta tono rijiyar daya dade da kafewa.

Dan Haka yanzu ba lokacin kamin tambaya bane 'nahango abunda nagani shiyasa nake baka hakuri Akan abunda take ' kasan abunda babba ya hango ' yaro ko yahau dala ,baze hangesa ba 'ina fatan kagane ,

Khalid da jikin sa 'yagama mutuwa dazancen Abba yace .

Eh n'a fahimta ',zanje aminu n'a kirana daga Haka yabar wajen abba.

Direct gidan aminu yanufa .

Yai saa yana kofar gidan su 'tareda wasu abokanan sa,

Murmushi kwance Akan fuskar aminu 'tareda yiwa khalid barka da isowa shida abokan sa.

Har cikin gidan su 'suka shiga 'khalid nagaisa da iyayen aminu basu wani bata lokaci ba.

Sukai dakin aminu.

Aminu ruwan Gora me sanyi hade da juice din kwali 'yakawo gaban Khalid.

Khalid shi kwata kwata hankalin bekan wannan abun sha.

Shiru 'sukai na dan wani lokaci ' kowa da abunda zuciyar sa ke saka masa.

Aminu yai karfin halin cewa 'amma dai Khalid 'tun zuwan ka 'na lura kaman Kana cikin damuwa.

Hawaye shar shar Haka idanun khalid ke fitar da kwalla...

Ya sallam abokina 'wai meyake damun ka 'ne.

Cikin kukan dayaci karfin sa , tareda dafa aminun yace 'wallahi aminu innaga kallon da fatima keyiwa deen 'kaman in kashe kaina nakeji.

Subuhanallah gayamin meke faruwa ne Haka.

Bashi labarin abunda yafaru 'yai .

Aminu hankalin 'sa ya tashi amma bé nuna ba 'sasaita nutsuwar yai ' yace abokina 'karka saka wannan aranka ninasan fatima tana Sonka 'tanayin hakane dan kaji haushi.

Shawara daya zanbaka shine 'dole ka nuna mata Kai fa mijin tane .

Wai ma ka taba auren Macé me tsaurin ido kaman Fatima kuwa ?

KHALID yace inafa 'sauran matana tsorona sukeji 'banda wannan yarinyar 'da ubanta karkashina yake ci.

Aminu cikin son bashi karfin Gwuiwa yace kaide tunda ubanta naci akasan ka 'intaimaka rashin ,ka nuna mata matsayin ta ,Dana uban ta .

Haka dai sukai ta fira 'har khalid yasamu nutsuwa Aran sa.

Yau kwana biyar da sallamar fatima daga asibiti.

Ta warware sossai da taimakon su' umma Inna Farida 'sumayya da indo da Balaraba .

Ita kakar fatima tunda tazo 'gidan babu abunda takeyi sai 'kallo 'tv ' Fatma tayi magana har tagaji taki daina 'haka data idar da sallah asuba .

Saidai suji karar tv ya barbade duka gidan .

Da fatima't'ai magana 'umma zata Hana ta 'akan me zaa damu Kaka t'ai yanda takeso gidan ta ne.

Yau takama jumaa 'kaka tashirya kayanta saf 'zata koma gida'.

Fatima ta hada mata sha tara n'a arziki itada umma.

Sunzo rakiyan ta 'zata shiga mota ' Kaka ce ta kara kallon umma 'da sam bata gajiya da kallon ta 'yanadaga cikin abunda yasa t'ai kwanaki agidan.

Harta shiga mota 'umma tajuya tace 'hassana .

Umma ta waigo cikin sakin fuska 'tace naam .

Dan Allah ke yar wace gari ce?

Shiru t'ai n'a wasu dakiku dan tabbas 'bazata taba mance fuskar kakar fatima 'amma t'ai alkawarin bazata bata amsar da takeson ji ba.

Kinyi shiru !

Kaka ta dawo da ita cikin duniyar tunanin data fada.

Yi hakuri Kaka 'nikaina n'a mance 'sunan garin mu.

Daga Haka tasakai ta shige cikin gidan.

Tsororo Kaka ke kallon shigarta rike da baki.

Fatima dake kallon abunda ke faruwa tace kedai wlh Kaka kinfiye son jin kwa kwaf .

Kaka ta jero tsaki .

Ai uwarki hussaina' itace mai son jin kwakwaf din ehee .

Abu daya kawai nasan zakice kice nafiye gulma ko ?

fatima ta gyada mata Kai alamun eh hakane.

Sai ji t'ai tace ai auwalu shiya koyamun gulma 'bakiga katoton cikin shi ba 'saboda tsabar gulma cikin ya turo.

Fatima 'turo baki t'ai gaba 'cikin Bada umarni tace drever dan Allah ka wuce da matar nan ' Kana ajiye ta .

Ka juye ta kadawo .

Salati Kaka tasoma 'tace drever saukeni 'watau Kai jifa dani take nufi .

Ko takanta fatima bata bi 'ba .

Tashige gida .

....

Shamsu ne gaban 'ummu suna hira yace kinga ko 'umma wlh nakosa mu samu yancin kanmu 'kodan muyi aure.

Murmushi t'ai tace aika manta yau bithday din nusy saura sati daya .

Kasan taro akeyi nabugawa ajarida ' nidai dan Allah inason naga yata 'zanje wajen taron bithday .

Zazzare idanu yace haba 'sokike asirin mu .

Yatonu.

Kinsan dai khalid saiya gane ki.

Murmushi t'ai tace wlh baze ganeni ba 'zan badda kamanni n'a.

Shiru yai 'yana nazartan ta Kana yace to Allah yakaimu ' daga Haka in kinje kiyi iya kokarin .

Kiyi magana da matar khalid 'nombar ta Zaki karbo mana 'ki amso mana Nata wannan shine matakin farkon nasaran mu .

Inhar tabamu hadin Kai.

Ummu tace nifa haushin fatima nan nakeji.

Kamanya fa 'shamsu ya tambaya.

Kaduba fa 'itace zaune amatsayin Dana taka agidan.

To dan kin taka matsayin da takeciki kema ai kafun ke 'wasu Sun taka Sun barshi .

Bayan ki ' ai Maryam ta taka bakiji haushin su ' ba sai ita kadai wacce take kula da yar cikin ki.

Jikinta ne yai sanyi tace Allah natuba.

Murmushi yasakar mata.....

..........

Fatima suna zaune kan dinner kowa ya hallata anacin abinci.

Deen da SHIGOWAR Kenan 'a yunwace yadawo kallo Khalid ta gefen idanu t'ai 'talura ya zuba msu idanu.

Lale lale oyoyo ga deen Dina yadawo .

Aguje ta taroshi ' tareda yi masa iso 'murmushi yake sakar mata batareda ya lura da khalid awajen ba.

Abinci ta zuba masa.

Umma da abba Sun tashi Sun fice da akwai inda zasu je.

Ganin Sun tashi Khalid nazaune sai inna Farida da indo da sumayya.

Dubanta takai ga deen, cikin wani fitannan kallo da take jifan deen dashi 'shima still ita yake kallo .

Kwantar da murya 'tai cikin shagwaba tace haba deen Dina ' bude bakin ka .

Inringa baka kanaci .

Tsawa Khalid yaso ya d'Oka musu 'amma ya taushi zuciyarsa dake ta' tafarfasa 'ahankali ya dago jajayen idanun sa' da sukai jajir kaman gauta ' mamaki begama sakin shi ' fatima dake ta yauki 'tana ba 'deen abinci a baki ' shikuma deen ya kidime ' babu wacce yake kallo sai kwayar idanun fatima

Duk Wanda yagansu ' yasan sundace ' bakaramin macin sukai da juna ba.

Ahankali wasu zafafan hawaye ke silalowa daga fuskar Khalid' , fatima n'a lure dashi .

Deen yace anti Fatima 'bara inje indan kwanta ' shshi shhii fatima tace akul inkara ji 'kacemin anti 'fatima 'kaiko sunan nan me dadi baka iya fadi ba 'tana rausaya idanun ta.

Am sorry to dawani suna kikeson in kiraki dashi' yana dariya .

Ina laifin kace min *gwanata* murmushi yayi cikin jin dadin kalaman ta 'yace to gwanata saide nadawo 'tareda haurawa sama 'ko khalid belura da Zaman sa 'ba.

Khalid dake dafe da kansa 'ahankali ya dago Kai 'ya kalli Fatima stil ita shi take kallo ' gyaran murya t'ai ' tace mallam wani Abu n'a damunka ne?

Dago jajayen idanun sa 'yai yace babu komai ' inason kishirya anjima Dana fito sallah azahar 'zamuje restaurant da gidan marayu.

Amma ' taya zakace zamu fita 'ban sanar da Deen ba ?

Caraf yake kallon ta ' Mike wa yai 'ransa abace 'bangane baki nemin izinin deen ba.

Cikin 'daga murya tace eh man haka nace !

Saboda shine amatsayin mijin ,da kanka ka sallama mishi ni!

Kuma nima n'a karbeshi hannu bibbyu ,dan Haka inya amince zanje 'ko ya...

Tass taji saukan mari Akan fuskar ta' daidai da fitowar 'umma daga daki 'idanunta yasauka Akan khalid dake kokarin Dukan fatima .

Ahanzarce ta karaso falon 'tarike masa hannu 'cikin fada tace me yarinyar nan taimaka ?

Huci yaketa yi 'sama-sama cikin muryan sa dake nunin 'akaishi Makura ya kalli umma yace wlh umma fatima inhar bata gyara halayenta b ' uhmm zatasan dani take nosens ya haura sama 'yana tafiya kaman ze tashi sama.

Umma jikin ta 'yai sanyi Kamo hannun fatima 'tai ta zaunar da ita' cikin muryan lallashi tace yata yi hakuri duk da bansan meya hadaku ba , dan Allah kinji n'a rokeki .

Cikin sheshekar kuka fatima ta kwantar jikin 'umma t'ai lamo 'cikin jin dadin bayanan umma 'tace 'umma ni Abunda Khalid yaimin be dameni ba.

Ywwa yata Haka nakeson jin Allah yaimiki Albarka,ta amsa da ameen.

Inna Farida 'dariya take tace iyeh soyayya ce , ta motsa 'umma da yarta

...................

Yusuf ne 'a kotu yakai 'report da bayanai ' hade record din voice din da fatima ta dauka 'lokacin data tunkari wayanda sukaiwa 'aisha fyade.

Registra ya shigar da Dukan bayanan yusuf ' tareda saka ranar shari'a .

Nan da sati uku 'masu zuwa 'rajista ya bukaci Aisha tazo 'wajen sharian 'dan amsa wasu tambayoyi.

Yusuf yace to babu matsala yasan yanda zeyi ayi sharia lfy batareda zancen yafita ba.

Dawowar sa gida 'dirshan yakwanta 'falo alamun gajiya atare dashi'

Kukun 'sa ya runsina yana masa barka dashigowa da yww ya amsa masa ' cikin kasala da gajiyar dake tattare dashi 'yace kawomun abinci .

Kai tsaye kukun ya nufi kitchen.

Wayar sa 'ne Yafara ring ' yana dubawa yaga nombar sumayya..

.daga wayar yai tareda kara wayar akunnen sa.

Cikin husky voice din ta 'mai daddan zakin murya 'tace inawuni yaya yusuf '

Lfykalau alhmdulillah yabata amsa yasu umma da Inna ta.

Tabashi da amsa kalau suke.

Shiru sukai n'a wasu dakiku zuciyoyin su 'babu abunda suke sai bugawa da karfi ...

Yusuf yace kinga dadina dake in kin Kira kirasa 'me Zaki cemin bayan angaisa.

Dagacen bangaren' ta turo baki kaman yana ganin tace tace laa daman dan mugaisa ne 'nakiraka 'yaushe zaka zo katsina.

Kwanciya yai kan jurer dakin tareda lumshe idanun sa 'yace yaushe kikeson nazo ?

Rau rau tai da idanun ta 'tace ai amsa zakaban 'ba tambaya zaka jefomin ba.

Toshkn tunda bazaki fadi 'lokacin da kikeso nazo ba,sai.anjima ko?

No.pls.karka katse Kiran nasan halin ka.

Murmushi yai Wanda ya bayyana kyawawan hakoran sa,

Inajin ki yana mejin kansa a nishadi 'karo n'a farko dasuke waya betajin Haka ba 'sai yau.

Mu haɗu a na 8