KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka Chapter 9

by @kyautadagaallah10

Kai ka jawa kanka 9

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah



Page 9


Cikin fushi yace abba wlh nagaji nagaji da abunda akemin.


Abba yace yi hakuri Dana kabari zanyi magana da Deen.



Shamsu da ummu sunata kokarin suga sunje inda nusy take zaune da su tabata amma zuciyarsa cike da fargaba



Fatima da tasha rawa itada deen hannunta taga ankamo waigowa dazatai taga mommy



Cike da zallah mamaki

Tace momy kece yaushe kikazo naga daddy amma bansan tare kuke ba .


Zonan yata wannan rawar da kikeyi beda dake ba 'saboda cikin jikin ki.


Dukar da kanta kasa t'ai tarasa taya zata sanar musu batada ciki.


Yusuf ne yashigo tareda tawagar sojoji dukan su .


Dauke da kakin soja jikin su.


Kallon wayanda ke cikin taron yasoma .


Ummu da shamsu


Suna ganin yusuf hantar cikin su ya kada.


Yusuf cikin kalle kallen sa da yatsaya yi daga tsakiyar falon idanun sa yasauka akansu su'


Ummu da shamsu dasuke gefe daya.


Cikin kaduwa har bakin su n'a rawa .


Kallon su yake babu ko giftawa ' rike da kugun sa yana tafiya kamar Damisa ya iso falon cike da izzar sa .


Ma'aikatan suka take masa' baya kowannen su daure yake da bindigogi a bayan sa' cike girmamawa suka karaso falon dukar dakai sukai 'suna gaishe da jamaa sannan kowanne daga cikin su yakoma gefe suka jeru kaman wayanda zasuje yaki.


Hankalin abba da khalid yai mugun tashi ganin fuskar yusuf babu digon mutunci .


Ummu da shamsu 'sukazo wucewa sadaf sadaf 'harsun sa kafa zasu fita.


Sukaji tsawar yusuf saida hantar cikinsu ya kada 'gabadaya gidan kowa yasha jinin jikinsa har ita umma da ta haifeshi 'saitake ganin sa.


Kamar ba danta datasani ba.


Ku dakata shine kalmar dasukaji yafurta .


Atsorace suka juyo jikinsu n'a Bari hade zallah tashin hankali .


Ina zakuje ne bayan da Dukan alamun bakuci abinci ba atsaye n'a ganku fa.


Ajiyar zuciya suka sauke amma duk da Haka tsoron be bar jikinsu ba.


Shamsu ne ya juya harshe kaman n'a buzaye yace alhamdulillah munci munsha ' Allah yaraya maku yar Ku .


Zankai madam gida ne naga yamma tayi.

Yusuf n'a kallon su .

Yana nazartan kalaman su , cikin kwanyar kansa.


Mungode Allah yakaiku lafiya yafurta .


Kaman jira suke suka bar gidan cikin hanzari.


Yusuf kallon abba yake da kasan idanu 'cikin takamar sa yakarasa gabansa yace Abu Khalid inawuni ya akaji da taro , musamman yau da take spécial rana gareka .


Inafatan Allah yakara kawo wata babban rana me cike da abun al'ajabi yana gama fadin Haka yai gun 'su umma risinawa yai ya gaishesu.



Umma da faraa ta amsa masa tanata nazartan kalaman da yusuf ya gayawa abban sa 'mai cikeda ma'anoni daban daban' kauda wani tunani t'ai tare dayi masu babban tarba n'a musamman shida tawagarsa waje Aka basu n'a musamman suka zauna .


Jama'ar dake wajen taron kowa yakama kansa shiru kakejin wajen babu wata hayaniya .


Ahaka taro yatashi kowa ya watse .


Isma'il zewuce Aisha ta nuna masa yayanta yazo a mutunce suka gaisa .


Yusuf yace ashe kaine surukin nawa?

Eh nine yaya yusuf yagida ya iyali.



Yusuf yace iyali akace maka n'a ajiye yana kallon gefen sa .


Sumayya data dukar da kanta tana Wasa da yatsun hannunta.


Yi hakuri yaya yusuf wlh namance ashe duk mune .


Murmushi yai yace cikin son kawar da zancen yace ance gobe ne 'zaku turo sa rana Allah yakaimu.


Bejira amsar isma'il yabar wajen.


Fatima rike da jakar mummy zatai mata rakiya 'daidai lokacin ne .


Yusuf yafito daga gidan danko takan sumayya bé bi.


Yana cike da haushin kinzuwa office dinsa da batai ba.


Mummy zata shiga motar ta 'ganin yusuf yasa tafasa shiga motar


fitowa tai tace dan Allah mallam kai dan gidan nan ne ?


Tana masa kallon sani.


Cikin sakin fuska yace eh a'a Abu daya nasani uwata tana aure gidan ne.


Mamaki cike da fuskar ta 'tace wacece uwar taka?


yace hassana yana mai tsareta da idanuwa 'so yake yaji tushen tambayoyi nan datake ta jefo masa.



Amma kuma kace uwarka ce ke aure gidan mijin fatima ba ya'yanka ne ko kaninka?


Eh to nidai nasan dai umma '.....ganin Khalid yana doso inda suke yasa yabude murya da karfi yanda zejiyo su.



Kara nanata zancen yai nadesan umma tazo da agola gidan nan .


Bayan shi ne tahaifeni sai kannena .


Fatima rike da baki tace mummy wannan ai tatsuniya ce wlh 'dukansu uwarsu daya ubansu daya.


Khalid da ransa yagama baci waishi yusuf ke danganta wa da agola.


Boye fushin sa yai 'batareda yazo inda suke ba.


Mummy tace Dana wlh kamun kama da yaya'na ne wlh sak shiyasa nake maka tambayoyi.


Allah sarki yusuf yace ai kama da yawa 'nasan kece mahaifiyar fatima.


Akwai zama n'a musamman da zamuyi nidake cikin satin nan inshAllah Dana rage ayyukana.


Yana gama fadin Haka yai mata sallama.


Ma'aikatan suka bude masa mota yashiga 'kowannen yashige cikin motocinsu na 'sojoji .


Sukabar gidan.


Mummy tace diyata kina iya komawa ciki 'dan Allah ki kula da kanki .


Sallama sukai inda mummy tawucewarta.


...


Cike da tarin gajiya tashigo gidan kama hannun nusy t'ai takaita daki taimata wanka .


Tashirya ta cikin Kayan barci ta kwantar da ita.


Hamma taketa jerowa akai akai.

Sabar gajiya dakyar tayi wanka tafito idanunta Sun rufe babu abunda take bukata dayawuce takwanta barci.



Tuno da abunda yafaru tsakanin ta da Khalid t'ai wannan shakar dayai mata ,nan take taji ranta yasoma baci.


Kaman an tsira mata allura ta tashi tadau hijab ta saka cikin hanzari tabude kofar dakin ta .


Direct sashin deen ta nufa 'buga kofar tashiga yi da karfinta .


Gbo Gbo Gbo Haka taketa bugawa iya karfinta..



Deen a magagin barci yatashi dan kowa yagaji.


Waye ne yafurta cikin muryan me barci.


Fatima ce yaji ta bashi amsa ...


Tashi yai cikin kasala da barcin dake idanunsa yana hamma.


Yabude kofar kallon ta yake stil itama shitake kallo kusan mintuna biyu suna ahaka bawanda yai magana.


Deen yai karfin halin cewa yanzu kuma mekikazo kicemin?


Bangane menazo incemaka ba.


Kina tunanin zan yarda cewan yaya khalid ze iya kashe koda kiyashi ne bare mutum kuma.dan uwansa n'a jini abun soyuwar sa.


Nan da nan duk wani mood dinta ya canja kamar ba itaba.

.tace aidaman banson kayarda dani tunda naga kamar kanka yana rawa


Ina me tabbatar maka duk sanda yaimaka sanadin mutuwar ka kajika a lahira ba daman dawowa bare ka gyara kuskuren fahimta dakamin .



Kakosan abunda kake fadamun kuwa deen n'a Saïda rayuwata dan inceto ka amma karshen zancen ka 'shine baka yarda daniba.


Wayar ta kunna yakawo haske tashiga gallery din wayar.


Inda t'ai recordin din voice din Khalid 'batareda yasan tana daukaba .


Ta kunna masa.


Kasa kunne yai Yana sauraron inda Khalid ke fadin.


Kwana nawa Zaki dauka kina kareshi 'saina kashe Deenee'''



Zazzare idanu yai yana gama sauraron voice din .


Yadawo kalan tausayi idanunsa sunkawo ruwa 'cikin ban hakuri yace wlh nayarda da zancen ki.


Tabbas wannan muryan yaya khalid ne.


Cikin kuka' yake magana tareda durkusawa cikin kuka' yace fatima kiyafemun n'a miki mugun fahimta.


Kama hannun t'ai yatashi 'cikin kukan daya kwace mata tabashi labarin dalilin dayasa yace yaringa kwana dakinta .


Deeennn


Dago jajayen idanun sa yai yana kallon ta yace naam gwanata.


Ajiyar zuciya tasauke inason Kaci gaba dashigowa dakina Kana kwana kamar yanda Khalid yanema ' zaka ringa kwana falo.


Duk yanda kikace gwanata wlh zanyi babu makawa good muje to.



Karar Bude kofar Khalid suka jiyo Dukan alamu hayaniyar su 'ta tashe shi.


Canja zancen dasuke t'ai .


Tace Deeen pls rikemun hannuna muje daki badan ka gaji ba .


Danace ka goyani


Deen yace gwanata kodai in dagaki ne .


No muje daki ainasan zakamin tausa.

Yana huci sama sama sai Safa da marwa yakeyi nan da nan idanunsa 'suka ciko da kwallah '



Deen bin fatima Yai dakin ta 'nuna masa kujerar falon ta' tabashi bargo me taushi yarufa Akan kujera dakin ta 'takoma tahau gado tana murmushi 'adua takaranto tareda shafa Dukan jikin ta .



Washe gari tun da asuba ta tashi t'ai sallah asuba 'tagyara dakinta ko ina yadau kamshi wanka t'ai cikin hanzari taiwa nusy wanka tashiryata cikin Kayan makaranta.


Falon dakin ta 'tafuto bargon da Deen yakwana dashi take kallon yanda ya ninkeshi ya ajiye .


Sa hannun t'ai tadauka 'sauri take takai dakin Nata ta ajiye .



Cike da nutsuwa tadawo tagyara falon air fresher mai dadin kamshi ta feshe dakin dashi cikin dan hanzari takama hannun nusy sukai kasa .


Bata bata lokaci ba wajen gaisheda su 'umma da Inna Farida duba ga lokacin makaranta nakurewa.



Daidai fitowar ta harabar gidan ta hango khalid da Deen suna jerowa atare fira suke ' murmushi ta sakarwa deen tace ina kwana Deeen Dina .


Cikin shagwabe fuska kaman wacce zatai kuka tace shine da ka tashi asuba baka tasheni ba 'uhhhmm tana fari da idanunta .


Deen da yamance kwata kwata gaban Khalid yake 'yace gwanata yi hakuri yau dawuri naje masallaci nasan baki Wasa da ibada lokacin sa nayi Zaki tashi afuwan yace cikin karya murya harda kama kunnensa cikin ban hakuri.


Khalid da yakejin kamar numfashinn sa zedauke yace deen inkagama kasameni aciki.


Fatima ta karbi zancen da ina kwana yaya khalid 'sakaka yake kallon kalmar data furta wai yaya khalid sabon salo .


Lafiya kalau ya bata amsa .


Fatima tace Deeen Dina pls Zoka kaimu makaranta.


Deen yace angama gwnata 'gaba yai tana biye dashi abaya 'inda yadauke su 'a motar sa


Mai gadi yabude masa Gate.


Khalid natsaye awajen harsuka bar gidan 'dakyar yaja kafafunsa d sukai masa nauyi yashigo cikin gidan .



Sécurité din gidan ne yashigo hannun sa dauke da jarida kasancewa a kullum sai yakawo sabon jarida .



A mutunce ya gaida Khalid inda ya Mika masa jaridar ,cikin bacin Ran da yake ciki Beko duba me ke cikin jaridar ba.


Yace masa ya ajiye kan kujera .


Cike da ladabi sécurité ya ajiye tareda juyawa yakoma bakin aikin sa.


Zaman falon yaji ya gagaresa kasancewa yasan wannan time din umma tana dakin abba ne yasa direct yawuce dakin sa.



Itako fatima suna ajiye nusy suka jiyo gida fira suke a mota 'deen yace kina ganin Khalid baze dauki matakin da bazamu taba iya gano lagon sa ba.


Duba fa kikagani dazun banga yaji haushin abunda mukai masa ba.


Murmushi fatima t'ai tace kaine kake ganin Haka dauriya ce 'kuma beda wata dabarar dazata d'Anne nawa dan atafin hannuna yake .


Fira suke cikin nishadi suna dariya har suka dawo gida.



Shamsu ne gaban makarantar nusy adu'a yaketa jerowa Allah yabashi saa ayau dinnan yasace nusy 'dan yasha Alwashin indai yaukam besamu nasarar sato ta ba yahakura gaskiya.



Horn Deeen y d'Anna da karfi mallam isa cikin hanzari yabude masa Gate 'cusa hancin hancin motar yai agidan cike da kwarewa yai parking din motar sa.


Fitowa daga cikin motar yai ya zagayawa yabudewa fatima mota'. Ahankali ta sauke kafafun ta ' kasa tafito tana kallon iskan dake kadawa kaman zaa'i hadari garin duk ya hade.


Deen yace muje mana gwanata 'murmushi ta sakar masa 'tana mejin ina ma ace shine mijin nata data rungume shi ko zataji dadi dan ba karamin kyau yai mata ayau ba.


Tana gaba yanabiye da ita abaya .


Suka karaso falon.

.deen yace kinga Nina tafi dakina inkwanta pls pls kuci brek fast dinku basai kun tasheniba n'a rokeku dan haryanzu gajiya bata fita jikina ba.


Dan batarai Fatima t'ai cikin Wasa tace aibaka isaba banson kana zama da yunwa .


Murmushi yasakar mata yayinda yake taka matakalan step zewuce sashin sa.


Wash Allah nagaji tareda fadawa kan kujerar falon 'lumshe idanunta 'tai tana ganin hoton deen n'a mata gizo afuskar ta 'musamman inda ta tuno firar dasukai a mota 'tace ina ma ace su kasance ahaka har abada .


Dan mirginawa t'ai daga kan kujerar kasancewa itakadai ce Akan 3ster kokarin Mike kafafun ta 'takeyi inda taji ta ture Abu yafadi akasa.


Cikin idanunta da suka kada alamun me jin barci .

Ta bude su ahankali dantaga menene.


Jarida tagani yafadi 'cikin hanzari tasa hannu tadauko tana kokarin maidashi inda yake..


Akokarin ta n'a ajiye jaridar taga an rufe saman jarida kamar Haka


*Ankashe KACALLE shaharraen dan daban nan da Yan sanda suke nema ido arufe adaren jiya a hôtel din (zaria road)*


Innalilahi wa'inna rajun fatima tashiga maimaitawa bude jaridar t'ai tana karanta abunda kecikin 'nan da nan idanunta suka kawo ruwa dan tabbas tagane kacalle shine sunan dataji abba yana waya akan aje akashe shi.



Rike da jaridar hannun ta 'tarasa ta ina zata fara ne yasallam wannan karan dole in nemi iyayena su raba wannan auren tun kan abun yawuce tunani.


Sabon kuka yakwace mata tace ina ni fatima bazan iya daku ba Khalid saiyanzu n'a tabbatar bansan halin naku.


Rasa Waze bata amsoshin tambayar ta' yasa Kai tsaye ta nufi sashin umma .


Cike da hanzarin ta .


Sallama dauke abakin ta 'tashiga kallo daya zakai mata ka fahimci tarin damuwa tattare da ita.


Cike dason jin komai abakin umma tace .


Umma nasan kinsan waye uban mijina rannan naji yana waya akan kacalle nan ta kwashi labarin komi tabawa umma.


Umma hankalin ta yai mugun tashi tasan wannan bakomai bane cikin ayyukan mijin nata .



Bata fuska ta tace fatima nadaukeki yarinya mai hankali ashe akasin hakane taya zakiyi banzar tunani akan uban mijin ki.


WANNAN maganar dakikai kada inji koda wasane kinyi agaban wani 'juyawa fatima baya t'ai Takara dacewa .


Sani YARO bé iya kashe koda kiyashi ne bare dan adam me rai dan Haka akul inkarajin Haka abakin ki.


Cikin kuka Fatima ta karaso gabanta tarike hannun umma 'kiyi hakuri bansan maganar nan zata bata Miki rai ba



Kuma nima nayi kuskure danai banzar tunani akan Wanda yake kaman uba agareni ki gafarceni umma daga Haka tafice dakin aguje t'ai dakinta.



Umma ta baya baya tazauna bakin gado tasake rushewa da sabon kuka 'fadi take

Fatima ki yafemin n'a boye Miki gaskiya .


To Taya zan fada mata gaskiya bayan nasan kwakwalwata baze dauka ba.


Ya Allah narokeka ka kawomin karshen wannan mutanen cikin kuka Takara da cewa fatima ke jinina ce saboda uwarki dani ciki Daya Muka fito



Kuka sossai fatima takeyi adaki idanunta Sun kada jajir kamar wuta 'zuciyarta tafarfasa takeyi cikin kunan rai


Tace ya Allah ka sassauta mun wannan al'amarin

Ni fatima



Karar buga kofa yasa takai kallon ta Akan kofar waye ne ?

Ta furta


Safiyya ce tabata amsa


Kyalle tadauko tafara share hawayen ta' tareda boye jaridar cikin rigar ta.


Bude kofar t'ai cikin hanzari suka 'rungume juna sukai itada safiyya .


Nayi kewar ki sossai safiyya saiyau kikazo .


Safiyya tasaki jikin Fatima tsareta da idanu t'ai tace yana ga kin rame Haka.


N'a rame kuma... murmushin yake t'ai tace aikuwa banda matsalar komai agidan nan.


Jaridar data boye ajikinta ne yafado kasa 'zuru zuru t'ai da idanunta tana kallon safiyya dake shirin dauko jaridar .


Safiyya tashiga karanta labarin dake cikin jaridar tace fatima wannan ai dan ta'addan da Aka dade ana nema ne .


Yanzu Haka wani Mara Imani ne suka kashe shi dan kada ya tona musu asiri '


Fatima naga tarin damuwa a fuskarki karki mance nifa kawarki ce 'mai rike sirrin ki .


Ki fadamun damuwar ki inyakama in baki shawara saina baki


Zama sukai bakin gado suna face din juna .


Fatima Takara fashe da sabon kuka Wanda yasa safiyya taji idanunta sun kawo ruwa tun bataji damuwar ba.


Fatima tafara ba Safiyya labarin komai tun zuwanta gidan 'kisan deen da Khalid ke shirin yine kadai bata furtaba


Sai mutuwar KACALLE .


Tashin hankali karara Akan fuskar safiyya tace what ...


fatima yaushe kikai sanyi Haka har kike rayuwa da Wanda beda lafiya .


Soyake kiringa bin mazane awaje irin wannan auren aiba shiru akeyiba

Fatima cutar da kanki kikeyi Zaki kare rayuwar ki ne ahaka wallahi karya kike babu Macé me lafiya dazata iya daukan wannan kaddarar face yaudaran kanki kikeyi .


Kiyi gaggawan neman saki hannun Khalid tun wuri wallahi ni harma kinban haushi ina kika taba ganin Haka


dama ace lafiyarsa kalau haihuwa ne bayayi dole ne ki rungumi Kaddara .


Wallahi Maza ki dau mataki nagayamiki.


Ajiyar zuciya mai karfi fatima tasauke tace safiyya nadade da tunanin barin gidan Khalid amma sainake ganin baze barni ba kinga mahaifina karkashin kamfanin sa yake aiki.


Harara safiyya ta jefa mata t'ai tsaki mtsss


To dan mahaifinki n'a aiki karkashin ki shike nuna basuda iko akanki?

Karki mance sune suka haifeki zasu fahimceki bazasu taba yiwa khalid son da suke maki ba.


Kuma naji mahaifin ki Yana shirin bude kamfanin mai suna *FATI GLOBAL* daga jin sunan kinsan danke yai Haka kidawo hankalin ki kawata dan Allah narokeki .


Safiyya naji zantukan ki naji dadin shawarwarin Ki ina ga zuwa gobe zanbar gidan nan koma me ze faru saide yafaru inshAllah.


Daga Haka suka dade suna hira tadan saki jikin ta tana walwala jallof din taliya ta dafa musu da naman kaza 'safiyya tanaci sai zuba uban santi take 'tace waike Fatima wai a ina kika koyi girki ne .

Naga dai agida ko kwanu baki dagawa


Fatima tace atare atare zata gudu


Aikuwa safiyya ta fashe da dariya tace kinason kicemin santi nakeyi .


Zazzare idanu fatima tasoma yi tunowa datai lokacin daukar nusy yawuce harda minti goma.


Cikin hanzarinta tace Safiyya Zaki jirani inje indawo ne?


Eh jeki dawo dan yau wuni nazo Miki.


Jakarta ta dauka cikin hanzari tashiga motar Deen dan yanzu batada mota tunda akai gobara .


A 360. Tafigi motar ta cillashi kan titi gudu take shararawa 'ko kallon gabanta batayi



Bata dade sossai ba sai gata gaban makarantar nusy .


Ganin kamar babu dalibai duk Sun watse yasa cikin hanzari tasauko daga motar' Kai tsaye wajen me gadin ta nufa.


Cikin damuwa tace dan Allah ko kaga yata nusy .

Mai gadi yace 'A''a banganta ba.



Ya ilahi ta furta ganin an kulle makaranta waige waige takeyi tanata leka lungun da sakon unguwar ko zata ganta amma shiru.


Wata yar ajin su.nusy tahango da uban ta zasu shiga mota.


Ahanzarce Takarasa wajen su.


Inawuni ta gaida uban yarinyar ya amsa da lfykalau


Fatima tace baby na da kuka fito makaranta kokunga nusy .


Yarinyar tace eh naganta


Wani uncle dinta ne yazo yadauke ta .


Innalilahi wa'inna rajun ta shiga maimaita wa wani jiri taji yana dibanta hannayen ta duka biyun ta daura saman kanta.


Nashiga uku ni Fatima mezan gayawa Khalid idanunta Sun ciko da kwallah dirshan tazauna kasa batare da ta Lura me takeyi ba .


Wani matashi ne yazo wuce wa kallon ta yake cikin mamakin ganin ta zaune akasan titi itaba mahaukaciya ba.



Baiwar Allah lafiya kike zaune nan ' dago idanunta dasuka rine suka koma jajir dan kuka.


Tace abunda yafi Haka sai inyi bawan Allah 'yata Aka sace fa tana sheshekar kuka .


Tausayinta ya mamaye masa zuciya 'yace Allah yasauwake amma ki sanar wa uban yarinyar yafi ki zauna kan titi daga Haka yai wuce yabarta cike da alhini


Dakyar ta iya daga kafafunta murfin motar tabude tashiga ta 'daukar wayarta tayi takira Khalid awaya bugu biyu ya daga.


Dagacen bangaren yace lafiya yau kika dade WAJEN dauki nusy.


Gaza magana t'ai sai sheshekar' kuka da takeyi


Kinyi shiru ina magana!!


An sace nusy


Zumbur Khalid ya Mike daga kwance dayake bangane ansace nusy ba.


Garinya kuma kina aikin me.


Garin ya kuma kina aikin me har yarinya ta bata .


Shiru tayi tana kuka Wallahi bakuwa nayi banlura lokacin dauko ta yawuce ba.


Katse wayar yayi cikin hanzari ya sauko kasa .


Sanar da su umma da Abba batan nusy yayi duk gidan hankalin kowa ya tashi musamman ma umma.


Abba ne yakira jami'an tsaro ya sanar musu' da batar jikar sa.


Duk inda ake tunani zaa sa cigiya shiru kakeji babu amo babu labari.



Fatima dakyar ta karaso gida 'iske kowa cikin tashin hankali datai yasa kuka ya kwace mata aguje taje ta rungumi umma.


Khalid sai banka mata harara yakeyi 'kasa jure kallon sa tayi.


Umma tace garin ya Haka tafaru diyata .


Wallahi Umma bakuwa nayi sam n'a mance lokaci yatafi sanin kanku ne kullum ina zuwa makarantar kafun atashe su.


Abba rike da kugun sa yace Abu indai zakasa mata ciki to tabbas wataran zakasha kunya .


Yanzu Haka Yan garkuwa da mutane ne suka dauke ta.


Inna Farida tace zeyi wuya hakan takasance mudai jira jami'an tsaron muji me zasu ce.


Ko Akira yusuf ne dan ya kware a irin wannan fannin.


Da tsauri Abba ya katse ta basai kin kirashi sokike yazo gidan ya kara mana tashin hankali kinsan ba hankaline dashi ba.


Fatima kasa jure zama falon tayi direct sashin ta ta nufa Khalid nabiye da ita abaya .


Sanin akwai bakuwa dakinta yai maza ya Kamo hannun ta ' batareda ta bude dakin ta ba.


Kuka take ina zaka kaini ne Khalid tsaya dan Allah tsaya kaji wallahi kuskure akasamu ko sauraron beyi ba 'yayi dakin sa da ita.


Jifa yayi da ita kan gado da sauri tafara ja da baya baya Yana kara matso ta.


Saida takai karshen bango cikin kuka' tace Khalid wai me kake shirin aikata min ne.



Shakar wuyar ta dayai yasa Zara zaran idanun ta suka bayyana ' khaliiid taja sunan sa kasan makoshin ta.


Besaketa saima kara shakar yake dan da biyu khalid yake mata wannan muguntar batar nusy ga kuma daman ta cikamai ciki fam.


Yana sakin ta ' tafara maida maida numfashi sama sama.


Keeee!


Wallahi yau inbanga nusy ba wannan da kikagani kadan ne .


Shashar banza !


Kuka take iya karfin ta ...


Kayafemun khalid saboda rashin kulawa ta yasa Aka sace nusaiba natuba inshAllah zanyi iya kokarin ganin ta dawo gidan nan.


Zan gayawa yusuf yasa hannu cikin lamarin nan '


Gaban khalid ne yafadi jin ta ambaci yusuf .


Juyowa yayi ya kalleta cikin sanyin murya da beson ta gane yana tsoron yusuf.


Yace A'a fatima ai Abba yasa jami'an tsaro karki damu n'a fahimceki kuskure ne kuma yana kan kowa daga Haka yafita .


Yabar dakin ' azuciyar sa sai fadi yake in ba Haka nayi mata ba 'zataje ta dauko mana hauka ta kawo amatsayin mai bincike.



Fatima dakin ta 'ta nufa idanunta duk Sun kumbura...


Safiyya da batasan wainar da ake toyawa ba .

Tana waya akan ansamo mata labarin salamatu tazo gari...


Sallama dauke abakin tashiga '


Safiyya n'a ganin Fatima ta katse wayar cikin farin ciki tace Albishirin ki?


Cikin sanyi murya wacce bata cikin hayyacin ta 'tace goro.


Mama ne kwance fuskar safiyya ganin kawarta ta canja daga dawowa...


Cigaba da zancenta tayi .


Salamatu tazo gari yau dinnan dan Haka kishirya muje very inportant ance kaman a asirce take zuwa garin nan.


Ganin duk bayanan da takeyi besa fatima tayi farin ciki Akan abunda ta dade tana jira ba.


Dafa ta tayi tace kawata wai lafiya kuwa.


Kuka ta fashe dashi . safiyya ina lafiya diyar khalid ansaceta ta daliin sakaci n'a .


Salati safiyya tasoma tace garin ya Haka kawata yanzu me khalid yace?



Kasa bata labarin abunda khalid yayi mata tayi .

Yace ansa jami'an tsaro inshAllah zaa ganta .


Maganar salamatu in akaga nusy komi dare zamu je.


Dan Haka zo mu sauka kasa ...

Kinsan kowa n'a c'en.


Tare suka sauko da safiyya .


Safiyya tagaida kowa n'a gidan tareda jajanta Al'amarin .


Abba sai Safa da marwa yakeyi .


Sécurity ne yashigo yasanar dasu ga jami'an tsaro nan sunzo.


Abba ya Bada izinin ashigo dasu



Su wajen bakwai suka shigo .


Dauke da computer hannun su.

.babban cikin yace yallabai yarinyar nan inda masu garkuwa da mutane ne suka dauke ta


Tabbas da yanzu Sun Kira waya Sun fadi adadin kudin da suke so


Amma mu muna zargin gaskiya n'a cikin gida ne yadauke ta.


Umma hankalin ta yatashi dakin ta .


Ta nufa taje ta dauko gyalen ta da Jakarta ta saka waya aciki .


Falo ta same su 'kowa idanun sa akanta .


Kallon Abba tayi tace wannan yarinyar ita kadaice jikata .


Bé kamata inyi zauna banyi koda yunkurin komi ba.


Dan Haka zanje babban masallaci juma'a.


Inyi sadaka wannan Karon da hannu n'a zanyi saboda jikata tayi Saurin bayyana inshAllah


Cikin gamsuwa da Haka da kuma rashin yarda da ita.


Yace Bodyguard sukai ta .

Su jira ta gama su dawo da ita.


Jami'an tsaro zama sukai suna tattauna wa.


Umma tafito tanata adu'a Allah yabata nasara Akan fitowar da tayi.



Nan da nan Bodyguard suka bude mata mota tashiga...


Direct babban masallaci suka kaita .


Tana fitowa tace musu Ku jirani anan dan zanbi Dukan almajirai in basu sadaka.


Gyada Kai sukai cikin gamsu da zancen ta .


Suka tsaya jikin motar.


Tafiya take tanata waige waige taga hankalin su .

Sam baya kanta.



Baya ta zaga inda ta tari me napep cike da tsoron karsu ganta tashige ciki.


Me napep yace hajiya ina zankaiki



Muje zan nuna maka dan nima bansan sunan unguwar ba 'kuma karka ji. Komai kudi ko nawa ne zan baka.


Tafiya suke mai nisa kusan minti talatin tanata gwadamai hanya har suka ISO wannan dokar dajin.



Sauka tayi tadauko kudi da batasan adadin su .

Tabashi .


Kai tsaye ta nufi cikin dajin nan tafiya take cikin sauri sauri hartana tuntube daidai wani daki ta tsaya shikadai ne ginin blog a jejin .


Kwankwasa kofar tashiga yi da karfin ta.


Daga cen ciki akace waye


Tace hassana ce ..


Ba bata lokaci ba wajen bude kofar .



Kallon kallo suka fara yiwa juna itada ummu

Zata rufe kofar 'umma tayi Saurin sa hannu ta tare ta .


Ummu tace umma lafiya naganki nan wajen adaidai wannan lokacin


Murmushi mai kama da ciwo mama tayi tace ai dole ki ganni nan ummu kema kinsan da Haka..


Ina jikata nusaiba take.

.ware idanu waje ummu tayi tace nusaiba kuma meya kawo ta nan.


Umma kallon ta take n'a nazartan kalaman cikin fahimtar datai mata tace ninasan nusy tana gidan nan Allah karki tsaya bata mana lokaci.


Ganin ummu taki bata dama yasa tafara ihu tana Kiran.


Nusy ! Nusy nusy da karfinta aikuwa saiga nusy ta taho aguje tarungumi umma tana tsalle .


Umma kallon takai ga ummu tace ninasan kece kika sace ta meyasa zakiyi Haka bayan kinsan cewa yin hakan kamar tona asirin Ku ne.


Kuma nusy tana samun cikakkiyar kula agun fatima kinsan bakowace matar uba bace take yin Hakan.


SHAMSU dake tsaye Yana sauraron su' yakaraso gaban umma cikin gaskata zancen ta yace tabbas ni sheda ne nusy tana samun kulawa 'yauma saa ce Allah yabani kinsan ance me son Kayan ka yafika dabara .


Yanzu menene mafita umma kinga dai yarinya tana hannun mu amma yanzu sainaji kamar bamu Kyauta muku ba


Kiyi hakuri ki tafi da nusy .

Ummu tazare idanu kamar ya su tafi da nusy ina murna yata tazo hannuna lokaci daya ka canja tsarin.


Nusy rike hannu umma tayi tace ina mama ta Zaki kaini wajen ta.


Shamsu da ummu suka kalli juna jin furucin nusy.


Umma tace mama tanacen tana kuka saboda rashin Ganin ki 'zakije ki ganta ?


Gyada mata Kai tayi duk jikinta yayi sanyi.


Saké Kai dubanta ga ummu da shamsu tayi tace n'a rokeku kubar nusy takoma gida.


Shamsu yace ai babu matsala yanzu ya zaai takoma?


Umma tace saidai ka Kira waya kace Yan garkuwa da mutane ne Kana bukatan kudi masu yawa .


Shamsu yace haba umma ai nafi karfin aban kudi Akan yata.


Bazaka fahimta bane shamsu wannan shine kadai solution kagane ...


Maryam zuwa tayi ta same su suna magana Daya ,a ladabce ta gaishe da umma cikin jin dadin saké haduwa da ita 'tace yaushe rabon ki da nan sai yau' tana rike da bakinta.


Umma tace Maryam kuyi hakuri fitowa n'a ba Abu bane mesauki shiyasa baku ganina.


Dan Haka nizan koma nabar Bodyguard masallaci suna jirana.


Pls Dan Allah kuyi abunda nace cikin gamsuwa da hakan ummu da Maryam da shamsu suka gyada mata Kai.


Nan da nan tajuya cikin sauri .


Suna tsaye suna kallon ta harta bace musu da gani.


Shamsu yace matar 'nan tafimu gaskiya kada garin daukar nusy suyi binciken da ze lalata komi.


Daukar wayarsa yayi ya d'Anna Kira lambar khalid yakira ...


Ganin n'a ganin wayar n'a ring ya matso kusa da jami'an tsaro suka sa wayar a Hans free dagacen bangaren yace


Nine n'a sace yarka nusy inason kaban millions dari kacal .


Khalid kallon jami'an tsaro yakeyi yana jiran su bashi daman Bada amsa.

Babban cikin yaimasa alamu da hannu Daya bata amsa yakuma tambaya ina zasu Kai kudin kuma ina za'a samu yarinyar.


Gyaran murya khalid yayi yace nawa zanbaka kuma ina zankai maka kudin ina zan samu yata



Bashi amsa yai da kebabban waje nan da Awa Daya inda zekai kudin duk Yamasa bayani sannan ya katse wayar yacire layin awayar shi ya jefar saboda tsaro badan tsoro ba.



Umma cikin hanzari tadawo massalaci iñda ta fiddo kudi taringa rabawa almajirai harta zo wajen motar su Bodyguard ta iske suna nan inda ta barsu.


Ajiyar zuciya tasauke tace musu n'a gama muje.


Bude mata mota sukai tana shiga suka rufo motar direct hanyar gida suka nufa.




Deen yace Alhmdulillah tunda ansamu labarin inda zaa amso ta .

Fatima ajiyar zuciya tasauke .


Khalid zaune suke shida abba suna jiran lokacin daya diba musu yacika.


Safiyya kama hannun fatima tayi sukai sama.


Suna shiga daki suka zauna safiyya tace kinga tunda yarinyar zata dawo gida yau inshAllah.


Ki shirya karfe takwas n'a dare karki dauki mota inzaki fito kihau napep.


Gyada mata Kai fatima tayi nagode kwarai kawata inshAllah ina nan tafe.


Safiyya tadauko Jakarta tace to Allah yakyauta in yarinya tadawo gida kin sanar mana sauri nake saurayina zezo duk da ba yaro bane amma naji ya kwanta min.


Fatima murmushi tayi tace su oh oh ansan dadi love innazo kin hadani dashi mu gaisa.


Daga Haka safiyya tafice daga gidan.



Umma tashigo sallama bakin ta' kallon kowa yake.


Cikin damuwa tace waiko ansamu labarin jikata kuwa.


Abba yace eh ansamu ashe Yan garkuwa ne.


Buga kirji tayi tace Yan garkuwa kuma tana zare idanu oh mutane ba gaskiya


Allah yasa kada su cutar min da jikata.


KoWa ya amsa da ameen



Lokaci n'a cika suka shirya tafiya dan Kai kudi da dauko nusy.


Har Sun fita umma ta biyo su aguje tace Ku tsaya ...

Kallon ta Abba yake yace lafiya.


Inason inbiku kunsan nusy yarinya ce ganina zesa tadan saki jikin ta ...

Cikin gamsuwa da bayanan ta yace tashiga motar.



Tafiya mai nisa sukai wajen gari.


Inda jami'an tsaron suka faka Khalid kadai yasauka yaje ya ajiye kudin inda akace.


Sannan yakoma mota suka nufi inda akace zasu dauki nusy.


Suna isowa wajen sunata waige waige inda zasu ganta.

.

Shamsu n'a ganinsu ya tashi kusa da nusy yasamu wani lungu ya boye Yana kallon abunda suke .


Ta baya baya yabi aguje direct inda suka ajiye kudin ya nufa Yana dauka yakara gaba.


Umma itama tasauko daga Kai dazatai tahango nusy zaune.


Aguje tayi wajen tace musu gata c'en.


Aikuwa nan da nan suka yo wajen ta.


Khalid yai Maza yarike hannun nusy yace baby n'a gayamin waya saceki.


Ya tsareta da idanu

Umma ta karbi zancen da kabari aje gida mana


Kasan arikice take kuma kaman batada nutsuwa ...

Jami'an tsaron sukace eh lallai maganar umma gaskiya ce.

a kyalete da tambayoyi abari aje gida.



Cak Khalid ya daga nusy sama suka yo titi da ita tareda shiga mota Dukan su.




Cikin Abunda Da befi minti talatin ba sai gasu gida .



Mallam Isa ya Bude musu Gate suka d'Anna hancin motocin su.


Batareda Bata lokaci ba sukai cikin gidan.


Zama sukai falon zagaye da nusy 'Fatima sai kukan farin ciki take Allah yataimake ta anga yarinya.


Inna Farida kasa rufe bakin sukai itada Aisha da sumayya dan farin ciki.


Inspecta ya matso gaban nusy yace yawwa m'y princesse ko Zaki gayamin ina ne uncle yakaiki Yana karairaya murya irin ta Yara.


Kallon sa take tagaza magana kara maimaita tambayar yayi nan ma tayi shiru babu amsa.


Ran khalid yabaci zuwa yayi Yana jijjigata cikin tsawa yake mata magana.


Keeee

Waya daukeki kuma ina Aka kaiki kinki magana.


Umma tarike mai hannu tace yi hakuri mana Khalid yarinya ce kila Bata gama dawowa hayyacin ta bane .



Jami'an tsaro sukace to su zasu wuce in ansamu wani bayanai agun yarinyar asanar musu ...


Daga hk sukai sallama .


Abba da khalid da Deen sukaje yi musu rakiya tareda godiya bisa kokarin su.



Fatima tashiga da nusy daki tayi mata wanka ta canza mata Kaya 'kayan sanyi masu taushi tasanya mata..


Zama kusa da nusy tayi tace yata meyasa Kika bi wani daban Wanda baki sanshi ba.


Nusy tace ai nasanshi kuma wajen mamata yakaini.


Fatima murmushi tayi tace kinada maman da tafini ne a yanzu aiba wajena yakaiki ba tana shafa fuskar nusy cikin so da kulawa.


Nusy tace eh ina nufin mahaifiyata wacce ta haifeni wajen ta Aka kaini.


Zazzare idanu fatima tasoma tana rinste idanun ta kodai Bata ji dakyau bane abunda nusy ta fada.


Zumbur ta Mike tsaye tace a zuciyar ta Kenan ummu tana raye ya akai tasa Aka sato nusy.


Kuma meya canja raayin ta harta maida yarinya rasa me Bata amsa yasa.


Takai kallon ta Akan nusy Dake fama da chocolat tana sha saï lumshe idanu take gardin chocolat din Yana ratsata.


Nusy ko Zaki iya gayamin inda maman taki take inje in mata godiya .



Nusy tayi wuki wuki da idanu tace ai bazan iya gane wajen ba 'amma ki tambayi umma tazo c'en wajen mama ta yau.


Cigaba dashan chocolat dinta tayi itako Fatima lissafi ya kwance mata umma kuma 'ya'akai tasan inda nusy take.


Lallai kam akwai abunda umma take boyewa Wanda batason asani.


Daukar wayarta tayi takira safiyya ta sanar mata karfe takwas zata zo tajirata.


**********



Yusuf gaban shugaban sojoji sai fada yaketa musu cikin tsawa hall dakin duk sojoji kowanne kansa aduke yake .


Yace yusuf bansan ka da Wasa da aikinka ba sai yanzu saboda jajircewan ka Akan aiki yasa Aka turaka maiduguri.


Amma ace case din dake hannunka babu amo babu labari kasan justice bazata taba lamunta da hakan ba 'saita samo wani labari ko yaya ne.



Gaskiyar magana nabaka Awa 48 ko halin yaya ne kasamo mana shedar daze tabbatar mana wayanna matan basu mutu ba ko Sun mutu.


Yusuf cikin ban girma irin tasu ta sojoji ya sarawa ogan nasu tareda fadin inshAllah ranka yadade.


Bayan kowa ya watse yarage dagashi sai Ahmad da abdullahi suna tattauna wa .


Yusuf yace su shirya gobe da safe zasu je 'inda akai hadarukan.


Dan tsananta bincike daganan zeje gidan nasu ya karasa sauran bincike nasa .


Abdullahi yace Ranka yadade Allah yataimakeka hakika Kana namijin kokari amma taya kake ganin zaa cimma case din da yayi shekaru .


Yusuf kallon sa yayi cikin damuwa kwance Akan fuskar sa yace case din bakaramin dauremin Kai yayi ba amma inada yakinin zanyi nasara Akan Haka inshAllah.


Cikin gamsuwa da zancen nasa Ahmad yace Allah yataimaki oga .


Gabadaya suka amsa da ameen.


Wayar yusuf tafara ring kallon screen din wayar yayi Yaga sumayya ce.


Tsaki ya jero yafita waje yabar su Ahmad wayar n'a kunnen sa.


Dagacen bangaren tace yaya yusuf wai lafiya Inna kiraka baka daga wayata.


Cikin halin ko in kula yace lafiya lau to in daga wayar in cemiki me?

Bayan kin isa da kanki da har zanbaki umarni ki tsallake.


Shagwabe fuska tayi kaman yana ganin ta 'tace wallahi Umma tahana mu zuwa katambayi Aisha har mun fito tadawo damu .


Wallah Allah ka yarda dani tana matso kwalla daga cikin idanun ta.


Yusuf dake sauraron ta yace kinga matsala ta dake kullum bakisan kin girma ba gashi ana shirin Miki aure 'amma kina magana kamar Zakiyi kuka .


Tunda umma ce tahana kizo wajena babu komai yawuce .

Cikin jin dadi tace


Tace godiya nake m'y sweety .


Yusuf yace banji ba mekika ce.

.rufe idanunta tayi kaman yana gabanta tace cewa nayi yaushe zaka zo gida.


Murmushi yayi yace matsoraciya dakin maimaita bejira cewarta ba ya katse wayar .


Sumayya ta kalli wayar taga ya katse tace ikon Allah wani dakira wani da katse wa 'yana iya tunda inason shi hakuri zanyi Allah yasa in anyi auren ya canza ko yaya m'a zamuyi rayuwar aure nidashi oho dai tana turo baki waje hanyar dakinta ta nufa tana wakar.


Zan rayu dakai zana mutu dakai habadan dani dakai zamu zauna.


Umma dake shirin shiga daki tace tofah jirgin masoya ne yatashi.


Cikin jin kunyan tarufe idanunta tayi dakin nasu aguje tafada kan Aisha dake waya da isma'il.


Aisha tace Kai Amma dai anyi rikitatta wallahi jibi yanda Kika fadomin ina tsakiya da jin dadi n'a.


Sumayya tace oho dai ina dadi tunda bezo tadi ba.


Ware manyan idanun ta Aisha tayi tace iyeeeh .


Kedin yusuf tadin yake zuwa ba gwamma ni dake.


Shi naki in yazo banda fadin rai babu abunda yake Miki.


Pillow sumayya tadauka taringa jifan Aisha dashi cikin Wasa .



*********


Fatima tana gama sallar isha'i tafito sadaf sadaf .


Kai tsaye waje ta nufa Allah yabata saa mallam isa Yana sallah.


Ahankali tabude Gate din ta faki idanun sécurité.


Tana fita napep ta tare ta gayamai inda zekaita...


Tana isa babu bata lokaci salamatu tafito daga gidansu,

tashigo napep DIN tareda gayamai inda ze kaisu..


Fatima suna tafiya sai kallon agogon wayarta take tace safiyya ina son kada mu bata lokaci wajen salamatu.

Kinsan mijina dan bin kwakwafi ne


.......


Kowa ya halatta wajen cin abinci khalid Yaga bega fatima ba.


Nusy yakira yace jeki kiramun mamar ki...


Nusy ta tafi tadawo tace dad batanan fa .


Mamaki ne yacika shi yace to ko compound din gidan ta tafi ne tazauna...

Barin wani tunani yayi sukaci gaba dacin abincin su.


Abba n'a lura dashi hankalin sa 'sam bé jikinsa.



Allah Allah yake yagama CIN abinci yatashi dan dubo iñda fatima tashiga.


****†***



Fatima da safiyya suna sauka napep DIN Kai tsaye gidan suka nufa .


suka shiga suna kokarin cusa kan su gidan suka cin 'karo da salamatu tana kokarin fita daga gidan cikin hanzari da alamu sauri take.


Shan gabanta Fatima tayi.


Salamatu tsabar rudewa ganin Fatima gabanta tace.

Tace anty Fatima daga ina Haka kuma wa kike nema tajero mata tambayoyi arude


Fatima murmushi mai kama da ciwo tayi hade rai tayi tace ganina ya razana ki ko?


Salamatu tace A'a akanme zan razana kawai de ina saurine.


Safiyya takama hannun salamatu tajata suka shiga napep 'Fatima tace aida kinbari munyi maganar anan ma.


Kedai shigo muje tabata amsa.

.

Sun nisa cikin tafiya.


Fatima tace daman ina neman ki da jan ido.


Inason ki gayamin duk abunda kikasani Akan Khalid 'kuma antin ki shin dagaske mutuwa tayi?


Shiru ne yabiyo baya tafara wuki da wuki da idanu gabanta ne yafadi tuno haduwan ta n'a karshe da khalid.


Cikin son boye damuwar ta tace ai antina ta dade da Rasuwa bé fadamiki bane.


C'en lokacin danaso in Miki bayanai Akan khalid rashin fahimta ne .


Nidai Dan Allah narokeku karku gayama khalid kun ganni idanunta Sun ciko da kwalla.


Safiyya tace ai Rashin gayamana gaskiyar shine zesa mu sanar da khalid kina gari.


Gabanta yabada raasss


Dago idanunta da suka canja kala zuwa ja.


Ta kallesu cikin muryanta me kama wacce Aka takurawa Tace zan sanar daku duk abunda nasani.


Dafarko dai suna n'a Salamatu Bashir ni kanwa ce ga Maryam Bashir matar khalid ta goma.



Lokacin da akai bikin Maryam ni Bana kasar .


Maryam taji bakin cikin rashin halatta ta 'mahaifiyar mu taita murna Maryam zataje gidan hutu.


Babban Attajiri ne da Nigeria tasan da Zaman sa Dansa ne ze auri yar uwata...


Nima n'ai farin ciki sossai dajin yabon da aketayiwa gidan nasu.



Maryam tunda tashiga gidan khalid bêta ba kusantar ta ba 'asalima datayii masa magana sai cemata yayi Bata da Surar dake jan hankalin sa .


Tundaga wannan lokacin tashiga matsanan cin damuwa tana tambayar kanta yasan da Haka meyasa ya aureta.


To wai ma surar jikin ta ze kusanta ne ko ita.


Taki hakura da zancen nasa .


Wataran khalid nabarci taje dakin nasa saide yaji ta Haye kansa tanata masa wasanni dazesa yaji sha'awar sa ta motsa



Firgit yafarka tureta yayi Saida tabuga kanta da bango goshin Nata ya kumbura.


Cikin hasala yace watau duk kauce Miki danake Saida kikeson ki kureni.


To banda lafiya Maryam 'bazan iya kusantar ki ba.


Rabona da shiga farjin Macé tun lokacin Danayi auren sha'awa da kausar mata ta tafarko.


Tunda nabiya bukatata na saketa ,pénis Dina yadaina aiki .

Naje asibiti an gwada ni .


Ance baa ga wata matsala ba.


Babu neman da banyiwa kausar ba khausar ba .


Gidan Dana kamawa iyayen ta haya naje nan akace baa san inda sukaje ba...


Kafun tabar gida n'a Saida tacemin tana dauke da cikina nabata millions Daya taje acire cikin tace sam bazata cire ba' Amma tamun alkawarin yanda n'a maida ita bazawara inshAllah bazan kara moruwa ba agun ko wace ya Macé...


Korar kare ya mata dan yar tallah ce ya auro ta akauye dakyar ta amince ta aure shi duk da talaucin gidan su...


Iyayen ta ya nasiye da kudi...


Hartakai ga mahaifiyar ta tace mata Inde Bata auri khalid ba zata tsine mata ...


Khausar tanaji tana gani ta hakura da Wanda takeso ta auri khalid



Cikin kuka' yakewa Maryam magana yace bayan khausar nakara aure inata murna zanyi daren farko da amaryata abun soyuwa ta .



Mun gabatar da wasanni amma sam banajin wata shaawa n'a tasomin.


Saida nazo kusantar ta .


Naga pénis Dina Yaki tashi ...


Kullum saina jaraba amma sam .


Amaryar tashiga damuwa sossai akan Haka .


Munje asibiti asibiti likita ya Auna ni yace lafiyata kalau nan gaba pénis Dina Yana iya aiki .


Inje in jarraba n'a gargajiya.


Yashiga matsanan cin damuwa sossai.


Yakasa jurewa malamai babu inda beje ba 'duk inda yaje sai suce yaje ya nemo khausar dan gaskiya itace taimasa Haka ...


Dole yahakura dan babu neman duniyar da beyiwa khausar ba.


Cikin kuka' yace Maryam ki rufa min asiri ki zauna dani Haka muyita rayuwar mu.


Maryam tace sam bazata iya ba zata iya fadawa zina kuma babban laifine da aure akanta



Bayan wata biyu da faruwar Haka .


Khalid ya umarci direban sa shamsu Daya ringa kusantar Maryam.


Shamsu cikin matsanan cin damuwa ya amince.


Yana nadaman kusantar ummu da yayi a baya har ta samu cikin nusy.


Koda yazo dakin Maryam kasa yi mata komai yayi yasanar da ita gaskiyar abunda ke faruwa .


Sossai tashiga damuwa suka yanke shawarar tona masa asiri .


Khalid duk take Taken su Yana Lure dasu.



Shamsu yadauki Maryam wataran zasuje unguwa Akan hanyar su.


Babban mota tazo ta hankade su suka fada jeji .


Dakyar shamsu yafito daga cikin motar ya zaro Maryam suna fita motar takama da wuta bal bal.


Jami'an tsaro duk sunyi iya binciken su basu ga alamun wani Abu me kama da gawa ta Kone ba.



Salamatu ta numfasa sannan tace ni kinga iya abunda nasani Kenan sauran sai itada kanta zata gayamiki .


Wannan dalilin ne yasa naje amatsayin me neman aiki dan in samu kusanci dake in gayamaki ko wanene khalid.


Amma sam baki bani damar Haka ba.


Shikuma khalid yanada wayau fiyeda tunanin mutum cikin dan karamin lokaci yake iya gano Abu komai nisan da yayi masa.



Fatima da safiyya wani zufa ne ya keto musu duk da iskar da kadawa a napep DIN.


Cikin kuka' Fatima tace yanzu wannan rayuwar nashiga bansani ba.


Iyayena Sun makance ne da basuyi bincike Akan sa ba.


Safiyya tace kidaina fadin Haka kila iyayen naki halin sa nagari suka sani shiyasa .


Salamatu tace zanbaku lambar shamsu 'amsar wayar Fatima tayi tasa mata nombar.


Koda wata matsala ta taso baa fatan Haka kina iya neman shamsu wannan nombar sa ce ta sirri babu Wanda yasan ta 'saini sai iyayensa .


Daga haka.salamatu tasauka daga napep DIN tana daga musu hannun ...


Cikin sauri sauri tabar inda suke .


Wayar fatima ne yasoma ring tana kallo screen din Taga khalid ne ke kiranta.


Gabanta ne ya tsananta bugawa take suka kalli juna iitada safiyya .



Kin dagawa tayi tacewa me napep yajuya yakaita unguwar su sabon layi.


Sauka safiyya tayi tace .


Fatima banda bugawa babu abunda zuciyar ta keyi tana tsoron abunda zataje ta tarar agida.



Tafiyar da befi minti talatin ba saiga ta kofar gidan nasu.



Dagacen baya tasauka...

A kasa takaraso kofar gidan iñda taci karo da khalid dake tsaye hannayen sa goye abaya

Yanata Safa da marwa A kofar gidan '


Kallon yake yake cikin tsawa yace .


Keeeeee


Daga ina kike.


Cikin kakkarwa bakin ta n'a rawa tsoro ya bayyana Akan fuskarta .


Tace wallahi safiyya ce batada lafiya shine narakata asibiti.


Da izinin wa Kika fita Yana doso ta.


Tana ja da baya baya harta buge wata bishiya.


Tace ashhh kafana


Dakatawa yayi Yana kallon yanda tarike kafar ta Alamun buguwa.


Shhhhhhh


Matsowa yayi kusa da yace Kamo hannun ta yayi yanata janta.


Murda handle din kofar gidan nasu yayi Yana janta .


Cikin kuka' tace Khalid katsaya kafa n'a ciwo yake.


Beko saurare ta ba jan hannun ta yake cikin zafin nama .


Yana karasowa falon babu kowa Hakan yabashi daman direct yayi ciki da ita.


Suna shiga dakin ta ya ya murda hannun ta da karfi yanata jujjuya hannun Yana kara murdawa ..


Wani razannanne kara ta saki wayyo mummy n'a.


Kizo ki taimakeni .


Sakin hannun ta yayi ya shiga kitchen yadawo ruwan me mugun sanyi babban rofar faro yabude shi.


Tass yajuye mata ajiki .


Nan da nan jikinta yadau karkarwa gab gab bakin ta n'a rawa .


Markarkata jikin ta yasoma yi ba kakkauta wa.


Kasancewa lokacin sanyi ne hunturu.


Cire hijabin jikinta tayi kanta a yashe gashin kanta ya baje Akan fuskar ta.


Cikin kuka' tace khalid menai maka ne .


Wannan ai kiyayya ce karka manta 'matar ka ce ni ,bafa baiwa bace.


Kallon banzan ya watsa mata yace au ashe kinsan ni mijin ki ne?


Taya Zaki fita baki sanar mun ba kuma fitar dare.


Nabaki last one duk ranar dakika kara aikata irin wannan kuskure wallahi kinji na rantse saina Miki hukunci mafi muni Wanda bazaki taba mance dani ba har karshen rayuwar ki.


Har juya zefita sai ya waigo yace saura inji wannan maganar Abakin

Wani nonsen kawai.


Yafita cikin gadara da takama .


Yana fita Fatima ta taso aguje tarufe kofar Key ta murza mishi tadawo dakin tana maida numfashi sama sama.


Gadon ta ta Haye Taja bargon ta 'tanata rawan sanyi .


Ahaka barcin wuya yai gaba da ita.



Deeen sai Safa da marwa yakeyi adaki rashin ganin Fatima ya sanyashi a damuwa.


Kasa hakuri yayi yazo Budé kofar dakin ta.


Jin shi arufe ya tabbatar masa tadawo harta samu barci ajiyar zuciya yasauke Yana mai hamdala.


*******


Isma'il da aisha ke waya cikin jin dadi tana lumshe idanun ta 'tace Yanzu gobe fa 'za'ai sanya mana ranar auren mu.


Dagacen bangaren Yana kwance kan gadon sa 'lumshe idanun sa yayi kaman tana ganin sa.


Yace indo ranar dakika tare gidana zan nuna miki so da kauna da kulawa .


Zan mayar dake cikakkiyar Macé.


Nan da nan duk wata annurin dake kwance saman fuskar Aisha yadauke jiyayi tana sheshekar kuka.


Cikin rudewa yatashi daga kwance da yake yace sahiba ta n'a Bata Miki raine.


Bashi amsa tayi bakai Komai ba kukan farin cikine nakeyi 'pls m'y isma'il ko zaka Bari gobe munci gaba da waya Bata Jira cewar shi ba.


Ta katse wayar.


Kallon wayar yake saké da baki bekawo tunanin Komai ba yakwanta Yana murmushi.



****


Aisha kuka take sossai dan sai gani take kaman yannzu ne mummunar al'amarin yafaru da ita.


Sumaiyya dake barci tafarka jin sheshekar kuka tace .


Lafiya ?


Aisha Bata tanka mata ba.


Tacigaba da rera kukar ta.


Sumayya tace in bazaki gayamin ba abunda ke damun ki ba.


Dan Allah zoki kwanta kiyi hakuri rayuwa dan hakuri ne bakiga yayan ki .

Hakuri nake da halin sa ba...

Duk a tunanin ta isma'il ne ya bata mata rai.


Aisha tace bakomai sumy kaina ke ciwo daga Haka ta Haye gadon ta kwanta.


Rungume juna sukai cikin bege da kaunar juna sumayya n'a bubbuga bayan Aisha Alamun rarrashi.



Washe gari



Tunda asuba fatima tashirya kayanta tsaf a akwati ta ajiye gèfe Daya.


Wanka tayi ta gabatar da sallah t'ayi lazimi .


Ta gyara dakin ta' kasancewa jiya nusy WAJEN umma ta kwana shiyasa t'ayi aikin ta .

Atsanake...



Zuwa 'karfe tara kowa ya hallata WAJEN brek .


Fatima tana CIN abinci sam babu walwala tare da ita Abba da kansa ya Lura da Haka.


Deen yace anti Fatima naga baki cin abincin sossai.


Murmushin yake tayi tace tace bakomai Deen .


Sanyi ne kawai kedamuna baka garin ya canza sossai ba.


Murmushi yayi yace kuma hakane m'y anti.


Khalid n'a kallon su yanacin abinci .


***


Bayan kowa ya watse duk Balaraba tazo ta kwashe kwanuka ta gyara WAJEN.



Fatima ganin babu kowa falon cikin hanzari ta tafi dakin ta.


Tadauko Jakarta da akwatin Kayan ta.


Tafito harabar gidan ta hango mallam isa ...


Tunani take Taya zata fita be ganta ba.


C'en dabara ya fado mata.


Ta ajiye jakarta ta gèfe.


Gun mallam isa ta nufa tace yww mallam isa inakwana.

Fuska saké ya amsa mata.


Daman ko kanada biro ka aramin banga nwa ba.


Eh inada bara induba daki n'a inazuwa...


Yana wucewa aguje taje tadau Jakarta tabar gidan.



Mallam isa yadawo beganta ba yace to hajiya ina taje ne bayan Bata karba ba.


Mu haɗu a littafi na 10 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah