FATIMA ZAHRA SA'EED

2

by @muntasir1997

Washegari ya kama ranar lahadi ne, misalin ƙarfe goma da rabi na safiya motar Asiya ce ƙirar HYUNDAI ke cilla gudu a saman titi tamkar masu shirin zuwa ƙarshen duniya a ƙayyadajjen lokaci. Asiya ce ke tuƙa motar yayinda ita Zahra take gefen mai zaman banza. Sunyi kyau har sun gaji kai kace gasar sarautar kyawun duniya suka nufa. A cikin motar suke cigaba da tattaunawa akan matsalolin gidan Alhaji, Asiya ta cigaba da fayyacewa Zahra dukkan wasu al’amura da suka shafi gidan, tare da bata shawarwarin da take ganin zasu taimaka mata.

Lokacin da suka isa gidan ƙarfe sha ɗaya saura mintuna goma sha uku. Asiya tayi horn aka buɗe musu wawakeken gate ɗin gidan mai kama da ƙofar shiga gari. Ta danna hancin motar zuwa harabar adana motoci bayan sun gaisa da mai gadi. Ta gyara parking motar inda ta saba ajiye motar tata. Jim kaɗan suka fito daga motar, tuni Zahra ta gama ƙarewa harabar gidan nazari, wani irin zumuɗi ne kwance akan fuskarta wanda ba lallai ne daga kallo ɗaya mutum ya fahimci haka ba, ita kaɗai ta san abinda take aiyanwa a ranta. Suka tunkari ƙofar shiga babban falon gidan, a lokacin ne kuma bugun zuciyarta ya ƙara gudu, sai dai bata yarda kokaɗan Asiya ta fuskanci wani canji a tare da ita ba har suka ƙarasa bakin ƙofar falon, Asiya tayi knocking, jim kaɗan aka zo aka buɗe musu ƙofar, wata matashiyar budurwace wacce ta kasance ɗaya daga cikin hadiman gidan, ta russuna ta gaida Asiya tare da baƙuwar data gansu tare. Cike da kulawa ta amsa, “Yauwa Hajara, mun kwana lafiya?” 

“Lafiya lau.”

“Sanar da Hajiya mun iso dan Allah Hajara.” Hajara ta amsa da to ta juya ta nufi sashen Hajiyar. Ita kuma ta juya ga Zahra tace, “Bismillah mu ƙarasa mana, kya tsaya a nan?”

Zahra lumshe idanunta tayi yayinda zuciyarta ke cigaba da luguden duka, ta sa ƙafarta a hankali cikin falon, wani ni’imtaccen ƙamshi wanda ya cakuɗu da tatacciyar sassanyar iskar A.C suka marabce ta, sai taji ta tsinci kanta cikin baƙon yanayi. A hankali kuma ƙwaƙwalwarta ta fara bijiro mata da wasu tarin ɓoyayyun ƙudire-ƙudirenta, ga dukkan alamu haƙarta zata cimma ruwa, ga dukkan alamu mafarkinta zai iya zama gaskiya, ga dukkan alamu ranar yau zata kasance mai matuƙar muhimmanci a gareta, ga dukkan alamu yau zatayi arba da abinda zuciyarta ta daɗe tana tanadi a kansa… ga dukkan alamu yau… abubuwa da yawa zasu faru.

Ta dage ƙwarai dan kar Asiya ta farga da sabon yanayin da ta shiga, ta tattaro dukkan dauriyarta da ƙarfin halinta ta aza a fuskarta, ta ƙirƙiri murmushin wucin gadi ta adonta fuskarta dashi.

‘Lallai masu kuɗi suna hutawa.’ tace a zuciyarta. Yayinda a zahiri hancinta ya shaƙo mata wani shahararren ƙamshi wanda shi ya ankarar da ita ƙarasowar Hajiyar. Rass! Gabanta ya faɗi lokacin da suka haɗa ido da Hajiyar, tayi saurin janye idanunta daga na Hajiyar tare da sunkwi da kai ƙas. Ita kuwa Hajiyar tsayawa tayi ta ƙare mata kallo tsaf sannan ta taɓe baki ta ƙarasa gujera ta zauna.

“Ina kwana Hajiya?” Asiya ta gaida Hajiyar.

“Lafiya.” Ta amsa a daƙile.

“Ina kwana Hajiya?” Ita ma Zahra tayi kamar yadda Asiyar tayi. Ko kallonta Hajiyar ba tayi ba, maimakon hakan ma sai ta juya ta dubi Asiyan cikin gadara ta tambayeta, “Wannan ita sabuwar mai kula da Faruƙ ɗin?” “Eh itace.” Ita ma Asiyar ta faɗa da kakkauran sauti, kana ta ɗora “Ayi mana iso gurin Alhaji.” Hajiyar ta miƙe ta fara tafiya cikin isa da taƙama, “Sai ku jirashi, yanzu suna online meeting” 

Zahra da Asiya suka dubi juna, ‘online meeting?’ zahra ta aiyana a ranta, ‘to akan me?’ ta kuma tambayar kan nata. A zahiri kuma Asiya miƙewa tayi tare da cewa, “Ok, Zahra zo mu ƙarasa gurin mutumin.” Kamar dama hakan take jira tayi zaraf ta miƙe ta bi bayan Asiyar data doshi wani sashi daban. Hajiyar ta juya ta bi su da kallo, taja dogon tsaki, “Wahalallu.”

Ɗan madaidaicin falo ne wanda ya ƙunshi ɗakuna daban-daban, akwai ɗakin karatu wato study room, sannan akwai gym wanda yake ɗauke da injina na motsa jiki irin na mutane masu larurar Faruƙ. Bayan su kuma akwai resting room da ainahin bed room. Kai tsaye bed room Asiya ta jagorance su suka nufa inda a nan take saka ran ganin Faruƙ ɗin. Sallama ta fara yi sannan ta tura ƙofar ɗakin a hankali. Kamar yadda ta tsammata yana zaune akan wheel chair a gabansa wani ɗan madaidaicin teburi ne da computer sa akai yana yin game da ta zame masa ƙa’ida, kullum sai yayi. “Game at this moment Bamboy (game a wannan lokaci)?” Asiya ta faɗa yayinda ta ƙarasa gabansa da sauri ta durƙusa dai dai yadda zata iya kallon fuskarsa. Ya juyo da karkataccen kansa, fuskarsa fal murmushi ga dukkan alamu yau babu mood na anxiety a tare dashi, Kamar yadda yake magana da juyayyen bakinsa wanda ba ko wace kalma ce ke fita dai dai ba yace, “Good morning Mrs.” (sunan da yake kiranta dashi kenan)

“Ka tashi lafiya Bamboy?” Bata jira ya ƙara magana ba ta cigaba, “Yau nazo maka da sabuwar Mrs ɗinka ku gaisa.” Ya fara kiciniyar ɗaga kansa dan yaga wacce aka zo da ita, ganin yana neman faɗuwa daga wheel chair ɗin yasa tayi saurin dafa shi, “Hold on Faruƙ, basai ka matsawa kanka ba, tare fa zan tafi in barku.” Nan da nan taga yanayinsa ya fara sauyawa daga murmushi zuwa yanayin damuwa, “Sorry ɗan ƙanina, ba fa tafiya zanyi forever ba, zan dinga zuwa ina ganinka time to time (lokaci lokaci), aure zanyi, ya zame min dole ne kuma hakan shine abinda ya dace, saboda kar in tafi in barka alone ya sa na zaɓo wacce nafi ƙauna cikin ƙawaye na dan ta cigaba da kula dakai, kuma I promised (nayi maka alkawari) zata kula dakai fiye dani, fiye dasu Kabiru, fiye da kowa ma, ka yarda dani na san hakan will surely pain you (hakan zai dameka) amma bamu da other options (wani zabi) da zamu ɗauka wanda ya wuce hakan, kayi min uzuri kaji Bamboy, kar kayi fushi dani kaji Daddy’ son.” Ta ƙarashe maganar da sigar da take amfani a duk lokacin da take son yin convincing (gamsar) ɗinsa akan wani abu. Babu laifi fuskarsa ta sassautu daga mood ɗin da ta fara shiga, “Yauwa ko kai fa, nasan ba zaka taɓa fushi dani ba, kuma nasan zaka so ANTY ZAHRA wataƙila ma fiye dani, ko fiye da Daddy ma zance? Kai ina! Never! Babu wanda ya isa ya ƙwace son Daddy a zuciyar Bamboy, haka ne ko?”

Gyaɗa kansa yayi cikin son nuna farin ciki a fuskarsa, “Where is my new Mrs?” (ina take?) Ya tambaya yana jefa idanunsa zuwa bakin ƙofar. Sai a lokacin Asiya ta farga ashe Zahra bata shigo ɗakin ba, ta miƙe da sauri ta nufi ƙofa. Zahra na tsaye ajikin bangon ɗakin, idanunta a rufe suke yayinda hannayenta biyu ta ɗora su a saman ƙirjinta dake ta tsananin bugawa, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, ita kaɗai ta san zaruruwan da ƙwaƙwalwarta ke saƙa mata… jin an dafa ta yasa tayi saurin dawowa hayyacinta, ta buɗe idanu sukayi arba da Asiya. Asiya ta ƙare mata kallo sama zuwa ƙasa. “Lafiyarki kuwa? Tunda muka shigo gidan nan na lura gaba ɗaya yanayinki ya canza, gashi kuma yanzu kin tsaya baki shigo ba meke faruwa ne?”

Zahra ta sauke gauron numfashi, “Babu komai ƙawata, mu je.” Akwai rashin gamsuwa a tattare da Asiya, amma da yake ba lokacin bin ƙwaƙƙwafi bane yasa ta share ta juya zuwa cikin ɗakin.

Dafe ƙirjinta Zahra tayi tare da karanta bismillah a zuciyarta sannan tasa ƙafa ta shiga ɗakin. Karaf! Idanunsu suka gauraya da juna, Rass! Gabanta yayi mummunan faɗuwa, nan da nan idanunta suka rufe, ƙwaƙwalwarta ta tafi hutun wucin gadi, gaba ɗaya sai taji wata irin juwa na ɗibarta ƙafafunta na neman gagarar dakon gangar jikinta da taji yayi mata nauyi da kilo masu yawa, dole ta zaɓi zama jaɓar a dandagaryar ɗakin, hakan ya ja hankalin Asiya ta juyo da sauri ta kalle ta sai dai bata tanka ba, juyawa tayi ga Faruƙ cikin murmushi tace, “Faruƙ ga Anty Zahra, Zahra ga Faruƙ.” Zahra ta lura idan ta biyewa zuciyarta zata sata ta buɗe ƙofar da Asiyan zata fuskanci wani abu a tattare da ita, wannan ta sa ta tattara dukkan nutsuwarta guri guda ta fatattaki dukkan wani ruɗani data shiga, ta ari murmushi ta aza fuskarta. “Sannu Faruƙ! Yaya jikin naka?”

“Feeling better” ya faɗa tare da zuba mata korayen idanunsa. 

Sauyin da suka ji na yanayin ƙamshin ɗakin a cikin hancinansu ne ya tabbatar musu da shigowar wani cikin ɗakin, “Salamu alaikum” Alhajin yayi sallama yana ƙoƙarin ƙarasawa garesu fuskarshi cike da sassanyan murmushi. Zahra tayi babban kuskuren karambanin ɗaga kanta suka haɗa idanu da Alhajin, a wannan karon sai da taji tamkar zuciyarta zata keta ƙirjinta ta fito waje dan tsananin bugawar da tayi, har abada bazata taɓa mance wannan fuskar ba, yaya ma za’ayi ƙwaƙwalwarta ta goge mata hoton fuskar da ta share sama da shekaru ashirin tana haddarta, ta yaya zata manta fuskar da dukkan ƙudirinta akan ta yake?. Fuskarsa ce dai babu abinda ya canza sai yanayin girma da ya bayyana a jikinta. Bata yadda sun sake haɗa ido ba dan wani tunani daya ɗarsu a zuciyarta na ganin kar yayi saurin ganeta kamar yadda ita tayi saurin ganeshi, sai dai ga mamakinta bama ta ita yake ba, kamar ma bai lura da kasancewarta a gurin ba.

“Sorry fa, tun ɗazu Hajiya ta sanar min da zuwanku da yake muna gabatar da meeting ne yasa kuka jini shiru, ina fatan kunzo lafiya.”

“Lafiya lau Alhaji, ai muna nan ma gurin mutumin muna shan hira.”

“Faruƙ rigima! Yau tun safe ake aikin wannan jarababbiyar game ɗin… oh sorry ba jarababbiya ba.” Yayi saurin bauɗewa ganin yadda lokaci guda fuskar Faruƙ ta sauya zuwa yanayin jin haushi da ɓacin ran abinda yace. Ya matsa ya sa hannu ya shafi kan Faruƙ ɗin yace, “Kar ka damu my son, duk abinda kake so shi zakayi.” Ya juya dubi su Asiya, “Mu koma falo ko? Sai mu cigaba da tattaunawa a can… baƙuwa ina miki barka da zuwa.” Sai a lokacin ya bada hankalinsa ga Zahra wacce gaba ɗaya jikinta ya gama yin la’asar, kiɗima da gigita sun lugwigwita mata dukkan kuzarin data yi guzirinsa. Da ƙyar ta iya ɗaga harshe ta amsa da taƙaitattun kalmomi. Alhaji da kanshi ya tura Faruƙ zuwa falo suka rufa masa baya.

A cikin katafaren falon Haj. Ikilima ce ta hakimce bisa kujera hannunta riƙe da kafceciyar wayarta data kusan girman littafi, da alama waya ta gama yi. A haka suka tarar da ita, ta bisu da sakaren kallo har suka zauna a kujerun. Faruƙ yana gefen mahaifinsa , Zahra da Asiya suna kujera ɗaya. Suna zama aka fara gabatar musu da ababen sha da motsa baki.

Falon ya ɗan ɗauki shiru na wasu ƴan daƙiƙoƙi kafin Asiya ta ƙatse shirun da cewa, “To Alh. Ga Zahra nan, duk da dai na riga na gabatar maka da ita tun tuni amma ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, dan haka ga ta nan sai ta gabatar da kanta.” Ta ƙare tare da kai dubanta ga Zahran.

Haƙiƙa da Asiya tayi shawara da ita kafin ta furta hakan da bata bari tayi wannan katoɓarar ba, yanda take jin harshenta yayi mata nauyi bata jin zata iya furta wasu dogayen jumloli bare har ta tashi wani labari da zai bayyana ita wacece a taƙaice. Dalili kenan daya sa ta shiga muskuce-muskuce kamar wacce cinnaka ke mintsina. Duk suka zubo mata idanu wanda hakan ya tilasta mata yin ƙasa da kanta, har yanzu ta kasa yiwa Alhaji cikakken kalo balle ƙwaƙwalwarta ta samu damar saƙa zaruruwan nazari akansa, haka shima Faruƙ, tana so ta ƙare masa kallo dan ta tantance kamanninsa, zubin halittarsa da sauran abubuwan data ƙudiri gabatarwa amma fargaba da tsoro sun mata shamaki ga duk tanade-tanadenta.

Jin shirun ya tsawaita yasa Alh duban Asiya da wani sabon yanayi daya bayyana a fuskarsa yace, “Asiya ƙawar taki lafiya take kuwa? Na ganta gaba ɗaya cikin sanyin jiki take.” Murmushi tayi ta dubi Zahran, “Hmmm! Haka take, wani lokacin akwai miskilanci.”

“Kice hali yazo ɗaya kenan ita da mutumin, lallai zamu dinga shan drama a gidan nan kenan.”

“Lallai kam.”

Duban Zahra Asiya tayi, “Ya kamata muyi abinda ya kawo mu ƙawata, yau fa nake son kaiwa Naja’atu Bala invitation card, kinga kuwa idan bamu yi sauri ba lokaci zai ƙure mana.”

“To ni mai zance Asiya? Kince kin faɗa musu komai akaina to me kike so in ƙara a kai, ko kuwa so kike in faɗi abinda zai ƙaryata abinda kika faɗa?” Zahra ta faɗi haka cikin wani yanayi mai kama da shagwaɓa.

“Ai cewa akayi waƙa tafi zaƙi a baƙin wanda ya rera ta” cewar Alhaji.

Kanta a ƙasa tace, “Kamar yadda ta faɗa sunana ZAHRA SA’EED, ina zaune ƙarkashin kulawar ɗan uwan mahaifina, nayi karatu har tsayin matakin degree a fannin halayyar ɗan Adam wato psycology, sannan nayi kwasa-kwasai da dama da suka shafi clinical psycology da sauran abubuwan da suka shafi physical therapy, na fara yin aiki da wata rehabilitation center amma wani dalili yasa na dakata da aikin. To wannan a taƙaice shine labarina.”

Murmushi kawai Alhaji ke yi tun da ta fara magana har zuwa ɗisa ayarta, dan haka tana ajiyewa ya jefo mata tambayar ta zo ranshi a lokacin, “Banji kinyi zancen aure ba, KO BAKI DA AURE NEHHHH?”

Kamar saukar guduma haka taji tambayar ta dirar mata a ƙwaƙwalwa, nan da nan ta kiɗime, tambayar tazo mata a bazata, bata taɓa tsammanin haka daga gare shi ba, to ko ya shaida ta ne? Tambayar data ji wani sashe na zuciyarta ya antayo mata kenan wanda kuma hakan ya tilasta mata sabuntuwar fargabarta. A ɓangaren Alhajin shima kuma sai jikinshi yayi sanyi daya fuskanci kamar tambayar tashi ta sosai mata rai, amma duk da haka sai ya basar ya ma maida dubansa ga ɗansa wanda ko ƙwaƙƙwaran motsi baya yi.

“My son, ai kai itama wannan Antyn taka gwauruwa ce kamar waccan, kaga ita ma nan gaba sai tace zatayi aure ta tafi ta barka, ina ganin maganin hakan kawai AURA MAKA ITA ZANYI!”

Tabbas wannan maganar ta kusa tsinko zuciyar Zahra, dan ji tayi gaba ɗaya komai ya tsaya mata cak! Wai me mutumin nan yake nufi ne? shin me ya kawota gidansa ma yake neman jawo mata mummunan ciwon hawan jini a ranar farko?

A ɓangaren Asiya kuwa dariya ta saka harda tafawa ta dunƙule hannunta ta ɗaga babban ɗan yatsanta alamun jinjina ga Alhajin. “What a good idea (kyakkyawan tunani) Alhaji! Wallahi kamar kasan dama kuwa babu wanda yake a layi, tun tana da jajayen sahu ta hana samarin da ke mata zarya a ka dama, yanzu kuwa tsufa ya fara zuwa samarin sun janye ƙafa, kaga mu shikenan kayan mu sun tsinke gindin kaba sai muyi tuwo-na-mai-na kaga sai ta cigaba da lelen abinta.”

“Lalala ban yarda ba, bazan bari ɗana ya auri tsohuwa ba sam!” Haj. Ikilima tasa baki.

Alh ya kalleta yana dariya, “Ba zaki bari ɗan naki yayi kwaikwayon ma’aiki S.A.W ba kamar yadda ya auri wacce ta girme masa a farkon aurensa? Ai kinga yin hakan babbar sunna ce kuma nasan my son bazai ƙi haka ba ko?” ya ƙare da duban faruƙ wanda ya juyar da kansa can gefe ya ma ƙi yarda su haɗa ido da mahaifin nashi.

“Shikenan dai yanzu mu bar rahar haka nan mu koma kan abinda yafi muhimmanci… ammm Malama Zahra nasan dai ƙawarki tayi miki bayanin komai, amma kamar yadda kema kika gabatar mana da kanki haka ya kamata nima in gabatar miki da kanmu da kuma maƙasudin daya yasa nasa a nemo min ke…” ya ɗan numfasa, “Da farko dai kamar yadda kika sani sunana ALHAJI SA’EED wanda aka fi sani da BABAN NAIRA, na fuskanci ma ashe sunan MAHAIFINKI gareni, abu yayi kyau .” Da zolaya ya faɗi haka yana duban Zahra wacce har yanzu kanta a sunkuye yake. Ganin bata ɗago ba yasa cigaba “wannan mai ɗakina kenan Haj. Ikilima sarauniyar matan farko da ƙarshen zamani” Haj. Ikilima ta saki uban murmushi cikin jin faɗin kan irin kirarin da Alhajin yayi mata. “Faruƙ shi kaɗai ne ɗana ɗaya tilo da Allah ya bani a duniya wanda nasha matuƙar wahala kafin na sameshi, sai dai da Allah ya tashi bani shi sai ya bani shi cikin tarin larurori da naƙasun da suka zama tarnaƙi garemu dashi baki ɗaya. Tunda aka haife bai taɓa taka ƙafarsa ba yau kimanin shekaru ashirin da biyu kenan, hasali ma ƙafar tashi ba’a gama halittarta ba, sannan kansa a karkace, harshensa baya karkaɗawa, suma ƙwayoyin hallitar bakinsa wato cells basu gama kammaluwa ba yazo duniya, dalilin daya saka kenan baya iya furta wasu kalmomin dai dai. Baya ga wannan kuma binciken likitoci ya tabbatar da yana ɗauke da cutar ASPERGER’S wato asperger syndrom wani yanayi da akan haifi yaro dashi da zai iya zuwa da wasu ɗabi’u da suka bambanta da sauran lafiyayyun yara da ake haifa, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da rashin son shiga mutane, rashin iya haɗa ido da mutum, basa iya yin magana a mafi yawan lokuta, basa iya abota da mutane, da kafiya kan abinda ransu ya aiyana musu. Sai dai kuma suna da tsantsar basira wacce ta shallake hankali, wani lokacin sukan yi abinda lafiyayyen mutum bazai iya yi ba, kuma ita ba ɗaukarta ake yi ba, bincike ya nuna cewa anfi gadarta daga ƙwayoyin hallitun iyaye, sannan kuma bata da taƙamaiman magani, kuma in ta kama mutum yana iya kaiwa har ƙarshen rayuwarsa tare da ita. Babu wani magani dazai magance cutar baki ɗaya sai dai kawai a samarwa mai ita extra ordinary care (kulawa ta mussaman) tare da physical therapy wanda su zasu taimaka masa wajen gudanar da rayuwarsa ba tare da ya faɗa cikin mentality problems ba… waɗannan sune kaɗan daga cikin bayanai dana samu a game da larurar Faruƙ wanda nasan kin riga kin san komai a kanta.

Da farko na tashi hankalina kan wannan larurar da sauran abnormalities ɗin da suke tare dashi, munje ƙasashe da dama mun ga likitoci daban daban amma bamu samu nasara ba, a ƙarshe na haƙura muka dawo gida bayan na gudanar da bincike da kaina akan larurar da kuma mafitar data kamata in nema, wannan dalilin yasa na nemi waɗanda suke da sani akan halayyar ɗan adam musamman a irin wannan ɓangaren da su dinga bashi therapy da zai bashi damar rayuwa mai kyau, to kan haka muka haɗu da Asiya har tsawon shekaru uku muna tare har kawo yanzu da Allah ya ƙaddara lokacin aurenta, wannan dalilin yasa na bata dama ta nemo min wacce zata cigaba daga inda ta tsaya sai Allah ya sa ta kawo min labarinki, to madallah da zuwanki kuma ina fatan zamu samu abinda muke so daga gareki kamar yadda mukayi tsammani.”

Tuni jikinta, zuciyarta da ƙwaƙwalwarta sunyi laushi luɓus, zantukansa sun ƙarasa sarayar mata da kuzarinta tas, sai dai ba iya wannan taso ji daga gareshi ba, ya ɓoye mata abubuwa da yawa kamar yadda ita ma ta san ta ɓoye masa abubuwa da yawa. Amma duk da haka taso taji ya ɗauko wata gaɓa mai muhimmanci cikin labarin wacce ta tabbatar idan taji zata ɗan samu sassaucin abinda take ji a ranta game dasu. Amma zata bi komai a sannu har ta samu ta kai inda take son zuwa. Tayi matuƙar ƙarfin halin ɗaga harshe da ƙyar tace, “Bani da matsala in sha Allah.”

“Masha Allah, yanzu sai maganar yanayin gudanar da aikin, kinga ita Asiya ba anan take kwana ba zuwa take da safe ta koma gida da dare, shin kema hakan zaki cigaba dayi ko kuwa mu baki matsugunni ki dawo kacokan nan ki cigaba da aikin dan ina ganin kamar haka zai fi sauƙi.”

Ba ita da aka yiwa maganar ce ta girgiza ba, Haj. Ikilima ce ta matuƙar girgiza da jin hakan, ‘kai! Me Alhaji ke nufi da ta dawo nan?’ abinda ta aiyana a ranta kenan, kuma har a fuskarta an samu sauyin yanayi, ta ƙanƙance idanu, bata bari wani ya tanka cikinsu ba ta jefo tata togaciyar ga zancen Alhaji. “Alhaji! Ya zakayi saurin yin wannan maganar? Macece ita fa, ta yaya kake tsammanin zata bar gaban iyayenta ta taho wani gida aiki? Me kake tunanin hakan zai haifar?”

“Babu abinda hakan zai haifar sai abinda zuciyarki ta aiyana miki” Ya bata amsa kai tsaye.

Ta ƙara tamke fuska, “Alhaji yaron nan fa ba ƙaramin yaro bane, na tabbata ba dan wannan larurar da yake da ita ba da yanzu ya fara yi maka zancen aure.”

“Na san da wannan, kuma tuntuni nayiwa hakan kyakkyawan tanadi.”

“To amma Alhaji…”

“Kinga Ikilima dan Allah ki saurara min haka, ki barmu muyi abinda ya tara mu dan Allah.” Da alamun ɓacin rai a cikin wannan furucin nashi. Dole taja bakinta tayi shiru ba dan kalmomin bakinta sun ƙare ba, a’a sai dai dan kar ta nuna maitarta a fili su ɗora mata zargi, itama ta ƙudire a ranta zata bi komai a sannu har akai lokacin da zata juya duniyoyinsu a tafin hannunta.

“Ka bani lokaci inyi shawara da gida, abinda muka yanke na sanar da Asiya ta faɗa maka.” Cewar zahra.

“ko kuma dai ki sanar min kai tsaye ba, baki da number ta ne?” shiru tayi babu amsa, Asiya ce ta amsa tambayar da sauri, “Wallahi Alhaji nice na sha’afa ban bata ba, amma babu damuwa in mun koma gida zan bata.”

“Shikenan babu damuwa,” ya juya ga ɗan nasa, “my son, ni banji kana welcoming ɗin Antyn taka ba, ko baka farin ciki da samun sabuwar Anty?”

“She is welcome (ina mata maraba)” ya faɗa da ƙaramin sautinsa da ba kowa ne ma yaji me yace ba.

Asiya ta miƙe tana duban agogo, “Alhaji mu zamu wuce, sai yadda shawarar ta kaya zaka ji.” “ok babu damuwa, yanzu ke shikenan kin tafi?” “A’a Alhaji, cikin satin nan ne kawai nake busy, amma nan da ranar laraba zan zo muyi sallama sannan muyi handing over da mutuniyar.”

Alhaji Sa’eed ya karkace ya zaro kuɗi masu kauri ya miƙo musu tare da cewa, “Ga wannan kwa ƙara mai a mota.” Asiya ta saci kallon Hajiya Ikilima dan taga yadda fuskarta zata karɓi abin, bata ga komai da zata iya ɗorarwa ba a fuskar tata hakan yasa ta miƙa hannu ta karɓi kuɗin tare da godiya. Sukayi sallama suka fice.

*

Abubuwan da suka biyo bayan hakan sun haɗa da auren Asiya da akayi da kuma amincewar fara aikin Zahra sai dai ba kwana zata dinga yi ba, zata dinga wuni ne kafin tafiyar tayi nisa, idan taga yanayin tsayuwar ludayin sai ta yanke shawarar gaba. Sunyi handing over aiki da Asiya yayin da ita ta samu ta gomashin ƙarin albashi kan wanda ake biyan Asiya a baya.

Wannan kenan.