MASOYA UKU

Chapter 8

by @nanahaleema11

*MASOYA UKU*

_(The three lovers)_


_(True love, intense jealousy & betrayal.)_



Page 8



Not edited🤙🏻


...........Bayan an idar da sallar asuba kamar kullum Mai martaba Sarki shida aminin sa sun jero suna tafiya Daddy ya duba inda Ammar ke zama yace, "Aa wai ni kam yau Ina Ammar nee ban ganshi ba?".


Mai martaba Sarki shima yace, "Abinda nake tunani a raina kenan nima, Anya qalau yake kuwa Dan babu abinda yake Hana shi fitowa sallah." Daddy ya Kalli gefen sa yace, "Ahmad maza keja dakin Ammar kaga lafiya yake bai fito sallah ba, Allah yasa dai ba ciwon sa bane ya tashi."



Ahmad ya nufi part din Ammar da sallama ya shiga d'akin ya hango shi can k'arshen gado yana rawar sanyi, da sauri ya k'arasa gare shi yace, "Yaya Ammar lafiya me ya same ka? Ko ciwon Kane ya tashi?"


Zame blanket din yayi ya dago kai murya a dashe yace, "Ahmad bani ruwa da sauri". Da sauri Ahmad ya dauko masa ruwa ya bashi, Dakyar ya mike zaune ya bude jarkar ruwan Yana Sha yana runtse ido.


Ahmad yace, "Haba Yaya yanzu baka da lafiya shine babu Wanda ka sanarwa?." Murya can kasa yace, "Kaga Ahmad bana son magana Kuma bana so kowa yasan da maganar rashin lfyr nan." Cike da mamaki Ahmad ya kalle shi yace, "Au rashin lfyr ma abin b'oyewa ne? Bayan kasa yadda kake Shan wahala idan ciwon ka ya tashi."


Banza yayi masa Baice komai ba ya maida kansa ya kwanta.


Fita Ahmad yayi ya koma inda ya bar su daddy.


Daddy yace, "Ya akayi Ahmad lfy yake?". Ahmad yace, "Baya jin Dadi ne shiyasa bai iya fitowa ba Amma Yanzu yasha magani ya kwanta."


Daddy yace, "To madallah Allah ya bashi lfy, Amma gsky bashi da lfy sosai tunda har ya kasa fitowa sallah."


Tafiya suka cigaba da yi suna Hira shida aminin sa.


Da misalin karfe Sha daya na safe Ammar ya farka da salati a bakin sa, mik'ewa yayi Dakyar duk da yaji saukin ciwon kan dana kirjin ya shiga band'aki ya watsa ruwa hade da dauro alwala, a bakin mirror ya daure da rigar wanka gashin jikin sa ya kwanta sai digar ruwa yake, lumshe Ido yayi can ya bude ido ya dauko body lotion Mai kamshin gaske ya shafe jikin sa, body spray ya dauk'o ya feshe ko Ina na jikin sa Nan take dakin ya dau kamshi, ajiyar zuciya yayi ya mike ya nufi jikin wadrop ya bude ya zubawa kayan nasa Ido, wani blue din wando ya dauko hade da farar riga ya ajjiye a kan mirror, bbu bata lokaci ya shirya ya tsaya gaban mirror ya dauki perfume after dressing ya fesa a jikin sa, sallaya ya shimfida ya tayar da sallar walaha kamar kullum bayan ya idar yayi lazami ya mike tsaye.


Lokaci d'aya maganar Amatullah ta Fad'o Masa a rai, runtse ido yayi Nan take idon sa ya kada ya koma ja, da baya ya koma ya zauna a bakin gado ya dafe Kai,


Turo kofar da akayi yasaya dago Kai ya Kalli Mai shigowa, Umma ce ta shigo ganin haka yasa ya mike ya durkusa har kasa yace, "Umma barka da safiya."


"Barkan ka? Meya same Kane haka ka fada lokaci daya? Kodai ciwon Kane? Mikewa tsaye yayi yace, "ciwon Kaine Umma ba yadda kuke tunani bane ba"


Umma tace, "Badai Wanda ka Saba yi bane ba?". Daga Mata Kai yayi yace, "Bashi bane ba in shine ai ynz ban tashi ba."


"Haka ne sannu, Allah ya Kara lafiya" tana gama fadar haka ta juya ta fice daga dakin.


Komawa yayi ya zauna Jim kadan ya mik:e kamar an mintsene shi ya dau waya ya fita.


Dake ranar Zaman fada ce hakan ya saka ya nufi fada ya Kai gaisuwa a hanya ya hadu da Aunty suka gaisa ya fita daga gidan.


Bai wuce ko Ina ba sai gidan su Amatullah ya shiga ya gaida Dady yayi masa ya jiki suka gaisa da mama ya wuce part din Yaya, tana zaune tana karatun alkur'ani ya shiga ya samu waje ya zauna.


Sai da ta Kai aya ta tsaya ta dago ta kalle shi tace, "Ammaru yau Kaine da safiyar Nan?". Murmushi yayi Wanda rabon sa dashi tun jiya da yamma yace, "Barka da safiya hajiya Yaya".


"Barkan ka dai, Amma qalau kake kuwa Naga ka fada haka?". "Lafiya lau nake, magana nazo muyi dake ne."


Juyowa tayi ta kalle shi tace, "To Ina Jin ka." Gyara zama yayi yace, "Yaya me zai Hana bazaa dakatar da auren Na da Amatullah ba."


Cike da mamaki tace, "Akan wanne dalili kenan?". "No Babu dalili kawai so nake a fasa shi yafi alkairi kawai."


Zuba Masa Ido tayi tana son gano wani Abu tace, "Amatullah tace maka Bata son Kane?". Girgiza Mata Kai yayi yace, "A'a Ni bamu yi haka da ita ba kawai ni nace a fasa auren."


"Ammaru kenan ko mahaifin ka baizai min wayo ba balle Kai yadda kake son Amatullah baza ka tab'a cewa a fasa auren ba sai dai in ita ta nemi hakan, to bara kaji indai Ina da rai a duniyar nan auren ku kamar anyi ne an gama sai da biki ya kusa zaka zo da wannan maganar lefe fa za'a kawo gobe Kuma ka dinga maganar fasa aure an fad'a muku aure wasa ne."


Bud'e baki yayi zaiyi magana Amma ta dakatar dashi da fadin, "wanann hukunci nane an Riga an Gama, Kuma ahir naji ka fad'awa wani wannan maganar."


Duk da hakan yake so a ransa Amma sai yaji Babu Dadi sbida Yana so Amatullah ta samu Wanda yake so itama.


Bai wani jima a wajan taba ya mike ya bar gidan, yazo zai fita Amatullah tana shigowa cikin fararen uniform, tsintar kanta tayi da Kare Masa kallo sabida yadda kayan suka amshi jikin sa kamar balaraben Dubai, ya lura da hakan Amma ya dauke Kai Dan Yana ganin ta babu abinda yake hangowa sai lokacin da Anwar ya rungume ta, duk da idon sa yunwar ganin ta yake Amma hakan ya cize ya yi kamar Bai Santa ba.


A hankali tace, "Ina kwana" ya amsa da "Lafiya" ya bar wajan.


Da kallo ta bishi yadda yake tafiya ma abin kallo ne sbida yadda yake takawa a hankali kamar shine sarkin, mamaki take ganin daga daren jiya zuwa yau ya fada haka a ranta tace _maybe bashi da lfy_ ta shiga gida.


Tun kafin ta karasa Yaya ta hango ta ta Kira sunan ta tace tazo, karasawa wajan ta tayi ta shiga ta zauna tace, "Gani hajiy Yaya."


Kallon ta tayi tace, "Sai Kika je Kika cewa Ammar bakya son sa ko a fasa auren?". Kamar saukar aradu haka taji zancen a kunnuwan ta da sauri ta dago ta kalle ta bakin ta na rawa tace, "Ni yaushe? Shine ya fada Miki haka?".


"Ko daya Kar ki zargi Ammar Babu yarda banyi dashi akan ya fada min ke kike fada Masa a fasa auren Amma yace Shi Sam ba haka bane nice na fuskanci hakan dan yazo ya same mi akan a fasa auren nasan Ammar da hankalin sa bazai so a fasa auren ku ba kece Kika je Kika ce Masa a fasa shi Kuma dake Yana kaunar farin cikin ki yasa yake kokarin cutar kansa."


Ajiyar zuciya tayi Jin bashi ya fada ba tace, "Ni banje nace Masa haka ba kawai shine yake so a fasa auren tunda Kika ji yazo ya same ki ya fada Miki haka."


"Hmmmm yaro yaro ne, wato Amatullah inda kin San waye Ammar baza ki taba fadar abinda kike fada ba, aure dai baza'a fasa ba in ke Kike son hakan to ki sani bazai Yu ba Dole ki aure shi."


"Nidam bance bazan aure shi ba Amma yadda baya Sona Nima bana sonsa ai BA A SO DOLE."


Yaya tace, "a yau na tabbatar da baki da wayo Sam shi Yana k'ok'arin ganin ya farantawa iyayen ki da nasa Amma ke dake farin cikin su baya gaban ki ko a jikin ki ko? Koda baya sonki din ya amince zai aure ki sabida iyayen ku Amma ke dake bakya bin abinda suka ce bai Dame ki ba, shikenan Amatullah kije kiyi duk yadda kike so kinji."


Jikin tane yayi sanyin Jin abinda Yaya tace hakan yasa tace, "Nifa yaya bance bazan aure ba zan aure shi ai Dan iyayen namu Amma batun so ne babu a zuciya ta".


Murmushi Yaya tayi tace, "yaro man kaza, tashi ki bani waje Ni". Mik'ewa tayi ta fice daga parlourn.


Dakin ta ta shiga ta zauna Tana cire Kaya tana tunani tabbas Bata kyauta ba abinda tayi, gwara ta hak'ura ta aure shi din kawai kodan iyayen su, Amma Yaya zanyi da Anwar? Ya zama Dole na daina kula shi ta haka zan samu saukin abinda nake jin a hankali na manta dashi, Ya zanyi da son da nake Masa, ajiyar zuciya tayi ta cigaba da abinda take yi,wayar tace tayi kara ganin Wanda yake Kiran yasa tayi kamar baza ta dauka ba Amma Sai ta kasa ta dauka ta Kara a kunne.


Daga can bangaren Anwar yace, "Zuciya ta ta Jima da narkewa wajan kaunar ki Amatullah, a ko wanne second kaunar ki karuwa take a zuciya ta ki taimaka min ki abaza Kar a rabu Dan Allah, tabbas in na rasa ki dai-dai yake da rasa rayuwa ta, I love u Amatullah I love u so much, wallhi Sam wannan mutumin Bai dace dake ba ba kaunar ki yake ba Kuma in Kinga tarin Yan matan sa sai kin rike baki ki taimaka min beauty" ya fada Yana muryar kuka.


Jin Yana kuka yasa hankalin ta ya tashi har ta manta alk'awarin da tayi ta fara fadin,"Ni taka ce har abada babu Wanda ya isa ya ramu Ina sonka Nima my Anwar duk inda nake kana cikin zuciya ta ka daina kuka Dan Allah."


"Ina so mu had'u yau Amatullah." Ajiyar zuciya tayi tace, "kasan muna exam's yanz karatu bana fita sosai."


"Shikenan beauty cigaba da karatun ki kinji na kira ki video call anjima gobe nazo school na dauko ki."


Sallama suka yi ya kashe wayar.


Zama tayi bakin gado wata sabuwar kaunar Anwar na ratsa ta tabbas Anwar zata aura ba Ammar ba, tunanin lokacin da Anwar yayo hugging dinta ne ya shiga yi Mata yawo a ka, tashi tayi zaune a fili tace, "Meyasa nafi tuna lokacin da Yaya Ammar yayi hugging d'ina fiye dana Anwar? Meyasa Kuma jiki na yafi yin weak dana jini jikin Yaya Ammar? Meyasa banji zuciyar Anwar na beating ba kamar ta Yaya Ammar?" Shiru tayi tabbas babu me Bata amsa sai zuciyar ta, tsaki tayi tace, "Daman ai Dole jiki na yafi sanyi sabida shine bana so" ta fada tana kwanciyar ta.


Shi kuwa Anwar Yana kashe wayar ya Kalli wayar yace, "Tunda baki zamo tawa ba bazan tab'a barin zuciyar ki ba Dole nayi abinda da da kanki Zaki kaso auren, sorry beauty" ya fada Yana murmushin mugunta.