Chapter 10
*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_
_(True love, intense jealousy & betrayal.)_
By
Neat Lady
Page 10
Not edited🤙🏻
..........fita yayi zuciyar sa fes da Jin ta hak'ura zata aure shi duk da Bata so din shi yasan ta yarda zai saka ta taso hakan yasa Yana tafiya tana murmushi.
Washe gari amatullah da wuri ta tashi Dan yau take da final paper hakan yasa da sauri-sauri take gudanar da abinda zatayi, shiryawa tayi cikin uniform din ta ya dauki jaka da wayar ta ta fito da sauri, Bata tsaya bin takan Mama Bata kawai ta fito, waya ta Kira Rahma anan take sanar da ita ai ita tana school ma, kashewa tayi tare da karasowa parking space din gidan.
Mai gadi ta kalla tace, "wai Ina Bala ne?"Mai gadi ya Bata amsa da fadin, "tun dazu ya fita bai dawo ba" dafe Kai tayi kawai ta fito bakin titi Dan tasan in ta tsaya jiran na gidan sarki Bata lkc zata yi gwara ta hau Keke napep.
Kusa mintin ta biyar a tsaye bb mota, dafe Kai tayi tana duba agogon hannun ta tana da exam karfe goma gashi yanzu har Tara da rabi bata tafi bama.
Har motar ta wuce ta dawo ya sauke glass ya kalle ta yace, "Shigo". Ba musu ta bude gaba ta shiga Dan neman taimako take a lokacin.
Tafiya suka Fara yi babu Wanda yake magana sai sautin Ac da yake fita, dakyar ta lalubo magana tace, "Ina kwana". Dago Kai yayi ya kalle ta ya kau da Kai yace, "Lafiya, karfe nawa kike da exam din?".
"Karfe 10" ta amsa tana sunkuyar da Kai, kallan agogon hannun sa yayi yace, "Shine Kuma baki fito ba sai yanzu?". Rau-rau tayi da Ido kamar zatayi Kuka tace, "Na rasa Wanda zai kaini ne shine na fito neman Keke napep."
Kallan ta yayi yace, "Kaf fad'in gidan kice an rasa Wanda zai kaiki makaranta."
Kallan sa itama tayi suka hada Ido ta dauke Kai tace, "basa nan ne duka sun fita Ni Kuma gashi Ina sauri." Dauke Kai yayi shima ya sake fad'in, "meyasa baki shiga cikin gida ba kin nemi Ahmad ba?."
Cike da kosawa tace, "Sauri nake ne shiyasa" ta fada kamar zatayi kuka. Hakan ya saka ya kalle ta daman fuskar sa had'e take babu fara'a cikin ta, ya sake cewa, "first and last kar na sake Jin labarin kin fito kince Zaki hau kake napep, kinji".
Ta amsa da to tana mamakin yadda yadda saki baki suke Hira haka duk da fuskar sa daure take, ita dai burin ta kawai ta ganta a school.
Bai sake ce mata komai ba har suka karasa makarantar, har zata bud'e sai ta juyo ta kalle shi tace, "Nagode" sannan ta bud'e motar ta fita da sauri.
Ajiyar zuciya yayi yaja motar ta ya nufi asibiti.
Isar sa ya fito daga motar tare da bude bayan motar ya dauki jakar sa, har yayi gaba sai ya dawo ya bude motar inda Amatullah ta zauna Yana neman face mask din sa, ganin waya a wajan ya saka ya dauka ya kalle ta ko ba'a fada ba yasan wayar Amatullah ce, rufe motar yayi ya nufi office.
Bayan sun fito daga exams Amatullah ta duba jakar ta baga waya ba hakan ya ta dafe kai tace, "wayyo Allah" Rahma ta kalle ta tace, "Qalau kike wayyo?". Yatsine fuska tayi tace, "Waya ta na manta a motar Yaya Ammar wllahi."
Tsaki tayi tace, "Shine kike wani wayyo Allah in Mun koma gida in ya dawo daga asibiti sai muje ki karb'o, ke ni ba wannan ba, kin fahinci page 10 na handout din community health?".
Amatullah tace, "Ina fa tun jiya nake maimaitawa Amma wallahi na kasa ganewa gashi gobe zamuyi sa ni duk jiki na yayi sanyi." Rahma tace, "Ai kawai in Mun koma kizo muje wajan Yaya Ammar ya Koya mana kin san halin malamin nan Kuma kin san babban course ne Dole mu iya."
Ajiyar zuciya tayi tace, "to maje Allah yasa dai ya Koya mana kar ya yarfa mu". Rahma tace, "bama zaiyi ba insha Allah, yanzu muje muci abinci sai mu wuce gida kinga hadari Yana hadowa".
Ammar kuwa yana ta aikin duba patient daga wanna ya shigo sai wannan ya fita, wayar Amatullah ce take ta Kara hkan ya saka yayi tsaki ya duba screen din wayar, My Anwar shine abinda ya gani a rubuce take ransa ya baci yayi tsaki ya ajjiye wayar akan table ya cigaba da abinda yake yi.
Kiran wayar ne ya sake shigowa ya dafe Kai tare da Kara kallan wayar yaga dai shine yake sake Kira, katse wayar yayi tare da kashe ta gabadaya.
Jin jinginar da kansa yayi jikin kujera kamar an tsikare shi ya Mike ya dauki wayoyin ya saka a aljihu ya kulle office din ya fito, sai a lokacin yaga yadda garin ya had'o da hadari ana ta Iska, bude motar sa yayi ya shiga ya Fara tafiya bai wuce ko Ina ba sai makarantar su amatullah.
Bayan sun Gama cin abinci Rahma ta Kira driver da yke zuwa ya dauke su Amma wayar taki tafiya, ta Kira Ahmad yace Mata baya kusa hakan yasa Dole suka Mike suka fito bakin titi su hau ta haya sabida yadda garin yayi baki har an Fara yayyafi.
Tsayawar su a titi ruwa ya Fara k'arfi ga jikin Amatullah baya kaunar ruwan sama yanzu sai ta Fara rashin lfy, tsayuwar motar Yaya Ammar yasa suka kalli juna cike da mamaki, horn yayi musu alamun su shigo da sauri Amatullah ta bude baya ta shiga ganin Haka ya saka Rahma ta shiga gaba.
Amatullah tana kwance jikin kujera kayan ta a jike ga sanyin AC Nan take ta Fara Jin zazzabi na neman rufe ta, kallan Rahma yayi yace, "Meyasa kuka fito bakin titi ga ruwa? Ina Bala?". Cikin nutsuwa tace, "Mun Kira wayar sa taki shiga Mun Kira Yaya Ahmad yace baya kusa ganin hadarin ya saka muka fito mu tawo".
"Ita Humayra fa" ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba, "basu da exmas yau shiyasa".
Amatullah kuwa tana kwance ta lumshe Ido sanyi na ratsa ta Nan take jikin ta ya Fara rawa, ta mirror ya kalle ta yace, "Bata da Lafiya ne" Rahma ta kalli baya tace, "Eh indai ruwa ya taba ta sai tayi zazzabi daman". Wani uban tsaki yayi cikin fad'a yace, "Sabida rashin sanin ciwon kai yasa kuka fito ai meyasa baku Kira Ni bani ehe"ya fada Yana kallan Rahma.
Jikin ta har rawa yake tace, "kayi hakuri" tsaki yayi kawai tare da kashe AC ya kunne car tempreture motar tayi dumi, kallan ta kawai yake ta mirror ji yake kamar ya dawo da ciwon jikin sa.
Suna Isa gida Rahma har zata bud'e kofar ta fita yace, "Ke! Kar ki sake ku fito sai ruwan nan ya dauke tsaf, Ina zuwa" ya fada Yana budewa ya fita da sauri.
Kallan amatullah Rahma tayi tace, "Sannu bestie" Kai kawai ta daga Mata Bata ce komai ba.
Babu jimawa sai gashi ya dawo duk kayan jikin sa sun jike ya kwankwasa glass din inda Rahma take ta bud'e ta kalle shi, Mika Mata ruwa da magani yayi ya daga mata gira alamun ta Bata Tasha, karb'a tayi ta daga glass din shi Kuma ya koma gida.
Bata tayi ta karba babu musu Tasha ta mayar da kanta ta kwanta, babu jimawa ta Fara jin zafi alamun zazzabin ya sauka sai dai ciwon kai da yake damun ta, sai da suka yi wajan mintina talatin a cikin motar snn ruwan ya dauke. Amatullah ta kalli Rahma tace, "Muje yanzu ai ba'a ruwan". Bude kofar sukayi suka fito tare da kulle Masa motar Rahma ta rike makullin suka nufi cikin gida.
Wanka amatullah tayi ta cire kayan jikin ta ta bude drower ta dauko sudrex ta Sha ta zauna tana ajiyar zuciya.
Rahma ta kalli amatullah tace, "Bestie sai naga kamar Yaya Ammar Yana kaunar ki Allah". Tab'e baki kawai tayi ta Mike ta fice daga dakin.
Bayan sallar magariba Amatullah taji sauki suka dauki handout suka nufi part din Yaya Ammar Dan Koya musu karatu.
Yana zaune a parlourn sa gabadaya hankalin sa Yana wajan Amatullah, sallama sukayi suka shiga ya dago Kai ya amsa suka nemi waje suka zauna, Rahma tayi karfin halin cewa, "Yaya Ammar muna da exam gobe gashi course din da zamuyi goben bamu Gane wani waje ba shine muka zo ka nuna Mana".
Bai kula ta ba sai kallan Amatullah da yayi yace, "Ke y jikin?". Cikin sanyin murya ta amsa da sauki. Dauke Kai yayi yace, "Gobe ma Kya sake fitowa ana ruwa ai, ke Kuma me kike cewa" ya fada Yana kallan Rahma.
Maimaita Masa tayi tare da Mika Masa handout din, karba yayi ya dauko medical glass din sa ya saka sannan ya Fara duba abinda akace. Sai da ya Gama karantawa tsaf sannan ya dago ya kalle su yace, "iya nan ne baku Gane ba?". Daga Kai suka yi alamun eh.
Ajjiye handout din yayi kusa dashi yace, "meye da meye suke haduwa su samar da da?". A tare suka kalle shi ya dauke kansa suka kalli juna sukayi shiru, Jin shiru ya saka ya dago ya kalle su yace, "Daku fa nake magana". Cikin dauriya Rahma tace, "female sperm with male sperm". Daga gira daya yayi yace, "Like how?" Ya nuna Amatullah alamun ta bashi amsa.
Sunkuyar dakai tayi tace, "During sexual transmission" girgiza Kai yayi yace, "Explain". Cike da Jin nauyi Amatullah take Masa bayanin yadda ake Allah ya nufa ake Samar da da har karshe.
Jinjina Kai yayi yace, "Good, Kun Gane abinda wajan yake nufi yanzu?" A tare suka amsa da eh, yace, "meyasa mace tafi saurin daukar virginal infection akan namiji?."
Rahma ta amsa da "Sabida virgina din mace a bude yake ba kamar na namiji ba" daga gira yayi ya sake cewa "Explain well".
Rahma tace, "kamar wajan fitsari ne mace in ta tsuguna a waje Mara tsafta tayi fitsari bata san Wanda yayi a wajan ba maybe akwai Mai wannan cutar da tayi a wajan sai virus din ya taso ya shiga jikin ta, while namiji kuma yadda pravite part dinta zai bude lokacin da zatayi fitsari ba kamar na namiji ba." Jin tayi shiru yasa ya nuna Amatullah alamun ta cigaba.
"Bayan amfani da public toilet ma Ana iya daukar wannan cuta ta hanyar yin tsarki, idan mace ta gama stool wajan tsarki in ta Fara ta gaba zata jawo shi ne zuwa vagina dinta, sabanin namiji da Koda ta gaba ya fara infection din bazai je cikin jikin sa ba." Amatullah ta karasa fada cike da Jin kunya.
Ammar yace, "Good, I hope yanzu Kun fahinci abinda page din ke nufi?" Daga Masa Kai sukayi a tare alamun eh, yace, okay kuzo ku sake research kai dan akwai somemany where da ake iya daukar inpection,in baku Gane ba zaku iya dawowa" ya fada Yana Mika musu handout din.
Rahma ta karba cike da farin ciki tace, "To Mun gode sosai Yaya Ammar". Daga Mata Kai kawai yayi baice komai ba.
Dakyar amatullah ta iya cewa, "Yaya Ammar d'azu nabar waya ta a motar ka?" Kallan ta yayi ya lumshe Ido sannan yace, "Kin barta tana waje na". Kallan sa ta sake yi tace, "tana Ina?". Kafa Mata ido yayi ba daukewa yace, "Zoki caje Ni ki dauka". Shiru tayi Bata ce komai ba tana jiran ya Bata.
Mika hannu yayi ya sauki wayar yace, "Gata nan" ya fada Yana Miko Mata, ta Mika hannu zata karba ya dauke ya hade fuska yace, "make sure ki fadawa masu Kiran ki su dinga sanin lokacin Kira time exams ba time din waya bane ba right" ya Mika Mata wayar ta karba suka fito.
Rahma ta kalli amatullah dake kunna wayar ta tace, "Gaskiya ban taba fahimtar abinda ke wajan nan ke nufi ba sai yanzu ashe ma common abu ne ba me wahala ba,gsky naji dadi wallahi." Amatullah tace, "Nima Haka, Amma ya dinga mata waau tambayoyi ko kunya babu". Dariya Rahma tayi tace, "likitan Mata ne fa kunyar me zaiji ya Saba da irin wnn maganganun da wanda suka fisu ma."
Amatullah tace, "Wayyo my Anwar ya Kira Ni har sau goma, kenan shi Yaya Ammar yake nufi maganar da yayi" ta fad'a tana bude message din da ya turo Mata. Tsaki Rahma tayi ta shige part din su Amatullah tayi gida.
*BIKI*💃