chapter 7&8
by @autarmama
👩🎨👩🎨ƳAR GAN-GAN👩🎨👩🎨
*STORY AND WRITTING BY SALMEERT (AUTAR MAMA,ƳAR LELEN ROYAL STAR🧚♂️🧚♂️🧚♂️*)
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, KI TABBATAR KIN BIYA KAFIN KI KARANTA DAN BAZAN YAFEWA WANDA BAI BIYA BA,SANNAN KUMA WANDA SUKA BIYA KUJI TSORON ALLAH KAR KU FITAR MIN DASHI
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊAN TARWA GAMIDA WA'AZANTARWA HUNMM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITE'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITTE'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCINMU*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAID BOOK, PAGE 9&10
""""""""""""""""""""Daki suka shiga suna dan tattauna maganganu su, shi kuwa Humaid yana chen parlour shi kaɗa sai lallatsa waya yakeyi da alama aiki yakeyi.
yananan zaune *Yar gan-gan* ta fito da shigarta da ta saba domin koda tasa kaya normal, bazata iya zama dasu na 3 hours ba ,dan a cewar ta cizon ta sukeyi.
karar takunta ne yaja hankalinshi ga kallonta ganin irin shigar dake jikinta ne yasa, ya watsa mata wani kyamataccen kallo, tsaki yaja da mugun karfi.
har saida ta runtse idonta domin a rayuwarta, ta tsani ayi tsaki koda bada ita ake ba.
"keee!!!! nonses bakya ganin mutane ne da bazaki gaishesu ba , mutum kamar dabba bayayi abu irin na mutanen kirki sai dai na jahil.." bai karasa ba sai ji kake tassssss,ta wankeshi da wani irin fitinannen mari wanda kararshi ma kaɗai ta isa ta firgitar daka ballan tana zafin shi.
nuna shi tayi tana wani irin huci sai kace zakanya, "kaiiii!!!! dakata bana ciki da irin wannan wulaƙancin dan haka ka kiyaye ko kuma Wallahi nasa amin gunduwa-gunduwa da naman jikin ka", ta fada tana wucewa kitchen abinci kawai ta dauko ta fita daga gidan .
shi kuwa saƙale ya yi ya kasa iya furta komai, ya kuma kasa taɓuka komai ,dan Yarinyar tayi mugun sashi jin shock.
dan rabonda a mareshi yariga da yaman tawa rayuwarshi , shine har wata ajawo, zata mareshi lalle kuwa ya yi alkhawarin lasa mata ɓacin rai fiye da wanda tasa shi.
sosai gurin ya yi jazir, shatin hannun ya fito, abinka ga farin mutum, ga kuma idanunshi da sukayi wani irin rinewa.
yana zaune yana tufka-da-warar-wara dai ga su Ammie sun fito.
tun kafin su karaso ya yiwa Hajiya sallama ta fita waje,ita kuwa Ammie cewa tayi "dan Allah a kawomin ita da karki manta", ta fada tana dan kara jadadda mata maganar.
"yawwa ina ma take muyi Sallama?" cewar Ammie.
"inajin ta fita bata gidan nan", cewar Hajiya tana takowa dan yiwa Ammie rako .
"to shikenan ki gaishemin da Alhaji idan ya dawo".
" to zaiji, insha Allah, ku gaida gida",cewar Hajiya tana juyawa cikin gidan.
********************
police din da suga Daddyn Ihisan ,wadda *Ƴar gan-gan* ta daka ne sukayi nasarar kama Jagwal, direct chaji office sukayi dashi, dukan shi suka fara ba ko sassauci damin an riga an basu order ne.
tun kafin ta karasa labari yazo kunnen ta, hakan yasa ta fiddo wayarta , Daddynta ta kira batayi ring biyu ba ya dauka yana cewa.
"Lafiya dai Mamana, ko kinason na taho miki da wani abu ne , idan zan dawo?" ,ya fada da alamar tambaya.
"Daddy dama Abokina ne yan Bilaja'u suka kama, kuma baiyi musu komai ba hasalima nice nayi laifin da aka kamashi akanshi", tayi maganar da iya gaskiyar ta .
shima Daddyn yasan indai zatayi magana to da iya gaskiyar ta takeyi, hakan yasa yace ,"to shikenan wane policestation ne?".
fada masa tayi bayan sun gama maganar ne ta kashi wayar ta nufi Asbitin dan tasan suna chan suna jiranta.
*****************
wanin yau gaba daya baiyi masa dadi ba domin rashi a jagule take, sosai yake cikin bakin ciki, sannan kuma yake saƙe-saƙen yarda zai rama.
Ammie tayi tanbayar duniyar nan, amma ko magana yakiyi sai dai ta kyaleshi.
*******************
zaune ta samu Yarinyar ana bata abinci a baki, alamar dai sauki ya samu, murmushi Mamar Yarinyar da Yarinyar sukayi.
ita kuwa batayi murmushi ba kawai dai tasaki fuskarta ne, akan da da take cin kushe, yau babu wannan daure fuskar, sai fuskar ta ta tayi fayau, da ita sai wani sihirttacen Annuri yake fita daga kan fuskar tata.
zama tayi kusa da Yarinyar ta dan shafa kanta tana cemusu, "Ya jikin, babu wata matsala ko?", ta fada tana dan warewa Mamar Yarinyar Ido.
"aa babu wata matsala likita ma yace , za'a iya sallamar mu ko yaushe, mun gode Allah ya saka da mafificin alkhairi, Allah ya baki abinda kike nema, ya kuma kareki daga sharrin mahassada", ta fada idonta ya yi kwar-kwar kamar zatayi kuka.
"Ameen ya rabbie" ,ta ansa a kan laɓɓan ta.
suna zaune sai ga wata ta shigo cikin dakin, ganin yarda ta shigone yasa suka kalleta da sauri, ganin *Ƴar gan-gan * ,a dakin ne yasa ta yin turus tana kallon ikon Allah , sai kuma jikinta ya fara rawa, kai kace mazari ce.
"dan Allah baiwar Allah karki cutar damu, Wallahi mu masu matsakaicin karfi ne, kuma mu babu abinda mukayi, dan Allah", ta fada tana zubar da hawaye.
kallonta sukeyi su duka sai chan *Ƴar gan-gan* ta nisa tace, "kinji ni nace kunyimin wani abune, kuma ni ai banayi wa mutum komai idan bashine ya fara ba, amma tun dama kika faɗi wannan maganar sai na tsinke miki harshe saboda abinda kikace batare da kin ji ta baki naba",ta fada tana daure fuska tamau .
aikuwa kara tsurewa tayi ,dan taga alamar rashin imani cikin kwayar idanun *Ƴar gan-gan*.
hakan yasa ta ringa bata hakuri tana kuka, su kuwa su Mama shiru sukayi sunajin wannan lamari, ita kuwa uwar gayyar kawai dan ta tsokani Matar ta fadi haka.
sannan ita tana son irin wannan Action din yana matukar sata nishad...
muje zuwa......
*Ruwan comment Pls*
idan kuna da bukatar wani abu ko littafina to kawai ku tuntuɓeni akaitsaye akan number ta kamar haka ***.
*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE*🧚♂️🧚♂️🧚♂️