MAHAƊIN RAYUWATA

Chapter 3-4

by @ummuaffan

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



Page 3-4



*WACECE AMEERAH*

Malam Sa'adu Kabiru shine cikakken sunan mahaifinmu,haifaffan garin Kaduna a Umguwar Sanusi aka haifesa mahaifinsu Malam Kabiru ya dad'e da rasuwa saidai mahaifiyarsu Baaba Kuluwa tana nan da ranta,sana'ar Malam Sa'adu itace babban shago ne garesa a kasuwar Kawu da yake sayar da kayan masarufi na hatsi danginsu Shinkafa,masara,gero,alkama da dau sauransu,ba laifi yana samun ciniki domin sosai akasanshi,su uku ne gurin iyayensu,babbarsu Macece Mummy Sakina shine na biyu sannan ƙaninsa Lawal,Momy Sakina tana aure Abuja wani attajiri me arziƙi take aure domin babba ne d'an siyasa me riƙe da badafin riƙon ministan Abuja,yaranta hud'u biyu maza biyu mata,shima Baba Lawal yana da mata da yaransa biyu anan gidan muke tare dasu,Matan Babana hud'u ne domin shi mutum ne me son tara mata,




"Matarsa ta farko Hadiza ita ce uwargida wacce muke kira da Yaya bata da ƙyirki ko kad'an masifaffiyar macece ga yawan bin bokaye da malamai,yaranta bakwai,Kabiru da ake kira Abba shine babban duka gidanmu sai Sani da Salis sannan ƙaraminsu D'ahiru,sai matan Sadiya da Karima sai ƙaramarsu autarsu kuma Mariya,dukansu sun girmeni,Matarsa ta biyu itace Annata wato mahaifiyata sunanta Zainabu ita kuwa fulanin Katsina ce kyakkyawa Babana ya ƙaunar Anna matuƙa domin mace me ladabi da biyayya ga haƙuri,irin so da ƙaunar da yake nuna mata ne yasa Yaya ta shiga ta fita domin ta raba wannan soyayya sam ta tsani Anna,mu uku Anna ta haifa,Yayanmu Bashir ne babba sai Yayata Maryam nice ƙarama a d'akinmu kasancewar sunan Kakata aka samin Hauwa'u yasa ake kirana Ameerah,Babanmu yana matuƙar ƙaunata kasancewar sunan Baabarsa gareni nida Yaya Abba mune 'yan lele duk abinda mukeso yake mana,idan anyi Magana yace mud'in iyayensa ne,hakan yasake lurara wutar ƙiyayyata a zuciyar 'yan gidanmu,komai ya gani sai ya sayamin ni kad'aice a gidanmu nake makarantar kud'i sauran duk ta gwamnati suke zuwa,wannan abu yana sakasu baƙin ciki,




      "Uwani ce matarsa ta uku wacce muke kira Inna,itama bata da ƙyirki tafi kowa tsanata a cikin gidan,ita yaranta biyar duk mata Sadiƙa ce babba sannan ƙannanta Kubra Asiya sai Fati da ƙaramarsu Amina,Sadiƙa tafi uwarta makirci bani da abokiyar fad'a wacce ta fita kima ta girmeni,Salamatu ce Amarya wato Anty ba afi wata biyar da auranba yarinya ce domin bata wuce sa'ar Yaya Abba ba,yarinyar abokinsa ce ya aura ba wai sonsa take ba dole mahaifinta ya mata,ba laifi tana da kyawu ga wayewa da ilmi domin saida tayi digiri aka mata aure yanzun hakama tana aiki ne a wani company,shiyasa babu ruwanta da kowa na gidan Anna ce kawai takewa Magana don sosai suke shiri tana bata girma sosai jininsu ya had'u dana Ameerah tana sonta sosai hakan yasa suma 'yan gidan tsanar Antyn domin Yaya da Inna kansu had'e yake,bangaran Anty ya banbanta dana kowa don ita babban farlou ne da d'akunan barci biyu da kitchen da toilet duk a farloun,sa6anin sauran ukun matan duk d'aki daya da uwar d'aka ne sai kitchen da toilet duk a waje guda d'aya suke amfani dashi,Aunty Abinda tayi niyyaryi shi take domin tana da goyan Bayan Babanmu don kusan amarya kuma yarinya duk itace ƙarama a cikinsu gashi ko haihuwa batayi ba,sam baya adalci domin mu zamu karya da koko ne ita kuwa tea da bread dasu madara milo da sauransu gurinta zakaga taliya indomie da su nama kifi amma cikin gida ba'acin hakan,donma Antyn na hanasa da abinda zaiyi akanta yafi haka,shiyasa ni wani lokacin gurinta nakecin abinci domin girkinta daban take,sosai take takewa su Yaya da Inna burki idan suna iskancinsu domin itace ta gaban goshi yanzu,komai tace Baba yayi shiyake mata kuma babu wani asiri da ta masa kawai duk tsabar son da yake mata ne,ko don yaganta ƙaramar yarinya ne akan sauran oho,




"Rahane kuwa itace matar Baba Lawal,itama ba laifi suna shiri sosai da Anna yaranta Hafsa ce sa'ata kuma ƙawata sai ƙanwarta Murja,gidanmu baza'ace ana zaman lafiya ba domin kowa abinda yayi niyya shi yakeyi,haka yaran gidan babu had'in kai kowa kallon kansa yake a sama,an tsani yaran d'akinmu musamman mani da ake kallon Babanmu yafi ƙaunata kaf gidan,ba sai an fad'a ba ni kaina nasan Babanmu yana sona yana matuƙar ji dani,a fili yake nunamin ƙauna gashi sosai nake kama dashi da ka kallesa kasan mahaifina ne saboda kamar da muke,




       "Kakata ma na matuƙar ƙaunata Baaba kenan babu ruwana da kowa ina da natsuwa sosai sanyin halina kesa ni saurin kuka domin magana kad'an saita sani kuka ko magana badamuna tayi ba shiyasa da yawa 'yan gidanmu ba magana ke shiga tsakaninmu ba,saidai Yayana Bishir da Maryam sai kuwa Anty Da Baaba sannan Hafsa,yaran d'akinmu suna da tarbiyya sosai yanzu ina JSS3 A wata makarantar kud'i dake ƙasan layinmu islamiyyama ajina hud'u,wannan kenan,



*CIGABAN LABARIN*


"Bayan na idar da sallar asuba na fito na nufi d'akin Anna,akan sallaya na isketa na duƙa har ƙasa na gaisheta,ta amsa tana kallona kamar zatayi magana sai kuma ta share ni,gyaran d'akin na fara kamar koda yaushe,na gyara gado na share d'akin fes na kunna tsintsiyar ƙamshi nan d'akin ya gauraye na ƙanshi,sannan na fito na fara sharar tsakar gidan,ina cikinyi Sadiƙa ta fito,inayi tana mayarmin baya ban dai kulata ba domin hakan tasaba min,




      "Ajiye tsintsiyar nayi sannan na kalleta kafin nayi magana ta rigani"Banza kawai ko akwai abinda zakiyi,banyi magana na juya da niyyar in wuce inbarta,saiji nayi ta bangazoni,tacimin kwala"so nake kiyi magana kici duka,fincike jikina nayi da ƙarfi har saida ta kusan fad'uwa,tace"bani da lokacinki,nayi wucewata nabarta a gurin inaji sai zagina take bandai kulata ba,D'akin Aunty na koma domin acen nake shirina gashi yau Monday,na iske Aunty har tayi wanka nima wankan na fad'a na fito na shirya cikin uniform d'ina na boko,mai da hoda kawai na shafa sai kwalli,nazo na iske Aunty na kwalliya ita ma ta shirya cikin wata atamfa riga da siket ta yafa mayafi,tare muka fito ta kulle 6angaranta,d'akin Anna muka shiga ta gaisheta nima na mata sai na dawo,na wuce d'akin Inna inda Babanmu ya kwana har ƙasa na duƙa na gaishesa ya amsa cikin fara'a,na gaida Inna ta amsa ciki-ciki tana hararata,"





"Yace"Mamana har an shirya,nace"na shirya Baba,kaina a ƙasa,"to Allah yayi miki albarka,na amsa da "amin,hannu ya saka cikin aljihun wandonsa ya ciro d'ari biyu ya bani kud'in mota dana break,amma nayi nace"nagode Baba sai na dawo,"to Mamana adai kula a hanya kar a tsaya wasan banza,"to Baba na gode,na fad'a tare da ficewa,





          "Tare muka hau keke napep da Aunty,aka sauke ni Skul zan basa kud'in tace"na barshi,godiya na mata tare da wucewa gate d'in makarantarmu,ita kuma suka wuce,





"Bayan anyi breakfast(Tara)ina zaune a ƙarƙashin wata bishiya ni d'aya domin ko ƙawa bani da ita 'yan ajinmu da yawa suna son yin ƙawance dani,ko don saboda ƙoƙarina domin ni ke zuwa ta d'aya a class d'inmu,ƙoƙarin da nake dashi yasamin farin jini a gurin malamaina harda wasu daga cikin d'alibai yayin da wasu kuma kejin haushina domin duka biyun islamiyya da boko ina da ƙoƙari,"




        "Nusaiba Hassan ce razo tare da zaunawa kusa dani,ajinmu d'aya da Nusaiba tana da ƙoƙari itama don idan batazo na biyu ba zatazo na uku,miƙomin hannu tayi muka gaisa tace"Hauwa'u Sa'ad Kabir nidai sunana Nusaiba Hassan kina burgeni yanayinki na burgeni sosai don Allah muyi ƙawance mana,ƙwarjini tayimin sosai don harga Allah banson surutu,lura da nayi itama kamar bata cika magana ba ko a class yasa na mayar mata da murmushin da takemin tun farkon zuwanta nace"babu matsala Allah yasa muyi ƙawance don Allah,tace"amin nagode ƙawata,duka mukayi murmushi,sannan mukaci gaba da karatu har aka koma class,'yan ajinmu sunyi mamakin ganinmu tare kasancewar ansan dagani har ita babu me ƙawa a cikin ajin,"Zaliha Nasir wata 'yar me kud'i ce ajinmu d'aya da ita sam bata da ƙyirki raini da girman kai ga iyayi,tana ganinmu tazo gabanmu ta tsaya tare da ta6e baki tace"ehye sarkin girman kai yau kuma kin farawa mutane magana ne?yaushe kika sauke rawanin jiji dakai da girman kan da taƙama ke ba d'iyar wani ba,ƙawarta da suke tare Ramla tace"ke saima kinga gidan ubanta zakiyi mamaki don taga tana da kyau ne kawai take iya shege,Zaliha taja tsaki mtsuuw"ƙyawun banza kedai ke ganin ƙyawunta nan har wani ƙyawu gareta ayi mace baƙa har kice tana da ƙyau ai yanzu farar mace ko bata da ƙyau ita ce ƙyaƙƙyawa domin yanzu farar mace ake yayi ta gaban mota farar mace alƙyabbar mata,cikin takaici Nusaiba tace"Ai duk kushen me hassada ba zaice Ameerah bata da ƙyau ba ai kuwa yanzu black beauty ake yayi sannan ba baƙa bace Ameerah Chocolute colour ce,Sannan yanzu fari ko a kanti ana sayensa,ta fad'i hakan ne saboda duk wanda ya kalli Zaliha yasan tana bilicin ne ba farinta bane,





"Nan fa Zaliha ta fara d'ura musu asha,Ameerah dai ko uffan batace ba saidai ta kalli wannan ta kalli waccen,Uncle d'insu ne da sukaga zai shugo sai kowa ya dare ya koma gurin zamansa,tun daga wannan rana suka fara takun saƙa da Zaliha sam basa jituwa da Ameerah duk inda suka had'u sai baƙaƙen maganganu,Ameerah bata ta6a mayar mata da raddi ba,saima wani sa'in Nusaiba ke shigar mata,6angare guda sun shaƙu sosai da Nusaiba ko wanne lokaci suna tare a skul,direban gidansu Nusaiba ke mayarda Ameerah gida idan sun tashi saboda hanyarsu d'aya,Nusaiba tasha shiga gidansu Ameerah tasan Anna da Anty dasu yaya Bashir da Maryam,amma Ameerah ko hanyar gidansu Nusaiba bata sani ba,


.............................................



        "Tafiya suke a hankali suna tafe suna hira kamar irin ƙawayen nan,Anty ce da Ameerah sun dawo gidan ƙawar Anty barka kasancewar ba wani nisa yasasu tahowa da ƙafa,kamar daga Sama taji an fara kiran sunanta "Ameerah"Ameerah"Ameerah"har sau uku,tare suka tsaya da Anty tare da juyowa,gabanta ne ya buga da ƙarfi ganin...................