KISHIYA KO BAIWA

13&14

by @realeshaa

*KISHIYA KO BAIWA???*

     _(TRUE LIFE STORY)_ 


 *NA MARUBUCIYA*

 *REAL ESHAA ~*



 *WATTPAD* _Realeshaa_



 *_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*



    *PAGE 13&14*🖌️


________________________📖Kawar da kai Ahmad yayi tare da janyo Sukainat tafado kansa, ha'de bakinsu waje 'daya yayi yana bata wasu hot kisses masu wuyar mantawa, yayinda yatura 'daya hannun cikin sumar kanta dake da damshi yana yamutsa gashinta"Cikin karfin hali Sukainat tajanye bakinta daga nasa tayi kasa da kanta cike da matsanancin kunya.

Hannu Ahmad yasanya yashafi sajen sa yana sakarmata dawani killer smile,cike da zumudi yasake mika hannu zejanyota taja baya dasauri,tana girgiza masa kai alamar yabari,Cike da begenta yace pls me da'dina kibarni insha wannan sweet mouth din, shiru tayi taki cewa komai kuma taki matsowa kusa dashi"Kamar Wanda akace ya'daga kai yahango Nadiya tsaye kamar wacce aka dasata awajen idanunta sunka'da sunyi jawurr dasu fiye dana farko.

Mutsits-tsika ido yayi domin tabbatar wa shin itace ko idanunsa ke masa gizo"innalillahi wa'inna ilahi raji'un yake maimaitawa aransa, zahiri Nadiya ce atsaye kenan in haka da farko ita yagani be gezau idanunsa kemasa ba,?ya tambayi kansa"wani matsanancin kunyarta da shakku ne suka diran masa a zuciya"Anma dake namijin duniya ne se yada go kansa Cikin basarwa yace My Queen karaso mana kikatsaya a can, shiru tayi takasa cemasa komai sema sake kafesa datayi da kananun idanunta,sake cewa yayi pls come in"Da 'kyar ta Iya cewa no basena shigoba nazo ne in sanar daku breakfast is ready tanagama fadin haka tajuya afusace tabude kofar tamkar zata tashi sama.Dasauri Ahmad yamike zebi bayanta"hannunsa Sukainat tarike tana kallon yanda fuskarsa ke bayyanar da tashin hankali karara,cikin dakewa tace ina zakaje ya Ahmad?, Bakiga yanda Nadiya tafita bane ranta a'bace yafada yana kokarin mikewa janyosa tayi yafada kan bed din,cike da mamaki yake kallonta"Kau da Kai tayi tace agaskiya bazaka bitaba domin ita tashigo dakin batare datanemi iziniba,aganina ita yakamata tabamu hakuri bamu ba saboda haka bawani hakurin dazaka bata.

Har yabude baki daniyyan magana tayi saurin hade bakinsu waje daya,tashiga aika masa da sakonninta masu wuyar fassarawa Wanda batasan ta Iya ba,besan time dayafara mayar mata da martaniba suka rikewa juna"seda taga takawar da tunanin Nadiya aransa kafin tajanye jikinta daga nasa ta'fada toilet"sabon wanka tasake sannan tafito hango shi tayi yayi matashi da hannunsa yakurawa P.O.P dakin ido,kallo 'daya tamasa tadauke kai, direct jikin siff tawuce Riga da skirt na atamfa pink da ratsin fari tasanya"dinkin yazauna 'das ajikinta,skirt din yafitar mata da shape dinta hakama rigan yaimatukar amsar jikinta zama tayi akan stool tayi simple make up sannan tashafe jikinta da humra masu dadin kamshi,'dan kwalin tadauko tayi daurin ture kaga tsiya(No respect)abin hannu da sarka dakuma dankunne tasanya.Masha Allah kawai Ahmad ke maimatawa aransa ganin wani irin masifeffen kyau datayi,kasa hakuri yayi danhaka yamike cikin san'da ya isa gareta ya runguneta tabaya yana shakar dadda'dan kamshin humran datake kansa yacusa atsakanin wuyanta ya lasa.Murmushi tayi tasanya Hannu tadauki wayarta dake gaban dressing mirror tafarayi musu selfie ahaka ganin yanda sukayi kyau.'dago kansa yayi yakarbi wayan yana kallon pic din data dauka yayi wani irin kyau naban mamaki tamkar wasu jaruman India"Shima selfi ya shiga yimusu kala kala wani yana kissing dinta wani tasakalo hannunta awuyansu wani tana kan cinyarsa sunyi pic sunfi kala ashirin kowanne style dinsa daban"wayarsa yadauko yatura baki daya pic din dasu kayi,kamar Wanda akace yaduba time yaga 12:00pm ido yazare yace oh my God My Kainat dubi yanda time yawuce bakiyi breakfast ba bejira amsartaba yasun gumeta yayi dining area dake sashen Nadiya da ita.


Nadiya na fita adakin afusace direct dakinta tawuce, kan tangamemen bed dinta ta'fada tare da fashewa da kuka,wurgi tashigayi da duk wani Abu dake kan bed din Cikin matsanancin tashin hankali tace karyane Ahmad karya kakeyi baka isa katozar tani ba nafi karfin wulakanci Ahmad nafi karkin wani da namiji yawulakanta kunyi ka'dan ta'fada tana fincike bedsheets dinta dakarfin gaske"wayar ta dake kan bedsite drower ne yahau ruri, dasauri tasanya hannu tadauko hannunta harrwa yake wajen picking Call din.cikin matsanancin tashin hankali tace hema Na shiga uku wlh mutuwa zanyi Ahmad zekasheni da ciwon zuciya ni Ahmad ze kuntatawa arayuwa wlh sena haddasawa wancan la'ananniyar yarinyar bakin cikin da harta mutu bazata manta daniba.

Daga daya bangaren hema tace dan Allah kitsaya ki yimin bayani yanda zangane anma ni bamfahimci komai Cikin maganar kiba ki nutsu"hawaye tashare kana tazayyanewa hema duk abinda yafaru daga daren jiya zuwa yau.....tsaki hema taja tace wai meyesa bakiyin Abu da lissafine Nadiya?, a tunanin ki wannan abin ne zekawo mafita?, kibari

Gobe zanzo danazo komai yakare dan haka ki kwantar da hankalinki sannan kinutsu,karki nuna musu komai sauran abunuwan kuma senazo yanzu kitashi ki wanke fuskarki sannan ki koma parlour ki kizauna dan karsu fahimci kina cikin damuwa.Sake share hawayen ta tayi tace toh inajiranki anma zakizo goben ai?,"eh zanzo kede kiyi abinda nace kawai,zanyi"kokefa tace da ita sannan sukayi sallama.mikewa tayi tashiga toilet tawanke fuskarta tafito tayi make up sannan taje parlour tazauna kamar yanda hema ta'fada mata anma kasan zuciyar ta wani irin tafasa yake...

Jin 'karan dariya yasanyata 'daga kai dasauri danganin kowaye?,Sukainat tahango ahannun Ahmad tamkar wata baby yadaukota tasakalo hannunta ta wuyarsa.Da sallama abakinsa yashigo, ganin Nadiya zaune awajen yasan shi saurin ajiye Sukainat yana sosa 'keya dan beyi zaton ganin ta a parlour ba yadauka yanzu tana bedroom dinta ne.'dauke kai tayi kamar batagan shiba"Ba'kin cikine yamamaye zuciyar Sukainat talura aduk sanda Ahmad yaga Nadiya muddin suna tare seyayi kokarin raba kansa da ita.Tana cikin wannan tunanin taga Nadiya agabanta hannunta tarike tace 'kanwata zomuje kiyi breakfast dan inkika biye Honey baze barki ki hutuba"murmushin dabe wuce saman la'b'ba ba Sukainat tayi tace toh momyn rufy"aranta kuwa cewa tayi lalle wannan matar muguwar she'daniyace wai nice kanwarta?"Dining suka zauna tayi serving din Sukainat,Ahankali Sukainat ta daga kai gani tayi haryanzu Ahmad yana inda yake atsaye.

Ka 'karasomana ya Ahmad tace dashi,hannu yasanya yashafi sajen fuskarsa yace naki tunda me dakin bata gayyaceni ba"wani shegen kallo Nadiya tawatsa mai tace aikuwa sede inbaza kaciba don babu wani gayyatar ka da zanyi"itade Sukainat shiru tayi batace komai ba taciga da breakfast dinta, tanagama wa tamike tace nagode aunty,ni zankoma ko kallon inda Ahmad yake batayiba tawuce sashen ta,ta lura kamar Ahmad tsoron Nadiya yake agaskiya bazata dauki wannan abinba.

Ahmad nagin fitanta yayi saurin karasowa kusa da Nadiya ya rungumeta tabaya yace I Miss u so much my Queen, wani irin turesa tayi tamike tsaye tace wlh karya kakeyi Ahmad bakayi kewata ba agabana fa ka ha'da bakinka da wata kuke romance din juna dan kaci min fuskarsa hakan be ishekaba seda kukabiyoni Har sashena dan kunsake kuntata min Ahmad kabani mamaki bantaba zaton haka daga garekaba takarashe tana me fashewa da kukan takaici. Rungumeta Ahmad yayi cikin muryan lallashi yace dan Allah kiyi hakuri My Queen wlh banyi haka dan intozar takiba hasalima lokacin dakikeje dakin banyii zaton ka bace nayi zaton idanu na ke yimin gezo dan Allah kiyi hakuri nasan kina dashi anma kikara akan Wanda kike dashi kinji kinsa Ahmad nakine kuma baze taba yin wani Abu danyasaki a damuwa ba pls kiyarda dani...da 'kyar yasamu yashawo kanta tahakura"sannan tayi serving dinsa yayi breakfast bashi yabar sashen ta ba se bayan la'asar....

Lokacin daya koma sashen Sukainat dan takaici bata Iya cemasa komai ba"daddare Nadiya takirasa wai suje sunyi dinner.Bayan sungama dinner suka dawo daki,toilet Sukainat ta'fada ruwa tawatsa tayi brush sannan tafito wani Jan sleeping dressed me kyan gaske tasanya kana tashafe jikinta da humran ta masu dadin kamshi Wanda Aunty Aliyah ta ha'da mata.Gefen Ahmad taje takwanta tare dajuyamasa baya hannu yasanya yajanyota zuwa jikinsa tabude baki zatayi magana yahade bakinsu waje daya ya shiga aika mata da sakonni masu wuyar fassarawa,jin sakonnin dayake aikamata yasa ta manta da fushin datake dashi daga nan suka Lula wata duniya me dadin gaske Wanda bakowa kesanin dadin dayake ciki ba....


Washe gari:misalin 1:00pm Hema tazo direct sashen Nadiya tashiga ganin bata parlour yasata nufar bedroom din ta zaune tasameta dawaya ahanunnta"dasauri Nadiya tamike tarungume hema Cike da farin ciki,zama hema tayi tana murmushi"Fita Nadiya tayi badadewa tadawo hannu ta rike da tray cikawa hema gabanta da snacks dakuma drinks tayi,bayan tasha drinks dinne tace bazama zanyiba shawarar da dazanbaki nafarko shine kiyi maza ki dauko 'ya'yanki sudawo gabanki domin bakaramin temaka miki zeyiba shawaran na biyu kuma kirike wannan tadauko wani kunshi magani tabata da takarda aciki tace duk bayanansa ya yana ciki wannan paper, sannan shawara na uku ki kima kanki daga gareta sannan ki kara kissa akan Wanda kike yi kada kice zaki garamarta,nizan wuce saboda Dadyn Muslima,besan nafitoba"Washe hakora Nadiya tayi tace ngd kawai semunyi waya har compound tarakata sannan ta koma cikin gida....Duk yanda hema ta'fada mata zatayi haka tayi ba'abinda tarage sema Wanda takara"sede mahaifiyar ta tace bazata tur mata su rufy ba senanda 1weeks....


Bayan sati daya yau yakama sati daya datarewan Sukainat agidan Ahmad ayaune kuma zekoma dakin Nadiya."cikin yanayin damuwa yace agaskiya zanyi kewar ki my kainat ,'dan murmushi tayi tace ba komai aikamar yaune zaka ga kadawo,fatanade kakulamim da kanka"murmushi yayi yace bakida matsala nima kikulamin da kanki,hira sukayi mecike da so da kaunar junansu Wanda basu ta'ba irin sa ko kafin ya aureta,duk inda zatayi yana manne da ita yinin wannan ranan komai tare sukayi.Da Yammaci Nadiya tasha wankanta cikin wani English wear's tayi make up,sannan tajere komai a dining area"jitayi anturo kofa tana juyawa taga kanwarta,murja,da rufy,Hanan,dakuma,junior "dagudu tatafi tarungume yaran tace I Miss u much my blood suma Rungumeta sukayi sukace miss u more momy.murja tasa tasakeyi musu wanka akashiryasu lokacin magriba tayi danhaka ana idar da isha suka zazzauna a dining lokacin murja tatafi sesukadai.Da sallama Sukainat da Ahmad suka shigo suky taci gayunta cikin Wani bakar abaya tayi rolling kanta da mayafinsa.Kujera Ahmad yajanyota yazauna yana Kallon fuskarsa yayan nasa cike da so,kujeran dake kusa da rufy suky taja zata zauna,cikin shammata rufy tasanya kafa tature,cikin rashin sa'a Sukainat tazame akasa tare da buga goshinta a tiles.....






 _VOTE_ ✅

 _COMMENTS_ 

  *AND* 

 _SHARE_







      *_ESHAA CE~_*🤙🏻

[3/23, 15:13] ESHA: