13-14
by @nimcyluv
"Haaa ur wife?" Yaushe ka samu mata ba na da labari? Wait when ka fara soyayya ma?" Haɗe fuska Sheikh yay ba tare kuma daya tanka Arjun da yake masa magana ba, cikin damuwa Arjun ya ce "I kon Allah! Ashe nine sakarai da nake faɗa maka sirri na, banda haka tayaya zaka samu matar aure bana da labari" Murmushi kawai Sheikh yake yana jin yadda Arjun ke ruwan masifa kamar zai ari baki, ajjiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Ohh Shut up my friend" da sauri Arjun ya ce "Why should i?" Taɓe baki Sheikh yay yana karya kwanar da zai kai shi Mosque ɗin,kamar ba zai magana sai kuma yaja gemunsa ya ce "You don't have any reason to talk about it, And wacce macan kake tunanin zata zauna da disabled like me Arjun, wallahi isn't necessary bedside ba na da wani feelings akan mace,ko dai kuje Allah ya taimaka" Sosai Arjun yay dry kafin ya ce "Eh babu komai zamu bauta wa mace,za kace na gaya maka wata rana sai kayi kuka dalilin mace, Uhm soyayya akwai daɗi akwai wahala, kuma duk cikakken Namiji mai jini a jika da lafiya zai so kasancewa da mace, nasan wata rana da kanka zaka gaya min yadda kake son wacce tai nasarar samunka matsayin miji" da sauri Sheikh ya ce "God forbid! Ni na so mace har na aureta?" Murmushi Arjun yay yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda soyayyar Aliyah ya ce "Of cos, ɗan sunna ai mazai ƙi sunna ba, rashin san auren ne yasa Granny ta ce taje tashinka da asuba taji kana ta nishi tare gurnani?" Shiru Sheikh yay bai ƙara kulasa ba har suka ƙarasa harabar masallacin, wasu manyan securities ne suka zagaye motar Sheikh Imam hamdan kafin Arjun ya fito da sauri tare da ɗaukan Wheelchair ɗin Sheikh, bayan Sheikh ya zauna Arjun ya fara tura Wheelchair har zuwa cikin masallacin securities na biye dasu.
Bayan an idar da sallar Sheikh ya juya tare da fuskantar Mutanan da ke cikin masallacin,cikin nutsuwa ya gyara zaman babbar rigar sa tare gyara zaman farin glass ɗinsa, Muryarsa ya saita kaɗan Sannan ya fara Bisimillah cikin nutsuwa da kamala ya fara huɗu bar Juma'a,gaba ɗaya ƴan jarida suka saita speaker nasu aka fara ɗaukar recording gidan t.v kuma suka fara ɗaukan vedio'n direct wanda ya kasance live
Bayan ya kammala Mutane suka shiga yi masa tambayoyi nan ya fara ba su amsa cike da ƙwarewa, Wane ne ya kalli Sheikh ka na ya matsa kusa dashi da alama dai shima babban Malami ne, cikin ƙasa da Murya yace "Sheikh wata ta turo tambaya ta cikin lambobin da muke badawa, na ga kuma tambayar na da muhimmanci ya kamata a amsa mata duk da cewa lokaci ya tafi" shiru yay Sheikh yay kamar mai nazartar wani abu can kuma ya numfasa ya ce "Faɗi tambayar, Allah ya bani ikon faɗin dai-dai" mutumin ya ce "Ameen" wayarsa ya fara dubawa can kuma ya ɗaga kai ya kalli jama'ar dake cikin masallacin, bakinsa ya saita a speaker ya fara faɗin;
_Assalamu alaikum,ina yiwa Sheikh Imam hamdan fatan alkairi Allah ya tsare sa ya kuma karesa daga sharrin mutum da aljan, Tambayata a nan shine (Shin zai iya yiyuwa a samu alaƙa tsakanin mutum da Aljan? Shin zai yiwu Ɗan Adam ya yi alaƙa da Aljanu? Idan har zai yiwu yaya hukuncin yin hakan yake? Tambaya daga baiwar Allah zuwa bawan Allah ka sani ina tsananin sonka da ƙaunar ka,dan Allah ka amsamin tambayoyi na)_.
Fesar da numfashi yay nan take yaji wata zufa ta shiga karyo masa, lumshe idanunsa yay tunanin His Fairy kawai yake a wannan lokacin, Wannan amsar mai sauƙi ce garesa sbd ga babban misali a garesa,duk da kasancewar sa babban Malami amma hakan bai hana Aljana shiga jikinsa harta aurensa ba, fesar da iska yay kana ya gyara zamansa sosai cikin nutsuwa tare ƙarfin guiwa da kuzari ya manna idanunsa a saitin camera cikin zazzaƙar muryarsa ya ce.
"Amsa a Dunkule
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani.
1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta sa ɓanin mutum shi da kasa aka halicce shi.
2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, yana iya yin magana kuma yana kafa dalili.
3- An wajabta masa ayyuka (na ibada da dss) da kuma nauyaye nauyaye.
4- Wasu daga cikin su muminai ne salihai wasu kuma kafirai.
5- Za a tashe su ranar alƙiyama kuma za a yi musu hisabi.
6-Suna iya keta sararin samaniya su sato ji amma daga baya an hana su.
7- Suna kulla alaka da wasu daga cikin mutane kuma suna yin amfani da masaniyar da suke da ita na wasu Ɓoyayyaun sirrika su halakar da mutane.
8-A cikin su akwai wa Danda suke da karfin da iko na gaske kamar yadda ake samu a cikin mutane.
Numfashi Sheikh ya fesar tare da sanya hannunsa yaja dugun sajensa wanda yake kwance luff,ya daɗe bai mgna mai yawan ta yau ba,kula da hakan wani securities ya tsiyaya masa ruwa mai sanyi a glass cup ya miƙa masa, amsa yay tare faɗin "Barakallahu fikaaa" bayan yasha ruwan ya sauke ajjiyar zuciya,cikin nutsuwa yaci gaba da faɗin.
9-Suna da ikon yin wasu ayyuka da mutane ke bukatuwa zuwa gare su.
10-Su aka fara halitta a doron kasa kafin a halicci mutane.
11-A cikin Kissar Annabi sulaiman (as) lokacin da Ifritu daga cikin aljanu ya yi da’awar cewa zai iya kawo gadon BilKisu wajen Annabi Sulaiman (as) kafin ya tashi daga mazauninsa,Annabi Sulaiman (as) bai Karyata shi ba duk da cewa wannan maganar ba ta zo a cikin Kur'ani ba cewa ya kawo gadon ba,
Daga cikin abin da aka amabata a cikin a yoyin da muka kawo zamu fahimci cewa aljanni ba halitta ce irin ta tatsuniya da labarai ba, shi halitta ne samamme a haKiKa, mai jiki wanda za a iya yin alaƙa da shi, kuma wasu daga cikin mutane sun yi alaƙa da shi, duk da cewa a zamanin da an fadi wasu nau’o’i na alaka daban daban tsakanin mutane da aljani, amma mu zamu takaitu da irin wacce muka samu a cikin Kur'ani da hadisi, da ita zamu isu don wannan kawai muka yarda da shi.
A nan za mu yi nuni zuwa ga yanayin alaƙar da muka samu a cikin Kur'ani da ruwayoyi da kuma maganganun da aka nakalto daga wasu makiya:
A.Neman tsarin Allah daga aljanai; ya zo a Kur'ani mai girma cewa: {haƙiƙa wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari wajen wasu mazaje daga aljanu sai suka kara jefa su cikin bala’i da “wahala”}[13].
Al’adar larabawa ta kasance duk lokacin da suka shiga daji mai ban tsoro (misali mai duhuwa) suna neman tsari daga aljanun wannan kwazazzabon, kuma musulunci bai hana yin haka ba kuma ya yi umarni da a nemi tsari daga shaiɗanun mutane da na aljan[14].
B.Tasarrufi da aljani; yin tasarrufi da aljani da yin amfani da su wajen yin hidima duk da cewa abu ne mai yiyuwa, sai dai malamai sun yi bahasi kan cewa shi ya halatta ko kuwa? Gwargwadon abin da suka yarda da shi, shi ne lalle ne kar wannan aikin ya zama ta hanyar da shari’a ta haramta, ko kuma ya zama sanadin cutuwar aljanu,Kuma lalle ne ya zama aikin da suke yi ba wanda shari’a ta haramta ba ne. kuma lalle yin aikin da shari’a ba ta yarda da shi ba ya haramta dai-dai ne da wasida ko babu wasida.[15]
An tambayi Marja’I Mai girma Sayyid Ali (as) Khamna’i kan hukuncin zuwa wajen mutanen da ke tasarrufi da rauhanai da aljanu wajen yi wa mutane magani tare da la’akari da cewa bisa yaƙini su aikin alkhairi kawai suke yi, sai ya bada amsa da cewa: wannan aikin ba shi da mushkila a kan kansa da sharaɗin cewa ya zama yana yin aiki ta hanyar da shari’a ta halarta.
Duba da Wannan misalan da aka samar a cikin Alkur'ani da kuma hadisai zamu iya cewa mutum na iya mu'amala da Aljanu,domin wasu Aljanun har Auren mutum suke, za'a ga mutum baya sha'awar aure ko kuma bashi da sha'awa gaba ɗaya,abinda nake nufi da sha'awa shine; ko yaga wani shashe na jikin mace ba zai taɓa ji mazantakarsa ta mutsa ba, bare har yay tunanin kasancewa da mace, zamu kawo misalan yadda ake gane Aljani ya auri Mutum ko kuma yana jikin mutum a haɗu bar mu ta gaba.
Ajjiyar zuciya Sheikh ya sauke mai ƙarfin gaske,kafin yaja baya kaɗan shi kaɗai ya shiga sauke tattausan Murmushi ya nayi yana jan ƙwantaccen bear ɗinsa, cikin ƙasa da Muryar kamar mai raɗa idanunsa akan camera yace "Baiwar Allah fatan kinji amsar tambayar ki kuma kin gamsu? Allah ya kyauta ya kuma tsare mu daga sharin kafiran Aljanu".
Gaba ɗaya cikin Masjeed ɗin suka amsa da Ameen. Suna cikin mota Sheikh yana driving cikin ƙwarewa ba tare daya saurar abinda Arjun yake magana akai ba, ganin Sheikh ya ɗauki hanyar zuwa gida yasa Arjun marai-raice fuska yace "Haba Buddy bana ce zaka rakani zance wajan Aliyah ba?" Ɓata fuska Sheikh yay yace "Nifa ba za'a kai ni wajan da za'a dinga zabga ƙarya ba" dry Arjun yay yace "Au ƙarya ake a zancen? Malam just wait and see za kaji yadda ake faɗar kalamar soyayya" shiru Imam yay Arjun ya ce "fara kai ni gida na ɗauko mata gift ɗinta" kallonsa Sheikh yay kamar zai magana sai kawai ya karya gwana, a compound ɗin gidansu Arjun yay parking Arjun ya ce "ba zaka shiga wajan Ummi ba?" Girgiza kai Sheikh yay yace "kace ina gaisheta,nasan za ta ce sai na ci abinci ni kuma am full" kafin Arjun yay magana Ummi dake bayansa ta ce "Daman always you're full,kawai kace furar Granny za kasha"
Murmushi kawai yay mata kafin ya lumshe idanunsa yace "Evening Ummi" "how are you?" Ya ce "Allahamdulillah!" Daga nan ta shige cikin gidan, Arjun yabi bayanta yana riƙe da hannunta, da kallon sha'awa Sheikh ya biso yana ji inama mahaifiyarsa ce Ummi.
Bayan sun isa gidan su Aliyah Arjun yay mata waya daga can ɓangaren ta sauke ajjiyar zuciya kafin ta ce "fatan mijina ya sauka lfy?" Murmushi yay mata har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Aliyah yana mutuwar sonta kamar ransa "Surprised?" Ware ido tayi ta ce "What a good news?" Cikin jin daɗi ya ce "Tare muke da Buddy" saurin faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" tayi sbd yadda taji gabanta ya faɗi,cikin ƙarfin hali tace "Sure?" Da sauri ya ce "I mean my words Matata" miƙewa tayi tsaye tana gyara zaman rigar jikinta wacce ta amshi jikinta sosai, Aliyah fara ce sosai tana da ɗan tsayi ba sosai Mahaifinta shine senator na lokacal government ɗin su, ita kaɗai ce wajansa,sun haɗu da Arjun taje shopping shi kuma yaje siyowa Sheikh sabbin jalabiyoyi, a nan sukai exchange na number "come in" daga can ɓangaren Arjun ya ce "No muna sauri lokacin shan furar Buddy yayi" ok kawai tace masa kana ta kashe wayar, parfume tasa masu ƙamshi ta gyara zaman veil ɗinta, but ƙasan zuciyarta taoroy da far gaba ne, tun daga nesa Arjun yake kallonta yana jin kamar yaje ya rungome ta sbd yadda ya kejin ƙaunarta a ransa, fuskarta ɗauke da Murmushi tai masu sallama, Amsawa Arjun yay yace "Ma sha Allah tawan kinyi kyau fiye da ko yaushe" cikin ƙasa da Murya tace "Fatan kana lfy kamar yadda zuciyata ta sanar dani?" Kallon Sheikh yay dake cikin mota ya lafe jikin kujera idanunsa a rufe sai ƙirjinsa dake ɗagawa da sauri yace "Wow ashe haka zuciyarki take da faɗin gsky?" Shira suka taɓa kafin yace "Ga Buddy ko gaisa zamu huce" kallon cikin motar tayi a zuciyarta tana faɗin Tubarkallah ma sha Allah barakallahu ahhasanal kaliƙin Ubangiji yay halitta a nan, da sauri Aliyah ta ɗauke idanunta ta ce "kamar bacci yake" dry Arjun yay yace "haka yake fa, ƙilan zaman ya damesa" cikin motar ya leƙa tare da bubbuga murfin motar yace "Buddy! Buddy!" Ware firgitattun idanunsa yay "What again?" Arjun ya ce "Ruhina ke gaidaka" kallon bayan Arjun yay kallo guda yay mata yay saurin janye idanunsa tare murza zoben hanunsa ka ɗan yace "Ykk?" A fili tace "tab" Arjun ya kalleta ya ce "me" girgiza kai tayi tace "Ina lfy ya jiki?" Ware fararan idanunsa yay kafin yace "Lafiya" Wannan idan bai ji dakai da kuma miskilanci ba ai sai Allah ya tambaye sa da sauri Sheikh yace "me kika ce?" Rufe bakinta tayi tace "No ba dakai nake ba" a zuciyarsa yace "Ƴar ficika kawai" bayan sun gaisa Arjun ya bata tarkacan chocolate daya siyo mata, Sheikh yace ya gaji dole suka sauya waje Arjun yay driving nasu zuwa gida. Misalin 10:30 na dare Sheikh na zaune a parlour'n sa daga shi sai 3gauther fresh skin ɗinsa sai Shinny take ga yadda 6packs ɗinsa suka ƙara buɗewa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa yana ta gyalli hanunsa riƙe da mug yana shan coffee, idanunsa ba kan cenema yana Kallon Tafsir a Sunna t.v, bayan an gama tafsir ɗin ya sauya channel zuwa zee world, samu yay ana film ɗin johda &Akbar bai taɓa tsayawa yayi kallo ba,amma ganin film ɗin na musulmai kuma na sarauta sai abun ya birgesa, lumshe idanunsa yay lokacin da yaga Akbar yay kissed ɗin Johda, cikin ransa yake faɗin ko meye abin daɗi a nan ohhhu? Yana nan zaune yana shan coffee kamar bai so amma gaba ɗaya tunaninsa yana kan Airah shi kaɗai yasan yadda yake a zabtuwa da rashinta a ɗan wannan lokacin da yay sabo da ita, tana ɗebe masa kewa fiye da tunanin mutum yana samu kwanciyar hankali da ita, at least ya samu wacce za tana rarrasbinsa zata rungomesa idan yay kewar Amininsa,tana ƙoƙarin bashi farin ciki shiyasa ya yarda da ita sosai ya bata dukkan yar darsa, ta riga ta samu gurbi a zuciyarsa baya jin akwai halin da zai shiga bai tuna da Aljanarsa ba, Aljana ta fi masa sauran mutane da yawa, Aljanarsa ta fi masa Amminsa ta fiye masa Abbansa, tayaya zai iya mantawa da ita, lumshe idanunsa yay yana jin ɗaci a ransa yaushe zai samu freedom ne kamar yadda kowa yake dashi? Yaushe zai zama cikakken Namiji mai lfy? Yaushe zaiji feelings akan mace kamar yadda Arjun yake gaya masa a kullum, cije lips ɗinsa yay tare da fesar da numfashi, hanunsa ya shiga miƙawa wajan table yana son ajjiye cup ɗin hannunsa cikin rashin Sa'a ƙafarsa ta zame daga jikin Wheelchair, ƙara ya ɗan saki saboda tsoratar da yayi kafin ya ƙarasa ƙasa Airah tayi saurin taresa ya faɗa jikinta.....