MAHAƊIN RAYUWATA

Chapter 5-6

by @ummuaffan

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



Page 5-6



Ganin ba kowa bane sai saurayin nan *El Manseer* ƙarasowa yayi fuskarsa da murmushi ya d'an ranƙwafa yace"Anty ina wuni,da mamaki na kallesa ya akayi yasan Antyna ce,ita kuwa Anty ta amsa masa fuskarta a sake"lafiya ƙalau,yace"daga unguwa kuke ne Anty?,tace"eh wallahi munje ƙasan layi ne barka,"Ayya to Allah yaraya,ta amsa da "amin tana kallona tace"Ameerah idan kin gama ki sameni gidan Maman Khalil,wata maƙociyarmu ce,ta fad'i haka ne saboda sun fito tare kar Anna ta tambayeta ni,yace"Nagode Anty"a'a babu komai,tayi wucewarta,ya dawo da hankalinsa gareni,nima ido na zuba masa don matuƙar mamakinsa nake,murmushi yayi wanda ke ƙara tona asirin ƙyawunsa yace"Ameerah ya kwana da yawa kin 6uya ko a hanya bana ganinki,bud'e bakina nayi a hankali nace"don Allah ka rufamin asiri idan aka ganni da kai za'a iya dukana gashi yanzu a gaban Antyna kayimin magana baka tunanin tayimin fad'a?,tunda na fara maganar ya zubamin manyan idanuwansa yana kallona,ganin haka yasa na saukar da kaina ƙasa ina wasa da gefen hijabina,




        "Yace"Ameerah banso kiyi shuru ba,naso naci gaba dajin muryarki me kama da busar sarewa me dad'in sauraro,da sauri na d'ago fuskata na kallesa jin yadda yayi maganar,murmushi ya sakarmin yace"da gaske nake Ameerah domin ke ta dabance ko a cikin mata samun kamarki sai anyi babban bincike anyama za'a samu?,na ƙara kallonsa a karo na biyu,yaci gaba dacewa"Ameerah inaso ki fad'a a gidanku zan dunga zuwa gurinki,"gurina kuma?,ta fad'a a d'an rikice muryarta na rawa,yace"eh gurinki bari in fad'a miki gaskiya Ameerah ina sonki kuma auranki zanyi,ai zufa naji ta fara fesomin duk kuwa da iskar dake kad'awa a gurin jikina kuwa rawa ya fara"meye haka lafiya kuwa?ya tambayeni,shima a rikicen,daurewa nayi nace"don Allah *El Manseer* kayi haƙuri wallahi ba za'a barni ba a gida ina da Yayu da yawa ko zance basayi bare ni,idan naje da wannan zancen gida dukana za'ayi,"wannan ai ba hujja bace,ya fad'a ya gyara tsayuwarsa tare da zubamin rikitattun idanuwansa yace"Ameerah bazan 6oye mikiba nidai ina ƙaunarki idan har kin amince kina ƙaunata kema to kibani dama na sami Baba da wannan maganar domin neman izinin tsayuwa dake,kasa magana nayi domin harga Allah yana da ƙwarjini ga kamala natsuwarsa yasa naji yana burgeni na d'ago a hankali ganin ni yake kallo yasa na mayar da kaina ƙasa "yace"bakice komai ba Ameerah gimbiyar mata,nace"ka bani lokaci zanyi tunani,yace"badamuwa na baki lokaci kiyi tunani a kaina sai mun sake had'uwa,ya fad'a tare da d'agamin hannu ya wuce,bin bayansa da kallo nayi ba zancen ƙarya "El Manseer ya had'u sosai fari ne tas dogo amma ba san6al ba yana da ƙirar ƙarfafa sumar kansa baƙa wuluk sai shaning take daga gani tana samun gyara sosai na mayamayai masu saka suma baƙa da sheƙi,idanuwansa manya ne masu matuƙar ƙyawu da haske,idan ka kalli idanuwansa sai kayi zaton barci yakeji don a lumshe suke yana da gashin gira sosai saboda yawanta har ta kusan had'ewa ga dogon hanci bakinsa ja me ƙyau masu tudun le6e,a tsaye yake ƙam sam baiyi kama da talaka ba sai d'an masu hali,





"Sauke ajiyar zuciya Ameerah tayi,"gaskiya nima ina sonka,ta fad'a a fili sai kuma tayi saurin toshe bakinta don batayi zaton maganar ta fito fili ba,tace"kin mance akwai wasu a gabanki ko kin manta da maganar Anna ne?ta tambayi kanta,juyawa rayi ta nufi gidan Maman Khalil suka fito tare da Anty suka wuce gida,sai bayan sunci abinci sun huta sannan Anty ta kalli Ameerah tace"ni kuwa Ameerah inason tambayarki ina kika sami wannan ƙyaƙƙyawan saurayin haka?,gabana naji ya fad'i na kasa magana ƙasa nayi da kaina Anty ta d'ago fuskata tace"Karkiji komai Ameerah ki sanar dani idan da temakon da zan iya miki zanyi,komai na sanar mata har yadda mukayi da Annata,murmushi naga tayi tace"kai amma nayi matuƙar farin ciki da murna Ameerah irin mijin da nakeso ki aura kenan wayayye d'an boko me ƙyawu da natsuwa wallahi bakiga yadda kuka dace ba,nace"Anty ya za'ayi ki fad'i haka bayan kinsan ina da Yayu,tsaki taji mtsuuw "to su zaisa kiƙi kulashi kin sami me sonki naki,ni da kaina zanwa Babanku magana idan kun sake had'uwa kice masa ya dunga zuwa gidanku ko baki sonsa ne?ta ƙarashe maganarta da tambaya,murmushi nayi tare da sadda kaina ƙasa don naji ina son El Manseer a zuciyata ,itama dariya tayi tace"Allah yasa alkhairi ni ganima nake kamar na ta6a gaaninsa,




        "Abin mamaki cikin dare haka nayi ta tunani El Manseer har mafarkinsa nayi nayi wai gashi muna soyayya mai dad'i dashi,haka na tashi cikin farin ciki har ƙosawa nayi mu sake had'uwa dashi har ƙofar gida na dunga futa wai a tunanina ko zan sake ganinsa,




@@@@@@@@@@@@@




*El Manseer* kuwa bayan yabar gurin Ameerah ƙarasawa yayi bakin titi inda yayi parking d'in danƙareriyar motarsa,yashiga,Abbas dake zaune a motar ya d'ago ya kalli abokin nasa kuma amininsa yace"El Manseer na Ameerah ba mamaki kadawo amma fa ka dad'e kaida kacemin yanzu zaka dawo,key yayiwa motar saida ya hau titi sosai sannan ya juyo ya d'an kalli Abbas ya sake juyawa yaci gaba da tuƙi yace"kasan idan ina tare da Ameerah ban sanin lokaci yaja da yawa gashi ban gama aiyukana a Office ba,Abbas ya d'an juyo da fuskarsa yana fuskantar El Manseer yace"ni kuwa abokina me yasa baka fitowa Ameerah a mutum ba wato yadda kake da kai waye,d'an murmushi yayi kafin yace."



"Ina da babbar hujja so nake mu shaƙu a haka ta soni don Allah badon wani abu da nake dashi ba,mata da yawa suna cewa ina da ƙyau kuma ga ilmi ga kud'i gani nake kamar saboda wad'an nan abubuwa suke sona ban ta6a ganin wata nace ina soba sai Ameerah nayarda da natsuwa da tarbiyyarta fatana tasoni kamar yadda nake sonta muyi soyayya don Allah badon wani abu ba,Abbas kasan banda uwa gashi mahaifina ni d'aya ya haifa yana da tarin dukiya wacce bata musultuwa kaima kasan a kullum burim Mummy (Matar Daddynsa),bai wuce taga ta auramin mataba duk a cikin za6inta ban yarda sa suba don ita kanta da wata manufa takeson had'ani dasu,Ameerah kawai nake kallon tazo daidai da tsarina duk da cewa ita ƙaramar yarinya ce sosai gani nake kamarma nata tsufa."




       "Abbas ya kwashe da dariya yace"lallai da auran wuri kayi ya isa ka haifeta"a'a Abbas bansan wulaƙanci duka-duka fa shekaruna 32 shine na isa haifarta?,Abbas yace"to ai ita bazata wuce 13 ba,El Manseer yace"a bincikena ance 14 take,kasan saida nasan komai akan Ameerah kafin na fara tsayar da ita sannan kaga lokacin da zata kammala secondry tana sha bakwai a lokacin nakeso na aureta sai taci gaba da karatunta a gidana,Abbas yace"harsai ta kammala secondry sannan zaka aureta banyi zaton zaku ƙara shekara uku nan gaba kafin kuyi aure ba kasan kuma Daddy ya matsu kayi aure,Ajiyar zuciya El Manseer yayi tare dacewa"Da mahaifinta zai bani ita a haka saina aureta naci gaba da rainonta a gidana amma ina ganin da kamar wuya."





"Shima Abbas ajiyar zuciya yayi yace"tunda haka ne kuwa kaga dole kayi aure kafin ta gama makarantar saitazo a ta biyu idan har kanason faranta ran Daddy,Numfashi El Manseer yaja bai iya cewa komai ba ya sami guri a harabar ma'aikatar yayi parking gaba d'aya suka fito,ma'aikata sai gaishesu suke har suka ƙarasa katafaran Office d'in El Manseer kamar na wani gwamna,kujera yaja ya zauna yana duban tulun aiyukan dake gabansa,Abbas yace"Abokina bari inje Office d'ina nima inada aiyuka,"Ok kawai yace masa yasa kai ya fita,shi kuwa shuru yayi yana tunanin maganar da sukayi da Abbas tabbas idan yanason faranta ran mahaifinsa shine yayi aure a kwanan nan."





        "Waye El Manseer?,Alhaji Abdulkarim Mansir shine sunan mahaifinsa haifaffan Adamawa Fulanine shi na usul,kasuwanci ne ya kawoshi garin Kaduna babban d'an siyasa ne domin ya riƙe muƙamai da dama yawa ƙasarsa hidima sosai haka fannin kasuwanci ba'abarsa a baya ba babban d'an kasuwa ne,yana da mantan kamfanoni a cikin Kaduna da Adamawa haka Lagos,babban d'an kasuwa ne wanda sunansa ya shahara a ƙasar nan tamu Nigeria da ƙasashen turawa,babban mai arziƙi ne wanda inda za'a lissafo masu kud'in Nigeria to idan baizo na uku ba zaizo na hud'u,Allah yayi masa arziƙi gashi da temako da son talakawa ya gina gidajen marayu da yawa masallatai bohul-bohul da rijitar birtsatse,haka yana ciyarda gajiyayyu da miskinai,shiyasa akoda yaushe dukitarsa ke ƙaruwa,matarsa ta farko Hajiya Saudatu 'yar uwarsa ce had'in gida aka musu yana matuƙar ƙaunarta macece kamila mai haƙuri da biyayya ga temako duk inda tasan ana neman temako tana temakawa za'ayi girki me ƙyau akai gidan marayu da kayan tea macece me hankali da tunani."





       "Shekararsu goma da aure masu sami haihuwa ba,gashi sunason haihuwar babu asibitin da basujeba sai ace lafiyarsu ƙalau lokaci ne baiyiba Allah ne bai basuba,hankalinfa Alhaji ya tashi sosai domin yana ganin ya kamata ace yana da d'a ko saboda idan girma ya ruskesa ya sami masu temakonsa,ganin haka Saudatu tace ya ƙara aure da farko ƙin yarda yayi amma daga baya daga an ƙara wasu shekarun biyar suka zama sha biyar ba haihuwa ko 6atan wata Saudatu batayi ba sai ya ƙaro aure,Asibi ya aura tunda Hajiya Asibi ta shugo gidan sai zaman ya lalace domin makirar macece ga bala'i sam bata da mutumci,Saudatu kuwa nashan gori gurin Asibi cewa ita juya ce bazata ta6a haihuwa yanzu tazo gidan ita zata dunga haifawa Alhaji yara har sai yace sun isheshi,Abu na Allah Asibi ta shekara biyu itama ko 6atan wata,Allah maji roƙon bawansa Saiga Saudatu da ciki don kwana take ba barci tana addu'ar Allah ya bata haihuwa me albarka,farin ciki gurin Alhaji Abdulkarim da Hajiya Saudatu ba'a magana,nan Alhaji ya dunga ƙyauta ya biyawa wasu da yawa kujerar makka domin idan sunje suwa matarsa addu'a Allah ya rabata da cikin lafiya,Saudatu kuwa ko tsinke bai barin ta kauda bayaso yaga tana aiki komai saidai ayi mata,Asibi kuwa baƙin ciki kamar zata mutu,shige-shige tayi sa gurin bokaye da malamai 'yan tsubbu domin a zubar da cikin amma abu na Allah cikin ikonsa Saudatu ta haifi ƙyaƙƙyawan d'anta son kowa ƙin wanda bai samuba,fari tas sai ya saje da 'yan ƙasar da aka haifesa India,Haka suka dawo gida Nigeria cikin farin ciki da annashuwa taci gaba da bawa d'anta kulawa,ranar suna yace MANSEER sunan kakansa,El Manseer yaro d'an gata wajen iyayensa suna matuƙar ƙaunarsa,yayin da Asibi keji ina wuta ta jefasa ta tsanesa burinta taga bayan El Manseer,shekararsa hud'u aka sakashi tsadaddar makaranta ta 'ya'yan masu dashi,boko da islamiyya,ganin har El Manseer ya shekara goma ba'a masa ƙani ba hakan yasa mahaifinsa ya tattara duka burinsa akan El Manseer komai ya samu nasa ne,






     "Asibi tana jin baƙin cikin wannan abu a kullum tana hanyar bin gidan malamai don ganin itama ta samu haihuwar amma shuru kakeji kamar an shuka dusa,Ganin irin so da kulawar da Alhaji kewa Saudatu da d'anta yasa ta amshi wani magani ta sawa Saudatu a abinci ta kama wani irin ciwo da bayajin magani wasu irin manyan ƙuraje suke feso mata ta ko ina a jikinta babu ƙyawun gani,maganin ake amma babu sauyi na gida da na asibiti har ƙasar waje Alhaji ya fita da ita amma abin yaƙi,sai abin dake ƙara gaba,ciwon nan dai shine yayi ajalinta lokacin El Manseer ya kammala secondry yana cukucukun shiga jami'ar ƙasar England tuni kuwa ya sauke ƙur'ani me girma,Alhaji da El Manseer sunji mutuwar nan sosai domun saida aka kwantar da El Manseer gadon asibiti don sumewa yayi Alhaji kuwa kusan zaucewa yayi saidaga baya ya dawo hayyacinsa,Lallai yaji mutuwar Saudatu kuma yayi babban rashin matarsa kamila me tsoran Allah,haka akayi zaman makoki har akayi bakwai."





Abbas shi ke tausar El Manseer akan yayi haƙuri dukkan me rai mamaci ne,El Manseer da Abbas abokaine tun suna yara makaranta d'aya sukayi,sanadin abotarsu yasa iyayensu ma suke abota suka zamo tamkar wasu 'yan uwa,shima Abbas d'an gidan masu haline sosai,Haka El Manseer yayi haƙuri ya dangana har akayi arba'in sannan suka wuce England inda sukaci gaba da karatunsu shida Abbas.".........