KISHIYA KO BAIWA

15&16

by @realeshaa

*KISHIYA KO BAIWA???*

    _(TRUE LIFE STORY)_ 


 *NA MARUBUCIYA*

 *REAL ESHAA ~*



 *WATTPAD* _Realeshaa_



 *_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*



    *PAGE 15&16*🖌️


________________________📖Dasauri Ahmad yataso yazo ya'dagota"subhanallah sannu Sukainat ya'akayi haka yafad'a yana kokarin zaunar da ita akujeran dining in Cike da tasauyinta.Goshin tadafe tanajin wani azabebben ra'da'di yana mamaye gaba 'daya ilahirin kanta.

Hannu yasanya yashafa goshin yana mulmula mata Ahankali" Ido taruntse hawayen azaba na mamala daga idanunta,se sannu yake mata cike da tausayin ta.Daga Nadiya har 'ya'yan ta babu Wanda yadaga kai yakallesu bare susan Allah yayi digon halittan 'dan Adam awajen sema cin abinci su dasukeyi cike da nisha'di.Wannan Abin dasu kayi ba'kara min zafi yayima Sukainat ba,kasancewar tana ganin time da rufaida ta ture kujeran tafadi da farko tayi zaton mistake ne anna yanzu ta tabbatar da gangan tayi,,mikewa tayi dafe da goshinta tanajin jiri na dibanta anma ta gwammaci tabar wajen da wannan takaicin.Dasauri Ahmad yabi bayanta yari'ko hannunta a'daya daga kujerun dake parlour Nadiya ya zaunar da ita kana ya tsugunna agabanta yace sannu, bari na dauko man zafi inshafa miki?"Kai tagirgiza cike da dauriya tace a'a zantafi in 'dan kwanta zedena zafin.Toh abincinfa ya tambayeta cike da kulawa?? sake girgiza masa kai tayi tace bazan ciba",cike da tausayinta yarike hannunta suka fice daga sashen.

Nadiya naganin fitansu suka fashe da dariya" hannu tamikawa rufy tace give me higt 5 yarinyar kirki,hannun rufy tabata suka tafa

Cike da tsiwa rufy tace wlh momy bana san Sukainat din natsaneta kuma se tabar mana gidan mu tunda bana ubanta bane,sede takoma tsohon gidan ubanta wanda babu AC aciki kuma babu tiles"Cikin dariyar mugunta Nadiya tace aidaman kwa'dayine yakawo ta gidan,So take dadynku yamutu ta kwashi kudin sa takai gidan su suyi facaka daahi.

Cab 'dijan wlh bata isa ba shegiya kawai kuma satabar mana gida, kota haifi yara bama sansu ba kannen mubane se mundinga dukansu cewar rufaida.'Kirji Nadiya tadafe cike da fargaba hakika bazataso Sukainat tahaihu agidan ta ba"domin dukiyar Ahmad mallakinta ne da 'ya'yan ta su ka'dai"cabbb aibazata tabari ta haihuba duk runtsi duk wuya...haka suka cigaba da kulla mugan kalamai akan Sukainat itada rufaida inkunji yanda yarinyar take magana zakuyi zaton babba wacce ta mallaki hankalin tane...

Suna shiga daki tafa'da kan gado tare dafashewa da kuka mai tsuma zuciya"tallabota Ahmad yayi yace haba Sukainat meye abin kukane inkuma haryanzu ciwon yake miki kitaso inkaiki clinic adubaki!!Cikin muryan kuka tace a'a basemun jeba zedena insha Allah"Ok Allah yakara sauki yanaga ma fadin haka yafice abinsa batare dayasake cewa komai ba"kuka taci mai isarta kafin tayi shiru,!Wayarta dake kan dressing mirror ne yahau ruri Ahankali tamike taje tadauki wayar sannan tadawo tayi picking"Muryan Aunty aliyah ce yakara de Cikin wayar Cikin yanayin maganarta na zafi tace wato Suky baki Iya Neman mutane awaya bako?ko duk amarcin ne yahanaki kira?ko kuwa Ahmad dinne yace karki kiramu dan nasan ze iya aikatawa!!Hawayen fuskarta tashare tace a'a aunty bahaka bane wlh katine babu awayata anma kuna raina kiyi hakuri,yasu Ummi da Abba na dakuma Uncle kice ina gaishesu kafin nakirasu dan nayi matukar kewar Ku...Dasauri Aunty Aliyah ta katseta tahanyar cewa ke suky yanaji muryan ki haka bakida lafiya ne?, ko kuma sakarcin kin kikaje kikeyiwa Kishiyar taki nakuka??,Sake share hawayen tayi tace a'a aunty bahaka bane banjin dadin jikina ne kuma bacci ma nakeyi kiran yatashe ni shiyasa kikaje murya ta haka.

"Kin tabbata babu wata matsala ko?"Eh babu komai Aunty" masha Allah, haka akeso"abinda nakeso dake suky kicigaba da hakuri kinsan yanzu kinshiga wata sabuwar rayuwa, rayuwar Aure wata rayuwa ce wacce zakiyita mecike da dumbin lada dakuma biyayya,anma sekin yi hakuri musamman keda kike da abokiyar zama dakuma 'Ya'yan miji" domin zaki fuskanci abubuwa da dama acikin zamantakewar Ku sekin yi hakuri kin kuma jure kafin kiga cigaba"kada kisakewa 'ya'yan mijin ki surenaki,bawai ina nufin kada kijasu ajikin ki bane a'a sede ina nufin kada kiyi abinda reni ze shiga tsakaninku haryakai kigamusu dasu ta yanda zasu fada miki duk maganan dasuka ga dama"Inma sukayi miki abinda bedaceba kifadawa mahaifinsu,ko mahaifiyar su,muddin basu dauki mataki akaiba toh ki dauki matakin daya dace akai"koda kuwa mahaifinsu bazeji dadin hakan ba kiyi saboda kar reni ya shiga tsakanin ki dasu matsayin ki na matar mahaifinsu ki kiyaye kanki daga matar Ahmad tunda tunfarko tanuna bata kaunar ki toh kifita ahanyarta,gudun kartacutar dake watarana."

Insha Allah Aunty zankiyaye ngd da wannan nasiyyan taki kuma insha Allah zanyi amfani dashi"karki damu kede kikula da kanki dakuma mijinki."toh aunty zankula,yaushe zakizo toh??,Dariya Aunty aliyah tayi tace se munzo suna dan yanzu hakama nakirane in miki sallama dan jirginmu yakusa tashi nace bari nasar dake kar kice natafi ban miki sallama ba"kuka Sukainat tafashe dashi tace Allah Aunty nibanyar daba taya zaki tafi bamuyi sallama ba..ke bansan shashancin banza fa saura minti talatin jirginmi yatashi ko sokikeke muyi missing flight din ne??A'a toh kijirani yanzu ya Ahmad zekawoni muyi sallama pls kijirani,tana gama fadin haka takashe wayar gudun kar tahanata zuwa.


Dariya aunty aliyah tafashe dashi tana munawa Ummi wayar, tace ohh suky rigima jifa wai se tazo munyi sallama"Dariya Ummi tayi tace aiduk lefin kine dakika fada mata kinsan Sukainat da jaraba yanzu seta taahin hankalin ta kan setazo kunyi sallama,kuma inace se jibine tafiyar naki??" dariya Aunty aliyah tasake akaro nabiyu tace kawai zolayarta nake fa daman sonike inji muryanta.Aikuwa kisake kiranta kisanar mata wasa kike inko bahaka ba nanda wasu mintina kiganta agidannan dan ba hankali gareta ba cewar Ummi"Cikin dariya aunty aliyah takira number Sukainat anma haryayi ringing y katse ba'a'dagaba"kallon Ummi tayi tace kinga bata yi picking ba da'alama tashiga toilet ne kokuma tasa wayar a silent "Kai Ummi tagya'da batare datace komai ba tacigaba da jan tasbahanta...


Cikin sauri tafice daga bedroom din ta tanufi sashen Nadiya tana Addu'ar Allah yasa Ahmad yakaita.

Zaune tahangosu Ahmad nawasa da 'ya'yan sa se dariya yake 'kyal'kyalawa da'alama hira suke mishi me ban dariya"Jitayi jikinta yayi sanyi daga ninsu ahaka da 'kyar a amince ya kaita,anma haka tadaure takarasa bakinta dauke da sallama"Ahmad ne kawai ya amsa shima hankalinsa nakan hirar dayake da 'ya'yan sa.'Karasawa gabansa tayi ta tsaya cikin yanayin na Neman temako ta langwa'bar da kanta tace Dan Allah ya Ahmad kakaini muyi sallama da Aunty aliyah zatatafi yau kuma saura minti talatin jirgin su yashi,dan Allah katemaka ka kaini plssss.

'Dan murmushi yayi yace toh muje in kaiki yafada yana mikewa"Kuka Rufaida tafashe dashi tace Abba inazakaje kabarmu muna hira shikenan kaje tunda kafi santa damu ta'fada na rugawa da gudu zuwa bedroom dinsu,Da kallo Ahmad yabita hartashi dakinsu "Wani dogon tsaki Nadiya taja tace karyar banza ko tayar mota babu agidan tsoho anma azo anayima na feleke da karyar hawa jirgi dan ba asaba hawa ba kai wlh duk kutunbinarki haka zakibarni da mijina ma'karyaciya kawai.shiru Sukainat tayi duk da taji zafin zagin,Maganan Aunty aliyah ce tafado mata arai inda takecewa karkirena ta kokuma kimusguna mata anma fa idan tayi miki karkiraga mata muddin kinason 'kwatar 'yancinki.

Cikin karfin hali tace ya isheki momyn rufy meye abincin mutunci acikin wannan maganar?,dan Allah kiyi hakuri dan bansaki cikin magana ta ba kikama girmanki wannan maganar tsakani na da mijina ne"Azabure Nadiya tamike tace ke harkin kai INA magana kina mayarmin ko?,wacece ke 'yar matsiyata kawai dangin jaraba?,Harara Sukainat tamaka mata cike da tsiwa tace yo ainaga arzikin basiyansa akeba kuma kema bashi ne ubanki keda...ai bata karasaba Nadiya tadaga Hannu daniyan kwasheta dawani azabebben mari,Dasauri Sukainat tarike hannunta tace karkisoma gangancin marina dan wlh zaki yi da nasani,tanagama fadin haka tayi wurgi da hannu.Kallon Ahmad dake tsaye kaman gunki Nadiya tayi cike da takaici tace ngd da abinda kukayimin agabanka wannan yarinyar ta keyimin zagin cin mutunci kana Kallon ta bakace komai ba, hakan yanuna kafifita akan ni da 'ya'yan ka!.Kamar jira yake Nadiya tayi magana ya Murtuke fuska 'bangaren da Sukainat ketsaye yajuya yace kibata hakuri,galala Sukainat tatsaya tana kallon sa jin wai ita zatabawa Nadiya hakuri,tabb abinda ba zefaru baa kenan tafada aranta.Ba magana nake dakeba,banza tayi dashi tajuya takoma sashen ta batare data sake kallon kowa acikin suba dan harga Allah Uba befi Uba ba tafara zagarmata da mahaifi sannan dan rashin adalici yace wai tasake bata hakuri aikuwa shima yasan fada kawai yake."Afusace Nadiya tace aiga irin tanan yarinya karama tarenaka saboda taga gadon baccin ka to wlh ni bazam dauki wannan rashin mutunci ba dan babu abinda nake nema awajenta,nawa wannan yarinyar take dahar zakaba umarni taki yi in banda tamaida ka sakarai Wanda bakasan mekakeba run wuri gwara kataka mata nurki "kalaman Nadiya bakaramin sake harzukasa yayiba na shariyar da Sukainat tamasa dan haka yanufi sashen ta cike da matsanancin bacin rai.....







 _VOTE_ ✅

 _COMMENTS_ 

  _AND_ 

 _SHARE_






       *ESHAA CE~*🤙🏻

[3/23, 15:13] ESHA