12
by @reza12
πββοΈ *UWATA CE SILA* πββοΈ
*By S REZA βοΈ*
βοΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* βοΈ
*WATA TAMIN TAMBAYA GAME DA WANNAN LABARIN NA UWATA CE SILA... TA CE "WAI SHIN MAI YASA HAR YANZU BA'A SANAR WA DA MASU KARATU WAYE UNCLE BA? ALHALIN YANA CIKIN LABARIN?* _TOM KUNJI TAM BAYAR DA TAYIπ_
*AMSARKI NA 'KASAN LABARIN WATO 'KASAN WANNAN PAGE 12 D'INπ*
*PAGE π1οΈβ£2οΈβ£*
.................. Jibrin ya ce "Kawai ni dai tin ranar da abun ya faru ban sake tinawa da mutumin ba sai yau, yau d'in ma bana tinanin shine wannan domin kuwa kaman ma ba shibane to ma wai me ya had'a ku da wannan mutumin har kuke son ganinn sa? Sai a lokacin Ameera tayi magana ta ce..."No babu komai dama kawai mun ta'ba yin wani ma'amula dashine to shine mukeson sake had'uwa da shi. Nusee ta ce "To yanzu dai baka san shiba ko? "Eh gaskiya ban san shiba amma daga yau zan tayaku nai man sa mutu'karr yana cikin garinn Benue steta to babu shkka sai na nemoshi.
Haka dai Jibrin ya dinga musu dad'in baki har ya samu ya bar gurin. Nusee ta kalli Meera ta ce "Shin me kika fahim ta a tare da wannan gayan naki? Meera dama ita bata ganin laifin Jibrin domin kuwa gayan ya gama da zuciyar ta harda gangan jikin natama, ita kuwa Nusee dama can bata son Jibrin domin kuwa sun sha yin cacar baki da Meera a kan sa, kuma dama tin ba yau ba tana zargin gayan to gashi yanzu ta samu tabbaci.
'Ban garan Alhaji mudi kuwa... Lokacin da yarinyar nann tayi wannan ihuun! To lokacin shikuwa Alhaji mudi ya riga ya afka ciki, yana yi shikuma BOKA yana dariya. Tin tana iya kuka har ta daina saide nishi sama-sama.
Kasan cewar Alhaji mudi d'in dama malalacine yasa bai kai a'wa d'aya bama yagaji, amma haka ya koma saida ya tabbatar da ya samu abin da yakeso kafin ya barta a kwance agurin idon ta a lumshe tana jin tamkar kasheta a kayi domin kuwa ji take kaman babu sauran laka a jikin ta.
Haka dai Alhaji mudi ya kaiwa BOKA abin sannan ya koma gurin da ya rinyar take. Alhaji Bashir shima lokacin da yaga yarinyar nann domin kuwa har an gyara mata jiki, ai shima take yaji yana filing ai kuwa shima ya afka mata, bayan ya gama ne kuma suka duba yarinyar bata numfashin take hankalin su ya tashi...
BOKA ne ya ce "Ai yarin yar ta mutu ku d'auketa ku je ku yar da ita kun gama aikin kin ku, BOKA ya sake rushewa da dariya mai 'karfi. Boka ya ce musu "Gobe su dawo su Kar'bi aikin su, haka suka saka yarinyar nann a bayan but sannan suka kama hanya.
"Ban ga ne abun da kike nufiba? Kina ji yace shima sau d'ay ya ta'ba ganin sa kumama ai kin ji ya ce ba shi bane suna dai kama da shi, kin san dai da a ce Jibrin yasan Uncle da zai sanar dani saboda ya yarda dani kuma nima na yarda dashi please kema dan Allah ki daina zargin sa kinji?
Nusee ta kalli Meera cikin ido sannan ta me'ke tsaya ta fara magana cikin fishi... "To i'na so ki bud'e idonki domin ki fahimci komai yanda yake, shi mara gaskiya ko a ruwa zufa yakeyi to alamar rashin gaskiya ta baiyana a fuskar Jibrin kuma babu ko shkka yasan Uncle kuma yasan abun da ke tsakanin ki da Uncle...
In kuma baki yardaba tom ina son ki bincike shi da sigar wayo zaki tabbatar ni dai abin da nakeson na sarmiki shine... Babu shkka kwanannan zamu kama Uncle domin kuwa ina jin hakan a jikina kuma zaki gani.
Meera ta yi shiru tana nazarin maganar Nusee, sam ita bata yarda da cewa Jibrin zai yaudare ta ba, amma kuma koma meye tasan abun yi. Haka suka tashi suka tafi ita dai Ameera bata yarda da abun da Nusee d'in ta ceba.
'Ban garan Mom kuwa, ta farfad'o tin jiya amma kuma bata magana sai ciyon zuciya da ya dameta amma yanzu ta fara mgn, Dr Lurwan ya kalli Uncle Bala ya ce "Gaskiya hajiya Aisha ta na cikin ma wiyacin hali sabuda jinin ta ya hau sosai, saboda ta shiga cikin tashin hankali sosai, shin Alhaji mai yake damun ta haka? Uncle Bala ya ce "Dr muma bamu san a'salin abun dake da mun taba saboda munyi iya tam bayar mu amma ta ce ba komai...
Dr Lurwan ya ce "ok tom ya kamata dai gaskiya ku kiyaye kar a sake ai kata mata maka mancin wannan mutu'karr kuna bu'katar ta a raye "Ok in Sha Allah zamu kiyaye in ji Uncle Bala ya na sake mi'kawa Dr Lurwan hannu kafin ya tashi ya bar opecc d'in.
Mom kuwa tin da ta farka take kiran sunan Ameera anty Zainab ta ce "Mom Ameera bata zoba amma zata zo. Suna cikin wannan halin Uncle Bala ya shigo ya samesu, nan dai Mom ta ce gaba da tambayar su ina Ameera? Ganin bazata daina kirin ta bane yasa Uncle Bala ya kira Ameera a waya ya ce tazo asbiti yanzunnan amma Ameera ta ce bazata zoba tana wani gurine...
Nann fa ta kashe wayar ta, Uncle Bala ya ce "Gaskiya da matsala dolema yarinyar nann ta bar wannan harka koda kuwa aure zan mata koda kuwa da waye, an jima kad'an ya sake kiran number ai kuwa ta shiga, Uncle Bala ya dinga rarrashinta har ta hagura a kan zata zo.
Wai shin a'ina kika san shi da har kika yarda dashi yazo ya koyar da d'iyar ki? Shin ma wai meye sunan sa? A'wani gari yake? Yana cikin Benue steta ne ko Yaya? Ke a ina kuka had'u da shi? Wannan sune tam bayar da Uncle ya watsawa mom cikin fushi domin kuwa yana son daukar fansa a kan abun da Uncle d'in yayi Koda kuwa kutu za a je.
Mom ta saki kuka wanda yariga da yazama mata jiki, sannan ta tashi zaune ta ce "Yaya wallhi ban san shiba harta sunann sa ma na 'karya ya sanar dani kuma shid'in tsinanne ne la'anannene ba zai ga annabiba, wallhi wannan mutumin ba dan aizi'ki bane, ya cuceni ya ha'in'ceni.
"Shin a ina kuka had'u? Uncle Bala ya katseta da wannan tam bayar "Nasarawa gurin aikina babu shekka d'an NASARAWA ne to amma nasarawa wani unguwa ban sani ba. Cak Ameera ta tsaya daga waje jin abin da Mom d'in ta ke cewa...
"Nasarawa Nasarawa shine abin da ta ke ambata take ta koma da baya ta fasa shiga d'akin, wayar Nusee ta kira tace tazo yanzu-yanzufa ai kuwa ba a yi cikekken minty ashirin 20 ba sai g Nusee. Meera ta ce "Uncle d'an NASARAWA ne pls yanzu zamu tafi naji komai.
Nusee kan ganin kamar Meera bata cikin han kalintane yasa ta Kar'bi tu'kin tana mata tambayoyi har suka nufi hanyar Nasarawa lafiya.
Haka suka fito da yarinyar nann saida suka yi nisa da gurin BOKA har sun kusa su hau hanya ma kafin suka tina da yarin yar. Alhaji Bashir ne ya sake watsa mata ruwa ko zata farka amma ina ko motsawa batayi ba, kawai suka daokota suka yar da ita suka bar gurin.
Jibrin kuwa ya kira number uban gidan nashi yafi sau nawa amma no amsar haka dai ya dinga kira har ya gaji, yana son sanar da shi cewa Yarannan fa sun fara gano shirin sa, saboda haka yasan abin yi, amma gashi baya d'agawa. Sai kawai ya masa text message, yana mai jin haushin rashin d'aga masa Kira da bai yiba.
Tafiya sukeyi suna tattauna abun da zasuyi in suka isa garin da kuma yanda zasu gano gidan sa, dede sun bar Benue steta kuma basu shiga Nasarawa ba sukayi gamo. Yarinya ce suka gani a gefen titi tana d'aga musu hannu kuma ta kasa tashi sai jan jiki takeyi har sun hucema sai Nusee ta dawo da baya.
Futowa daga motar sukayi cikin tsoro sakece bai war Allah lafiya? Yarin yar ta kasa magana sai ri'ke cikin ta takeyi, hakanne yasa suka d'auke ta suka saka ta a motar su, sai suka fara shwarar su komane ko dai su tafi da ita lafiya d'in. Haka dai suka tafi da ita, sunayi suna le',ken ta sai shure-shure takeyi tam kar zata mutu.
*SPECIFICALLY HOSPITAL* dake cikin garin NASARAWA ,suka kaita kuma a cikin asbitin Mom ta ke aiki, kasan cewar babu wani ciwo a jikin ta ne yasa likitocin suka 'kar'be ta, saboda sun ce musu yar uwar sunce ba ta da lafiya ne.
Haka dai suka cigaba da kula da yarin yar nan a wannan asbitin, in da likitocin suka tabbatar da cewa fyad'e aka mata kuma irin fyad'en da in a kayiwa yarin ya bata sake moruwa wasuma mutuwa sukeyi, wasu kuma sun rasa komai na 'yamace bazata sake dawowa dai-dai bai...
Wasu kuwa bud'e su a kayi koda an musu d'in ki to bazai koma dai-dai ba, wasu kuwa sana diyar irin wannan fyad'en har haukacewa sukeyi.
( *Ya Allah ka mana tsari daga ai kata zina ka shiryi masu yin fyad'e. Allah ka sakawa duk wacce a kaiwa fyad'e, Alfarmar Annabi Muhammad sallalahu a laihi wa sallama Amin ya Allah)*
likitan ya ce "Shin ita wannan yarin yar waye ya mata wannan aikin? Nusee da Meera suka kalli juna cikin tashin hankali sukace "likita fyad'e fa ka ce?
Likita ya kallesu shima cikin mamaki ya ce "Shin ba kunce 'kanwar ku bace? Nusee cikin d'an rikicewa ta ce "Eh eh dama ai ita ita ma ai dama bamu san wanda ya mata bane, mudai mun yi 'ko'karin ganin mun ceto rayuwar ta tukunnana kafin in ta farka sai ayi komai daga baya.
Cikin gam suwa likita ya ce "Yes hakan yayi kun kyuta yanzu dai nan da a'wa biyu zata iya farkawa in Sha Allah, sukace to likita mun gode sosai Allah ya saka.
Bayan sun bar gurin likitanne MEERA ta ce "Gaskiya ni wallhi na gaji kar muje daga tai mako musa kammu a cikin masifa ni dai gaskiya ina tsoro, sannan kuma muda mukazo aiki gashima har yanzu bamu fara ba mun fara had'uwa da wani damuwar.
Nusee dai bata tan ka mataba har suka shiga d'akin da a ka kwantar da ya rin Yar. Nusee ta je kusa da yarin yar tana kallon ta tana shafa mata kai locu d'aya taji yarinyar ta kwanta mata a rai.
Ita kuwa Ameera jakar ta ta ciro tana mai duba hotunan Uncle da tasa a ka wanko mata su, ko kallon gurin da su Nusee d'in ta kema batayi.
'Bangaran Mom kuwa, haka ta ci gaba da sanar wa da Uncle Bale cewa ita bata sanshiba kawai dai ta ganshi ne wata rana a asbitin su ya kawo mara lafi kuma ya ce min shima d'an lafiyane amma yana zaune Benue steta ne, na tam bayeshi wani ai ki yakeyi a Benue ya ce min shi koyarwa ya keyi.
Amma ban tam bayeshi a wani school yake koyarwaba, Kuma ban tambayeshi cewa a Nasarawa a wace unguwar yakeba, sai kawai da yake nid'in naiman wanda zai koyawa Ameera karatu na keyi, ban tambayeshi komai ba sai matakin karatun sa, to daga nann na bashi address d'ina shine yazo...
Yace min yana da mata harda yara uku, amma ban ta'ba tam bayar sa komai game da suba, sannan ya ce min sunan sa Kamal Amma ba haka bane domin kuwa nayi tabacin ba sunan sa Kamal ba. Ya kan cemin zai je gida yaga iyali sai na bashi abun arzi'ki yatafi, Mom ta 'kara rushewa da wani sabon kuka Mai tsananin zafi da ciwon zuciya.
Uncle Bala ya ce "Dole mana kowa ya ce Kece sila kece sila, dole Ameera tazo idon duniya tace Uwarta ce sila, ashe gaskiya ne kuma bari kiji na gaya miki wallhi in har kika sake Ameera zata ji'ka miki aiki domin kuwa naga take-taken ta tana gulla wani abunne wanda babu wanda yasan Mai take nufi.
Nann take ya sanar mata da yanda sukayi da Ameeran Wai bazatazoba. Daga baya Kuma tace zatazo gashi kuma har yanzu bata zoba.
'Bangaran su Nusee kuwa, Ameera ta fito da hotunan tana kallon Uncle wanda ta kejin in har suka had'u to komaima zai iya faruwa, ita kuwa Nusee tana cikin shafa kan yarinyar sai gani tayi ta bud'e ido ta 'kura mata ido. Ganin hakane yasa Nusee ta kira Meera, tazo itama Meera ta zo da saurin ta, dai-dai lokacin ya rin Yar ta kai kallon ta gurin Meera ai kuwa idon ta ya sau'ka a kan hoton hannun Meera ta ke yarin yar ta saki wani wawan ihuu tana nuna hoton hannun Meera da hannu tana kare jikin ta. Meera da Nusee sai bin hoton da kallo sukeyi, ita kuwa yarin yar bata daina ihuubaaaaa.π
*LABARI YA FARA KIKICEWA FA SHIN ME YARIN YAR NAN TAKE NUFI??*
*AMSAR MAI TAM BAYA*
shi Uncle ai bamu baiyana shi d'in wayeba tukun, ke dai kibiyo labarin a hankali zaki fahim ci komai kuma cikin sau'ki. Nagode da bibiya ta har kika min wannan tambayaπ.
Duk Wanda take da tam baya zata iya min game da labarin domin kuwa labarin Saida tanbaya. Ga number naπ*** S REZA βοΈ.
Please comment and Sher Dan Allah
My friendπ€
My FAN'Sπ₯°
One loveβ₯οΈ
Love all π
S REZA βοΈ