UWATA CE SILA

Part 16

by @reza12

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♂️

         By S REZA




☀️ *FIRST CLASS WRITER'S AS...* ☀️





    PAGE👉1️⃣6️⃣



.............. Nusee ta kalli gurin da babban Nana yake sannan ta ce "Da gaske kaine mahaifin Nana? Cikin tsananin mamaki itama Meera ta ce "Alhaji lawan da kaifa mukeyi. Alhaji lawan ya kalli gurin da matar sa take sannan ya kalli 'yartasa wato Nana wacce itama ta zuba musu ido takasa fahimtar komai. Cike da borin kunya da rashin gaskiya Alhaji lawan ya fara magana kamar haka... "Dama ashe kune kuka sacemin yarinya? Sannan ya kalli police d'in da yake tsaye ya ce opesar wallhi yarannan 'barayine ashe sune suka sace min Nana.


Cikin ranin hankali Nusee ta ce "Kai malam bamason wani borin kunya a nan gurin abun da kakeyi da yaran wasu shine kaima a ka maka, sannan kuma Wallhi da mun san wannan yarinyar kace da tin-tini munk.... Sai kuma tayi shiru. 


( *INA FATAN Dai MASU KARATU BASU MANTA DA WAYE ALHAJI LAWAN BA? SHINE WANDA YAKE KUSA DA UN GUWAR SU NUSEE, WANDA DAGA KANSA MEERA TA FARA BIN MAZA.... KUDAI BIYONI ZAKU FAHIM CI KOMAI CIKIN SAU'KI.)*


"Cikin sauri Alhaji mudi da ke sun kuye a gaban yan sanda ya d'ago kai ya ce "Ai dai kun gani bani bane mahaifin ta ne ya mata ni bam ma santaba... Cikin wani sabon salon tashin hankalin mahaifiyar Nana ta ce "Ban gane abun da kuke nufiba? Menene ya faru da Nana d'in? Kuma meye mahaifin ta ya keyi da har aka ma 'yarsa?


Alhaji lawan ya kalli Alhaji mudi sannan ya kalli Nusee da kuma Meera cikin rashin fahimtar in da zan censu ya nufa, ya ce "Ban gane ba me kuke son cewa ne? Ya karasa maganar muryar sa na rawa. Police d'in da ke tsaye tin-tini yana kallon ikon Allah da shi da sauran yaransa guda biyu da suke gurin, da kuma Dr shima yana kallon wannan lamarin, da su Meera sunce masa 'kanwar suce a shema basu ma santaba.


Meera ta ce "Malam yau Babu wani 'boye-'boye dole a sirrin ka ya tonu dama kuma hakane abun da kayi shi za'a maka. Mera ta fara bayani cewa "Wannan d'an uwan naka tana nuna gurin da Alhaji mudi take, shine ya sace yarinyar ka, kuma yamata fyad'e shida abokin sa, suka jefar da ita a kan hanya shida abokin nasa. Mukuma a hanyar mu tazowa nan Nasarawa shine muka tsinceta, yau kwana hud'u kenan to shine yanzu taga wannan mutumin ta ce shine.


Da wani irin ihu Alhaji lawan yayi kan Alhaji mudi ya fara naushin sa yana cewa "Me yarin yana ta muku kuma kaida waye d'an banza tsinanne mara mutunci. Police ne suka 'kwaci Alhaji mudi daga hannu Alhaji lawan, da kyir. Itama maman Nana taje ta kama wiyan rigar mijin nata tana cewa "wallahi sai ka sanar da ni a ina kasan wad'annan karuwan yaran da har suke zagin ka a gaban ka?


Police ne sukace yanzu abin da za'a yi dukkanin ku kutashi muje Police station domin mu gano gaskiyar abun da yarinyar nan ta ce. Nusee kuwa da Meera sukace Amma mu ai an gama damuko? Police ya ce "Hardaku za'a tafi. Haka suka tattara suka tafi police station gaba d'ayan su. To Amma me zai faru bayan sun bud'e 'kofar d'akin da suke ciki? .


Daddy ne tsaye shida Kabir da kuma Dr kadija suna jiran fitowar Police domin ya bashi matar sa. Alhaji lawan ne ya fara fitowa wanda d'aya daga cikin police d'in kebiye da shi... Sai kuma matarsa da ita kuma tari'ko hannun Nana... Sai Alhaji mudi... Sai Police da ya ru'komasa riga... Sai kuma Nusee da Meera...sai babban police d'in da ya biyo bayan su.


Dukkanin su baba wanda ya kula dashi domin kuwa kowa ransa a 'bace ya ke. Saida yaga suna 'kokarin huceshine ya ce.. "Yalla'bai gurin ka nazofa? Wannan maganar da yayine yasa dukkanin su suka tsaya domin kuwa da 'karfi yayi maganar. Daddy kuwa wanda ke tsaye shida d'an nasa guda d'aya wato Kabir, ya kalli police daniyar yin magana dominkuwa shi sam baima ga mutanan da suke tareba...


Ya ce "Nazo tafiya da matana ne tindade bata ai kata komai ba, shiyaron tindade shine mai laifi ai shiiii.... Tsayawa yayi cek da maganar ya kasa 'karasawa saboda ido hud'u da sukayi da Nana tana kallon sa. NANA kuwa muryar sa kawai ta ji ta gane shi ne, ai kuwa tana kallon sa ta tabbatar da cewa shine. Ta ke NANA ta sake sakin wani sabon ihun tana nuna gurin da Daddy ya ke tana cewa Abba wannan ne d'ayan wallhi shine wannan Abba...


Cikin mamaki kowa ya d'ago kai ya kalli gurin da Daddy ya ke Alhaji mudi ne yace "Alhaji Bashir!!! Sai yanzu Alhaji Bashir ya ga Alhaji mudi, ai kuwa ya bud'e baki da niyar yin magana kenan sukayi ido shida tsakanin sa da Nusee da Meera. Cikin tashin hankali ya ke bin su da kallon mamaki. Meera cikin mamaki da kuma tashin hnkali dasuka bayyana a fuskar ta ta ce "Uncle? Nusee ma cikin nata mamakin ta ce "Uncle?.


Babban cikin nasune ya ce "Tom shikenan Aisha munji duk abun da ke tafe dake saboda haka mun ji kinyi kuskure kuma kin nemi yafiya mun yafe muki, mumu Allah ya yafe mana gabad'aya? Dukka zauran suka amsa da amin. Sannan ya ce "Yanzu dai ki koma gida kafin Daddy ya dawo in ya dawo zamu tattaro duk muje gidannaki ayi maganar a cen. Cikin jin dad'i Mom ta ke musu godiya, tana jin wani sanyi yana ratsata, sannan tasa a ka turo yara suka zo suka foto da kayan abincin da takawo musu sannan ta had'a musu da kud'i. Haka suma suka d'inga mata godiya, tamkar babu abin da ya faru a tsakanin su.


'Ban garan Jibrin kuwa yayanke shawarar kashe Meera zaiyi in de zai samu kud'in, kodan kud'i fa kaman ya samu ne tindade ga shi ogan sa har yafara bashi, to amma wani hanzari ba gudu ba... Yanzu number ta bata shiga sannan kuma baya samun ta a online, kawai ya yanke shawarar gidan su zaije kawai.


Sulaiman wato SM Kallon wayar sa yayi akaro na babu a dadi yanajin wani irin matsanacin soyayyar ta na 'kara shigar sa, akoda yaushe hoton ta shine a kusa dashi, son da ya ke mata yayiyawa domin kuwa jinta yakeyi tamkar jinin sa yana jin cewa koda ita d'in wacece zai iya auranta, yasan karuwa ce ita kuma yasan yarin yar batada kunya kuma yasan batada tarbiya to Amma me yasa yake sonta!? Tabbas yasan gidan su to Amma yana tsoran zuwa gidansu karyaje ya tarar Uwarta ma hakan take, domin kuwa tasha sanar masa da cewa Uwarta ce sila, wannan abun ne ya hanashi zuwa gidan su. Sannan ya kasa sanar wa da Abban sa saboda tsoron da yakeyi, jiya yayi niyar ya samu abban sa da maganar amma sanadiyar tashin hankalin da ya samu family d'in su suka shiga jiya na rashin ganinn 'kanwar su yasa ya bar maganar.


Sake Kiran number ta yayi amma dai bata shiga afili ya ce "Haba Ameera mai yasa kike wahalar da zuciyane haka, wallhi da gaske ina son ki bansan irin son da nake miki ba. Nan dai yayanke shawarar zuwa gidan su kodai ba lafiya takeba.


Nasarawa kuwa 'bangaran mommy itada Najib, an saka su a motar Police tinn 'dazu amma an manta dasu, Mommy tayi kuka har ta gaji, ita babban ba'kin cikinta ma shine bata san halin da 'yarta ke cikiba, wannan wani irin masifane!! Mai suka aikatawa uban giji haka da zai jarabcesu da wannan masifar. Ace d'an ta babban d'anta shine yayiwa 'kanwar sa fyad'e!! Inna lillahi wainana ilaihi rajiun, allha kana gani wallhi bazamu iya cinye wannan jarabawar ba tamana tsauri da yawa.


 Haka dai mommy ta dinga sambad'a sa'bon allha bata saniba domin kuwa bata cikin haiyacinta.


Najib kuwa kansa ya yi Masa nauyi har baima san mai zaiyi ba, tinda yake bai ta'ba yin fyad'e ba, saide da amin cewar yarinya amma yau gashi shida kansa yayiwa 'kanwar sa fyad'e, yarinyarda yake mata son da ko Uwarta da ta haifeta bata mata, yarinyar da ya kejin a kanta zai iya yinkomai, tabbas yau ya tsinewa giya, yau yayi danasanin shangiya a rayuwar sa...


Kuka yakeyi yana kiran sunayen abokansa da suka sakashi a harkar shangiya da neman mata yana zaginsu d'aya bayan d'aya mommy tana jinsa amma tayi tamkar bata san dashiba, Kallon mommy yayi ya tunu da wata rana.


 *TINANI* Zaune mommy take itada IKLIMA suna kallon Arewa 24 shirin waiwaye a don tafiya, Kabir ya shigo yana tangad'i lokacin bai wani bugu sosai ba, mommy ta ce "Najib lafiyarka kuwa?


 Najib yace "Mommy wallhi yau bansan cewa nafi Moto guduba saida muka kasa tsere yanzuma haka motar tana baya basu 'karaso baa nasan baza su iyaba wallhi, yana maganar yanayi kamar zai fad'i. 


Mommy ta ce "Najib karde ace giya kakesha? Cikin kuka mommy ta masa wannan tam bayar.


 Najib yace "Giya kuma mommy ana magar yau nafi kowa gudu kekuma kina wani zancen na daban kawai dai ni yanzu ki cire wannan abun da ke gabana zan huce, yana maganar ne yana nuna gurin da kujerar gaban sa take.


Cikin kuka mommy ta ce "Ya Allah kana gani wallhi bansan yanda a kayi yaron nanan ya fad'a wannan yaruwar ba... Sai kuma ta tashi cikin sauri ta nufi gurin da yake tafara zagin sa tana dukansa wai yabar mata gida, ta tsine Masa ya Kai sau 7. 


Suna cikin hakane Iklima tazo da gudu tana kuka ta fad'a jikin yayan nata tana kuka ta kamo hannun sa ta d'agashi dukdade ya mata nauyi haka suna fad'uwa suna tashi har ta kaishi d'akin sa, ta kwantar da shi a kan gadon sa, sannan ta cire Masa ta'kalmin 'kafarsa.


Inde har ya je yayi shaye-shayan sa to haka ta kemasa. Daddy kuwa dama baya zaman garin shiyasa ma baisan halin da yaran nasa ke cikiba. Saida Najib yayi nisa a harkar shangiya kafin Daddy ya sani, nanna fa Daddy yayi iya yin sa Amma ina Najib yayi nisa baya jin Kira.


Mommy da Daddy kuwa Najib yariga da yafi 'karfin su, hakanne ma yasa suke tsoran Masa maga, harta d'an uwan nasa ma wato Kabir tsoransa ya keji.


Lokacin da Najib yadawo daga wannan tinani sai kawai ya fashe da kuka yana mai 'kara tinanin irin abubuwan da IKLIMA ta masa na alkairi.


'Bangaran su Alhaji mudi kuwa kallone ya koma sama domin kuwa abubun sun har gitse mu.


Nana ta ci gaba da cewa "Daddy wallhi wannan ne d'ayan, kungan su shida abokin sa ne gashinan tana nuna Alhaji mudi.


 Daddy kokuma na ce muku... Uncle take ya manta da abun da ya kawoshi ya kalli Alhaji... mudi ya kalli... Nusee ya kalli... Meera ya mayar da kallon sa izuwa gurin Nana sannan ya kalli ma haifin Nana haka zalika ya kalli police d'in dake ri'ke da Alhaji mudi, sannan ya juyo ya kalli d'ansa wato Kabir, a ta'kaice dai saida ya kalli kowa da ke cikin d'akin kafin ya saki jiki take ya zu'be agurin tamkar babu numfashi...


Ai kuwa da wani irin sauri Nusee... Meera.. Kabir... Sukawo kansa kowa da nasa nufin a kansa. Meera ce ta fara isa gurin da yake, take ta ri'ko rigarsa ta fara magana cikin masifa da tashin hankali...."Wallhi sai katashi tsinanne matsiyaci d'an a kuya yau asirin ka ya tonu kuma Wallhi saik.... Ai bata 'karasa ba taji wani lafiyayyan mari a kumatunta har sau hud'u, jikake tass tass tasss tass, Wanda kowa da yake cikin d'akin saida ya tsorata, wanda shikuma mai yin Marin bai barta haka ba saida ya yi booll da ita cikin 'bacin rai.


Nusee ce tabi gurin da Mai marin yake cikin tsananin tashin hankalihi da 'bacin rai ta kalleshi , babu shekka ko Babu tambaya d'an gidan Uncle ne domin kuwa ga kama nann wato Kabir.....📝





 *HAMMMM. SHIN MAI ZAI FARU A GURINNANE. KUN TINA CEWA MEERA TA CE ITA A KAN 'DAN GIDAN UNCLE ZATA RAMA KUMA GASHI YA MARET???*




Gaskiya Yan fexxbookk kun ra'ke yin comment yanzu.



PLEASE comment and Sher Dan Allah.



My FAN'S 👍

My friend's🤝

One hause 🥰

Love all♥️

By S REZA ✍️