UWATA CE SILA

25

by @sreza12

🙆 *UWATA CE SILA* 🙆


    

       ( *By S REZA)*





☀️ *first class writers asoso☀️...*




 *KASHI NA ASHIRIN DA BIYAR*


      *PAGE* 👉2️⃣5️⃣


.............Haka suka kwanta kowaccen su tana aiyana abun da zai faru gobe. *WASHE GARI*. Kaman yanda suka saba sai rana tafito suke tashi suyi sallar assuba, amma yau tin qarfe hud'u da rabi Nusee ta tashi sannan ta tashi Meera akan suyi salla, ai kuwa babu musu ta tashi taje ta d'auro alaula suka tada salla. Bayan sun idar da sallane Nusee ta kalli Meera wacce take 'ko'karin komawa barci ta ce "Meera magana nakeso muyi wacce zata amfanemu, Meera najinta amma tayi banza da ita ta hau gado ta fara 'ko'karin shiga bargo. Dasauri Nusee ta je ta ri'ke bargon tana mai sanar mata da cewa magana zasuyi mai amfani. Wani irin kallo ta watsa mata domin kuwa ita har yanzu haushin Nusee ta kaji akan abun da ta mata jiya. Tashi tayi zaune kafin ta ce "Tom ina jinki?


Nusee kuwa cikin jin dad'i ganin ta fara saw'kowa dama tasan halin mutuniyar tata bata da dogon fishi sede rashin ha'kuri kamar wata kuturwa. "Akan abun da yafaru jiyane inaso muzauna muyi tinani wannan rayuwar tamu wallhi ba rayuwa bace, kwara mu bar wannan rayuwar muje muyi aure munemi yafiyar iyayenmu tundade Allah yasa suna raye please dan Allah karkice komai, tindade ke Allah ya baki wanda ya ke sonki dukda yasan irin rayuwar ki, kwara kawai ki amin ce masa, nikuma ki tayani neman soyayyar kabir please?


Meera tayi shiru tana kallon Nusee da a lamu maganar da Nusee d'in tayi sun shigeta. Itama Nusee d'in ganin hakane yasa kafin Meera tayi magana ta sake cewa "Kigodewa Allah ma ke kinada wanda ya keson ki ko a yanzu kika bada dama biki kawai za'a sha. Ta 'karasa maganar da alamar tsokana. 


Meera ta ce "To ai ni wallhi bana son SM ne, ni bai ta'ba burgeni ba ko sau d'aya. Nusee cikin jin dad'in ganin ta shawo kan 'kawar tata ta ce "Karkidamu ai shi yana sonki kuma dama samun wanda ya keson ka yafi samun wanda ka kesoso, karkiji komai a hankali SM zai koya miki yanda zaki soshi kin ji, amma fa sai kina nunamasa cewa kina yinsa, ki dinga sakar masa fuska kinji.


Meera ta ce "Anya kuwa zan iya? 


"Eh zaki iya Kar ki ji komai ai shi yana sonki.


Meera ta ce "To yanzu ya maganar Kabir d'in? Nusee ta ce "Wallhi kullum sai nayi mafarkin yazama mijina, yauma nayi kumafa acikin mafarkin shima yana mutuwar sona amma bansan a zahiri ba ko yana sona ko akasin haka allahu a'alamu. Ta'karasa maganar kamar tayi kuka.


Meera ta ce "Karki damu in Sha Allah zai soki kamar yanda kike sonsa kedai kibi komai a hankali kaman yanda na cemiki. Haka dai suka shirya cikin farin ciki da al'kawarin sun daina harkar karuwanci. Har rana tafito suna cikin d'akin suna hira cikin farin ciki, kafin suka fito domin samawa cikin su abinci.


 *KABIR* Babu abun da suka tsira dashi sai gidan da sukeciki, domin kuwa motarda aka siyarma bata kai kud'in da ake bu'kataba, saida a ka siyar da d'aya motar hakan ma saida Mommy ta sake ciro komai da ke cikin acont d'inta da kuma na Kabir d'in. Kaida ka gansu saika tausaya musu tsananin sake kamanni da sukayi lokaci d'aya.


 *SM* Gaba d'aya yau tamkar wanda a kaiwa bishara da kujerarr hajji, farin ciki kamar gonar auduga, barcci ma yau rabi da rabi yayi, aikuwa tunda ya farka da asubu ya dinga samun kira daga gida amma babu wanda ya d'aga dukda kuwa yaga kiran Mom d'in sa yafi na kowa yawa , yasan dole zata kirashi akan auran da Daddy zaiyi hakanne yasa ya 'ki amsa kowani kira, ya shirya domin zuwa hotel d'in da su Nusee ke ciki.


Babu yanda Daddy beyiba a kan a d'aura auran yau tindade anga Ameera amma Mom ta ce "Itafa sai taga Ameera a gabanta ta nemi tafiyarta kafin a d'aura aure, hakanne yasa Daddy yake ta kiran number Sulaiman akan ko sun taso amma no amsar. Suma 'yan babban gidan kowa ya goyi bayan Mom akan sai Ameera ta dawo.


 *FATIMA* Tin bata fahimci komai ba har ta gano cewar a shima wai yarinyar tana tare da 'danta kuma saitazo kafin a d'aura auren aikuwa bazata ta'ba zuwaba saide kar auran ya d'auriu. Haka ta dinga kiran number Sulaiman tin bata shiga har tafara shiga amma no amsar, take ta shiga zagawa a cikin d'akin tana neman abunyi domin kar Sulaiman yazo da Ameera.


SM kuwa shi abun ma har mamaki ya ke bashi ganin irin Kiran da a kemasa, Daddy Mom Anty kadija da ku sauran dangi kowa kiransa yakeyi ganin hakane yasa ya kashe wayar sa ya ajiyeta a jaka, domin shi duk a tinanin sa ko saboda yace yau zaidawo kokuma auran za'a yi, kodai akan abun da a kasabane tsakanin Fatima da Daddy.


Kallon su yakeyi tamkar yau ya fara ganin su tsabar wani kyu da suka masa, gakuma wani irin kwarjini da Meera ta sakeyi a idanunsa sai kawai yaji tamkar ya saceta ya gudu. "Dama dai kun shirya domin zuwa nayi mu huce daga nann? SM ya fad'a yana kallon Meera wacce sai wani sunkuyar da kai takeyi kamar amarya a daran farko. Nusee ce ta bashi amsa da cewa "Yanzu dai kafin mu tafi ka fara kwato 'yancinka a zuciyar mutuniyar taka kafin mutafi ko?. Tana gama fad'a tabar d'akin gaba d'aya ta nufi gidan su Kabir zuciyar ta na harbawa tamkar wacce tayi sata.


Tsaye take a 'kofar gidan wanda take ganin kamar shigar ta cikin gidan tamkar shiga ramin kurane, amma kasan cewar zuciyarta a dake take da soyayya kawai ta kwankwa sa amma taji shiru alamar ba mai gadi a gidan kenann.


Hakane yasa ta tura get d'in gidan ta shiga, tin daga harabar gidan ta fara ganin alamar suna cikin matsala, haka cikin dakiya da jin cewar zata iya ta fara takawa har cikin 'kofar palorn gidan.


Noking tayi har sau uku kafin taji alamar ana zuwa a bud'e tsayawa tayi tana jin fa'duwar kagan ta na 'karuwa a duk lokacin da mai bud'ewar ya kusanto 'kofar. Bud'ewa a kayi had'e da tambayar waye?


Caraff idanunsu suka had'u da na juna. Take Nusee taji tamkar tayi fitsari a wando tsabar tsorata da ganinn yanda ya had'e fuska lokacin da ya ganta.


 SM da Ameera kuwa Shiru sukayi kowa ya kasa maga yayinda Meera kejin tamkar ta rusa ihuu, ita kwata-kwata gayan baya daga cikin irin mazan da takeso baya burgeta ko d'aya. Shikuwa SM jin abun da Nusee d'in tace ne lokacin da zata fita ya bashi mamaki, wato dai tana nufin yanzu Ameera ta yarda zata amice dani!!.


SM ya ce "Kinyi kyu sosai kamar amarya. "Kaima kayi kyu kamar sabon ango. Tabash amsa kamar tayi kuka. SM ya sake cewa "Ai Nima nakusa zama angon in dai an bani dama? 


Meera ta ce "to waye zai baka dama? Ta bashi amsa cikin 'kosawa da surutun sa.


"Kece zaki bani dama.


 Wallhi Ameera ina sonki sonda ni kaina bansan a dadinsaba, ina miki so wanda babu wani ma'alu'kin da zai iya mikishi. Babu ruwana da cewar Wai ke karuwa ce mutu'karr zaki daina, to wallahi I'm ready to marry you. Ya 'karasa yana sun kuyawa 'kasa alamar ro'ko.


Jikin Meera yayi sanyi sosai hakanne yasa itama ta ce "Nasan kana sona SM amma abun da yasa bana son yin aure sabo nasan kowani namiji na aura bazai dinga kallona da kimaba, kuma dangin sa ma bazasu dinga girmamaniba, kuma shima nasan wata rana zai min gori, saboda haka please and please SM ka rabudani kaje ka samu yar mutunci...


Wacce bata zubar da mutuncin ta a wajeba, ba wacece babu wani na mijin kirki da zaiso tazamo uwa ga ya'yansa ba, nagode da irin soyayyar da ka nunamin. Takarasa maganar tana kuka tana tunowa da rayuwar da sukayi itada Nusee, take taji wani tsoran Allah ya shigeta taji ta 'kara tsanar Uncle wanda duk shine yaja mata wannan banzar rayuwa, amma in sha Allah daga yau na daina zantuba kuma na koma gaban Mom koda babu wanda zai soni zan rayu a haka har Allah ya d'auki rayuwata.


SM ya ce "Ameera wallhi na miki Al'kawarin dangina bazasu san ke wacece ba, kuma Kar ki mantafa ni a cikin harkar na ganki kuma nake sonki amma Mai zaisa na miki 'kori?


Zan soki zan baki kulawar da babu wani d'a Namiji da ya ta'ba baiwa matarsa a tarishi, Zan tarairayeki in riritaki in mayar dake tamkar jinjira, in dai zaki yarda da aurena? 


Dariya tayi jin irin kalaman da yayi, Ashe dai zai iya soyayya ta fad'a a zuciyarta tana mai jin cewar in dai ya iya irin wannan kalaman to babu shekka wataran zan soshi. Afili kuwa sai tace "Kamin Al'kawarin duk runtsi duk wiya bazaka gujeniba?


SM ya ce "Kome zakimin bazan barkiba zan rayu dake sannan na mutu da ke. "Meera ta ce "tom Allah ya sa hakane. SM cikin farin ciki ya ce "Amin ya Allah naji dad'in wannan ranar yanzu dai ina Nusaiba ta ke mutafi Kar naje wani yamin WUFF da ke?. Dariya tayi tana cewa "Au yanzu an daina cewa Nusee kenann sai Nusaiba ko?.


 Hakadai suka cigaba da hira irin ta masoya cikin farin ciki da kwanciyar hankali, dukdade ita Meera ba sonsa takeba Amma ganin cewa gayan d'an love ne yasa ta saki jiki dashi.


 *KABIR DA NUSEE* Ko magana bai mataba ya juya izuwa cikin palorn, ita kuwa ganin haka yasa ta bi bayansa. Mommy ce ta kwantar da kanta a kujera alamar dai barci ta keyi ko dai barcin ta keji. Kallo d'aya Nusee ta mata taga ramar da tayi har saida ta tausaya mata.


'karasowa tayi har gurinda Mommy take ta ce "Ina kwana saida ta mai-maita kafin Mommy tad'ago daga shigin gid'an da take tabud'e baki da niyar amsawa ai kuwa itonta ya sau'ka akan Nusee. Cikin mamaki Mommy ke bin Nusee da kallo.


Nusee kuwa take cikinta ya d'uri ruwa ta runtse idanun ta tana jinran jin mari kokuma taji an fara zagin ta ko bool da ita amma cikin mamaki da firgici jin abun da Mommy d'in ta ke cewa.


Mommy ta kamo Nusee ta na cewa "Haba yarinyar kirki tashi ki zauna a kan kujera. Tin lokacin da kika kwacemu a gurin wannan yar uwar take nakeson Allah ya had'a ni dake domin in miki godiya sannan in tam bayeki shin mai yasa kika taimakemu bayan kuna tare kuke dasu, kuma har Kabir nasa akan Dan Allah in ya ganki ko a cikin garine ya kiramin ke amma shima babu inda bai shigaba a Nasarawa amma ya ce bai gankiba.


Nusee kuwa tamkar ta zuba ruwa a 'kasa Tasha tsabar farin ciki, ta kalli gurin da Kabir d'in ke zaune ai kuwa karaf suka had'a ido, tayi saurin d'auke idonta tana cewa "Wai ya zagaya ko ina bai ganniba bayan jiyama a guri d'aya muka zauna a kotu amma zai wa Mommy na 'karya.


Mommy kuwa ganin Nusee tayi shiru yasa ta ce "'Yata kodai kin san nine yasa baki bar yar uwarki ta ai kata abun da tace a garemu ba?


Nusee ta gyara zama da kyu domin tasan irin 'karyar da zatayi domin wanke kanta da kuma 'kawar tata. Tafata magana kamar haka...


"Ita wannan yarinyar da kika gani 'kawatace kuma Ni bansa me zatayiba nidai naji ta ce nazo na rakata zata d'au fansa, hakane yasa na rakota, to bayan munzone naga abun da takeson ai kawa ba mai kyu bane yasa na cece ku, itama kuma bayan munje gida na tambayeta cewa dama ashe kin san irin wannan abun Zaki ai kata amma kika kirani? Sai ta sanar dani abun da mai gidannan ya ai kata mata, dukda na tausaya mata amma na ce mata ai ba'a kanku zata ramaba kansa zataje...


Shine ta ce min ai dama itama ba abun da zatayi kawai dai tana so ta tsorataku ne, dukda haka dai na mata fad'a sosai kuma ta ce min ta daina, sannan ta ce zatazo ta baku ha'kuri ku yafe Mata. 


Cikin sauri Mommy ta ce "ai saide mu bata ha'kuri, Allah sarki to Allha ya miki albarka yasa ki cigaba da ganar da ita gaskiya. "Amin ya Allah.


Kabir kuwa tin lokacin da Nusee ta fara bada labarin ya zuba Mata ido, Tabbas shima yayarda da abun da ta ce nann take yaji yarin yar ta bugeshi saboda irin temakon da ta musu, nann take ya zuba Mata ido bai ankaraba sai gani yayi idonta acikin nasa suna kallon juna...📝






 *KAI A JIN-JINAWA NUSEE DA 'KO'KARI* 🤔🤔🤣




To be continue.....


Please comment and Shering



By FAN'S 🙏

My friends 🤝

One hause 🥰

Love all ♥️♥️

By S REZA ✍️