UWATA CE SILA

26

by @reza12

πŸ™†β€β™‚οΈ *UWATA CE SILA* πŸ™†β€β™‚οΈ


     ( *BY S REZA)*




β˜€οΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* β˜€οΈ



 *KASHI NA ASHIRIN DA SHIDA* 


       *PAGE* πŸ‘‰2️⃣6️⃣


............ Dasauri Nusee ta kawar da kanta daga kallon sa tanajin kamar taje gareshi ta ce masa tana sonsa zata aureshi bazata iya rayuwa ba tare da shiba. Kamar daga sama taji muryar sa yana cewa "To mungode Allah yasaka miki da Allah kairi kicewa kwar taki muna mai bata ha'kuri akan abun da aka mata, munsan duk wannan abun hak'kinta ne yake bibiyar mu amma in har ta yafemana munsan zamu samu sau'ki in sha Allah.

Nusee ta mi'ke daga zaunan da take ta matsa kusa da Mommy sannan ta ce "ai ita ta dad'e da yafewa dama itace 'karfin zuwana gidannan akan naje na nemi yafiyarku in kun yarda sai tazo itama ta naimi ya fiyarku. Mommy ta ce "Allah sarki ai babu komai wallhi mun yafe mata itama tazo sai ta yafe mana.


Sun d'an jima suna hira da mommy kafin ta ce "To Mommy bari naje ana jirana domin yau zamu tafi gida dama mu yan Benue makurdi ne, Ta d'ora da cewa zamu biyo tananan da ita sai muyi sallama. Mommy ta ce "Tom sai kunzo Allah ya kiyaye hanya.


Nusee ta kalli gurin da Kabir ke zaune ta ce "Yaya Kabir rakani bakin get mana? Kafin yayi magana Mommy ta ce "Tashi ka rakata har bakin titi ta samu abun hawa kaji? Haka suka jero suna tafiya abun sha'awa kamar wasu masoya, tafiya sukeyi har suka bar gidan babu wanda yayi magana. Ita kuwa Nusee sai takejin ta tamkar ba'a wannan duniyar takeba. Wani 'bangaran na zuciyar ta na sanar da ita cewar wannan dama ce ta samu kar tayi wasa da ita ta fito fili ta sanar dashi abun da ke ranta.


"Me kukazo yi garin mu naji kin ce ku ba 'yan Nasarawa bane? Tamkar daga sama taji tambayar, hakane yasa ta rikece domin kuwa bata shiryawa tambayar tasa ba. "Amm amm dama dama kawai munnnn... Sai kuma tayi shiru, kafin tayi magana sukaji wasu yan zaman majalisa suna cewa...


"Ai wallhi anyi abun kunya yarin ya 'karama amma suka danneta har su biyu saboda tsinannune marasa mutunci. Na kusa dashi ya kar'ba da cewa "Ai ni Walhi naji dad'in wannan hukuncin da a ka musu saboda masu irin halin su shegu marasa mutunci. Wanima ya ce "Wai an ratayesu d'in ne kodai za'a musu halin girma afitar dasu kaman yanda a kasaba a wannan 'kasar tamu? Wanima ya cigaba da cewa "Ai wallahi mutu'karr suka saki mutanann idona idonsu saina hallakasu saide nima a kasheni. 


Haka dai suka cigaba da hirarr tasu, wacce Kabir da Nusee d'in duk sunaji. Nusee ce ta kalli fuskar sa domin ganinn yazaiyi aikuwa taga yana kuka lokaci d'aya taji tausayin sa, sai kawai itama ta fara hawaye ganin shima hawayen ya keyi. Ta ce "Please ka daina kuka wannan itace taku gaddarrar kowa da irin tasa kaide kayi haguri wataran sai labari. Kabir ya ce "Dole nayi kuka domin kuwa Daddy ya mana tabon da bazai ta'ba goguwaba, yasa kowa ya gujemu hatta yarinyar da nakeso kuma mukayi Al'kawarin aurema iyayenta sunsa ta gujeni...


Dik in da na shiga nunani a keyi ana cewa, yayana yayiwa qanwar mu fyad'e ta mutu, babana kuma sun yiwa yarin ya qarama fyad'e had'i da kashe jinjira 'karama saboda duniya. To in banyi kukaba mai zanyi?


Lokaci d'aya kukan Nusee ya tsaya jin cewar budurwar sa ta gujeshi, sai kawai taji wani abu yazo mata mai kama da dariya amma ta danne, take wani kwarin gyiwa yazo mata ta ce "Kabir kana sona zaka iya aurena?.


' *BAN GARAN MEERA* Ganin har yanzu Nusee bata dawo bane yasa Meera fara tinanin ko dai an samu matsala ne, ta kasa sukuni ganin kamar hankalinta baya tare dashi ne yasa SM ya tam baye ta.


Take ta sanar masa da komai akan Nusee taje gurin Kabir ne. Cikin mamaki SM ya ce "Gaskiya tashi mubi bayanta kar muje ko matsala a ka samu, ai kuwa take Meera ta had'a musu duk kayan su domin kuwa bazasu biyo ta nann ba sai de suhuce gida ta can.


Lokaci d'aya kukan nasa ya tsaya ya bita da kallon mamaki, kafin ya ce "wacece ke? An turoki domin shiga rayuwata ne ko? To in sha Allah na ri'ke Allah da manzan sa akan sharrin mutum ko aljan. Cikin sauri Nusee ta ce....


"Kabir wallhi tin lokacin da na ganka naji ina son ka, hakane yasa na dinga neman hanyar da zan samu kusanci da kai domin baiyana maka abun da ke raina, Kar kayi tinanin komai Allah d'aya kenann ni saboda Allah na ke sonka kuma so irin na aure.


Kabir ya ce "Kinada iyaye? 


Nusee ta ce "Eh inada uwa harda uba kuma duk suna raye.


Kabir ya ce "To dan sun da kike musu karki 'kara min wannan maganar, kawai kije da temakon da kika mana mun gode Allah yasaka. Kafin ya bar gurin ya ji ana cewa "Mlm Kabir ka godewa Allah da ya had'a ka da wacce takeson ka a lokacin da ka rasa wacce kakeso.


Juyawa yayi yana kallon bayansa domin ganin waye me magana. SM da Ameera ne a tsaye ta bayansa da alamar dai tin d'azu suke bayan sa, yayin da ita Nusaiba ta gansu shine dai baisan da zuwan suba.


Take SM ya bashi hannu suka gaisa. SM ya ce "Mlm Kabir karkayi watsida mutumin da ya nuna yana sonka, ka godewa Allah ma ita saida kowa ya gujeka kafin ta ce tana sonka, shawarata itace kaso mai sanka aduk halin da yake ciki. Kabir sai bin su ya keyi da kallo yayin da yaji wani mugun fa'duwar gama lokacin da ya had'a ido da Meera.


Nusee ta ce "Yanzu dai mushiga mota muje muyi salama da Mommy kafin mu tafi. Haka suka shiga mota duk su hud'un yayin shi Kabir ya kasa cewa komai sai bin su da kallo, har suka iso gidan.


Bayan sun gaisa da Mommy ne Nusee ta gaba tar mata da Meera, ai kuwa Mommy ta dinga bata ha'kuri itama tana Bata, sannan Nusee ta gabatar mata da SM akan shine mijin da Nusee d'in zata aura, ai kuwa Mommy ta saka musu albarka.


Basu bar gidan ba har saida sukayi sallar Azhar, kuma sukaci abincin rana wanda su Nusee d'in ne suka dafa, konace Nusee ce ta dafa domin kuwa ita Meera bawani iya gurki tayi ba. Ita kuwa Nusee tasha horon girki a gurin Rakiya. Kabir yaji dad'in kasan cewa da su Meera domi sun d'ebemasa kewa sannan kuma, sunyi canjen number da Nusee akan ya abinta da ita.


Haka suka shirya domin tafiya gida cikin farin cikin kowaccen su ta samu wadda ta keso. Mommy sai godiya ta keyi shikuwa Kabir har yaji baya son tafiyarsu domin kuwa sun saka Mommy cikin farin cikin da takai sati uku batayiba, gakuma lokaci d'aya da ya amin ta da Nusee d'in. Saida SM ya musu ihisani sosai wanda Mommy harda kuka domin kuwa dagaske suna bu'katar taimakon. 


Shima Kabir yayi godiya sosai, yayinda suma su Nusee suka baiwa SM akan ya 'kara musu amma kar ya ce "Sune suka bayar. Haka suka bar Nasarawa cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali izuwa Benue.


Ko a hanyama haka suna tafe suna nishad'i, yayin da Nusee ke tsinke fre itada Kabir suma SM da Ameera sai tsinke nasu fren sukeyi. Kasan cewar tsakanin Nasarawa da Benue babu nisa domin kuwa tafiyar auwa d'aya ne in dai kana sauri, ko awa d'aya da rabi.


 *BENUE STATE* babban birnin Benue State wato makurdi Hurkun, wanda ya tara al'umma kala-kala domin kudanar da kasuwancin su cikin tsananin son juna, garine wanda yayi fice acikin Naijera garine wanda ya had'a yare iri daban-daban amma suna zaune lafiya, garine mai tarin yararrika, kamar...Tibi...fulani.. yarbawa... Hausa... jukun...kanuri...idoma... Damade ssuran yare. Amma haka suke zaune cikin juna lafiya, jinjinaga ga al'umma Benue steta baki d'aya in ji salis m reza, wato *S REZA*. ✍️


 *WADATA* Acikin wadata suka tsaya da mutarsu SM ya kalli Nusee wacce tayi nisa wajan tsinke fure, ya ce "Mufara kaiki gida ne kodai muje gidan su Meera tare? Da hannu ta masa alamar sufara zuwa gidan su Meera tukun kafin aje gidan su. Haka suka huce gidan su Meera cike da kwarin gyiwar yasamo su.


Homm sukayi IRO Maigadi ya le'ko yana tambayar waye? Ai bai 'karasaba yayi ido biyu da uwar d'akin nasa ai da wani irin sauri ya bud'e musu yana zuba mata surutunsa yanda ya saba. Haka ya cigaba da mata kirari kamar ya fad'i a 'kasa, Nusee ce ta ce "Haba IRO ya isa haka mana bakaga yanzu muka dawo bane? Ai take itama ya fara mata nata kirarin har saida duka bashi wani abun. Hajiya mun yi kewar ki agidan, gidan tamkar kango in bakya cikin sa, haka IRO Maigadi ya ci gaba da cewa har suka shiga cikin gidan.


Ai kuwa dama mom tin lokacin da suka shigo a kan idon ta, ai kuwa suna shigowa babu irin kunyar nan ta 'yarfari taje da gudu da rungumeta tana kuka itama Meera d'in kuka takeyi sosai, yayinda itama Nusee take kuka shi kuwa SM ganinn hakane yasa ya bar palorn izuwa harabar gidan. Saida sukayi kuka mai isar su kafin Mom ta raba jikin ta nata kafin ta ce "Ameera ina kika shiga? Kin barni cikin fad'uwar gaba da tinani, nasan cewa nice silar komai amma mai yasa zaki tafi kibarni kin san bani da kowa sai ke d'aya dan Allah kiyi haguri kar ki sake tafiya kibarni, zan miki duk abun da kikeso.


Ameera ta ce *Mom wallhi ba laifin ki bane kawai nima harda nawa laifin nima Dan Allah ki yafemin abun da namiki Wallhi nayi nadama kuma mun tuba da irin abun da muke ai katawa please dan Allah Mom ki yafemin, ta 'karasa maganar tana wani irin kuka.


Itama Nusee ta taso daga inda take ta fara kuka tana cewa Mom ta yafe musu, haka dai sukayi kukansu mai isar su kafin sukayi shiru Mom ta ce "Suje su shigo da SM. Suna zuwa suka tararr SM baya gidan ya fita, IRO Maigadi ya ce musu "Yaje yin sallar ne Wai zai dawo.


Haka suma suka shiga gidan bayan sun yi wankane suka gabatar da sallar la'asar, kafin suka fara cin abinci, suna cikin cin abincin ne Meera ta ce "Mom wai ina Anty Zainab ne? Naga tinda muka shigo ban gantaba?.


Mom tayi shiru take fuskar ta yi alar kuka ta ce "Ameera Anty Zainab bata da lafiya kullum ciwo sai gaba ya keyi yanzu haka ma tana hospital. "Mom menene take damunta?


Mom ta ce "Kibari zuwa an jima sai muje ki dubota. Take Ameera taji abincin ya fita a ranta. Suna cikin hakane IRO Maigadi ya yi sallama akan SM zai tafi wai Nusaiba ta fito ya kaita gida sai ya tafi. Haka kuwa a kayi, da Nusaiba ta ce abari sai gobe sai suje tare da Meera domin Meera tana son ganin yanda zasu kwashe da uwar tata wato Rakiya, Nusee ta yi dariya ta ce "ai yanzu bazan biye mataba. 


Haka kuwa a kayi SM bayan sunyi sallama da Ameeran, suka kama hanyar unguwar AKEJA.


Bayan sun tafine Mom ta sanarwa da Ameera cewa ta gano dangin mahaifinta. Take Mom ta sanar mata da komai gameda yanda ta had'u da su, sannan ta 'kara da cewa zatayi aure, kuma yayan mahaifin ta zata aura. Da mamaki Mom ganin Meera tayi dariya tana cewa Allah ya tabbatar da al'kairi, nima dama nafi son kiyi auran Mom. Mom taji dad'i sosai ganin Mera bata 'bata mata komaiba.


Ita kuwa Ameera har ta matsu taje taga dangin mahaifin nata, sannan tana tinanin wani irin ciwone yake damun Anty Zainab!!! Haka dai ta cigaba da tinani abubuwa da dama da suka faru a rayuwar ta har izuwa yanzu, take take kallon irin rikicin da za'a yi tsakanin Nusee da Rakiya, take ta saki murmishii. Tana cikin haka kiran SM ya shigo, ai kuwa ta d'auka suka fara soyewa.


Mom kuwa ta kira yan babban Gida ta sanar musu cewar Ameera ta dawo guma gobe zasuzo kowa ya ganta, ai kuwa take kowa mai son ganin Mera ya hau murna, Anty kadija ma Ankirata kuma tace gobe itama tana hanya in Sha Allah. Mom bata sanarwa da Daddy dukda tasan zaiji. Aikuwa Daddy ya kirata ya ce mata "Gobe in sukazo babban Gida za'a gabatar da Ameera tare da d'aurin aure.


Itama Mom batayi musuba domin kuwa ita Meera d'in da kanta tace ayi aran, haka suka bar magar akan zuwa gobe za'a d'aura auran in Allah ya kaimu......πŸ“



Muhad'u a gurin d'aurin aure🀣.


Anya aurannan zai d'auru kuwa?



To be continue......


My FAN'S πŸ™

My friend'sπŸ₯°

One hause🀝

Love allβ™₯️β™₯️

By S REZA ✍️ comment