UWATA CE SILA

32

by @reza12

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA*🙆‍♂️


       *By S REZA*




☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


***


 *Kumin subscribe a YouTube channel d'in mu please.* 



 *KASHI NA TALATIN DA BIYU*


       *PAGE* 👉3️⃣2️⃣


..........Kuka takeyi tana neman yafiyar su ta kamo hannun Ameera ta ce "Amera na miki murna na rashin zuwan ki England domin Tabbas da kin je kema zakiyi gamo da sharin su Dele, sannan kuma na miki murnar auran ki Allah yasa albarka. Uncle Bala ya ce "Inna lillahi wainana ilaihi raju'n, haba Zainab yanzu ashe irin rayuwar da kika za'barwa kanki kenann, kin cuci kanki kuma kinsan mudai baki mana laifin komai ba keda uban gijin kine saboda haka kije..."kafin Uncle Bala ya'karasa Anty Zainab ta fara tari tana ri'ke zuciyar ta kamar wacce bata cikin haiyacin ta...


Tari takeyi sosai wanda har jinine ke fitowa ta bakin ta, gakuma gurin ya'kara yawaita da warin da takeyi, kowa dake gurin toshe hancin sa yayi. Sannu sannu shine kawai su Mom da Ameera suke mai-maita wa, tarugo hannun Mom tana son yin magana amma takasa sai kawai hawaye da suke bin fuskar ta lokaci d'aya idanunta suka kafe ta tsaya da kukan lokaci d'aya ta saki hannun Mom d'in.


Dai-dai lokacin Dr Lurwan ya shigo d'akin, nann take ya ce sufita zasu dubata ai kuwa fita sukayi kowacce zuciyar ta a karya. Yana dubata ya tabbatar Zainab ta amsa kiran mahalincin ta, lokacin d'aya shima ya shiga damuwa domin kuwa yana mutu'karr santa yaso ya baiyana mata tin ba yauba amma Allah baiyi ba, haka yaketa dakon sonta gashi tabar duniya, baisan sanda hawaye ya zubo masa saboda tausayin ta.


Haka yana fita ya ce da Uncle Bale ya sameshi a opecc, amma uncle Bala ya ce "A'a Lurwan ka sanar damu gaskiya nasan Zainab ta rasu, koda baka fad'a ba nagani a fuskarka, nann take hawayan Dr Lurwan ya sake zubowa, babu yanda ya iya ya sanar musu cewar Zainab Allah ya Kar'bi abarsa. Take suka shiga rusar kuka, sosai domin kuwa rashin Zainab a cikin su ba 'karamin ra shi bane.


Haka aka d'auki anty Zainab zuwa gida, aka mata wanka, wanda wankan ma saida kyair aka samu wacce tayi, bayan an kammala wankanne kowa dake danginta yazo yamata addu'a kafin a ka mi'kata gidan ta na gaskiya. Gidan da mmuma shi muke jira Allah kasa muyi kyakyawan karshi Amin ya Allah.


Kasancewar babban gida kowa sunsan da rasuwar ne yasa babu wanda yayi zancen kaiwa Ameera gidan ta, shikuwa Sulaiman yaso a kai masa ita ayau. Misalin qarfe takwas na dare...


Kwance take tana tinanin rayuwa daga wannan sai wannan, tana tinanin yanzu daga yanzu kuma ina rayuwar ta zata sake dosa, tana cikin hakane yaro yazo ya ce ana sallama da Nusaiba, Mama ta ce "Nusaiba kuma? Yaron ya ce "Eh.


Kafin Mama tayi magana Nusaiba ta fito da ga d'akin a guje ta ce "Jekace waye? Mana ta ce "Kai Jekace tana zuwa. Haka Mama ta mata dole ta d'au ki jijjabi sannan ta tafi tana surutai. Suna cikin mota a zaune suka hangota ta fito tana neman su, ganin hakane yasa Sulaiman ya fito ya na d'ago mata hannu.


Da mamaki take kallon sa domin kuwa ta ganeshi, da sauri ta je gurin tana mai sakin murmishii ganinn shima murmishii ya keyi. Bayan taje sun gaisa ya ce "Haba Nusaiba mai muka aikata miki a ce ranar bikin muma bazakizo ba? Bikin babbar'kawar ki amma ace babuke agurin, cikin tsananin mamaki take kallon sa ta kasa magana ta ce "Da gaske an d'aura auran ka da Ameera? "Yes andura to amma me ya hanaki zuwa? "Lokaci d'aya ta fashe da kuka tana cewa "Bani da lafiya ne kuma bani da labarin auran sanna kuma ina... "Kin aihu ne? Ta ce "eh amma yaron yazo ba rai "to Allha ya ji kansa "ta amsa da amin.


Sulaiman ya ce "Ya maganar Kabir damade kuna yin waya? Take ta sake sakin wani sabon kukan tana mai jin soyayyar kabir d'in na 'kara shiga zuciyar ta. Shikuwa Kabir ganinn bazai iya ha'kura bane, yana son ganinta ko zuciyar sa ta daina zafi sai kawai sukaji ya ce "To tana fishi dani ya za'a yi ta kirani ko ta amsa kiran wayana?


Cikin tsananin tsoro da firgici da tashigane yasa tayi baya-baya zata fad'i ai da sauri ya ru'kota sai gata ajikin sa, Sulaiman kuwa yana ganinn haka ya koma mota. 'kamshin turaren sa da ta sha'ka a 'kirjin sane ya kara tabbatar mata da cewa shid'in ne, take ta kwace jikin ta daga nasa ganinn ya'ki sakinta, tana tureshi tayi hanyar shiga gida bata masa maganaba ai da sauri ya kamota yana dur gusawa a gaban ta ya fara magana cikin so da 'kauna wanda yasa itama durgusawar tana kuka tana cewa...


"Haba Kabir yazakamin haka lokacin da zuciyata tafi bu'katar ka a wannan lokacin Kai Kuma zaka gujeni!!! Ta 'karasa tana kuka mai ta'ba zuciyar mai sauraron ta, Saida sukayi kuka sosai kafin suka tashi ya kawo mata tsarabar da ya siyomata harda sabuwar waya da SIM card aciki da number sa da ta Ameera, da gyar suka rabu zuciyoyin su cike da shu'kin junann su.


Washe gari Mom tasa dole a ka raka Ameera gidan mijin ta, ita kuma ta ce dole saide a je da Nana ta zauna a gidan ta, haka kuwa a kayi tare da Nana a ka kaita, yayinda dangin uwar mijin ta ke habaice-habaice, ranar kuwa Sulaiman bai samu damar zuwa garetaba domin kuwa haka kawai Hajiya Fatima ta ce masa wallhi in har ya shiga d'akin ta bata yafe masa ba. Hakanne yasa kullum saide su had'u a palor in ta gaishe shi ya amsa shikenan, kullum kuma sai dangin sa sun zo sun ci mata mutunci, hakanne yasa ta shiga tsananin damuwa, ga Sulaiman ko d'akin ta baya shiga ga wula'kancin Yan uwansa, saikawai kullum ta shiga d'aki ta dinga rusar kuka in sunzo ta'ki bud'e musu 'kofa hakane yasa Hajiya Fatima tazo da kanta.


Ganinn gidan a kullene yasa tayi magana da 'karfi yanda zataji "Ina kike yar matsiyata Dan gin karuwai masu tallan kawunan su a titi? Jin haka yasa Ameera ta je ta bud'e musu ai kuwa sai gata da sun shigo da iyalan ta a baya. 


"Har ke kin isa ki shiga tsakanin sa da yan uwansa, to bari kiji in fad'a miki wallhi Sulaiman yafi 'karfin ki!! In banda asiri irin na karuwai yaza'ayi ma ya aureki kuma in sha Allah wannan asirin sai ya karye. Haka Hajiya Fatima ta mata tatass kafin suka tafi suka barta. Ita kuwa Ameera babu abin da takeyi sai kuka, tana cewa yanzu shikenan wannan sunann karuwan ya bini kenann har abada, mai yasa bazasu daina cemin karuwaba bayan natuba? Haka taci kuka tamkar ba gobe.


Yau watan su d'aya harda kwana uku da yin aure amma Sulaiman bai ta'ba shiga d'akin ta ba, kuma ita bata sanar wa da kowa ba kuma ta hana Nana sanarwa da kowa abun da dangin Fatima suke mata, watarana tana zaune tana taya Nana tsifar kai, sai ga kira ya shigo wayar ta, kaman bazata d'agaba saida wayar ta kusa tsinkewa kafin ta d'aga tana sauraron ta cen gefen.


Kowa shiru yayi tsakanin su yayinda Meera ta duba taga ba'a katseba, har zata katse taji ance "Amaryar Sulaiman kin manta dani ko!? Ai da wani irin tsalle Ameera ta tashi har tana ture Nana bata saniba ta ce "My Best ke ce? Nusaiba ta ce "Nice bakin yi aure kin manta da niba? Sai kuma ta fashe da kuka itama kukan takeyi, saida sukayi mai isarsu kafin suka fara baiwa juna labarin abun da ya faru bayan rabuwa. Bayan Nusaiba ta sanar Mata da komai harda rasuwar d'anta da ta haifa sannan ta d'ora da cewa "Jiya magabatan sa sunzo an sa rana wata d'aya, ai kuwa Ameera tayi murna sosai, taso ta sanar mata da halin da take ciki amma ta fasa ta ce "Zan daure na cinye wannan jarabawar babu wanda zai sani domin kuwa dama dole hakan ya faru.


Bayan wata biyu da aure. Har yanzu babu abun da ya sauya game da zaman Ameera, shi kuwa Sulaiman yana son ya sanar wa da Daddy amma yasan in yaje to babu shekka zai saki hajiya Fatima gashi Kuma Daddy gobe lafiya jibi ba Lafiya bayason ya tasher masa da hankali, hakan yasa yaje gurin Hajiya Fatima ya dinga ro'kon ta a kan ta janye bakin da ta Masa Amma ta ce "Itafa Bata son had'a jini da karuwa ne Saboda haka kawai ya saketa, Sulaiman ya zaro ido waje kafin cikin tsananin mamaki ya ce "haba mommy yanzu in nayi haka nayi Mata adalci? Fatima ta ce "to Kai a dalcin ta maka? Haka dai duk takun da ya 'bullo saita kamashi har ya bar gidan cikin yanayin damuwa sosai, gida ya je yana shiga ya ganta a palor tana waya bataga shigowar saba ma har yazauna ya na mai kafeta da ido ganinn irin shigar dake jikinta, ai baisan lokacin da ya isa gare takeba...


Sai jitayi ya kamota, ta bud'e baki zatayi magana ya jawota jikin sa ya rungumeta sosai yana sauke a jiyar zuciya, ita kuwa Ameera tsorata ma tayi sai neman hanya takeyi ai kuwa tayi sa'a ta kwace jikinta ta filla a guje. Sulaiman ya zu'be agurin yana sauke a jiyar zuciya gami da tsananin son kasancewa da ita.


'Bangaran Rakiya kuwa ganinn Mama da Nusaiba sun dawo gidan da zamane yasa ta fara zage-zage wai wallhi bazata zauna da karuwa da kuma uwar karuwa ba, tsabar idonta ya rufe ma hard ABBA Bata bariba, ana gobe d'aurin aurane ita duk a tinanin ta angon baisan cewa Nusaiba tayi karuwanci a bayaba, bayan sun zone ta fita ko mayafi babu ta sami Kabir lokacin suna hira da Nusaiba ta dinga sanar masa 'karya da gaskiya akan Nusaiba d'in dai-dai lokacin kuma Abba ya dawo har yazo ya tsaya a bayanta bata saniba.


Saida ta gama tsaffff kafin ta 'karasa maganar da cewa "Yaro kana d'an mutunci mai zakayi da yar gidan marasa mutunci, kaje kanemi yar gidan mutunci kaji yaro, tana gamawa ta juya lokacin Abba ya shige gida, ai kuwa ta shiga taga motarsa sai ta nufeshi tana cewa "yanzu ina gidannan Ashe auran Nusaiba za'a yi shine ban da labar.... Kafin ta rufe baki Abba ya mi'ka mata takarda had'i da cewa, kince bazaki zauna da karuwaba ko? Tom kije nasakeki saki biyu, dama anyi d'aya yanzu kuma ga biyu yazama uku kenann.


Wani ihuuu tayi wanda yasa Mama da take cikin d'aki fitowa a guje amma ganinn Abba yasa ta koma, dai-dai lokacin Itama Nusaiba ta dawo da alamar Kabir ya tafine. Haka Rakiya ta dinga ro'kon Abba akan dan Allah yayi ha'kuri wallhi ta tuba amma Abba ya ce nabaki rabin awa kid'ebe kayanki ki bar min gida, haka kuwa cikin kuka da nadama Rakiya ta fara had'a Yan kayanta, ganinn Abba ya fitane Nusaiba ta shigo d'akin ta sameta ta ce "Alhamdu lillh yaude ga karuwar da kike zagi zatayi aure kekuma da kike gidan auran kin 'balla auran naki da kanki, Ni kuma in sha Allah gobe ina gsiyatar ki wannan gidan domin kisaka min albarka matsayin ki ta uwa agareni ko nace muna fuka a gareni. Cikin masifar da ke cin Rakiya da take neman wanda zata saukewa ta ce "Auran karuwa har wani abun alfahari ne? To menene matan ke alfahari da shi a gidan mijin budurci ne, kuma ke ina naki?


Rakiya tayi dariyar 'karfin hali kafin ta ce "Wallhi duk son da namiji ya kemiki in har baki Kai masa wannan abun ba aikin banzane, kuma in sha Allah ranar da yajiki fanko to ranar zai koroki gidan ubanki saide shi uban naki ya aureki. Tabbas maganar Rakiya ya soki Nusaiba sosai amma sai ta dake ta ce "ubana ba zai aureniba Amma nasan zai auri mahai fiyata kuma ki fita daga gidan nann kafin nasa ayi waje dake yanzu.


Haka Rakiya ta bar gidan tana mai cewa in sha Allah sai an saketa washe garin d'aurin aure.


 Haka Mama ta ci gaba da gyaran 'yar tata sosai. 


Sulaiman ne yaje gurin Daddy yana Kwance ya sanar dashi komai, sannan ya ce "dan Allah Daddy Kar kace nine na fad'a maka sannan dan Allah karka saketa please, Daddy kuwa da abun ya d'aure masa Kai a ce yanzu kimanin wata kusan uku da yin aure amma ta hana yaro zuwa ga matar sa to me take nufi kenann. Daddy ya ce "ba komai tashi kaje nasan abunyi.....📝





 *HAMMM TOFA ITADAI AMEERA AURE YA ZAMA SABON WAHALA*



 *Mudad'u a Page d'in 'karshe in Sha Allah* .




TO BE CONTINUE....


 *RAMADAN IS COMING OOO.*



Comment🙏

My FAN'S 👍

One hause 🥰

Love u all ♥️♥️

By S M REZA ✍️