UWATA CE SILA

Basket d'in S REZA, 1to end

by @reza12

*RAMADAN BASKET*


             *ƊIN*

                   *S/REZA*


     © AMEERA ADAM


Sadaukarwa ga masoya S/REZA musamman masoya littafinsa na UWATA CE SILA.


NOTE: Labarin ƙirƙirarre ne bai faru a gaske ba.


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


        1-End


  Sautari waɗannan abubuwan guda biyu yanayinsu ba sa ɓoyuwa ga ɗan'adam, sai dai duk da kasancewarsu tagwayen juna hakan bai sa sun kasance masu zama wuri ɗaya ba. Domin matuƙar za a iya haɗa ruwa da wuta, to tabbas za a iya haɗa farinciki da baƙin ciki wuri ɗaya. 


S/reza zaune yake ya haɗa kai da gwiwa cikin zurfafa dogon tunanin da shi kansa bai san lokacin da ya afka ba. Ƙarar wayarsa ce ta ƙatse masa tunaninsa da ta fara ruri, firgigit ta ɗago yana kallon screen ɗin wayar, lambar abokinsa Uncle Dee ya gani ya ɗan yi guntun tsaki da farko kamar ba zai ɗauka ba, sai kawai ya ɗauka a daƙile yana faɗin:


"Ya a ka yi?" Daga can ɓangaren Uncle Dee ya shi amsa da cewar, "Mutumin me ya yi zafi haka? Ka san dai ni da kai bama haka, ni kaina da ina da yadda zan yi da na yi ko aro ne na yi don na baka mu samu ka fita kunyar yarinyar nan." S/reza ya furzar da iska mai zafi ya ce, "Shi kenan na gode, sai an jima yanzu uzuri nake." 


Uncle Dee ya yi murmushi ya katse wayar don ya lura har lokacin abokinsa na cikin fushi, kuma ya san halinsa don haka ya katse wayar.


S/reza na gama wayar babban yayansu ya yi sallama cikin manyan kaya, bayan sun gaisa ya dubi S/reza ya ce, "Salisu na yo maka transfer dubu ɗari ka ji alert kuwa?" Kasancewar S/reza na cikin tunani ya sa bai san lokacin da saƙon ya shigo ba, a hargitse ya shiga duba wayar har sai da Yayansa Mubarak ya yi mamakin irin rawar jikin da ya ga S/reza yana yi." Farincikin S/reza kasa ɓoyiwa ya yi nan take ya hau washe baki kamar wanda ya jii an ce an bashi kyautar su. 


Yaya Mubarak ya katse masa tunanin da cewar, "Account ɗina ya samu matsala, zan karɓi kuɗin daga baya don kar na kashe su shi ya sa na turo ka ajiye min." Bakin S/reza har rawa yake ya shiga zabga godiya don yadda yake ji kamar kyauta aka bashi. 


Yaya Mubarak ya dube shi da mamaki ya ce, "Salisu ajiya fa na baka kake godiya ko duk azumin ne?" Babu tantama azumi ma yana mola S/reza saboda yadda bakinsa ya bushe idanunsa suka yi zuru-zuru sai muzurai yake. Da dariyar yaƙe ya dubu Yayan nasa ya bashi amsa sannan suka yi sallama, yana gama yi wa S/reza magana ya wuce ɗakin Mama yana rangaɗa sallama.


  S/reza na ganin shigewar Yayansa ya shuri takalmansa ya fice, dama abin nema ne ya samu matar ɗan'sanda ta haifi kulki. Yana fita ya kira Uncle Dee cike da ɗoki, Uncle Dee na ɗauka S/reza ya washe baki yana faɗin, "Mutumin kana ina?" Da mamaki Uncle Dee ya amsa masa, "Salisu wata bushara aka yi maka ne?" S/reza ya saki dariyar farinciki ya ce, "Share sai dai mun haɗu kana ina ne?" Uncle Dee ya bashi amsa sannan suka yi sallama.


Ya katsewa ya lalubo lambar Lobin-lobin ɗinsa, sai da ya yi kira uku ana huɗu ta ɗauka da sallama, yana jin haka ya saki ajiyar zuciya murya na rawa ya ce, "Preety ina kika shiga ne?" A daƙile ta bashi amsa:


"Ba na kusa." 


Ya sake kashe murya dukda irin yunwar da ke ƙwaƙular cikinsa ya ce, "A wanne shopping Mall kike son na yi miki na siyo miki kayan Ramadan Basket?" Nan take ta saki murya har da murmushi ta ce, "Ka je shoprite." 


"An gama ranki ya daɗe." Daga haka suka yi sallama, yadda S/reza ya jin sa cikin ƙwarin gwiwa gani yake kamar zai iya saye kayan da ke cikin Shoprite ɗin gabaɗaya.


ƘARFE HUDUN YAMMA.


  Uncle Dee da S/reza ne tsuke cikin ƙananan kaya suka shiga Shoprite, fuskarsa a washe kamar gonar auduga. Babu ɓaya lokaci S/reza ya hau jidar kayan shayi kala-kala, daga haka ya koma har da su chocolate da alawowi iri-iri. Ba shi ya bar wurin ba sai da ya kashe dubu hamsin, ya ɗauki dubu biyu ya bawa Uncle Dee. Da mamaki ya ce masa:


"Salisu ni fa ka kashe ni da mamaki ɗazu mun yi waya baram-baram kana neman ramcen kuɗi, kwatsam yanzu na ga sai facaka kake yi." Nan take Salisu ya kwace komai ya gaya masa sannan ya ɗora fa cewa, "Ina target ɗin tallafin nan da aka ce gwamnatin tarayya za ta raba, ka san na cike komai da komai ba ni da kai jiya muka ji Muntasir ya samu rabonsa ba?" Uncle Dee ya gyaɗa kai.


Cikin ƙwalisa haɗe da ƙwambarewa Salisu ya fara takawa zuwa wurin biyan kuɗi ya ce, "At any time ina iya jin alert don haka ka huta kawai." Unclee ya bishi suka biya kuɗi sannan suka wuce, a ƙofar fita Uncle Dee ya hango wata yarinya Radiya yana ganinta ya sunne kai ƙasa yana ɗage kafaɗu don karta gan shi. Bai yi aune ba ya ji ta ce, "Wannan kamar Malam Boss." Da sauri Uncle Dee ya yi gaba ko waige baya yi.


(Ku saurareni a labarin UNCLE DEE A SHOPRITE don jin labarin Radiya da Uncle Dee.)


Salisu na komawa kai tsaye shagon Uncle Dee suka wuce ya ajiye uwar siyayyar da ya yi, a ciki har da ƙananan kaya kala biyu a taƙaice ya yi kashe kuɗi sun yi dubu saba'in da biyar, daga nan ya wuce gida.


BAYAN SHAN RUWA.


  A gurguje ya sha ruwa ya fice daga gidan bai tsaya ko ina ba sai shagon Uncle Dee a shagon ya sa sabbabin kayan da ya siyo suka kira Mai adaidaita ba su tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidansu Suhaila.


Yanayin gidansu na masu ƙaramin ƙarfi ne sai dai faɗin rai a wurin Suhaila har ta fi wata ƴar mai kuɗin. TK Guy yana ganinsu ya ƙaraso wurin yana murmushi ya ce, "Ranka ya daɗe za a shiga da kayan ne?" S/reza ya fara buɗa kafaɗa ya ce, "Wannan kayan ai sun yi maka yawa." Tk ya waiga ya yi wa abokan fito sai ga su wurun su uku sun ƙaraso. Haka suka jide kayan tsaf suka fara shiga ciki, Salisu ya sallami mai adaidaita sannan ya zaro waya ya kira Suhaila ya gaya mata yana ƙofar gida kuma tuni ya aiko da kaya za a shigo mata da shi. 


BAYAN MINTI TALATIN.


Uncle Dee ya dubi Salisu ya ce, "S/reza lafiya mutanen na basu dawo ba itama babu labarinta?" Salisu ya basar dukda shima a zuciyarsa wasuwasi yake ya ce, "Ka sani ko suna cen suna duba kayan ne, kai kasan kayan nan dana haɗanko ƴar Gwanma albarka." Uncle ya yi shiru suka ci gaba da tsayuwa har sai da suka sake shafe wata minti talatin ɗin sannan Salisu ya kira Suhaila.


Uncle Dee na tsaye bai ji mai suka tattauna ba sai gani ya yi Salisu ya jefar da waya a hargitse, Unclee na shirin magana sai ji ya yi Salisu ya kurma ihu yana faɗin, "Wayyo Ramadan Basket." Hankali a tashe Uncle Dee ya tambaya shi, gumi na zuba ya zayyana masa abin da Suhaila ta ce. 


Salisi na ganin wata yarinta ta fito da Chocolate tama siɗa ya fisgota ya ce, "Ke muje ki nuna mini sauran kayan muje har gidansu Suhailan." Bai jira cewarta ba ya figi hannunta suka shiga. Kansa ne ya kulle ganin gidaje ɓangare-ɓangare daga gabas da shi ya hango wata ƙofa yana zura kai ya ga wata hanyar ce. Kai tsaye yarinyar gidansu Suhaila ta kaishi, Mahaifiyarta na ganinsu ta rafka salati tana faɗin.


"Lafiya bayin Allah garada da ku, za ku shigo mana gida." S/reza ya dubi Suhaila ya ce, "Ina Ramadan basket ɗin?" Ta ɓata rai ta ce, "Bangansu ba." Auwalu ƙanin Suhaila ya shigo yana cewa, "Umma nima na samu rabona yau su TK ne suka yi sadakar alewa har sun ɗare adaidaita sun tafi. " Salisu na jin haka wata irin juwa ta ɗebe shi, wata walƙiya ta haska masa kawai sai ya tafi luuuuu ya faɗa kan Mahaifiyar Suhaila, ita da shi suka kife a ƙasa zafin buguwa a ka ya sa Mahaifiyar Suhaila ta sume. S/reza da idanunsa ke farfari ya fata juya kai yana cewa, "Purebliss"


Uncle Dee ya tallafoshi hankali a tashe, S/reza ya fara ƙoƙarin jan zanin sirikarsa yana cewa, "Wannan ce Indomie ko madara ce?" Uncle ya fisge hannunsa ya ce, "Sirikarka ce fa."


S/reza ya shafo ƙeyarta yana faɗin, "Daga jin wannan gwangwanin madara ne." Duk yadda Uncle Dee ya so shawo kan lamarin abin ya faskara, wayarsa ya zaro ya kira Yaya Mubarak ya sanar masa halin da Salisu yake ciki amma bai gaya masa maganar kuɗin ba.


Yaya Mubarak da mai binsa Khaleed suka ƙaraso, da sauri ya tallafi Salisu yana yi masa sannu ai kawai sai S/reza ya cakumi gemun Yaya Mubarak ya ce, "Wallahi wannan ganyen shayi ne." Da sauri Yaya mubarak ya sauke shi a lokacin Suhaila ta kai Mahaifiyarta ɗaki, ai kuwa Salisu ya tafi ɗakin da gudu yana cewa, "Wayooo Ramadan Baske." Suhaila na jin haka ta faɗa uwar ɗaki, Mahaifiyarta da ke lumshe ido sai ga ta da rarrafe ta faɗa uwar ɗaki ta banko ƙofa. 


Fitowa ya sake yi da gudu a daidai lokacin Baban Suhaila ya shigo, da yake irin gajeren nan ne sosai. S/reza na ganinsa ya tafi da gudu ya kai masa sura ya saɓa a kafaɗa ya fice da gudu yana cewa, "Ko za a mutu sai dai ɗauke Ramadan Basket ɗina." Mahaifin Suhaila sai ihu yake, su Yaya Mubarak suka rufa masa baya.


Da ƙyar suka samu aka tsaida Salisu, ganin abin bana ƙare bane ya sa Uncle Dee zayyane duk abin da ya faru. Yaya Mubarak na jin haka ya kwaɗawa Salisu mari zafaf biyu a fuska, nan take S/reza ya ware idanunsa ya ce, "Wabillahillahi sun gudu da ramadan baske ɗin." Yaya Mubarak ya sake kwaɗa masa mari ya ce, "Iskancim banza ashe kana sani kake danganta gemuna da lipton, baka san darajar gemun nan nawa ta fi dubu darin nan ba." Ganin za a ƙara kai masa wani marin Salisu ya sake yin kan Mahaifin Suhaila ya ce, "Wayyo Ramadan basket."


Intaƙaice muku dai a daren aka kamo su TK Yaya Mubarak ya sa aka haɗa har da Salisu da Uncle Dee aka kai su police station.


Kafin a shiga da su Salisu cikin Cell ya hango DPO yana zuwa ya kama tunbinsa yana girgizawa yana faɗin, "Ramadan basket." A fusace DPO ya sa aka yi ciki da Salisu aka fara haɗa masa jini da majina.


S/REZA A KIYAYE HANGEN DALA, TUN BA A SAMU KUƊIN BA A YI BAJAT ƊINSU DA KUƊIN WANI.😂😂😂😂


Barkanmu da shan ruwa🌚