WATA KISSAR..(Sai Mata)

CHAPTER 10

by @ayshercool

✨✨✨✨

    *WATA KISSAR...... *

         ✨✨✨✨✨


           ( *Sai Mata* )


      


             


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/***


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA

(Daddy's girl)

The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app ***


Gmail ***


   


ELEGANT ONLINE WRITER'S 


        


      


     Page 10


Haka Ammar ya haɗe rai Mufeeda ta karɓi magani rabi tasha, guri ta nema ta kwanta a falon saboda kanta yana ciwo sosai gajiyar biki se ƙara nuƙurƙusarta take.


Bacci ne ya sake yin awon gaba da ita bata farka ba se sha biyun rana, jikin ta duk ya mutu ta tashi zaune, Ammar ma yana kwance a ƙasan carfet yana bacci.


Ɗan ƙura masa ido tayi sannan tai murmushi ta miƙe, zaga gidan tayi ta lelleƙa, ta shiga kitchen ta sassauke kayan kitchen ɗin ta canza arranging ɗin kayan da basu yi mata ba, ta wanke kwanukan da suka ɓata dukda basu da yawa.


Fridge biyu aka sai mata, Ta buɗe fridge ɗin kitchen Ammar ya zuba kazar da ya siyo mata jiya da fresh milk, babu alamar shima yaci, ta rufe fridge ɗin ta koma ɗaki ta kira Mama a waya.


"Mama na ina wuni shine baki kirani ba ko?"


Mama tace "ya za'ayi in kiraki a wannan lokacin ke ba gashi kin kirani ba, ina fatan kindena kukan?"


"Hmm Mama kenan na dena, ina Baba?"


"ya fita tun ɗazu, Yaya ina fatan komai lafiya"


"lafiya ƙalau mama"


"Masha Allah ya mijin naki?"


Dariya Mufeeda tasa "wai yanzu fa miji nane ko? Wallahi ni dariya ma kika bani mama"


"dariya ko? Burinki ai ya cika Auta, Allah ya Sanya alkhairi"


"hmm Hajiya Mama kenan, ban taɓa zaton haka kike sona ba se jiya, Allah sarki Mama wayar nan da muke ji nake kaman inyi kuka wallahi"


"Mufeeda kenan in haifeki a cikina sannan ince bana sonki, rawar kanki ne yasa muke faɗa dake ai, yanzu dai ba wannan ba, ya batun Abinci zaki iya girkawa ko a kawo muku?"


Murmushi Mufeeda tayi tasan me Mama take nufi dan haka tace

"Mama kenan me ze hanani iya girki? Niba rashin lafiya ba, daga gidan suma ance za'a kawo mana yace karsuzo, ki barshi kawai"


Mama a ranta tace

"wannan yarinyar da wani abu ya faru tsakanin su yadda take da shegen raki, da banji muryar ta haka ba"


A fili tace "shikenan naji ana kiran salla ki gaishe shi"


"to Mama amma yaushe zaki zo?"


"Babu rana balle wata, ko gidan yayyanki kinga ina zarya ne?"


"haba Mama dan Allah, ni gaskiya kizo please"


"ke salla zanyi yanzu se anjima"


Suka yi Sallama, Mufeeda ta miƙe tayi alwala tayi salla, sannan ta ɗan shafa turare, ta fito falo Ammar yana inda ta barshi yana bacci da alama shima gajiyar bikin ce ke damun sa.


Ta tsaya ta ɗan ƙura masa ido, a ranta tace "Allah yasa yadda fuskarka take da kyau haka zuciyar ka take my Ammar"


Taje kusa da shi ta zauna daddaki gefen sa sannan ta kai bakin ta kunnen sa kaman da raɗa tace "Mijin Jaririya ka tashi lokacin salla fa yayi"


Jin ƙamshin turaren ta yasa a hankali ya buɗe ido ya sauke su a nata, tace "lokacin salla yayi, kar ya ƙure shiyasa na tashe ka" 


gani tayi ya kafe ta da ido, tsarguwa ta fara yi ko tashin sa da tayi ta masa laifi, shikam Ammar ƙananan kitson dake kanta da'akayi wa style yake kallo, dan kanta babu ɗan kwali tana da dogon gashi gashi baƙi sosai kitson yayi kyau. 


"wai ya naga kana kallo na, mena yi kuma?" 


Haɗe rai yayi ya miƙe ya tafi ɗakin sa yanawa kansa tsaki ko me yasa ya tsaya kallon ta oho. 


Tana nan zaune aka kawo wuta, ta miƙe tana ƙoƙarin gwada kayan kallon ta, taga Ammar ya fito da mukullin baburin sa ze fita. 


Da sauri ta miƙe tana faɗin" ina zaka kuma? "


Ba tare da ya kalle ta ba yace 

"zanje gida in karɓo mana Abinci" 


"Abinci kuma Yaya Ammar? Ba se in dafa mana ba, ni kaɗai zaka bari a gidan ni gaskiya dan Allah ka zauna" ta ƙarasa maganar kaman za tayi kuka. 


"Kece zakiyi girkin inci? Me zaki iya dafawa? Ko kuma wa kike tunanin zeci jagwalgwalon ki? Haka kurum ki samun gobara a gida, ban saki wani yin girki ba kinji na gaya miki, Sannan dole ki zauna ke kaɗai tunda kika ce ke Aure kike so" 


"Nice zan dafa jagwalgwalon ko? Shikenan naji amma gaskiya ba zaka fita ka barni ni kaɗai ba" 


Tsaki yayi yai gaba ze fice, ta bishi ta riƙe rigar sa tana kuka kaman ɗan yayen da maman sa zata fita ta barshi . 


Ƙarshe Ammar se haƙura yayi suka ci sandararriyar kaza data kwana a fridge da madara (🤣). 


Seda suka kwana huɗu Ammar baya fita ko'ina se masallaci, yana gida saboda ita, kuma ba shiga shirginta yake ba se dai su zauna kaman kurame, kullum sedai suci indomie, da safe kuma su sha tea, Ammar be iya girki ba, gashi ya hana ta girki wai ba zata tayar masa da gobara a gida ba kota girka jagwalgwalo ba, ita kuma ta gaji da cin wata indomie ga shi fafur ya hana a zo masa gida yace ba yanzu ba. 


A kwana na biyar bayan sun gama karyawa se ganin Ammar tayi ya fito da mukullin babur ɗinsa a hannun sa, ya wani haɗe rai karma ta kawo raini tace baze fita ba, tana ganin sa tai masa murmushi tace

"Mijina ina zuwa?" 


Jin tace masa mijina yasa shi ɗagowa ya Harare ta, ya lura kaman da gayya mufeeda ke fitowa babu ɗankwali akan ta, dan wani lokacin zuciyar sa har raya masa take kaman ya taɓa kitson nan nata, dan ba ƙaramin kyau kitson yayi masa ba, amma se ya basar dan karta raina shi, sake sakar masa wani tattausan murmushin tayi tare da karɓar agogon hannun sa, ta ɗaura masa sannan ta sumbaci hannun nasa ta riƙe hannun nasa cikin nata, cikin shagwaɓa tace


"mijin baby dan Allah ka dawo da wuri kaji, Allah ya kiyaye hanya ya wadatar da kai da halal komai ƙanƙantar ta ya nesan taka da haram komai yawan ta" 


"Ameen" ya amsa a taƙaice ya zare hannun sa a nata ya fice. 


Mufeeda ta ƙudurce a ranta cewar daga yau ta dena zaman kurmanci da Ammar dole ta koya masa hira, ta saki jiki dashi ta gane abunda yake so, da haka zata kama zuciyar 'yan mazan tayi wasa da ita yadda taso. 


Tunda Ammar yayi aure yau kwana biyar Zainab ta kasa sukuni ta kasa cire Ammar a zuciyar ta, dan har yanzu bata fidda ran zata auri Ammar ba. 


Gajiya tayi ta miƙe ta fita zuwa gidan Anty Jidda Yayar Ammar. 


Ta shiga tai Sallama suka gaisa, daga nan suka shiga hira, Zainab tace "Anty Jidda yau Ammar kwanan sa biyar da Aure kenan ko?" 


Jidda tace "eh abun haushi ba yau kwana biyar kenan da wannan shiriritaccen Auren danni a gurina shiriritacce ne" 


"Hmm Anty Jidda na kasa cire Ammar daga raina fa, Wallahi duk cikin mane mana shi kaɗai nake so, na kori kowa gashi yanzu ya barni yayi auren sa" 


Jidda tace "amma ke kam baki da wayo, har aure fa kika yi kika fito, dan yayi aure shine me namiji ne fa, mata huɗu aka halatta masa ya aura, dan haka ki ci gaba da bashi dukkanin kulawa, karki karaya ki ci gaba da kiran sa kuna gaisawa kina tura masa saƙknnin da zasu nuna har yanzu kina ƙaunar sa"


Zainab tace "Amma Anty Jidda kinfi kowa sanin halin ɗan uwan ki, kin sanshi da murɗaɗɗen hali, sam baya son irin wannan abubuwan, ni mamaki nake yi yadda aka yi yai Aure, ya Auri wannan 'yar Yarinyar" 


Jidda tace "waye yace miki sonta yake ya aure ta? To itace take sonshi, dan haka har yanzu kina da dama" 


Zainab tace "shikenan Anty Jidda nagode insha Allah zan cigaba da jarrabawa insha Allah" 


"Koke fa, se kace ba mace ba, Ammar ai be auri mace ba, ki dage mana zee" 


"to Antina zanyi ƙoƙari Insha Allah" 


Mufeeda tana zaune akayi knocking ɗin gate, ta saka hijjabinta tace "waye?" 

"buɗe ki gani" da sauri kuwa ta buɗe jin Muryar Yaya Amina, tsalle tayi ta rungume ta, suka shiga cikin gida. 


"wayyo Allah daɗi, ban zaci zakizo nan kusa ba, ɗazu mukayi waya da Mama ba tace min za kizo ba" 


"Ai bata san zanzo ba nace bari inzo dai in ganki" 


Yaya Amina ta daɗe sosai suna hira, ta kawowa Mufeeda Soyayyiyar Miya ta sha kaji da dafaffiyar shinkafa, da kuma snacks tace 


"ga wannan kuyi Amfani da shi, kafin akawo miki garar ki" 


"wayyo Allah na Yayata shiyasa nake matuƙar yinki, kamar kin san an hanani girki" 


"kamarya an hana ki girki" 


Dariya Mufeeda tayi tace "Me gidan yace girki ba yanzu ba" 


Yaya Amina tace "inyee ƙauna, Allah ya bar wannan ƙauna har mutuwa" 


"Ameen ya Allah my Yaya Amina" 


Nan suka dinga hira se Yamma Sosai sannan Yaya Amina ta tafi. 


Fa' iza ma cousin ɗin Ammar sam ta rasa abunda yake mata daɗi, a baya a tunanin ta izzar Ammar da kuma burinsa na auren mace me shekaru, baze bari ta iya fallasa asirin zuciyar ta game da shi ba, Amma yanzu tunda har Ammar ya auri yarinyar da bata kai shekarun ta ba to babu shakka zata gaya masa abunda ke ranta, ita koda Allah zesa ya saurare ta. 


Mufeeda bata ƙara ganin Ammar ba se dare, abunda take so yau taci shinkafa miyar da Yaya Amina ta kawo mata, ta turawa Ammar saƙonin soyayya kala kala bayan fitar sa amma babu wanda yayi responding, se bayan sallar isha'i ya dawo, gidan ko ina tsaf da shi ta gyara, se ƙamshin turaren wuta ne ke tashi. 


Tana jin shi ya shigo da Napep ɗinsa cikin gida bata fito ba. 


Ammar Ya shigo da kayan Abinci ya kai kitchen ya ajiye, ya jera mata kayan tea akan fridge ɗin falo, yana ta shirya kayan ne ta buɗe ƙofar ɗakin ta ta fito. 


Kallo ɗaya yayi mata ya saurin ɗauke kai saboda dogon wando ne a jikin ta da vest kanta ba ɗan kwali, Ammar gaban sa seda ya faɗi da ganin Mufeeda a haka, kayan sunyi fitting ɗin body structure ɗin ta sosai, amma 'yan mazan ya maze ya ci gaba da abunda yake. 


Ƙarasowa tayi tana masa shagwaɓa tace "shine ka tafi ka barni tun safe kaƙi dawowa har kuka fa nayi naita jin tsoro, dama haka ake rainon" 


"to mezan dawo inyi miki?" 


"ka dawo in ganka mana, kasan kana da Jaririya a gida amma ka tafi ka barta tana kuka" 


Girgiza kai yayi yaje ya nemi guri ya aje key ɗin babur ɗinsa ya zauna yana lumshe ido alamar gajiya. 


Ruwa ta zubo masa a cup tazo gaban sa ta durƙusa tace "ungo ruwa ka sha" 


Ba tare da ya kalleta ba ya karɓa yace "Nagode" 


"Yaya Ammar ɗina kaci Abinci kuwa?"


"Eh naci"


"Amma shine ni ka tafi ka barni bayan ka hanani girki ko? Ka manta dani ko Jaririyar ka taci Abinci ko bata ci ba ko?"


"da baki ciba ai da ban ganki a haka ba, da ina dawowa zan tarar kina kuka"


Murmushi tayi tace "da yake nice uwar kuka ko?"


Ammar ya kuma kallon ta yace "ke bakya jin kunya ne kike yawo da wannan kayan a jikin ki?"


Tace "kunya kuma me nayi ne, me kayan sukayi?"


"Kalli kayan jikin ki fa"


ta kalli kanta sannan tace "to aiba abunda nayi, kuma aini yarinya ce, ai bakomai dan nasa wannan kayan kuma naga ai gida nane" 


Ɗan guntun tsaki yayi yace "jeki kitchen ki ɗakko plate"


Ta miƙe ta tafi kitchen tana wata irin tafiya me cike da ɗaukar hankali, ya bita da kallo tana zuwa ta tarar da kayan Abincin daya siyo hada su cornflakes da kayan tea, ga kayan miya nan duk ya kawo, ta jinjina kai tace "Yaya Ammar da ƙarfin hali yake" ɗakko plate ɗaya da cokali ta kawo masa, ya ɗakko wata leda ya ɗakko takeaway a ciki ya juye.


Nama ya siyo da gurasa , ya juye a plate ɗin sannan yace

"ki ɗakko plate ki zuba kici naki"


Ta kalle shi tace 

"ni bana ci sedai in zaka bani a baki" share ta yayi ya fara cin na sa, ta dawo kusa da shi ta zauna, wani sassanyan ƙamshi ke tashi a jikin mufeeda, Ya ɗakko naman ze kai bakin sa ta riƙe hannun sa takai nata bakin, ta kalle shi ta yamutsa fuska tace


"Wallahi wannan naman babu daɗi, ka dena ci kar ya ɓata ma ciki kitse yayi yawa a jiki"


"A cikin ki nake zubawa ko nawa?"


"cikin ka ai cikina ne taya ya zanso cikin Mijin baby ya samu matsala, Yawwa Mijina naga Kayan Abinci daka siyo mana a kitchen, Allah ya ƙara mana Arziki, Allah ya saka da alkhairi"


"Ameen" ya amsa


Ta shiga kitchen ta Zubo masa Abincin da Yaya Amina ta kawo mata, ta ajiye a gaban sa tace "ka ajiye wannan naman kaci Abinci" 


"ina kika samu wannan?" 


"Kaci se in gaya maka" 


Dama Yunwa yake ji ba daɗin naman nan yake ji ba, dan haka Ammar ya kama Abinci ya cika tumbin sa. 


Seda ya ƙoshi sannan tace "ɗazu Yaya Amina tazo, ita ta kawo" 


Ammar yace "aina san kedai bazaki iya girki ba" 


"waini meka maida ni, to nama fita iya girki" 


"A'a ban yadda ba" ta tura baki tace


"duk ranar da nayi girki ko, seka manta hanyar fita dan daɗi" 


ya ɗan kalleta yace "kin fiye shiririta, kije ki duba fridge akwai lemon tsami dana zo dasu, ki dafa tea ki matse min ɗaya a ciki ki kawomin ɗaki na"


"shayi da lemon tsami kuma? Maganin mene hakan? Lemon tsami fa yana saka ulcer" 


"ke bana son tambayoyi, bana cin Abinci da daddare kinsa naci Abinci, zan shane saboda bana son inyi tumbi" 


Murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta, me Ammar ya maida itane, an gaya masa ban san ma'anar hakan ba? a fili tace "shikenan bari in haɗo maka" 


Ya miƙe ze tafi ɗakin sa yace

"Sannan karki ƙara fitowa falon nan da wannan shigar" 


"Aikuwa sedai a sa labule a raba falon" 

Ya waigo yana kallon ta, ta basar da shi. 


Ta haɗo masa tea ta kai masa ɗakin sa. Yana banɗaki yana wanka, ta ƙara gyara masa gadon sa ta ɗakko airfreshner ta fesa masa a ɗakin, ta samu guri ta zauna tana kaɗa ƙafa. 


Ya fito sanye da jallabiya yana tsane jikin sa, ya kalleta bece komai ba ɗakin se ƙamshi yake, ya zauna ya janyo tray ɗin data ɗoro kayan tea ɗin, har yanzu kayan jikinta ne a jikin ta bata canza ba, tai sauri ta karɓa ta haɗa masa, yasa hannu ya karɓa ya fara shan abunsa. 


Ya kalle ta yace "tashi ki tafi kije ki kwanta dare yayi" 


"Jira nake fa ka sha ka ragemin" 


"me zan rage miki?" 


"tea ɗin mana, nima bana so inyi tumbi" 


"ba zaki sha ba, Ke kam kin fiye rigimar tsiya, seki bari in kikafi haka girma se kema ki dinga sha" 


Miƙewa tayi ta ɗan juya tace "nikam wane irin girma kake so inyi ne, ina da nauyi fa" 


"Wai bance miki kar ki ƙara fitowa da wannan kayan ba?" 


"ni gaskiya zafi nake ji, idan nasa kaya ƙurajen zafi ne fa zasu fitomin" 


Girgiza kai yayi yace "to naji yanzu dai tashi ki tafi nagode" 


"gama shan tea ɗin se in tafi da kayan, daga nan na ƙara ganin ka" 


Ɗan murmushin gefen baki yayi ya ci gaba da shan tea ɗin sa a hankali, lokaci lokaci idan ya ɗago se sunyi ido huɗu da Mufeeda se lumshe ido take yi alamar bacci take ji, da sun haɗa ido se tayi masa murmushi, ga kitson nan me matuƙar ɗaukar masa hankali, gata tayi wani cas a cikin kayan dake jikin ta. 


Wayar sace ta fara ringing ya duba agogo sha ɗaya saura, kaman kar ya ɗaga amma dai ya ɗaga, daga sallamar da tayi ya gane me magana amma ya maze yace


"wake magana?" 


"Ammar har Aure yasa kaman ta dani? Zainab ce fa" 


"nagane, ya akayi? Dare yayi be kamata ki kirani yanzu ba" 


"Na kira kane inji lafiyar ka" 


"Ance miki bani da lafiya ne?" 


"hmm Ammar kenan, koba komai ai babu laifi dan masoyi ya tambayi lafiyar masoyin sa" 


A kunnen Mufeeda duk wannan tattunawar da suke, wani mugun kallo Mufeeda tayi masa taja tsaki ta fice tabar masa ɗakin. 


Gaba ɗaya shi Mufeeda ce ma ta bashi mamaki, da fari tana zaune tana ta masa kallo me cike da salona soyayya, Amma lokaci ɗaya yanayin ta ya canza, a hankali yace


"karki ƙara kira na a dai dai wannan lokacin bana so" 


ya katse wayar sa yana ci gaba da mamakin ƙwailar sa wai har wannan 'yar mitsitsiyar abar tasan kishi. 


Mufeeda zuciyarta har wani raɗaɗi take saboda ɓacin rai, zata iya jure duk wani abu da Ammar ze mata, in dak baze zageta koya dake ta ba, Amma kome za' ayi bata tunanin zata iya Yadda tayi sharing ɗin Ammar ɗin ta da wata 'ya kowace ce ita kuwa. 


"Ni yarinya ce kaman Yadda mutane suke faɗa amma duk mace mace ce komai ƙanƙantar ta kuwa, da yarintar tawa zan maida Ammar ɗina yadda nake so, zanyi abunda zan nesanta tunanin sa daga kowace mace in ba niba, bazan iya zama ina kallo wata mace tana kiran sa a waya ba"


Ayi managing da wannan am so much busy 


Ayshercool 

***