CHAPTER 15
by @ayshercool
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨
( *Sai Mata* )
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/***
P.W.A✍️
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba
Watpad @ Ayshercool7724
What's app ***
Gmail ***
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Page 15
Da Safe Ammar ya fito, se dai Mufeeda bata saka jambakin ba kaman yadda yayi tsammani, haushin kansa ne ya kama shi, komeya na son ganin ta da Jambakin ma oho, haka sama sama ya tambaye ta ya jiki, Sarai ta gane abunda yasa shi haɗe rai
Tace
"Jiki da sauƙi Alhamdilillah tunda Mijina yana tare dani"
Ƙin kula ta yayi ya karya abunsa yana wani basarwa.
Da ya gama ya kalle ta yace
"ya kamata ki shiga ku gaisa da maƙwabta, ɗazu mun haɗu da maigidan dake kallon namu, yace min baki shiga kun gaisa da matan su ba, kuma haka ake yi"
"to idan naje me zance musu?"
"nima ban sani ba" ya bata amsa.
"ce musu zanyi nice matar gidan nan, kokuma Jaririyar Yaya Ammar?" shiru ya mata tare da yi mata wata uwar harara.
Mufeeda tace "shikenan zan shiga Insha Allah"
"Sannan kuma ba cewa nayi kuma kidinga shige2 ba da tarkacen Maƙota ba, cewa nayi kawai ku gaisa bana son shige2"
"Shikenan insha Allah zan kiyaye, dama niba me shige shigen bace, saboda bana son takura da sa ido"
Ya gama karyawar sa ya shirya ya fita, yana ƙoƙarin tada babur ɗin sa ya fita da shi ne Mufeeda ta ƙaraso da sauri ta riƙe ƙarfen Babur ɗin, cikin shagwaɓar ta ta tace
"Wai fita zakayi?"
"A'a zama zanyi, in kinji yunwa ki dafani ki cinye"
"idan na dafa ka na cinye na zauna da wa? Wani abu nake son baka ne"
Juyowa yayi yana kallon ta, ba zato ba tsammani ta sumbace shi a kumatun sa na hagu tace
"take a good care of your self My love, Allah ya kiyaye hanya, ya wadata mu da halal" tsayawa yayi yana kallon ta, yayin da ita kuma ta koma gida.
Seda ta kammala aikace2 da zata yi a gidan sannan ta shiga maƙota suka gaisa kaman yadda Ammar ya urmace ta, wasu sun bayyana mamakin su kan cewar itace matar gidan, yayin da wasu kuma suka ɓoye hakan, ita kuwa ko a jikin ta, tai musu sallama ta koma gida.
Ta koma gidan ta babu daɗewa Yaya Usman ya kira ta a waya yace "ke buɗe mana ƙofa muna waje.
Aida gudu ta miƙe ta tafi gate ta buɗe, gurin Baba ta tafi da gudu ta rungume shi, Baba ya shafa kanta yace
"I really miss you Auta na"
Mama tace
"Baban ki kaɗai kika gani ko? Ni baki ganni ba"
Ta ɗan tura baki tace "Aini duk fushi nake, tunda aka kawo ni masoyyiya Amina ce kawai tazo gidan nan"
Yaya Usman yace "mu koma kenan?"
Tai murmushi tace "ni bance ba"
Mota biyu suka yi, duk Yayyen ta da yaran su, haka suka zo.
Mufeeda ta rasa inda zata saka ranta dan murna, nan suka shiga shigo da kayan Abinci na garar Mufeeda.
Yaya Fadeela tace "Auta naga kin ƙara haske ko dai an gamu ne?"
"Eh na gamu dake mana"
Anty Murja tace "Lallai Autar Baba, wallahi kin ƙara nutsuwa"
Suka dinga tsokanar ta.
Taji daɗin ganin 'yan gidan su, nan suka dinga hira, tana raha.
Sedai ba' azo da Yaya Amina ba cikin ta ya tsufa.
Mufeeda tace "Mama bari in kira shi, yazo ku gaisa"
Mama tace "A' a, ƙyale shi kar a takura masa"
Iyayen Mufeeda sunji daɗin yadda suka ga Mufeeda ƙalau da ita, alamu sun nuna gidan Ammar ba yunwa yana iya ƙoƙarin sa.
Se la'asar sannan suka yi mata Sallama, da zasu tafi Baba ya bawa Mufeeda Naira dubu goma taita godiya, suka ce ta gaida Ammar, sannan suka tafi.
Mufeeda taga uban kayan garar da Baba yayi mata, ta dinga murna tace "Allah ya biya ka da Aljanna Baba na, kwana biyu Yaya Ammar ya huta"
Bayan la'asar Ammar ya dawo, seda ta bari yaci Abinci ya huta take gaya masa su Mama sunzo.
"meyasa baki kirani kin gayamin ba?"
"Baba ne yace in ƙyale ka, maybe kana aiki kar a takura maka"
"Gaskiya banji daɗi ba, naso a ce nazo na tarar dashi"
"Dukan su suka zo harda su Anty Murja gaba ɗayan su"
"Naso mun haɗu dasu, but insha Allah very soon zamuje"
"duk suna gaishe ka"
"Ina amsawa"
Yana zaune yana kallo, yaga Mufeeda tana cin wani abu, ya kalleta yace
"me kike ci? Se an jima ki lanƙwashe kice ciki na ciwo ko?"
"gullisuwa ce fa"
Ammar yace "Madarar kike gullisuwa da ita, za'a raba madara kowa ya ɗau tasa, in kika ƙarar da taki seki koma shan tea baƙi ko kuma cin cornflakes ba madara"
Ɗan tura baki tayi tace "idan na shanye semu koma shan taka"
"Seki sha ɗin in gani"
"Ai da kanka zaka bani, saboda bazaka iya shan shayi da madara ni kuma ka bani ba madara ba"
Hararta yayi ya ɗauke kansa
Wani cup ta ɗakko me kyau da murfin sa a jiki ta miƙa masa kofin tace "ungo naka"
Ya kalleta yace
"meye wannan?"
"taka gullisuwar ce"
"Ni bana shan wannan kayan shiriritar da yarinta, kedai kije kiyi tayi"
"da daɗi fa ka ɗanɗana kaji"
Girgiza mata kai yayi yace
"Ke nace bana so"
Ta ƙyale shi bata kuma takura masa ba, se bayan ya dawo daga sallar magariba Mufeeda tace
"Yaya Ammar zo kaga"
Tana ɗakin tsakar gida, dan haka ya leƙa ɗakin, kayan Abincin daya gani a ɗakin ne ya sashi yin turus, yace "Wannan fa?"
"Kayan gara ne dasu su Baba suka kawo mana"
Shiru yayi yana kallon kayan yace
"Amma wannan kayan ai sunyi yawa ya zamuyi dasu, ni badan ina tsoron kar Baba yaji babu daɗi ba gaskiya da bazan karɓi kayan nan ba"
"Haba Yaya Ammar meye sa? Ai bamu kaɗai zamuyi Amfani da kayan ba, za'a ɗibarwa su Abba, Su Yaya Maryam ma duk a basu, Baba zeji ba daɗi idan kai magana akai"
Ɗan girgiza kai Ammar yayi yace "Kayan nan sunyi Yawa fa"
"Yaya Ammar babu wani yawa da suka yi, da Baba baze iya ba baze takura kansa yace se yayi ba, dan Allah kawai ka bar zancen nan, muci Abincin mu kawai ko?"
Tai maganar tana leƙa fuskarsa, wani ɗan murmushi yayi wanda iya kacinsa leɓensa, ya koma falo, ya kalleta yace
" Ni zan kwanta seda safe"
"Amma ina fatan ba ranka ne ya ɓaci ba akan kayan nan?"
Girgiza mata kai yayi yace
"A'a inajin Bacci ne kawai"
"shikenan Allah ya tashemu lafiya"
Yace "Ameen" ya wuce ɗakin sa itama ta wuce nata.
Harta kwanta taji kawai bata ji daɗin yanayin yadda ya tafi kwanta ba, dan haka ta miƙe ta fito ta tafi ɗakin sa.
Har ya kashe fitila ya kwanta, ta shiga da sallama sannan ta kira sunan sa
Amsa mata yayi sannan yace
"Ya a kayi?"
Gadon ta hau ba tsammani yaji Mufeeda a jikin sa, a hankali yace "lafiya kuwa?"
"Yaya Ammar zuciya ta ta kasa samun nutsuwa, gaba ɗaya yanayin ka tun jiya zuwa yau baya mun daɗi, dan Allah idan laifi nayi maka kayi haƙuri"
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ni nace kin min laifi ne?"
"Yanayin ka ke nuna kaman na maka laifi, bana jin daɗin ganin ka a haka, idan kuma akan kayan nan ne se in kira Yaya Usman yazo a mayar da su"
Tai maganar jikin ta a sanyaye, gyara kwanciyar sa yayi yace
"ni babu abunda kika yi min, kawai dai ɗan Adam dole wataran ya tashi babu daɗi shikenan kawai"
Kwanciya tayi sosai a jikin sa tace "Duk da haka yana da kyau in san damuwar mijina, dukda Mijin nawa yana ganin Yarin ta ta, Amma bazan so in ganshi cikin damuwa ba"
Nannuyar Ajiyar zuciya Ammar ya sauke, yace
"Naji zan dena damuwa, tashi kije ki kwanta seda safe"
"Zan tafi Amma buɗe bakin ka"
"Me yasa zan buɗe bakina"
Yana maganar ne ta saka masa Gullisuwa a bakin sa, shiru yayi yana tunawa, tayi masa daɗi Sosai dukda shi irin wannan abubuwan basa gaban sa yana ganin kaman shirita ne.
Wata ta kuma saka masa a bakin sa, ƙamshin turaren jikin ta, da yadda ta kwanta a jikin sa ya sashi cikin wani farinciki dabe san dalilin sa ba.
A hankali cikin raɗa tace masa
"da Daɗi kuwa?"
"Babu daɗi kaman inyi amai"
Murmushi tayi tace
"koma babu daɗi tunda ka riga ka sha shikenan za'a raba madara dai dai, kuma tawa seta fi Yawa"
"Naji tashi ki bani guri, mara kunya ji yadda kika biyoni har ɗaki kika wani kwanta min a jiki"
"Ba jikin mijina bane, kuma dai naga ni Yarinya ce"
Kasa cewa komai yayu, Ƙasan zuciyar Ammar kuwa bugawa yake da ƙarfi yana saƙawa yana kwance abubuwa daban daban game da matar tasa da yake mata kallon tayi ƙanƙanta da Aure.
Miƙewa Tayi daga jikin sa, ta sumbaci goshin sa tace
"Honey seda safe, I love you Baby"
Riƙe hannayen ta yayi, kaman ya hana ta tafiya, se wata zuciyar tace masa "She's still young, Yarinya ce raini ze shiga tsakani na da ita, tayi ƙanƙanta"
Sakin hannayen ta yayi kaman an masa dole yace "Seda Safe" ya juya mata baya.
Dukda a cikin duhu ne bin bayan sa Mufeeda tayi da kallo tareda ɗan girgiza kai, Ammar akwai taurin kai da izza.
Ta koma ɗakin ta, Ammar kam baccin sa rabi da rabi ne, juyi kawai yake akan gadon har Asuba.
Da safe yana fitowa yai tozali da ita akan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana ta kaɗa ƙafa ta sha kwalliya ta kashe ɗauri, bakin ta se shining yake da jambaki, ga ƙamshin girki dana turare ya gauraye falon, gani yake kaman tana sane take wannan abubuwan.
A hankali ya tako falon kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, ya samu guri ya zauna, ta ɗago ta kalle shi tare da yi masa murmushi, ta taso daga inda take tazo gaban sa ta durƙusa ƙasa tace "Barka da Safiya Yallaɓai" kallon ta yayi tayi kyau sosai, yana jin daɗin yadda lokuta da yawa take bashi girma, wani lokacin kuma ta maida shi kaman ƙaramin yaro, yace
"lafiya ƙalau prof. Kin tashi lafiya?"
Miƙewa tayi ta zauna a kusa dashi ta ɗan tura baki tace
"Bayan jiya dan naje ɗakin ka ka koreni"
Murmushi ya ɗanyi bece komai ba, ji yake kaman yace mata tayi kyau, amma ya fasa.
Ta jingina a jikin sa tace
"A kawo breakfast ne?"
"Bari se anjima kaɗan"
"yau bazaka fita da wuri bane?"
"Eh se lokacin salla yayi zan fita"
Mufeeda a ranta tace
"Yaya Ammar manya maganin ƙanana, na gane Lagon ka sarai, Jambakin nan da gashin nan ba ƙaramin tafiya suke da kai ba"
Ta kamo hannun sa tace
"Yau Friday ya kamata a yanke maka farce" bece komai ba ita kuma ta ci gaba da wasa da yatsun hannun sa, can ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa takai hannun ta fuskar sa tace
"in taɓa?"
"in kika taɓa sekin biya"
"dan Allah sau ɗaya fa"
"kika isheni sena aske gemun nan"
"aikuwa idan ka aske na dena kulaka, dan ina son gemun nan sosai"
Ammar yace
"tashi ki kawomin Abinci"
Ta tashi ta kawo masa Abinci, ta haɗa musu Tea, zata sa masa Madara yace "bar madarar nan ki shanye abarki, naga ta kusa ƙarewa"
"Se insha tea da Madara kai kuma ka sha ba Madara?"
"Eh kece 'yar gayu ai, ni ban damu da shan me Madara ba, kiyi Addu'a Allah ya hore kafin ta ƙare in siyo wata"
Shiru tayi tana kallon sa, duk faɗan Ammar yana da sauƙin kai Sosai, kuma yana matukar ƙoƙarin ganin ya wadata da Abinci, baya bata Abinci mara daɗi, ko alawar da tayi jiya da madarar be mata faɗa ba.
"Allah ya ƙara maka Arziki na halal My love"
"Ameen" ya amsa mata.
Suka kammala karyawa, ta ɗakko nail cuter ta yanke masa farce tsaf.
Ammar yace "in Allah ya kaimu ranar Saturday zamu ɗan fita, Umma nata mita har yanzu ban kaiki ba"
"Wayyo Allah daɗi, Allah ya kaimu lafiya nima na ƙagu ka kaini in gansu"
Wasa2 Ammar seda ya kusa makara zuwa masallaci saboda yadda Mufeeda ta narke masa a jiki take ta zuba taɓarar ta iri2.
Se azahar sannan yai wankan juma'a ya fita salla.
******************
Fa'iza taga abubuwa sunƙi tafiya yadda take so, ta kuma wanke ƙafa ta tafi gidan Yaya Jidda, suna ta hira Fa'iza fa sako maganar gidan Ammar
"Nikam Yaya Jidda kinje gidan Yaya Ammar kuwa?"
"hmm ina fa naje, idan naje gurin wa zani gurin wannan ƙwailar Yarinyar kokuwa? Bani da lokacin su daga shi har ita"
"Amma ai gidan ɗan uwan ki ne Yaya Jidda ya kamata ku dinga zuwa kiga a wani hali hake ciki? Idan kuma ya tattara ya koma gurin ta gaba ɗaya fa, ku kuma ko oho kenan?"
"Aini bana son zuwa inga abunda ze ɓata min rai, ranar da nayi masa magana akan wulaƙancin da tayi muku, seda mukayi faɗa dashi ya kare ta"
Fa'iza tace "kinji abunda nake gaya miki ko Yaya Jidda wallahi ki dinga zuwa, idan ba haka ba ana ganin ƙanƙantar ta da haka zata raba shi da kowa, tunda tun yanzu ya fara goyon bayan ta"
Jidda tace "kuma fa hakane, zanyi ƙoƙari inje gidan nasa, zan kuma yiwa umma maganar ta ja masa kunne, akan ya kula da 'yan uwan sa, dan nasan ita zata gaya masa yaji ko kuma Maryam, in be ga dama ba idan Maryam ta faɗi magana ze rusa maganar uban kowa ya ɗau tata, duk wannan masifar tasa ita baya yi mata"
Fa' iza tace "haba dai Yaya Maryam ɗin?"
"ita fa, ai baya shiri da kowa a cikin mu kamar ita, indai Maryam na san abu ze hana kansa ya hana uban kowa ya bata"
Jinjina kai Fa'iza tayi, a ranta tace "dole inje in ziga Yaya Maryam itama, zata taimaka min"
Suka ci gaba da hirar su daga nan suka yi sallama.
A hanya Fa'iza tana tafe tana zancen zuci akan ya zata ɓullowa lamarin Ammar, taji ana mata horn tsayawa tayi ta juya, me motar yazo dai2 inda take sannan ya sauke baƙin gashin motar yace
"Manya maganin ƙanana, ke kuwa talaka na ganin ki"
Murmushi tayi tace "Ba gashi ka ganni ba, yaushe rabon da in ganka?"
"Shigo motar se muyi magana" ba musu ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shige.
Ya kalleta yace "Ni ko a bikin Ammar ban ganki ba ina kika shiga haka?"
Tsaki ta ɗanyi tace
"me zanje inyi masa a gurin bikin, dan abun kunya kuna gani kuka barshi ya auri wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar, bayan a duniya ya tsani Auren ƙaramar Yarinya"
"kinfi kowa sanin Halin sa ɗan uwan ku ne, ke zaki gayawa wani halinsa, shekaranjiya na haɗu da shi da matar tasa ya kaita Asibiti se zuba shagwaba take yi, Wallahi Yarinyar nan za tayi saurin tafiya da Imani namiji, duk jin kan Ammar lallaɓa ta yake ranar, ina ga ko ciki ne da ita "
Wani dogon tsaki ta ja tace
"dan Allah ka dena ɓata min rai, dan abun kunya 'yar wannan Yarinyar Ammar zewa ciki, mtseww"
Dariya sosai Faruk yayi yace "Kai
Fa' iza, to shi kna ruwan sa, Wallahi tun ranar ɗaurin Aure da naga yarinyar nan na kasa samun nutsuwa, wallahi dana ga Yarinyar nan kafin bikin su da bazan taɓa bari Ammar ya aure ta ba, Idan naga Yadda take wa Ammar shagwaba wani irin kishi ne yake kamani, Wallahi ina jin ƙaunar yarinyar nan har a cikin zuciya ta"
Wani irin Murmushi Fa'iza tayi tace "dagaske kana son ta"
"Wallahi Fa'iza ina mata so bana wasa ba, ni ko ban Aure ta ba kawai dai in same ta, kin gane ai balle ma ina son in Aure ta, wallahi tunda naganta mata ta dena birgeni"
Jinjina kai tayi tace
"Me ze hana mu haɗa kai mu taimaki juna?"
Ya gyara zama yace "kamar Yaya kenan?"
Murmushi tayi tace "zamuyi waya"
********************
Kasa nutsuwa Yaya Jidda tayi, dan haka ta tambayi mijin ta zata fita unguwa, shiryawa tayi ta tafi gidan su Ammar.
Koda Mufeeda ta buɗewa Jidda ƙofa taga kammanin ta da Ammar, sannu da zuwa tayi mata tai mata iso ciki, wani irin kallon banza take bin Mufeeda dashi.
Tun kafin Jidda ta shiga falon idon ta ya sauka akan jibgin kayan Abincin dake ɗakin tsakar gida, tayi ƙwafa suka shiga falon.
Ta kalli Mufeeda tace
"Ina Ammar ɗin?"
"be daɗe da fita ba kuma, yana gida tun ɗazu, amma se in kira shi a waya"
"Ammar ɗin da yake fita tun farar Safiya shine yake zaune a gida har bayan azahar sannan ya fita"
Shiru Mufeeda tayi tace "bari in kawo miki ruwa"
"Ke dawo bana son gulma, ni bazan sha ruwan ki ba, sannan ki buɗe kunne da kyau ki jini, Wallahi daga yau idan wani daga dangin mu yazo kika kuma masa wulaƙanci sekin bar gidan nan dan baze yuwu ba, 'yar mitsitsiya dake kin san wulaƙanci, su Fa' iza sa'anin kine da zasu zo ki musu rashin mutunci, ko gidan uban kine? "
Mufeeda ta girgiza mata kai alamar A'a, Mufeeda a ranta tace" wannan ce Jidda kenan? "
" to ko yanzu yai niyya ze iya sakinki ya auri wata, 'yan uwa kuwa ba' a canza su, ance miyar ki hadda kaji alhalin be kaiwa namu iyayen ba, shafaffiya da mai, ni ina tunanin kin haɗawa Ammar da ƙulumboto dan Ammar ba sakaran namijj bane, daga zuwan ki ki kainainaye shi, kalli uban kayan Abincin daya tile miki a ɗaki, Amma iyayen mu ko oho, se anyi magana yace bashi da kuɗi ina ya samu kuɗin daya siya miki wannan kayan haka? Algunguma baki isa ki rabamu dashi ba"
Jidda taiwa Mufeeda cin mutunci tsaf, Sam Mufeeda bata tanka mata ba, se dai zuciyar Mufeeda kaman ta fashe, ga Jidda ta girme ta sosai balle tace zata rama.
Seda ta gama sannan ta tashi ta tafi, bayan tafiyar ta se da Mufeeda tayi kuka dan ba ƙaramin jin zafin abunda Jidda tayi mata tai ba.
Ammar ne ya dawo ya tarar da ita a falo, ba haka ya saba ganin ta haka ba in ya dawo, amma ya basar ya miƙo mata leda yace
"gwada wannan takalmin in gani ɗazu na ganshi yayi kyau na siyo miki"
Ƙoƙarin maida hawayen idon ta take, Ammar ya ga idon ta da ƙwalla, ya ɗan haɗe rai yace
"kukan me kike yi?"
"bakomai bafa kuka nake ba"
"bana son ƙarya, meke damunki?"
"bana jin daɗi ne"
A fusace yace "ƙarya kike lafiyar ki ƙalau, meya same ki? Bana son ƙarya"
Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
***