E3
*🧚🏾♀️SHU'UMA🧚🏾♀️*
_Ƴar mutan zazzau Naanarh M Sha'aban✍🏾_
*🌟⚡ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION⚡🌟*
{R.S.W.A}
***
```Marubuta masu aiki da fasaha da zallar tsagwaron Amana, faɗakarwa tare da nishaɗantarwa.```
_Alƙalaminmu ƴancinmu✍🏾_
*SADAUKARWA GA YAAYANARH💕💫*
_Note:Wannan littafin free book ne (littafin kyauta ne) kawai dai kuyi comments kuma ku yi ƙoƙarin sauke Arewabooks a playstore domin samun litattafan hausa masu daɗi nawa da na wasu marubutan_
*Gargaɗi: ban yarda a juya min wannan littafin ba, ba tare da izinina ba, a kiyaye wannan doka ce.*
**______________
E3
Habu ya miƙe yana dariyar mugunta ya ce "au haba? ni zaki saka a ɗaure? to ai shikenan ki je duk inda zakije ki kira duk wanda zaki kira, na farko dai kin san waɗannan jakunan iyayennaku masu shegen son abin duniya ba za su taɓa barin kije ko da gurin ƴan sanda ba, kuma ko da sun ji abinda na yi wa wannan dabbar wasu ƴan chanji kawai zan basu shikenan ba za su damu ba, dan sun fi son kuɗi akan komai shiyasa ko da na kasheta babu abinda zai faru" Hassana a fusace ta miƙe tana cewa "idan kana tunanin cewar akwai wanda zai tsayar da ni domin na kai ka gidan yari to ka yaudari kanka, ko iyayena ba su isa sun hanani ɗaureka ba, idan ka na tunanin ƴan tsirarun kuɗinka zai rufe musu baki, inda zan kai ka ba za su taɓa karɓar cin hanci ba, dan ko ubanka bashi da arziƙin da zai siyesu" Tana kai wa nan a maganarta ta zuge jakarta ta ɗauko waya, ta ɗauki kusan minti ɗaya tana danne-danne sannan kuma daga baya na ga ta kara a kunne "Kamalu ka cewa Ladidi ta shigo zata taimaka min mu ɗauki Usaina" abinda tace kenan ta kashe wayar, Habu cikin zafin rai yace "karki sake ki fitar min da matata daga gidannan" Wani mahaukacin mari ta ɗaukeshi dashi sai da ta jera masa sau biyar, cikin huci tace "Habu ka ke ko wa? to idan baka cikin hankalinka ko ka fara shaye-shaye kasan da wacce ka ke magana, kai har ka isa, har ka na da bakin da za ka ce karna fita da ƴar uwata, to ina so na tabbatar maka idan ka ƙara furta ko da kalma ɗaya ce sai na kumbura maka bakinka, sai na tabbatar na saɓa maka kamanni ta yadda uwar da ta haifeka ma ba za ta iya gane ka ba, bare ƴan gari" Asabe wacce tun shigowar Hassana ta ja baki tayi shuru, dan kuwa ta fuskanci Hassana ba kanwar lasa ba ce, bata da mutunci ko kaɗan, zamewa tayi ta shige ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, Ladidi ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Hassana ta amsa mata tare da nuna mata inda Usaina take kwance tace "taimaka ki tayani ɗaukarta mu kai ta asibiti, bari na goya Ilham" tayi maganar tare da nufar inda Ilham take ta saɓata a bayanta, ta taimakawa Ladidi suka ɗauki Usaina suka fita da ita daga gidan, Habu ya bi su da kallo zuciyarsa a ƙuntace, wayarsa ya zaro ya shiga kiran lambar mahaifin Usaina, ringing ɗaya biyu ya ɗaga bakinsa na rawa wajen furta "Hello Alhaji da fatan kana lafiya" cikin muryar isa da taƙama yace "dakata malam! na kiraka ne domin na faɗa maka cewar ƴarka Hassana ta zo gidana ta ci min mutunci akan ta tarar ina hukunta Usaina saboda matata tace mata bamu da ruwa ta je ta ɗebo mana, kuma tayi wanki ta tsaya tana mata rashin kunya, to ni ba zan ɗauki wannan iskancin ba, daman irin tarbiyyar da ku ka ba su kenan? har ni Hassana ta isa ta kalli cikin idanuwana tace zata ɗaureni a gidan yari, kuma na ce mata kar ta fitar min da matata ko ina ta ɗauketa suka fita, to abinda nake so na faɗa maka shine, ka ja wa ƴaƴanka kunne, musamman ma Hassana dan idan har ka na son ƴarka Usaina ta cigaba da zaman aure a gidana, ka hanata zuwa gidana idan ba haka ba, dukkanku zaku fuskanci hukunci babba a wajena" Yana gama faɗar haka ya kashe wayarsa, ya shige ɗakinsa.
A ɓangaren Mahaifinsu Usaina kuwa hankalinsu ya gama tashi shi da matarsa, da yake wayar a handsfree ya sakata, ta ji duk abubuwan da Habu ya faɗa, "Malam ka ga wannan shegiyar yarinyar zata ja mu rasa jin daɗin da muke sha a cikin gidannan ko? dan kuwa idan har mukayi sake, ba mu takawa Hassana burki ba, to zata kashewa yarinyar nan aure shikenan mun rasa Habu ba zan ƙara taimaka mana da ko naira biyar ba, kalli fa irin kuɗaɗen da yake bamu duk wata, amman Hassana da yake tsinanniya ce, ba ta ganin abinda yake mana, ai kamata yayi ta dinga kallonsa tamkar mahaifinta, saboda duk abin ci da abin sha da take ci a gidannan shi yake siyowa ya kawo mana, amman da yake yarinyar nan ba ƴar arziƙi ba ce har ta je tana yi masa rashin mutunci" Baba yayi caraf da zance tare da cewa "ai wallahi bata isa ba, zan koya mata hankali dan na fuskanci kanta yana rawa, bari na kirata sai na yagata, yarinyar nan so take mu saka ƙafar wando ɗaya da ita" yayi maganar yana lallatsa wayarsa, lambar Hassana ya kira amman ya ji ta a kashe, baƙin ciki ya lilliɓe zuciyoyinsu, haka suka cigaba da tattauna akan irin sharaɗan da zasu gindayawa Hassana.
•••• •••• ••••
Tun ranar da Nazeer sukayi faɗa da Khadija ya kwashe kayansa ya koma hotel da ƴammatansa suna holewarsa, kamar kullum yana zaune akan gadonsa shi kaɗai daga shi sai gajeren wando, hannunsa riƙe da shisha yana zuƙa, turo ƙofar ɗakin da aka yi ne yasa ya ɗago kai yana kallon me shigowa Khausar ce, cikin shigarta ta matsastsun kaya riga da wando blue, kanta babu ɗan kwali, ta ba za gashin dokin da ta saka a kafaɗarta, idan ka kalleta ba za ka yi tunanin musulma ba ce, ƙarasawa tayi kan gadon ta zauna ba tare da tace masa komai ba, shima tunda ya kalleta sau ɗaya ya ga ita ce ya komar da hankalinsa kan shisharsa, kusan mintina goma suna zaune babu wanda ya cewa ɗan uwansa ko da sannu ne, saboda dukkansu fushi suke da juna, Khausar da ta ga Nazeer bashi da niyyar yi mata magana yasa tace "Yanzu ka kyauta abinda kayi min ranar saboda wata banza" Nazeer ya juyo yana kallonta tare da cewa "na'am da ni kike magana ne?" Juyowa tayi dan jin maganar rainin hankali da yayi mata, idanuwansu suka haɗu da na juna, "Baby! nii...." maganar ce ta maƙale mata saboda kukan da ya sarƙeta, Ajiye shishar yayi tare da matsawa kusa da ita, yana ƙoƙarin rumgumeta, tayi saurin miƙewa tsaye tana cewa "karka taɓani tunda dai ka tsaneni" Nazeer ya zabga tagumi yana kallonta na tsawon lokaci kafin yace "Khausar ban tsaneki ba, ina tsananin sonki sosai, kaf ƴammatan da nake kulawa ban taɓa haɗuwa da wacce ta shiga raina kamarki ba, kuma saboda irin yadda nake jinki a raina ne yasa na baki PA a companyna" Khausar tace "Amman meyasa lefin matarka ya shafeni bayan ni ba abinda nayi maka, ga shi daman har marina ita ma tayi, amman baka iya ɗaukar mataki ba, kuma a haka ka ke cewa baka sonta, ni na san daman kawai faɗa ka ke yi, tunda gashi ka nuna min a fili" Dariyar takaici Nazeer yayi yana cewa "ba za ki taɓa ganewa ba Khausar, wannan yarinyar da kike gani ba ƙaramar shaiɗaniya ba ce, a garinsu ma ta addabi kowa, ita ce sakawa mutane ido, ita ce haɗa makirci, shiyasa ƴan garin suke kiranta *SHU'UMA*, macijin sari kanoƙe kenan, ga bariki a gabanki zatayi maganarki, amman ba za ki taɓa kawowa a ranki da ke take ba, dan har ki saka baki ma, ban san yadda zan fasalta miki irin makircinta ba, dan duk yadda kike tunani ta huce haka, kina ganinta a haka kamar mara wayo, amman idan ta kullo miki wani shaiɗancin Allah ne kawai zai fitar da kai" Khausar ta zauna a jefen gadon tana cewa "to amman kasan irin yadda take har ka yarda aka aura maka ita" Nazeer yace "ba zan taɓa iya ƙin bin umarnin Abbana ba, a duk duniyar nan ba ni da abinda nake so, irin ganin farin cikin Abbana, wannan dalilin yasa na amince na aureta, wanda hakan yayi matuƙar faranta masa ransa" Khausar ta numfasa tare da cewa "Amman ya kamata ka ɗauki mataki akan yarinyar nan, duk shu'umancinta kayi maganin ƴar iskar ƙauye" Dariya yayi tare da cewa "ina nan ina haɗa mata babban tarko, wanda idan ta faɗa sai ta gwammace kiɗa da karatu ba SHU'UMA ba, idan ma hatsabibiya ce, sai na ci ubanta" Khausar tayi dariya tare da cewa "yauwa baby" janyota Nazeer yayi jikinsa suka shiga aikata fasiƙancinsu, wa'iyazubillahi.
Anan zan dasa aya✍🏾
*Share*
*Comments*
*ƳAR MUTAN ZAZZAU CE❤🔥*
_{Sarauniyar Royal Star👑}_