FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Allah first☝ Prophet muhammad (s.a.w)💔 Proudly muslima❤ Daddy's queen👑 Mommah's princess💓 Writing novels is my hobby❤💙 Author queen❤ C.e.o royal star writers association✍🏽
Sample · E1
*🧚🏾♂️SHU'UMA🧚🏾♂️*_Ƴar mutanan zazzau Naanarh M Sha'aban✍🏽_*🌟ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION🌟* _{R.S.W.A}_*** Masu Aiki Da Fasaha Cike Da Zallan Tsagwaron Amana,Faɗakarwa Game Da Nishaɗantarwa Tare Da Wa'azantarwa,Alƙalaminmu 'Yancinmu_*_Alhamdulillah! Allah ina ƙara gode maka da ka bani damar sake yin wannan sabon littafinnawa me suna SHU'UMA, masoyana da fatan zaku tayani yaɗa wannan littafin wanda yake ɗauke da faɗakarwa, ilmantarwa tare da nishaɗantarwa, karku manta dai kyakkyawan alƙalami baya rubuta shirme🤞🏽🤩_*_Ina yi wa ɗaukacin jama'ar musulmi murnar zagayowar bikin ƙaramar sallah, Allah ubangiji ya karɓi ibadunmu, da fatan anyi sallah lfy Barka da Sallah masu daraja🥰😘__SADAUKARWA GA YAAYANARH ABIN ALFAHARINA💗😘(NASAD😉)_**__________________*E1*____✍🏽Wani irin mahaukacin mari ya ɗauketa dashi, sai da ya jera mata sau uku sannan ya fara magana cikin zafin rai da tsantsar ƙiyayya "ke kin isa! ke wacece da har budurwata zata zo ki koreta ƴar talakawa kawai, matsiyaciya wacce bata san abinda yake mata ciwo ba" Abinda ya ba ni mamaki duk irin marin da ya sharara mata gani nai ta ɗago tana murmushi tace "Nazeer ni ka mara?" Tayi maganar tana nunasa da yatsa, cikin fushi ya ɗaga hannu zai sake marinta, tayi saurin riƙe hannun, ta yar dashi tace "karka kuskura ka sake marina wallahi, kayi na farko shima ɗin ba wai kyaleka nayi ba, ina so ka ajiye wannan a ranka sai na rama marin da kayi min, dan ni Khadija ba na yafiya sannan kuma ba na mantuwa, kuma ƴammata ne duk shegiyar da ta ƙara shigo min gida da duka zata fita, domin nan gidan aurena ne ba gidan karuwai ba" Nazeer ya kalleta a ƙufule yace "Wallahi Khadija sai na tabbatar na koya miki hankali, na san wannan fiffizgar da kikeyi duk saboda kinga Abeey ya tilasta min na aureki ne, amman ki bari na gama shirin da nake yi sai na yanke alaƙar da take tsakaninmu, idan yaso sai ki koma ƙauye ki cigaba da zama a gidan kara, dan nan ba gidanki ba ne, gidana ne kuma gidannan na ƴammata ne, tun kafin ki zo gidannan ƴammatana suke zuwa domin su ɗebe min kewa, dan haka ke baki isa kin hanasu zuwa ba, ina so ki saka a zuciyarki yanzu ma suka fara zuwa gidannan, kuma idan na sake jin sun ce sun zo kin hanasu shigowa ko kin koresu wallahi ranar babu me ƙwatarki sai Allah" Khadija tace "to yayi" tayi maganar tare da shigewa ɗakinta, tana saƙe-saƙe a cikin zuciyarta, shi kuwa Nazeer ganin yadda ta basa amsa yasa ya fara tunanin ko ta fara jin tsoronsa ne, (ni kuwa Dijarty nace anya kuwa Khadija zataji tsoronka Nazeer.) shima ɗakinsa ya shige yana rera waƙar turanci kamar ba shine ya gama ɗaure fuska ba.*** *** *** ***"Haba Usaina ba zaki cire wannan damuwar da kike fama ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.