chapter 8
by @zeety
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*_
_Barkan mu da sallah, da fatan kowa yayi sallah lafiya, karku manta naman sallah na, saura inji kunce yakare😋_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
8📚
Abbas da halamu dai kano yayi daɗi ko labarin zuwa kagan mu bakayi.. no mum babu wani daɗi fa, dama weekend ɗin nan nakeson shigowa abuja, Allah ya kawo ka saika zo, Amin ya ansa mata sannan sukayi sallama … gaskiya yanason zuwa abuja amma haka kawai wani ɓangare na zuciyar shi yakejin kamar kar yaje…
Kwance take a kan gadon ta daga ita sai bra da under wear tanata latsa wayanta… take wayar ta hau ruri… ganin number dake ƙiran ta shi yasa ta sakan wani murmushi, saida ya kusa tsinkewa sannan ta dɗauka, hello tace cikin dakewa… rabin raina yace daga ɗayan ɓangaren, lumshe idanunta tayi sannan tace watakila kayi kuskuren kirane don rabin ranka tana makofta… shshshh kidaina faɗan haka, ni hasib na farida ne ko kema kinsan banida kamar ki, ina da irinki mezanyi wata bakauyiya, dariyan fari ciki tayi sannan tace ai na ɗauka saboda ta fini shiyasa ka gujeni… ko kaɗan my sweet love, ko kama ƙafan ki ma batayi ba, take taji wani farin ciki na lulluɓeta mirginawa tayi tareda lumshe ido tana dariya… amma dai kinsan nayi missing ɗinki ko? Nayi missing komai a tattare dake, more especially ur sweet lips…., juyi tafarayi akan gado ko buɗe idon ta batayi, shiko sai kara zuzuta ta yakeyi da kazaman kalaman shi a sunan soyayya, suna gama wayan yabi wayan da kallo sannan ya sheqe da dariya yace shashasha, dake zanyi amfani wajen cimma buri na, kuma bayan haka kema sai na jiyar dake daɗin da baki taɓaji, sai na koya miki dainajin tsoron baban ki.
Yau Friday kuma yaune Abbas zaije abuja don haka yau ko office baije ba saida yagama shiri tsaf, yayi bankwana da uncle hanif da antin shi harya fito da motan shi sannan yakira mardiyya tace mishi tana school yace gashi nan zuwa, bayan ta buɗe motan ̂tashiga , tace yau bakaje aiki bane, eh… dama nazo muyi sallama ne zanje Abuja yau, haka kawai taji ranta baiyi daɗi ba, a hankali tace kuma sai yaushe zaka dawo? May b Sunday ya fada, rausayar da kanta kawai tayi tareda cewa Allah ya kaimu ka gaishe da mutanen gida, ɗagowa tayi ta kalle shi, murmushi ya sakar mata, sannan yace hope dai bamuda wani pending assignment, dariya tayi wanda ya bayyana fararen hakwaran da dimple dinta… sannan tace babu, idan ma ansa mu nasan zamuyi tareda ya Harun yace yana zuwa yau… ganin mood ɗinshi ya canja ne yasata cewa meyafaru? Baice komai ba face juyowan da yayi yace mata waye kuma ya harun? Murmushi tayi sannan tace mishi yayan zeezee ne, tun muna yara shi yake mana assignment yanzu ma haka yakoma kaduna da zama ne, zanso ku haɗu da ya harun don yanada kirki kamar ka… murmushi ya ɗan kakalo wanda bai wuce iya leɓen shi ba, yace oh really ni ɗin inada kirki ne, eh tace mishi tareda kaɗa kanta, tace sosai ma, harma ka kusa fin ya harun, saboda kai rana tsaka kasanni kuma kake kyauta ta min.. murmushi yake tayi batare da yace mata komai ba, agogon hannu shi ya duba sannan yace ni zan wuce saboda insamu in isa dawuri… Allah ya kiyaye hanya tace tareda sa hannu zata buɗe motan, MARDIYYA! Sunan ta ya kira da wani irin voice Wanda bata gane yanayin shi, juyowa tayi ba tareda tace komai ba, kafeta yayi da manyan idanun shi itama shiɗin take kallo, har zatayi magana sai ya rigata cewa shikenan Allah ya temaka.. murmushi ta mishi tareda fita a motan, amma sai ta kasa tafiya tsayawa tayi har saida ya juya ya ɓacewa ganini ta sannan ta sauke ajiyan zuciya ta koma.
Sosai farida da Hasib suka dawo da soyayyar su, anata tunanin ta ɗauka saboda ita ya rabu da mardiyya don haka yanzu zagewa takeyi wajen nuna mishi sabon soyayya harma ji take zata iya bashi kanta, shima gogan zagewa yakeyi wajen bata zafaffan soyayya wayanda zasu gigita ta wataran taji ita da kanta zata iya bashi kanta, amma kuma can kasar zuciyar shi baidaina saka abubuwan da yake shiryawa akan mardiyya ba, don yace wallahi tayi kaɗan tayi nasara akan shi.
Suna dawowa daga skul sukaga motan ya harun a kofar gida da halamu bai jima da zuwa ba, zeezee ce tafara cewa lah ya harun ya iso, hannu mardiyya tasa ta rufe bakinta sannan tace bari inyi sauri inje gida, yanzu zan dawo kinga zeezee ko girkin ma bamu mishi ba, a ah kinsan me za’ayi kizo mushiga tare ki mishi sannu da zuwa, kaɗa kanta tayi halamun a ah tareda cewa haba zeezee duk mun wani shawo ranan BUK muje kanshi da kaken fuskokin mu… yanzu zan watsa ruwa in fito, toh zeezee tace tareda buɗe motan tafita da yake dama motan gidan su mardiyya ne ya dauko su.
Ko da taje gida a gurguje ta watsa ruwa ko mai bata shafa ba saboda ana zafi, wata abaya ash me duwatsu tasa yawanci dama kayan mardiyya abayu ne kalakala da wuyama kaganta dawani kayan da ba abaya ba, don atamfa kam dakyar take sashi, shima yawanci dogin rigunane, bata cika sa riga da skirt ba, kuma ba komai bane yajawo hakan ba saidon kawai batason kayan dazasu na bayyana surarta tunda ba kullum takesa hijab ba. powder zikel ta ɗauko kalar fatanta ta shafa, lipgloss tasa a bakinta ɗan kaɗan don ko fitowa ma baiyi ba sannan ta fesa body spray tabishi oil arabian perfume ɗinta me suna Bushrah har zata fita ta tuno bata ko sha ruwa ba, fridge ta buɗe ta ɗauki wani yoghurt saida ta zauna akan kujera tayi bismillah tafara sha… wannan yana ɗaya daga cikin kyawawan dabi’un mardiyya, yawanci abubuwan ta tana binshi daidai yadda addini ta tanadar mana. Tana cikin sha antyn ta tashigo falon, cewa tayi ah ah su adda andawo ne, ya naganki da shirin fita? Saida ta sauke goran yoghurt ɗin sannan tace gidan su zeezee zanje, yaya harun yazo zanje in mishi sannu da zuwa, ahh lallai mutane kd ba, inkinje kice muma muna mishi sannu da zuwa, kuma tunda ya koma kd ya guje mu, rabon da da insa haruna a idona ya kusa shekara, nima anty saida na mishi wannan gorin, shikenan kidawo lafiya yauwa tace tareda fita.
Tana shiga gidan shi kaɗai ta hango a falo, faɗaɗa fara'arta tayi… ƙamshi turarenta ne yafara bugan hancin shi, lumshe ido yayi sannan yace yakira sunan turaren BUSHRAH, saboda soyayyar mardiyya da wannan turaren shima yasha saya mata shi, kuma duk inda yaji kamshin itace take faɗo mishi a rai, juyowa yayi yana murmushi tareda cewa can’t wait to see my sister, daina dariya tayi ta tura baki sannan ta zauna a ɗaya daga kujerun falon tace, gaskiya nayi fushi yaya… harda juya mishi baya ita nan a dole tayi fushi, kujeran gefen ta ya dawo sannan ya ciro wani abu acikin aljihun shi, ya ɓare a hankali ya kaishi gefen kunnen ta, kamshin chocolate ɗinne ya ya bugi hancin ta batasan lokacin da ta juyo tace lahh ya harun my favourite chocolate please give me, maidashi yayi bayan shi sannan yace I bought bunch of it amma saikin daina fushi dani zan baki… da sauri tace Allah nadaina mika mata yayi da sauri takarba tana cewa thank you ya harun…. Fara sha tayi kobi takan shi batayi ba shi binta yayi da kallo yana murmushi, zeezee da take bayan su tana kallon su ne tace umh umh wato ni shine ba a kawomin ba, zama tayi a gefen mardiyya, cewa yayi ai ita dinma ƙwace abuna zanyi don ko gaisuwa bamuyi ba tunda na bata ta manta dani a wajen… da sauri ta juyo tareda sa hannu ta rufe bakinta, sorry ya harun ina wuni, dariya yayi sannan yace nima nayi fushi da sauri tace please mana yaya a shagwabe tayi maganar, juyowa yayi yana murmushi yace aini ba ke bane bazan iya fushi da kanwata ba… wayanta daya fara ringing shiya katse maganan, zeezee ta kalla tace lahh kinga na manta ban kira ya Abbas naji ko ya isa ba… da hannu zeezee ta nuna mata ta ɗauka kar ya yanke, ɗauka tayi tareda sallama, lumshe idon shi yayi sannan ya buɗe ya ansa sallaman, sorry ya Abbas I didn’t call you, ya hanya, hope ka isa lafiya ? murmushi yayi sannan yace lafiya kalau na jima ma da isa, ya skul nasan kin koma gida by now, eh tace mishi tare da mikewa don taga wayan yana tsayi… binta da kallo ya harun yayi zeezee kuma ta bishi da kallo aranta tana cewa, ya Allah kaddai ya harun son mardiyya yakeyi… shi kam tunda tafara wayan zuciyar shi ke bugawa, a hankali yace Allah yasa abunda nake tsoro bai faru ba, me kace yaya, dan firgigit yayi don baiyi tunanin a fili ya faɗa ba… a ah bance komai ba, lokacin mardiyya ta dawo mikewa yayi tareda cewa naji ana kiran sallah bari naje massalaci, saika dawo suka ce mishi, yana fita mardiyya tace zeezee ya maganan girkin naga dare yayi, ko zamu bari gobe so that duk abunda babu ma sai mu aika, umhmm hakan ma za’ayi yanzu dai muma muje muyi sallah, ɗakin zeezee suka wuce bayan sun idar da sallah, hannu bibbiyu zeezee tasa a haɓar ta tareda zurawa mardiyya ido, tana shafa addu’a hararan zeezee tayi don tasan ba wuce wani haukan take tunawa ba, bakin gado ta zauna tana linke hijab ɗin da tayi sallah, meye nifa kinsan banso yawan kallo, murmushi zeezee tayi sannan tadawo gefen ta tana cewa mardiyya ta ya harun da ya Abbas…
cikin hanzari mardiyya tace for God sake a ina kika taɓajin mace ta auri maza biyu kuma duka wannan fitinan naki kaf cikin su fa babu wanda yace yanasona kuma ma bansan lokacin da kikayi including ya harun a haukan ki ba…
hmm ke ai bazaki gane ba amma ni nasan me nagano, da kike cewa dukan su babu wanda yace yana sonki kijira nan bada daɗewa ba dukan su zasu bayyana miki sirrin zuciyar su, kuma na tabbata hakan ba karamin ruɗu zai saki ba… tohh yaushe kika fara aikin bokaye ban sani ba, har kina faɗan me zai faru… umh umh ko kaɗan ba wai ina nufin abunda zai faru bane hasashe nane kawai…
look kefa zeezee a rayuwar ki saurayi ɗaya kika rike bayan mujaheed bakya kula kowa amma ni saikiyita min labarin maza dayawa, hmm…
mardiyya nifa dakike gani kinfi kowa sanin hidiman tara samari baya gabana, narike mujaheed saboda inji a raina ina da saurayi so that bazan baiwa kowa chance ba, ke shedace akan yadda maza suke da negative thoughts akaina, don kawai sunga inason gaye dayawa sai kowa yayi tunanin kasan bariki, basuda burin da ya wuce lalata en mata, ni kuma I didn’t choose that in my life inason gaye kuma inayi badon in jawo hankali maza ba sai don ni dakaina inji daɗi nayi abunda nakeso, amma fa wai karkiyi tunanin nayiwa mujaheed riƙon da yau idan yace bayaso na ba, zaku kaini asibiti ko kaɗan I know how men are, zai iya canja ra’ayin shi ko yaushe a kaina balle ma irin yanzu da yake abuja zai iya ganin kowace irin classy mace, idan hakan ta faru I’ll just say Allah yasa hakan shine mafi alkhairi and move on, but mardiyya inason baki shawara please cikin ya harun da Abbas idan sukace suna son ki, don’t think about anybody just think about yourself, ki zaɓi duk wanda ya miki acikin su I’ll support you hundred percent, karki fara tunanin a'ah ke kar kice no to ya harun but kar yazamo banji daɗi ba ko kuma u love Abbas u ar afraid of farida bakisan me zai faru ba... kimanta da kowa da komai kiyi abunda ya dace a rayuwar ki idan dukan su bakya son su, fine kinada kyau da jinin dazaki samu samari, you are beautiful enough… kanta mardiyya ta rike tace hoooh, na shiga uku kinfara magana kamar radio ko breathing space babu nidai ya isheni haka.. duk kyanki ke baki tara samari ba amma ni in tara sannu zeezee da halamu bakya ganin kanki a madubi… nidai yanzu zan tafi gida don dare yafarayi, suna mikewa sukaga ya harun a bayan su ya jingunu da kofa ya nade hannu shi, baki suka haɗa wajen cewa yaushe kazo… yanzu yace musu sannan yace kuzo in baku tsaraban ku kafun ki wuce gida, binshi sukayi falo, ledoji manya manya guda biyu ya kawo musu mikawa mardiyya daya yayi zeezee ma yabata dayan tare suka rakata har cikin gida sannan suka koma , ko da ta shiga zazzage kayan ledan tayi akan gado, rabin kayan duka chocolate ne, sai perfume guda hudu da abaya guda biyar…. Waresu tayi tanagani daga ganin yanayi kyansu tace lallai ya harun ya kashe kuɗi anan.. cirewa antynta turare tayi kannen ta kuma kowa chocolate me yawa ta ware musu, kayan baccinta tasa, taje tayiyo alwalan kwanciya, amma sam bacci ya kasa ɗaukanta maganganun zeezee ne suketa dawo mata, karan shigowar sako taji a wayan ta, hannu ta ta mika ta ɗauko shi akan bedside drawer ta, tana buɗe message ɗin taga wani abu kamar haka
_salam da fatan kin shiga gida lafiya? Idan kinada lokaci gobe inason mu haɗu domin akwai wata muhimmiyar maganan da zamuyi_ _Good night_ _ya harun_ .
Ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta mishi Reply da
_Allah ya kaimu_
hannu ta mika takashe wutan ɗakin.
Tunda ta koma taketa fakon ko zataji motsin shi amma shuru, saida tayi isha sannan ta fito falo, mamata gani ita kaɗai, mama yau kamar ya Abbas baya gidan nan? eh ya tafi abuja ai tunda hantsi, duk da bawani kulata yakeyi ba, amma haka kawai sai taji ba daɗi… wayan maman ta ɗauka, ta duba number shi ta ɗauka sannan ta koma ɗakin ta, kiran shi tayi batare dajin komai aranta ba, yana fara ringing ya ɗauka, hello tace daga ɗayan ɓangaren, yanaji yagane muryan ta, amma sai yace wake magana please ? ajiyar zuciya tayi sannan tace Farida ce, ya Abbas shine tafiya ba sallama? Suman kanshi ya shafa sannan yace ai baɗewa zanyi ba, Sunday zandawo inshaa Allah.
amma ai duk da haka zamuyi missing ɗinka, shikenan Allah ya kaimu, Amin yace sannan yakara dacewa ki gaishemin da mama , toh zataji ta ansa, good night yace mata tareda kashe wayan… rufe idonta tayi tareda ɗaura wayan akan kirjin ta, jitayi kamar karsu daina wayan… a fili tace nasan yadda nake jinka a zuciyata kaima dole kaji wani abu a tareda ni, bazan taɓa bari mardiyya tayi nasaran ƙwace zuciyar ka ba.
*ZEETY DELIGHT*💖