E5
*🧚🏻♀️SHU’UMA🧚🏻♀️*
_’yar mutan zazzau Naanarh M Sha’aban_
*Sadaukarwa ga Yaayanah🤩💔*
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION💫*
*Book 1*
E5
‘’Wallahi Abba karku dakatar da ni yarinyar nan yau sai na tattakata, sai na ci ubanta,ni zata mayar mahaukaci, sai na ji mata ciwo idan har na rik’eta’’ Ya yi maganar tare da mik’e ya nufi Khadija gadan-gadan, Abba yay saurin rik’eshi, dan kuwa gabad’aya shi ya gama yarda aljanu Nazeer d’in ya tayar ganin yadda yake magana yana huci, ga shi jikinsa duk yayi ja, saboda susa,abinka da farar fata, addu’o’i ya shiga karanta masa yana tofa masa.
“Abban yara ya kamata mu kai shi gurin Malam Ado ya yi masa ruk’iyya fa, kalli yadda yarona ya koma lokaci d’aya” Mummy ta fad’a cikin damuwa. Nazeer ya d’ago yana kallo Mummy cike da bak’in ciki “Mummy yanzu kina tunanin aljanu ne suke damuna, Ina so ki sani ni ba ni da wani aljanu, duk wannan shaid’ancin wannan yarinyar ne, Abba sai da nace maka daman yarinyar nan bata da hali ku barni na auri Fanan, saboda ita ce zab’i ku ka k’i” Khadijah ta rushe da kuka tare da cewa “Haba Yaya Nazeer ya ji tsoron Allah, d’azun nan fa muka gama hira da kai lafiya, lafiya yanzu kuma nice abin tozartawa har ka na zagina, ko da yake ba laifinka ba ne, zan maka uzuri saboda yanayin da ka ke ciki” Nazeer cikin fusata yace “da uban wa kika yi hirar, Abba nace dan Allah ka barni na koya mata hankali, ka cika ni na ci ubanta”
Abba ya ce “muje waje, baka dad’e da fardad’owa ba” Sannan ya kalli Mummy ya ce “bari mu fita, kin san sha’anin aljanu, zan kai shi gurin Malam Ado yayi masa ruk’iyya sannan mu dawo” Mummy tace “To Abban yara ka kula da Nazeer d’in sosai dan Allah” Abba yace “insha Allah” sannan ya ja Nazeer suka fita, Mummy ta kama Khadija suka zauna akan kujera tana rarrashinta har tayi shuru.
“Mummy ban san meyasa aljanu suka shiga Yaaya Nazeer ba, da ana ganinsu da na rok’esu alfarmar su rabu dashi, bai kamata su shigeshi ba yana da kirki sosai” Mummy ta rumgumeta tana bubbuga bayanta “ki kwantar da hankalinki, zai samu lafiya kinji” Khadeeja ta lafe a jikin Mummy tana jin dad’i dan ta san ta gama samun nasara ko da Nazeer zai kwana yana ce musu karara ta zuba masa ba za su tab’a yarda ba, idan kuma har ya furta musu zata ce ya kawo shaida, Kuma ta san ba zai tab’a yarda ya kira su Khausar akan su zama shaidarsa ba ko yace har da su ta zubawa karara, dan kuwa Abba zai tambayesa meya had’asa da ‘yammata da har suka shiga d’aki nan ma tasan wani babban bala’in ya janyowa kansa dan Abba zai iya yin fushi mai tsanani dashi idan har yasan bai daina neman matan banza ba.
••• ••• •••
Kwance take akan gadon asibiti an saka mata abin yin numfashi a hanci, yau kwananta hud’u kenan tun ranar da aka kai ta asibitin ta farka waje gari wajen bakwai na safe, tana wani irin numfashi dak’yar sai da kusan likitoci sun kai biyar suka zagayeta. Suka samu akayi mata wata allurar bacci mai k’arfi bata sake farkawa ba, hankalin Hassana ya tashi gaba d’aya da ba dan numfashin da take ji Usaina tana yi ba, da tuni ta saka kukan mutuwarta, kwata-kwata bata iya bacci, kullum cikin addu’a take Allah ya tashi kafad’un masoyiyarta abar k’aunarta Usainanta, ta rame sosai.
Wayarta ta d’auka ta shiga kiran lambar Commissioner ‘yan sojoji na gaba d’aya Nigeria, har ta kusan katsewa ya d’auka cikin sanyayayyiyar muryarsa yayi Sallama “Assalamu alaykum” Hassana cikin dasasshiyar muryarta da ta sha kuka ta amsa masa sallamar “Amin wa’alaykumussalam yallabai an wuni lafiya” Commissioner ya amsa da “Alhamdulillah” Hassana tace “madallah na san baka gane wacece ba, ni ce wacce Commissioner ‘yan sanda yayi maka magana akan zaka taimaka mana akan d’an gidan Alhaji Sule akan yunk’urin kashe min ‘yar uwa da ya yi, dan Allah ka taimaka mana, yau kusan kwana hud’u Usainata bata farka ba, na rok’eka, ko nawa ka ke so zan ba ka indai za ka sa a kulle Habu” wani lallausan murmushi ya yi kafin ya yi gyaran murya yace.............✍🏽
*#Share*
*#Comments*
*#Book 1*
*’Yar mutan zazzau (Dijartyluv🥰)*