E6
*🧚🏻♀️SHU’UMA🧚🏻♀️*
_’yar mutan zazzau Naanarh M Sha’aban_
*NA SADAUKAR DA LITTAFIN NAN GA YAAYANAH, ALLAH UBANGIJI YA BIYA MAKA BUK’ATUNKA*
ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
_Ku sauke Arewabooks dan a chan zamu koma posting d’in Book 2 idan na gama Book 1, duk wanda ya sauke yayi following d’ina._
arewabooks.com/u/shaabandaughter01
Book 1
E6
“Kwantar da hankalinki yarinya, zan tabbatar Habu an koya masa hankali, insha Allah ba zan tab’a barin abinda yayi miki ya tafi a banza ba” duk da irin yadda Hassana take cikin tashin hankali da damuwa, amman jin abin da Commissioner ya fad’a bata san lokacin da murmushi mai had’e da dariya ya kwace mata ba.
“Alhamdulillah nagode sosai yallabai Allah ubangiji ya biya maka buk’atunka ya raya zuri’a, nagode! nagode!! nagode!!! Ni Hassana na rasa wace iriyar godiya ma zan maka” Commissioner ya ce “bakomai ai yi wa kai ne, kika ce ‘yar uwar ta ki tana asibiti ko?” Hassana tace “eh wallahi kusan kwana nan mu uku bata farfado ba, ita da ‘yarta ne amman ita ta farfado tun a ranar, amman ya ji mata rauni sosai, bata iya magana saboda bakinta da ya kumburar, abinci ma bata iya ci ko ruwa sai da dabara take karb’a” Commissioner ya jinjina kai duk da bai gansu ba, amman ya ji yana jin tsananin tausayinsu, yasan ahalin Alhaji Sule kwarai ba su da mutunci, ga mugunta da mugun hali, ba su da daraja mutane kwata-kwata, “Allah ya ba su lafiya zuwa gobe zan zo na ga yanayin jikinsu sannan zamu fara gudanar da aikinmu, ki saka ranki a inuwa zan tabbatar na karb’ar muku ‘yancinku” Hassana tace “Nagode sosai” Commissioner yace “bakomai Sai anjima” kafin tace wani abu ya kashe wayar, farin cikin da take ciki yau ya huce misali burinta zai cika za’a kama Habu ji take kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha, kukan Ilham da ta ji ne yasa ta tashi ta koma gadon da take kwance tana murmushi, da yake duk a d’aki d’aya aka kwantar da su zama tayi kusa da ita tana rarrashinta har ta samu tayi shuru.
••• ••• •••
“Yaayah ya kamata ka d’auki mataki akan wad’annan ‘yan biyun, k’ila ma yanzu yawonsu suka tafi yi wai nan da sunan matar aure ce, ko da yake daman sun saba, aure-aure bai yi ba wallahi, gashi kai a garin aure ka auro ‘yar bariki, ni tsorona ma d’aya ka da ta je ta d’ebo wannan cutar mai karya garkuwar jiki HIV” Habu wanda ya gama cika yace “Asabe kin yi gaskiya sosai, nima kai na nasan yawace-yawacensu suka tafi, tunda iyayensu sun nuna basu San inda suke ba, na san da sun san inda suke da irin barazanar da nayi musu sun fad’a min” Asabe tace “au iyayennasu ma ba su san inda suke ba, lallai sun shahara, to gaskiya Yaayah ka zab’a ko ni ko ita, dan ba zai yi na zauna da kai, ka na tare da ita, ta d’ebo lalura ta yab’a maka, nima ka yab’a min ban ji ba, ban gani ba” Habu ya kalleta sosai sannan ya sauke ajiyar zuciya yana cewa “Asabe ba zan tab’a iya sakin yarinyar nan ba, dan mun yi yarjejeniya a k’auyensu, kin san yare ne, zan iya samun matsala duk lokacin da nace zan rabu da ita” Asabe ta fashe da kuka tare da cewa “shikenan sun gama da kai, sun shanyeka” tayi maganar tare da mik’ewa ta shige d’akinta ta rufe, Habu ya bi ta da kallo, har ta shige d’akin, mik’ewa yayi ya fita waje zuciyarsa na wani irin suya kamar ta fashe.
**** **** ****
A b’agaren Nazeer kuwa suna isa gidan Malam Ado, driver ya fito ya bud’e musu k’ofa suka fito Abba yana rik’e da Nazeer, suka shiga gidan, a farfajiyar gidan suka sameshi, yana zaune yana jan carbi, yana ganinsu ya mik’e ya nufosu yana tambayar Abba lafiya kuwa? Taimaka masa yayi suka zaunar da Nazeer d’in akan dadduma sannan Abba ya kalli Malam Ado yace “Malam Ado wallahi Aljanu ne suka shafeshi, ba ka ga abinda yayi ta yi ba” Nazeer cikin muryar kuka yace “Abba wai meyasa kafi yarda da maganar yarinyar nan akan ta wa, wallahi na rantse maka, ni ba ni da aljanu karya take, abin k’aik’ayi ta saka mana ni da su” shuru yayi dan ya san idan ya fad’awa Abba cewar shi da su Khausar aka sakawa karara ya shiga uku, Abba yace “k’arasa mana kai da su wa?” Nazeer yace “ni kad’ai, ya kamata ace ka yarda ni ban da aljanu, wai meyasa ba za ka yarda ba ne Abba” Malam Ado yace “Sharrin aljanu yawa garesu ai, a haka za ka yi tunanin ba ka da komai, dan idan sun tashi ba sani za ka yi ba, za ka ga kamar bacci ka yi ka farka” Nazeer ya juyo yana kallon Malam Ado yace “au kai ma kallon me aljanu ka ke yi min Malam? Allah ya isa tsakanina da ke Khadija wallahi sai na rama, ba zan kyaleki ba, wallahi sai na kasheta kowa ma ya huta” ya yi maganar yana k’ok’arin mik’ewa, Malam Ado ya rik’o masa hannu, “ka sakeni! Ka sakeni Malam idan ba haka ba zan had’a da kai, zan fara ta kanka, ba ruwanka, ba ruwanka nace, karka saka kanka a ciki, ka cika min hannuna” Malam Ado yace..................✍🏽
Anan zan dasa aya🥰❤️
_Kun ji ni shuru yau, ban da chaji sai yanxu na samu na yi muku, da fatan zaku gafarceni😩_
*#Share pls😥🙏Dan Allah ku dinga share d’insa*