E7
*🧚🏻♀️SHU’UMA🧚🏻♀️*
_’Yar mutan zazzau Naanarh M Sha’aban_
*Sadaukarwa ga Yaayana mai daraja*
_Ku dinga comments, ba na son sticker, idan kuma ba haka ba 🙄😥_
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
Ku sake Arewabooks dan a chan zamu koma posting d’in Book 2 idan na gama Book 1, duk wanda ya sauke yayi following d’ina.
arewabooks.com/u/shaabandaughter01
Book 1
E7
“Tohm naji Babana zan sakeka, amman dawo ka zauna zamuyi magana da kai” Nazeer ya kallesa kamar zai yi magana sai kuma ya dawo ya zauna yana sauke ajiyar zuciya “Malam wallahi ba zan kyaleta ba, sai na k’aryata, sai na illata ta, ni bani da wani aljanu sharrinta ne, su kuma su Abba suka yarda da maganarta, makira ce wallahi shaid’aniya” Malam Ado yace “to na ji nima na yarda ba aljanun ba ne” Nazeer yayi murmushin jin dad’i yace “yauwa Malam Ado shiyasa na yarda muka zo dan na san zaka fahimceni sosai” Malam Ado yace “sosai ma kuwa” wani ruwan addu’a ya d’auko yace “sha wannan yadda zamu ji dad’in yi mata rashin mutunci” Nazeer ya karb’a ya shanye, wani irin jiri ya ji yana d’ibarsa bayan ya gama shanyewa “wayyo kai na” Malam Ado yace “sannu kwanta ka huta” Nazeer ya zame ya kwanta, Malam Ado ya kalli Abba yace “Alhaji kasan sharrin Aljanu yawa garesu, akwai buk’atar ya kwanta ya huta, amman yana farkawa zai dawo daidai” Abba yace “Alhamdulillah nagode sosai Malam” Malam yace "bakomai Amman ya kamata ku duba sosai, ku saka ido a tsakaninsa da matarsa, dan zai iya yiyuwa akwai abubuwan da take yi Masa, kasan mata sun fi shaid'an iya shaid'anci, tunda ku ka ji yana kuka da ita, to yana fuskantar matsaloli daga wajenta" Abba ya girgiza kai tare da cewa "Malam ban tari numfashinka ba, Amman Khadija mutuniyar kirki ce, tana da tarbiyya sosai kuma tana girmamashi matuk'a, shiyasa ba na tunanin zata iya sakashi cikin damuwa, shine dai tun farko baya son auren kasan dai irin tak'addamar da muka Sha dashi sai da nayi da gaske sannan ya amince" Malam Ado yace "hakane Kuma zai iya yiyuwa aljanun ne suke tusa masa tsanarta a zuciyarsa, tunda ka ga har aure suke hanawa" Abba yace "hakane kam" Malam Ado yace "insha Allahu zamu dage da addu'o'i sosai zai samu lafiya zasu barshi" Abba yace "to bari na kira driver ya taimaka min mu d'aukeshi ku sakashi a mota mu tafi gida ya farka chan dan hankalin matarsa da na mahaifiyarsa ya kwanta, dan gabad'ayansu hankalinsu a tashe muka fito" Malam Ado yace "badamuwa bari na ba ka wasu magunguna idan ya farfa a shafe masa jikinsa da su" Abba yace "to" wayarsa ya zaro daga aljihu ya shiga kiran Muhammadu driver yana d'agawa yace masa ya shigo, ko ajiye wayar bai yi ba sai gashi ya shigo, Malam Ado ya basu magunguna a wata bak'ar leda, Muhammadu ya taimakawa Abba suka d'aga Nazeer suka fita dashi daga gidan Malam Ado a mota suka sakashi, Abba ya juyo ya kalli Malam Ado wanda ya rakosu har bakin mota yace "nagode sosai Malam, Allah ya saka da alkhairi" Malam Ado yace "bakomai wallahi ai yi wa kai ne" Abba ya shiga mota Muhammadu ya ja suka nufi gida.
∆∆∆∆
Kamar yadda commissioner yayi alk'awari washegari da safe wajen sha d'aya sai gashi ya zo asibitin da yake ba wani b'oyayyan asibiti ba ne, da kwatance ya k'arasa d'akin bakinsa d'auke da sallama ya shiga d'akin
"Assalamu alaikum" gado biyu a d'akin "Wa'alaikassalam" Hassana ta amsa sallamar tare da d'aga ido tana dubansa, tayi mamaki ganin matashin saurayi kyakyawa mai jini a jika a matsayin commissioner dan ita har ga Allah tayi tunanin babban mutum ne” k’arasawa inda Ilham take kwance yayi yana kallonta idonta biyu ta k’ura masa ido tana kallonsa, abin da ya bashi mamaki jin yarinyar yayi tace “kai ne Babana?” Duk da yadda take jin azaba idan tayi magana sai da ta ji tana son tambayarsa, dan ita ma tana son ta ga Babanta dan su Ikilima su daina yi mata gorin bata da baba kuma Habu ya daina dukanta ita da Mummynta, Hassana cike da tausayi tace “ba shi ne Babanki ba Ilham, Babanki yayi.....” maganar commissioner ne ya katseta daga maganar da take son yi “eh mana ‘yar babyna, kina sona ai ko?” Da sauri ta gyad’a kai tana murmushin jin dad’i “daga yanzu za ka dinga rama mana dukkan da Babansu Ikilima yake mana ni da Mummy ko? Kuma za ka dinga kai ni makaranta kullum ka na siya min abin dad’i” Commissioner yace “eh zan yi miki duk abinda kike so habibiyar zuciyata, amman fad’a min wani abu mana waye yayi miki duka ke da Mummynki?” Ilham tace “Babansu Ikilima ne” Commissioner yace “To meyasa ya dukeku? Wani abu ku ka yi masa” girgiza kai tayi tace “ba abinda mu ka yi masa, sai da nace wa Baba Asabe Mummyna tana ciwon ciki” nan ta kwashe duk yadda akayi ta fad’a masa tana kuka.
“Yi shuru mana jarumar yarinyata” yayi maganar yana share mata hawaye, juyawa yayi ya kalli Usaina da take kwace kamar gawa sannan ya komar da dubansa kan Hassana wacce ta sunkuyar da kanta tana share hawaye, “ki daina kuka insha Allah yau zamuje har gida mu kamo Habu da Matarsa dan su fara fuskantar hukunci” mik’ewa yayi yana kallon Ilham yace “anjima zan dawo gurinki kinji ‘yar yanzu zanje na rama miki abinda Babansu Ikilima yayi muku” tafi ta shiga yi tana dariya.
Sumbatarta yayi a goshi sannan ya nufi hanyar fita daga d’aki da ya kai k’ofar d’aki ya juyo yana kallon Ilham wacce sai d’aga masa hannu take tana dariya “ka dawo da wuri Babana” yace “tohm Insha Allah” haka ya fita daga d’akin ya ji zuciyarsa gabad’aya ba dad’i ji yake kamar ya zauna da yarinyar dan tun kallon da yayi mata na farko ya ji ta shiga ransa, da yake yana bala’in son yara, amman shi Allah bai ba shi haihuwa ba, shiyasa duk yaron da ya gani ji yake kamar ya rik’eshi ya dawo na sa.
Wayarsa ya ciro ya kira Captain Sani yace “ya ta ho da motoci guda biyar su sameshi a kan titin asibitin Waqas, yana gama fad’a masa ya kashe wayar, inda yayi parking d’in motarsa ya nufa yana zuwa ya bud’e ya shiga ya ja motar ya fita daga asibitin daga chan nesa ya hango motocin sojoji sunyi parking suna jiran k’arasowarsa da yake daga asibitin zuwa barikin sojoji ba nisa, yana zuwa, da yake ya fad’a musu inda zasuje suka ja mota suka nufi gidan Habu.
*#Share*
*Comments*
*’Yar mutan zazzau ce🥰💃🏻*