DUK TSANANI 4
[5/11, 12:36 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI
[Yana tare da sauk'i]
BY Mmn AMATULLAH
Paid book 200
Free page
Phone Number ***.
Chapter {10}
Agurguje ya yi wanka ya shirya tsaf,,,,
Inna da baba yayiwa sallama "To Allah ya tsare yasa kafita a sa'a" "amen" ya amsa tare da jan,Kurar rakensa ya fice, daga gidan,,zuciyarsa fal da tinanin Nasreen,,,cikin ikon Allah yau da kafar dama,ya fito,,tin da ya fito daga gida yake ta ciniki,ganin beyi wani nisa da gidaba,yasa ya koma Dan ya D'an barmusu wani,Abu tin da yasan ko sisi babu a cikin gidan,,,da sallama ya shiga gidan,,su Inna suna zau ne in da yabarsu "Aa nasuru lafiya kuwa naga kadawo tin bakayi nisah ba" cewar Inna,, "Wallahi Inna lafia kalau, dama ciniki na samu,,to shi ne,da naga banyi nisaba shi ne nace bari na dawo sai na barmuku,D'an wani Abu asamu a Dan sarrafa,ko da zanyi dare nasan ban barku da yinwa ba",,D'ari uku ya Ciro ya mik'awa,, Inna,, "Angode Allah ya k'ara Budi Nasuru kaima Allah ya baka masuyi maka" "Ameen Inna" baba ne, yace,"maza tashi kaje,Allah,ya yi maka Albarka",,"Ameen baba"...
•••••••••
Yau tabbas ya yar da a sa'a ya fito,,Dan ba Dan yanaso ya koma unguwar nan ko zai sake tozali da wannan kyakkyawar fuskarba,,da babu abin da zai kaisa,unguwar,sabi da ko yan zu,ya kusa siyarwa,,,haka ya tare Dan mashin ya kuma sanar da shi inda zai kaisa ko da ya sauka ya biya Dan mashin,shikuma ya dirfafi layin, yana tafiya yana addu'ar Allah ys,,, yada ce,da samun ganinta,,,,Dan gaban gidan da yaga ta shiga jiya nan ya samu ya tsaya ajikin wata,bishiya Dan yafi kyautata zaton nanne gidansu,,tsaye yake yana kallon masu shige da fice,,, Amma ko alamar ganin ta beyiba,,,wasa_wasa har anyi azahar,,yaje ya dawo,,amma babu ita babu dalilinta,,,ji ya yi zuciyarsa ta fara bugawa da sauri da sauri,,,,addu"a yafarayi,,,Allah dai yasa lafiya,,,, cin ikon Allah rakensa ya kare tas, yana tsaye agurin sai daifa babu alamun zai ganta,,gashi,har magariba ta kawo kai....
Haka dole ya hak'ura ya ja Kurar sa ya tafi,gida duk jikinsa a sanyaye,,,haka ya koma gida duk jiki babu kwari, Inna naganinsa haka ta tambayesa ko lpia sai cemata ya yi lpia k'alau,,, kawai gajiya ce,,,,,wanka yayi ya wuce,, masallaci ko da ya dawo bayan isha,,,abinci yadanci sama_sama yau ko fira be zauna ba,,,ya yi musu sai da safe,yawuce dakinsa,,,,babane ya dubi Inna yace ''Anyakuwa yaronan babu abin da ke damunsa kuwa",,"Ashe kaima ka kula malam aini tin da yadawo n kula Amman da na tambayesa sai yacemin babu komai,,gajiya ce,,, Amman gadikkan alamu yana cikin damuwa","To ai shikenan,,tin d be fad'a ba INA tinanin bayaso musani,,mabisa da addu'a" inna ta hamsa da ,"haka ne,, malam"
••••••••••••••
Wasa_wasa yau sati guda kenan kullum sai yaje,layin su Nasreen Amman,, ko inuwarta,betab'a ganiba,,,yan zu har ta kai ya dena zagayawa,da rake,sai dai yazo ya zauna,,,,a gindin bishiyarnan,,,,yana hangen gidansu ko zaiga giftawarta Amma ko sau d'aya be gani ba,,,,,gaba d'aya zuciyarsa ta gama tsinkewa,da lamarin gakuma wani irin sonta da ke nunkuwa,a kullum a cikin zuciyarsa....
Yauma kamar kullum haka ya gaji da zama,har zawa dosowar magrib,, Amman babu ita babu dalilinta,,,in Dan cinik ine Alhmdllh yanasamu sosai a gurin,so sai sai dai,rashin nasarar ganinta da kumah Sanin awanne hali take ciki,sune suke daga masa hankali,,,sosai,,, jiki,asanyaye ya ke tura kurarsa Dan zuwa titi abin hawa ya tare,ya hau ya fad'amasa in da zai saukesa,,,yauma kamar kullum,haka yashiga gida babu kuzari,,,su inna yanzu har sun Saba da ganunsa a haka,kuma babu irin tambayar da bisiyi masaba ,sai dai kullum yace,babu komai,,,,.......
••••••••
Kamar kullum,,bayan ya gama duk wani Abu da yasaba,kafin kwanciya bacci,,,kwanciya ya yi,ba wai Dan ya yi bacciba,,Aa sai Dan yabawa zuciyarsa daman tinanin abar kaunarsa,,,haka kuwa,akayi idaninsa ya rufe,yana ganin kamanninta,tare da jin sautin zazzak'ar muryarta,,tana cewa,malam,rake nakeso,,,,bai San lokacin da wani,,kayataccen murmishi ya sauka a kan kyakkyawar fuskarsah ba,wan da yakara fito da ainishin kyawun fuskarsa,,,
•••••••••
Yajima yana kwance yana tinanin,,ta ,kafin ya tashi ya fita ya d'auro alwala yana dawowa ya tayar da nafila ya fara kaiwa Allah kukansa,,,ba shi y samu bacci ba,sai gefin asuba...
•••••••••••
Tin ranar da Nasreen ta sai rake a gurin,Nasrenllah,cikin dare ta kamu da zazzabi mai zafi wan da ya kwantar da ita har tsayin wa"yannan kwanaki,Dan ko gurin aiki bata zuwa,,shiyasa,,Nasrenllah bayaganin shigarta ko fitarta,, Amma Alhmdllh,,zuwa yanzu,,,taji sauki sosai,,Dan gobe take saran komawa bakin aikinta,...
Sakamakon rashin baccin da beyiba da wuri,,shine ya haddasa masa makara,a gaggau ce,ya shirya,karyawa ma a gurguje,,ya yi ,Dan yanaso yaje sarin rake,kafin ya k'arasa unguwar su Nasreen,,,,ko da yakaraso,,tini Nasreen tawuce gurin aikinta,,,haka ya zauna yana sai da rakensa Amman idonsa,yana kan kofar gidansu,,,,,,sai wani Dan matashin saurayi da yake d'an zuwa,yana tayasa fira,,yan zu har sun Fara sabawa,....
•••••••••••
Misalin,,karfe, 6 saura,,yaga D'an a dai-daita sahu ya yi parking a dai_dai kofar gidan,,addu'a yafarayi a zuciyarsa Allah yasa ita ce aciki,,,bai gama addu'a ba yaga ta fito,, wata ajiyar zuciya ya sauke, me karfi,,tare da fad'in Alhmdllh,,,wani lallausan murmushi ya sauke a kan fuskarsa,,wan da rabonsa da shi y kai sati,,,fuskarta ya zubawa,ido sosai,yake kallonta yan da take komai cike da nutsuwa,,mai keke,ta sallama,,, sannan ta juya ta shige gida,,sai da tashige sannan ya dawo cikin tinanin sa....
•••••••••••
Hmmm nisawa yayi tare da cewa,, "wai nikam sani na tambayeka mana" "To INA saurarinka",,,"Wai Dan Allah wannan yarinyar da tashiga gidannan yan zu,,nanne gidansu? "wa wai kana nufin Nasreen?wunanta kenan,? Nasenllah y tambaya,,tare da mai_maita sunan,a Kasan zuciyarsa,,,,"Eh sunanta,kenan",inji sani,,sannan yacigaba da cewa,,"nanne gidansu,,,Nasreen yarinyace mai nutsuwa da hankali,,,sai dai wasu abubuwa da suka dinga faruwa da ita marasa, dad'i",cike dason yaji mewannan abin Nasrenllah yace,,"me y faru da ita marar Dad'i'?...
Nan sani y kwashe komai ya fad'a masa,sosai Nasrenllah ya tausaya mata,sai dai tawani gefen yaji dad'in faruwar haka,,,Dan yaji ajikinsa ita d'in rabonsa Ce....
Ummu Amsad😘
[5/11, 12:41 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI
[Yana tare da sauk'i]
BY Mmn AMATULLAH
Paid book 200
Phone Number ***.
Chapter{11}
Yau jiyake gaba d'aya farin ciki ya mamaye masa zuciyarsa Sani ne ya tab'asa tare da cewa,, "Wai tinanin me kakeyi tin d'azu inata magana babu amsa,, murmushi ya yi tare da cewa,, 'Babu komai kawai dai INA tausayawa rayuwar tane" "lallai kuwa,ai abin da tausayi sosai" cewar Sani.
"To yan zu tana da wani da ke zuwa ne? ko kuwa",Nasreen ya tambaya "Aa gaskiya a iya sanina babu wan da yake zuwa,a yan zu sai sai dai ko nan gaba,towaima me yasa kake ta yimin wa 'yan nan tambayoyin?, "Babu komai kawai dai, natambaya ne"
••••••••••
Yau cike da farin ciki ya koma gida kai da kakalli fuskarsa,,zaka san yana cikin farin ciki,, Inna naganinsa tace "Aa Nasuru yau da alama kataka wani kulli ko?,dariya ya yi,tare da cewa,, "Haba Inna,wanne irin kulli kuma,,kawai dai najini cikin farin ciki,ne yau d'in nan,","To ai shikenan intayi tsami ai maji", dariya ya yi tare da cewa,, "Wai Inna ina baba ne? "Babanka ya yi wata 'yar tafiya,,shi da abokinsa,,malm Sale" "To Allah ya dawo dasu Lafiya" Inna ta amsa da Ameen....
••••••••••••
Yau ma kamar kullum kwan ce ya ke yana tinanin abar k'aunarsa,,yana murmushi,,,,dan jin zuciyarsa yakeyi Fe's,,, *NASREEN NASRENLLAH*, kai gaskiya bakaramin da cewa,,sunnannan yayi ba,,kamar yan da zamu da ce,da juna,marmushi ya sakeyi,wata zuciya ce ta ce masa,,kai kana tinanin,zatasoka ne,,kokaman ce,kai waye,kaifa talaka ne,,baka da komai,baka ajiyeba haka bakabawa wani ajiya ba,sannan ko ka manta da cewa "yan matan yan zu basason talaka,,sunfison,,mai kud'i,,ko dan kaga,kai kyakkyawa ne?,To yan zu " yan mata sundena kallon kyawunka,,sai dai mekatara ko me kake da shi,,,sannan ko kamance,ko a bangaran karatu ta fika,ita degree ne da ita kaifa,secondary school ne fa kawai da kai,kaga kuwa,ya zaka had'a kanka, da ita,,ai sai nake ganin kamar kayi d'age..
•••••••••••
Jiyayi gaba d'aya jikinsa ya yi sanyi,,gawata harbawa,da zuciyarsa takeyi da sauri da,sauri,agaskiya bayajin zai iya hak'ura da ita muddin ba'ita ce tace bata sonsa ba Dan haka ya zama dole ya gwada sa'arsa,gareta....
Ganin duk wannan sake-sake ba zai kai shi ko inaba yasa ya ta shi ya d'auro Alwala nafila,ya dingayi yana kaiwa Allah kukansa,,ba shi ya kwantaba,,sai gab da asuba....
•••••••••••
Yau kusan amakare ta farka sakamakon rashin,baccin da batayi da wuriba,,,agaggau ce,,take shiryawa,,,,ko da takammala kintsawa,,,da kyar ta iya kurb'an ruwan,tea,sallama tayiwa, Mama,da Salma,dan yau tare zasu fita,,"To Allah ya tsare ya kare hanya" cewar,,,mama suka amsa da ameen,,,,,,,,,,cikin sauri take tafiyah tana gyara mayafin kanta,,,batayi aune ba,,taji taci karo da mutin,,da sauri ta dago Dan ganin dawa sukayi karo,,, Hari ce,kafin ta bud'e baki tayi wata magana,,tini ta wanketa,da wani lafiyayyan mari,,,sannan ta kara da cewa,,''kewacce irin wawuya ce,sakarai kinatafiya Amma baza ki dinga kallon gaban kiba,ko an fad'amiki,,nan gidanki ne,,to ba gidankiba ne,,nan gidana ne,,dan ke ko Rabin gidannan baza ki samuba,,amatsayi gidanki,,ban za mai,,farar k'afa,,amyi gado agurin uwa...
•••••••••••
Wata irin tsawa SALMA ta daka mata,,tare da nunata,da ya tsa, had'e da cewa,"ke malam,ki iya bakinki,,ko dan kinga ana raga miki,,to shiru_shiru batsoro ba ne gudun magana ne,,ko Dan kinga,,ana kyaleki,,to bari kiji na fada miki, Daga yau sai yau,,,karkisake saka mahaifiyarmu,,a cikin shirmen magan ganinki,,,idan kuma kikayi kuskuren sakata,,,to Wallahi sai kinyi mamakin abin da zanyi miki.....
••••••••••
Hari wacce ke tsaye ko kyakkyawan motsi ta kasayi sabi da mamaki,,,,,bata gama mamakiba,sai da tatsinkayi muryar,,Nasreen tana cewa,,,"WANNAN haka yake "yar uwa,,,duk wani rashin mutincinki,,da za kiyi,ya tsaya a kanmu,,,ammah akul karkisake ko da gigin saka,mahaifiyarmu a ciki,,,sannan maganar gida da kikeyi,,ke duniyata dama,,,mu bamu da buri,,marar amfani,,,munbarki lafiya",,ta fad'a tare da Jan hannun Salma sukafi ce Hari kasa ko da motsi tayi sabi da tsabar mamaki da Al'ajabi...
••••••••••••
Yana zau ne agurin sana'arsa suka fito,,idonsa akan Nasreen,,gani yayi,,takara, yimasa wani kyau na musamman,,,jiyayi sonta ya k'ara shiga,,,ransa...
Suna fitowa,,idon, Nasreen ya sauka,akan rakennan,,jitayi har yawunta ya biya,,,dayake ita,ba daga nanba,,,,gurin sanrake,, Salma ta kalla,tare da cewa,,,"Wai dama me rakennan anan yake zama?,,,"eh,kinsan be Dad'e da fara zama ba Dan befi sati d'aya ba zuwa biyu" "Kai Amma baki kyauta bah,,kindaisan yan da nakesan rake Amma kina ganinsa,,,kullum ko kifadamin,","To yaya,Nasreen keda nasan ba kyason abin siyarwa sosai'',"To Amma dai ai kinga shi wannan yana da tsafta sosai,,,agurinsafa na siya kwanaki" "to yan zu dai ayimin afuwa", "To naji, amman fa yau babu makawa sai na sha rakennan,",duk wannan maganganin d sikeyi,DUK suna tafiya ,sukeyi,,..
•••••••••••••••
Bangaran ,Nasrenllah,, tin bayan da idonsa ya yi tozali,da kyakkyawan fuskarta,,ya kasa nutsuwa,,gaba d'aya,,,,,jiyayi zuciyarsa tana azal zalalsa akan ya Isar da sak'on zuciyarsa zawa gatata zuciyar,tabbas ya zama dole,a yau na'isar da wannan sakon konarage wani Abu azuciyata,...
Hmmmm""""""my fan's kunaganin kuwa,,Nasreen"""""""zata amince da soyayyar''''''""""""Nasrenllah??
Nidai nace.........hmmn bari dai nayi shiru na faraji DG bakinku.
Ummu Amsad😘
[5/11, 1:29 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI
[Yana tare da sauk'i]
BY Mmn AMATULLAH
Paid book 200
Phone Number ***.
Chapter {12}
Tabbas wannan kawai itace,,mafita Dan bai kamata,,ya yi taso shikad'ai ba wacce yakeyi dominta batasan yanayiba,,ya kamata,yasan in da yanufa,,duk wannan magan ganun Yana yine a cikin zuciyarsa..
••••••••••••
Yau tin misalin karfe,,,4 ya tashi,,daga wajen sana arsa Dan,yasamu dama ya kintsa sosai,,ko da ya iso gida Inna tayi mamakin ganinsa "Nasuru lafiyaa yau kadawo ba kamar yan da kasaba ba? "Wallahi Inna lafiya k'alau,,kawai nadawo ne,sabi da anjima,,zan Raka,abokina wani guri" "To to ai babu laifi"...
•••••••••
Yana da wowa daga sallar magrib,, ya je ya sake sabon wanka,,,,sannan ya shafe jikinsa da Vaseline,, sannan,ya dauko wani yadi,wan da kai da kagansa kaga,,karamin yadi,sai dai ya d'auki guga sosai,,,, tirare ya dauka y feshe dukkan ilahirin jikinsa,,sannan ya taje sumar kansa,,,d'as ya fito abinsa duk da rashin tsadar kayan da yasaka,,hakan bai hana shi yinkyauba,,ya yi kyau ,,matuka,,,,hanky ya d'auka ya rik'e a d'aya hannun,,,,takuyake cike da nutsuwa.tini naga,,Nasrenllah yazama cikakken handsome,,,fitowa ya yi,,"Aa Dan Inna sai ina haka irin,wannan wanka haka?,k'eya ya sosa, had'e da murmushi sannan yace,, "Inna,ba d'azu nacemiki,,,zanje,nayiwa abokina wata rakiyaba" "To....to natina,,to Amman irin Wannan wanka haka,, kai dai ka fad'amin,,ko dai wata tayi nasarar sacewa tilon D'ana zuciyarsa ne? dariya ya yi sosai ta yan da sai da fararan hakoransa suka bayyana,Kafin ya ce, "Haba Inna aini ba yan zuba tukunna dai" "To ai shikenan intayi tsami ai maji,,,Allah ya tsare hanya" "Yawwa Inna ameen" ya fad'a tare da ficewa,daga gidan,...
Sai misalin karfe 6 saura,sannan ta dawo gida ko da tadawo Tatar me rake ya tashi Sam bataji dad'iba,,sabi da tariga ta kwallafarai akai,da sallama ta shiga parlour'n Mamansu,,,,duk suna,zau ne,,, Salma ce ta amsa tare da cewa,,, "Yaya Nasreen sannu da zuwa,, haka ma Husna,amsamusu tayi da yawwa,,,, Mama barka da gida,, yawwa,, Nasreen y wajan aikin naki?,,Alhmdllh,to masha Allah "Yaya Nasreen ina raken nanfa duk zamansa mukeyi,,cewar Salma" "Wallahi nima da son raken na dawo ,,ama abin ,takaici,,sai n dawo na tarar ya tashi" kash amma banji dad'iba" "ke ni barikiga na tashi naje nayi wanka Dan naga magariba ta kusa,,OK in kinfito maci abincin" "Da kuwa yafiyemiki,wanna zancen naku",cewar mama,,,dariya Nasreen tayi tare da shigewa d'akinsu...
Lokaci'n da tafito wanka har anfara kiraye kirayen sallan magrib,,lotion, tashafa,,,doguwar riga ta d'auko ta atamfa ta saka,,,hijabi ta zura ta tayar da sallah,,,,,bayan ta,,idarne,,ta yi "yan addu'o'i'n ta,sannan ta fito parlour,,, abinci,,,, Salma ta d'auko musu,suka faraci,,,,,salma ce ta kwad'awa, Husna kira,da gudu ta k'araso tare da cewa "gani,ya Salma", "Yawwa, maza kije gidansu Hasana,,kice,wai tabaki,,,book d'innan ki kawomin kuma saura ki zauna wasa,,karkiyi sauri ki dawo" "to ai yan zu zan dawo" Husna ta fad'a tare da,tashi ta fice...
•••••••••••••
Dawowanta ya yi dai-dai da zuwan Nasrenllah, yana tsaye yana Neman wan da zaitura,,,ya ganta tazo shiga "k'anwata,ya kirata,tsawatayi tare da juyowa,tace "Na'am" "Dan Allah Dan tsaya n baki sako" to tace,,,"Dan Allah inkin shiga ciki,,kice,,ana sallama da,Nasreen" "Wai kana,nufin Yaya Nasreen? "Eh ita"to tace tare da shigewa ciki da sallama ta karaso,ko da tashigo har sungama cin abinci,,,suna zau ne,suna FIRA su da mams,,, "Yaya Salma gashi wai tace,,,ta gode Yaya Nasreen wai ana,,sallama dake a waje" baki sake take kallonta,,,,kafin tace "waye? ",wani ne,,kamar nasan fuskar amma kuma na manta in da na santa" "To sai kikoma kice,,,bana nan"....
•••••••••••
Har tata shi,, mama ta da katar da ita,tare da cewa,"Akan me gaki za'a ce bakyanan" "Haba Mama kin dai San abubuwan da suke ta faruwa,,chan baya ni Wallahi gaba d'aya soyayya ta ficemin arai kwata_kwata "to naji,nakuma yar da abubuwa,marasa dad'i sun faru abaya,to Amman ai hkan bayana nufin zai cigaba dw faruwa,ba ne in dai har kin d'auki abin a matayin kaddara..
Ya kamata kije ki sauraresa kiji da me yazo,,,bawai kice bakyananba,,in baki fitaba kin sau rari samari ba dauwama za kiyi acikin gidan ai dole watarana,,kiyi aure, Sanin kan ki ne kin san halin da mukeciki,,a gidannan,kuma kinsan mahaifinku ya baki lokaci,to ko da iya wa"yan nan hujjojin ka d'ai kyaje ki sauraresa ,kuma bawai nace dole sai kinsoshiba Aa,,,in beyi mikiba,babu dole,sai dai zan cigaba,da yimuku addu'a Allah ya baku mazaje na gari"..
•••••••••••••
Sosai jikin Nasreen ya yi,sanyi,,da jin kalaman mahaifiyarta amatuk'ar sanyaye tace , "Ameen mama" "Yawwa, kokefa,maza jeki" "ke Husna ta shi kije ki kai kujeru na roba guda2 sai ki dawo ki kai Ruwa" "to mama,,,Ku jeru ta d'auka ta fice, Daga chan wajejen bakin get ta ajiye,,,sannan ta leka ta cemasa ya shigo,,,shigowa ya yi,,,guri ta nuna masa tare da cewa "kazauna tana zuwa" "to k'anwata,ngd,,, Amma daga gani ke kanwarta ce ko? Nasrenllah ya tambaya,,,, "eh" tabasa amsa,"Aifa gakama nan ya ya sunanki? "Husna" ta fad'a a tak'aice "to Husna nagode ko ki gaida mama" to tace tare d wucewa ciki,tana kokarin shiga Nasreen na k'ok'arin fito wa...
Da sallama takaraso,,gurin,,jiyayi zazzakar muryarta ta daki dodon kunansa,,harsai da ya limshe idonsa amsawa ya yi,,cikin ta shi zazzakar muryar,,wacce,, tasa,,,tsigar jikin Nasreen tashi,tin da take samarinta bata tab'ajin wan da muryarsa ta ratsataba kamar tashi," Barka da fitowa abar kaunata, Nasrenllah ya fad'a Yana kafeta da idanu, "Yawwa, barka,ya hanya? amsawa ya yi d lpia kalau,, Alhmdllh sannan ya k'ara da cewa "DA fatan dai nasameki lafiya,sannan kuma ban takura mikiba" "Aa,,babu komai",,tin da yafara magana,,take tinanin iin da tasan,muryar Amma ta kasa tinawa,,sannan duk wannan maganar da sukayi kanta a sunkuye yake bata d'ago ba ,balle ta gakowaye...
Tsintar zazzakar muryarsa tayi,,wan da hakan ya dawo da ita Daga tinanin da tatafi,,,,,,,"Malam a,,,Nasreen" yan da taji ya kira sunanta,,ne ys ta dago ta kallesa,,,Dan bata tabajin wan da ya iya fad'ar sunan taba kamar shi,,,,dagowar da zatayi suka had'a ido,,wani lallausan murmushi ya sakar Mata da sauri ta janye idon ta,,,murmushi ya k'arayi sannan yaci gaba da cewa, "Nasan za kiyi mamakin ganina,,,,sannan nasan zakiyita tambayar kanji dalilin zuwa na,,to ba komai ya kawoniba,face,,alkairi,da farko dai ni sunana,Nasrenllah,,,,nazone Dan na isar da sakon zuciyata,zuwa,gataki zuciyar,,wato a gaskiya Nasreen, bazan b'oye mikiba,,tin ranar da nafara Dora,,idona a kanki zuciyata,ta kamu da matsanancin sonki..
Shiyasa nace bari nazo na Sanar miki da sakon zuciyata,da wuri tin kafin,wani ya rigani,
Sai dai wani han zari ba guduba,ni bawani ba ne,face,bawan Allah,,,sannan kuma,,aduniya ni ba wani ba ne,,,sannan kuma ni ba d'an wani ba ne,,face,,na ce miki,,ni talaka ne,,ban ajie ba Haka ban bawa kowa,ajiya,,ba,,atak'ai ce dai
Ayanzu,,sana,, ata ita ce sai da rake,,kuma cikin ikon Allah da ita nake rike mahafana,,sannan b'an garan karatun boko,,,iy secondary School natsaya,sakamakon halin rayuwa,,,ban garan islamiyyah kuma Alhmdllh Ina da hadda sannan na haddace littattafai da dama"....
"Nasan yan zu a zuciyarki,kinanan kinacewa,,toke meye alakarki da wannan gajeran,,lbr'n,,,,,,,dalili na,na fad'amiki wanna'n labarin,,,shi ne ni dai tsakani da Allah da maganar aure nazo ba maganar wasa ba, Dan haka ya zama dole na sanar da ke koni waye,,,,,tin kafin ki fara sona,,shi ne da lilina"...
••••••••••••
Tin da ya fara magana bata dago ta kallesa bahm haka bata ce k'alaba,,,sai dai tanajin magan ganinsa suna ratsata,,,,sannan sai yan zu ta tina in da tasansa.....
••••••••
Jin ya yi shiru ne,ya bata tabbacin ya gama dan haka tace,, "DUK naji bayananka,,,kuma nagode da soyayyar da kake yimin,,,,,,
Sannan aishi,arziki da rashin sa duk DG Allah yake,,,Dan kaga mutin da arziki ba shi yake nuni da cewa Allah ya fi son Saba ne ko Kuma Kai da baka da shi Allah baya san ka ba ne shiyasa ya hanaka,,,,,Aa duk yan da Allah ya tsarawa bawa rayuwa to kamata ya yi ya karb'eta hannu,,bibbiyu sannan kuma ya gode masa" ,,jiyayi ta k'ara shiga ransa fiye da Da,,jiyake kamar ma ta amince da shi ne...maganar ta ce ta katse Masa tinanin da ya tafi..
"Sannan magana ta karshe kabani kwana biyu zanyi shawara,duk hukuncin,da na yake za kaji in Sha Allah" ,"To ai in dai wannanne karki samu da muwa,,,,sannan INA godiya da Wannan tarba da kikayimin na gode sosai" "AI babu komai ni bari na Shiga,ciki ka gai da gida".
,"To ngd gida yaji".
Ummu Amsad😘