Shafi Na Biyu
by @huguma
Duk wannan aikin da yake baisan tari ko adani ba,burinsa daya samu kudin ya siya abu mai dadi yaci,ya kuma kawowa mahaifiyarsa a boye,baya taba bari mahaifinsa ya gani,don yana da tabbacin indai ya gani ba rabonsa bane kudi ko abinci,koda na nawa ne kuwa,zai karba ya kalmashe a aljihunsa,rashin kawo musu baisa yaji kunya yaqi amsar nasu idan sun samu.
Sosai abun ke cima kaltum tuwo a qwarya,tana qaunar bilal sosai,yana da sauqin kai,bashi da rashin ji ko hayaniya irin ta yara,wahalar da yakeyi tana ganin tayi yawa,saidai kusan ta zame masa jiki ma,ya zama tamkar bawa,don baya iya zama wuni guda a gida ba tare da yayi aikin komai ba,saidai idan bashi da lafiya.
Shi dinma da kaltum taso yayi karatu koda su din basuyi ba,tunda shine da namiji guda daya tilo da mahaifiyarsu keda shi,amma sam yaqi,ya nuna aikin neman kudinsa ya fiye masa,koda ta zauna tayi tunani,sai taga idan ta takura dinma sai yayi karatun dame zaiyi?,su din da kullum sai sunyi fafutukar abinda zasu ci?,saidai taci alwashin dagewa tuquru ta tara kudin da bilal din zai koma makaranta,koda baya so,saboda tana kallon shi ne tamkar shine madubin rayuwarsu,kuma wani tsani da zai kai rayuwarsu izuwa tudun mun tsira anan gaba.
Har azahar suna zaune zaman jiran gawon shanu,babu baban nasu ba alamarsa,dukka sun ukun idan ka kalli fuskokinsu babu tantama yunwa suke ji,daga nan sashensu suna iya jiyo qamshin man ja,wanda da alama ana soyashi ne daga sashen baba iliya,wato sashen dake fuskantosu,amma ba qamshin manja ba,ko qamshin me zasuji babu lallai a miqo musu koda babu yawa saboda haqqin maqotaka dana zumunci,saidai idan Allah ya tsaga da rabonsu.
Tana idar da sallar azahar ta miqe tana karkade baqin hijabinta daya kwashi qasa,ta dubi ummansu
"Ummanmu.....na tuna ina bin ladingo kudin kitson da nayi mata tun rannan ita da 'yarta,bari naje ko zan samo,saina siyo mana ko gari ne" cike da tausayi ta dubi diyar tata,wannan rayuwar da suke sam bata qaunarta,to amma ya zatayi da ranta,ita ba sana'a gareta ba,hasalima bata da jarin kuma bata dame bata,bata da wata kadara da zata saida ta zame mata jari,kai koda ta fara sana'arma mai gidan shike amshewa da wayo har sai ya durqusar da ita,dolen dole ta zuba idanu komai ma ke faruwa.
Saidai ko kadan bata bari ba,bata sanya idanu ba,hakanan batayi sanyi ba kan tarbiyya 'ya'yanta,bata da sauqi ko sanya wajen kula da tarbiyyarsu,kuma kowa yasan da hakan
"Karki dade,idan baki samu ba ki maza ki dawo gida"
"In sha Allahu....habiba zo muje" tace da qanwar tata,itama bata dade da idar da sallar ba,don haka ta miqe suka fice a tare.
Suna tafe a hanya saidai babu wanda ke magana a cikinsu,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,basuyi nisa ba suka hangi asiya tana tahowa,dauke da jakar makaranta kamar gaske,wato yanzun yayi dai dai da lokacin tasowarsu kenan,shine ta dawo gida.
Suna hada ido da kaltum tayi kicin kicin da rai,ta kuma dauke kanta bayan ta gasa mata harara,wanda kaltumen batasan daga inda ta faro kota samo asali ba,saidai hausawa sunce....tabarmar kunya da hauka ake nadeta,wala'alla abinda tayi shirin yi kenan.
Sai da suka giftata sannan habiba tace
"Wai yaya bakiga kallon da asiya tayi miki ba?" Kai ta jinjina
"Na gani habiba,tana son nannade tabarmar kunya ne da hauka" cikin alamun son qarin bayani habiban tace
"Me ya faru?" Kamar ba zata gaya mata ba,sai kuma taga cewa barin kashi a ciki baya maganin yunwa,hasalima duk duniya bata da kamae habiban,hakanan tafi kowa sanin halin habiba,bata da yawan surutu ko yarin qawaye,hakanan nutstsiya ce bare tace zata yi zancan da wani,abinda yayi habiba shi yayita.
Ta yadda zata fahimta ta gaya mata komai,ga mamakinta sai habiban ta tabe baki
"Na saba ganin asiya a wannan yanayin yaaya,saidai fatan Allah ya shirya" cike da mamaki da kuma baqinciki ta ware idanu tana dubanta
"Amma habiba kin sani baki taba yin wani abu da zai daqile 'yar uwarki daga fadawa halaka ba?,kinsan cewa kema kina da kamasho duk abinda ya faru tunda baki taimaka mata kin tunkudeta daga cutarwar da takeson jefa rayuwarta ba?" A sanyaye tace
"To ya zanyi yaaya?,na gayawa umma,tace mu tayata da addu'a kawai,kada nayi magana,saboda ita batason tashin hankali,don babu lallai baaba lami ta fahimci abinda zan gaya matan,kinfi kuma kowa sanin halin jarabarta,da yadda ta tsangwamemu hakanan babu gaira babu dalili" shuru kaltum tayi,ta kasa furta komai,hankalinta na wani irin tashi,jininta ce keson fadawa wannan hanyar?,me yafi wannan tashin hankali?,sam bata jin zata iya shuru koda baba lami zata tsireta,duk da ma basu da tabbacin zataqi amsar maganar,don babu wata uwa ta gari da zataso ganin lalacewar diyarta,itace mutum na farko da zataso ta gyaru,don haka taci alwashi cikin ranta ba tare data furtawa habiba ba.
Basu sake magana ba har suka iso gidansu ladingo,shima dai babban gidane irin na karkara,mai dauke da sassa sassa,ta gaida mutanen data taras a harabar gidan ta wuce sashen ladingo.
Zaune ta sameta daure da zani da riga mabanbanta,yaronta na saman cinyarta yana shan nono,ita kuma tana irgen kudi,fanteka ce a gabanta wadda take duqun duqun,ba'a jima da dawo mata da ita daga tallar awarar da take bayarwa tana biya ana yi mata ba,kitson da kaltum tayi mata har ya fara soshewa,amma har yau ta kasa biyan kudinsa,kamar yadda wasu daga cikin matan qauyen keyi mata,takanyi kitson ne kawai saboda ko banza yana toshe mata wata kafar,duk da cewa su din talakawa ne tilis....basu mallaki komai ba,amma mutane ne masu tsananin tsafta,kamar yadda suka gada daga mahaifiyarsu,ita dinma haka take,ta washi qazanta gaba daya,tana da tsafta qwarai,ta yadda duk kodewar kayanta da rashin kyansu ba zata ga datti kowani abu mai kama da qazanta ba,dalilin da yasa da qyar take iya kama kan wasu ta kitse saboda tsabar rashin gyara da tsafta,da yawansu suna ganin cewa zallar wulaqancine kawai da girman kai,saidai ba haka take ba,qazantarsu ce kawai ke damunta,tana mamakin yadda basu damu da jikinsu da kawunansu ba,mace saita wuni a tsaye tana aikin neman kudi,amma gyaran jikinta saiya gagareta,ba zata iya siyan man shafawa dangwali yaba ko turaren abulbula ta siya ba saboda kauda wari da qarni,duk da talaucinsu wanda da yawansu wasu sun fisu,bata taba ganin qazanta jikin mahaifiyarsu ba.
Tana jin sallamarsu ta soma qoqarin boye kudin ta hanyar cusasu cikin zaninta,sarai kaltum ta gani,amma saita dauke kai kamar bata gani ba,ta soma washe musu bakin qarfi da yaji.
Da qyar habiba ta samu wajen da yayi mata ta zauna,kaltum kuwa kasa zaman tayi,saita jingina da bango kawai tana gaida ladingo,yarinyar macace mai haihuwa daya tak,amma qazanta da zafin nema sun qara mata yawan shekaru a fuska da jiki gaba daya.
"Don Allah kudin kitson nan nazo ki bani ladingo,na matsu ne zanyi amfani dashi" kicin kicin tayi da fuska
"Kai kaltume.....ke kam baki da kara wallahi,kudin kitson nan har yanzu baki manta dashi ba fisabilillahi?,kwana wajen nawa?,ki rage son abun duniya gaskiya" sosai kalaman nata suka bata haushi da mamaki,uba uba yanayin yadda tayi zancan a wani gadarance,kamar ita ta tsuguna ta haifeta
"To ai da nazo cemin kikayi nayi miki kitso zaki biyani kudin,baki gaya min cewa kyauta kikeso nayi miki ba,kinga kenan ko kwana dubu sukayi ai haqqina ne ko?"
"Kinga kada kimin rashin kunya....ungo kudinki" saita zaro naira darin daga cikin kudin da take ta boyonsu cikin zani ta miqa mata,sauke qafafunta tayi ta soma zura takalmanta,a yanayin data nuna yasa habiba ta gane tsaf zata wuce bata amsa ba,saboda cin fuska daya shigo ciki,don haka ita ta miqa hannu ta karba,ta miqe tabi bayan kaltum suka fice daga gidan,suka bar ladingo tana mita.
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
***
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
***
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
[2/26, 7:11 AM] safiyyatulkiram: *DABI'AR ZUCIYA*
_FREE PAGE_
02
*Zafafa biyar books 2022*🔥🔥🔥🔥🔥
*SO DA ZUCIYA* _miss xoxo_
*DEEN MARSHALL* _Mamuhghee_
*HALIM GIRMA* _Hafsat rano_
*TAKUN SAƘA* _Billyn abdul_
*DABI'AR ZUCIYA* _Huguma_
*KU TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN*
***
KO KUMA
***