Chapter 6
*NAJAWA KAINA*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
(Sanadin Son jiki)
*Story&written by Mmn Amatullah*
*Dedicated to my fam
*BABI NA 10*
Yana shiga daki jakansa kawai ya ajiye tare d cire kayansa ya wuce bayi,,wanka Yayi,,tsaf, yafi to ya shirya Dan zuwa masallaci,,ko da yafito Babu kowa a falon,,Kai tsaye wucewarsa yayi,,,,,,
Lallai mah mutumin nan harni zeshawa kamshi akan Abin d bekai ya kawoba,hmmm wlh in dai akan tsarinane inanan daram Babu gudu Babu ja da baya,,yajima beyi fishi bah,Kuma Dani yake zancen,,,mikewatayi ta fito Najmah ta kwalawa kira,,da sauri t fito tana cewa gani Aunty,,,yww,,dama n kirakine a kan ,idan kinji shigowar me gidan to ki fito ki zuba masa Abinci ,,Nima ki hadonawa ki kawomin daki Dan yau a daki zanci,,to Aunty,,,mikewa Najmah tayi ta nufi dining ita kuma gimbiyar takoma ciki,,,komai ta zuba mata,takai Mata har daki,,, sannan ta fito t wuce dakinta,,itama sallah tayi sannan tace Abinci,,,tana gamawa ta dawo parlour ta zauna,,,,
Kamar Yan d ya Saba dawowa hk ya dawo,,Yana shigowa y wuce gurin cin abinci,,da sauri Najmah ta taso ,,tana Yaya barka da shigowa,yww ya amsa yana kokarin Zama,,Abinci t fara kokarin. Zuba masa,,,inah matar gidan,,y tambaya,a takaice,,,tana daki,can tace na kaimata nata,,adaki yau zataci ,,sannan tace najira,idan kadawo na zuba maka naka,,, okay kawai yace kasan zuciyarsa nayi masa wani suya,,,sai d ta zuba masa komai,, sannan ta koma cikin falo ta zauna,,,shikuma ya faracin abincin sah,,hankali kwance kamar Babu Abin d ke damunsa,,,,sai d ya gama tsaf,yatashi ,y tafi ta gyara gurin tsaf,,sannan itama t wuce nata dakin,,,,
Shirin bacci yayi tsaf y kwanta sai dai halayyar saudah ta damesa a zuciya,,yanzu ace duk kokarin d yakeyi na ganin ta shiryu amman sai mah Kara,fan darewa take,,yanzu har ankai lokacin d komansa me aikice keyi masa,,,,
Hmmmm nisawa yayi tare d cewa shikenan sauda tin d hk Kika zaba to muzuba mugani ni dake wake da riba,,zanyi maganinki,,,,,
Washe gari,,,
Kamar Yan d Najmah take tashi hk tatashi t shirya breakfast ta kyara ko inah,tayi wankanta tsaf,,ta dawo parlour t zauna tana kallo,,,tanan zaune guraren 8:30 Najibullah ya fito,,,yaumah kamar jiya kamshin tirarensa ne y daki hancinta,,juyowa tayi,tana ganin shine ta mike da sauri,,tana Yaya sannu d fitowa,,inah kwana,,fiska sake ya Amsa,,d lpia kalau, Najmah ko,ya Kare maganar d sigar tambaya,,eh Najima ta bashi Amsa,,to Najima yakika tashi lpia kalau,to Masha Allah,,,ya karasa maganar Yana Zama a saman Dining,,kara sowa Najmah tayi ta zuba masa shayine wan d taji kayan kamshi,, Sai,farfesun kaji,suma sai bada kamshi suke,,kamshin y Shaka tare d cewa hmm amman dagajin kamshinnan zeyi dadi,,,dry Najmah tayi tare d cewa,,Kai yaya tin bakaciba,,eh mana ai abun d zeyi dadi tin dg kamshi ake ganewa,,,kedai Allah ya biyaki sannu d kokari,,to yaya n gode,,,nan ya faracin abincinsa,,har ya gama yayi hamdalah ya mike,,,,mikewa Najmah tayi,,tana cewa,yaya kawo jakar n kai maka mota to Najma gata,,karba tayi tana murmushi,,bayan sa tabi har mota,,t ajiye masa jakar tare d cewa to yaya Allah ya tsare hanya ,,Amin Najmah nagode,, ciki ta koma shikuma ya tafi,,,,,
Tana komawa t kwashe kwanikan d ya bata,,ta Kai kitchen t wanke,,tafito,dakinsa ta nufa,,ta gyara ko inah ,,tana gamawa ta koma dakin ta itama karyawa tayi sannan t koma bacci,,,,,
Ko da saudah ta gama baccin ta tafito Babu kowa a falon,,,gurin cin abinci ta nufa t karya tana gamawa ta koma saman kujera,ta kwanta,,tafara chat,,cikin wani group me suna *MANYAN MATA* yini suke suna fira da ko wanne lokaci grp din baya rasa mutane ,dare ko rana,,HK tahau taga sako kusan 5k ,,nan ta hau akacigaba dayi d ita,,,,wasu nayi Mata korafin bata fitowa da wuri tacika bacci,,dry tayi tare d cewa karku damu Nima Zan dinga fitowa Dan kar adingayi Babu ni,yww kokefa,,babbbar yarinya,,hadai suka cigaba d tattaunawa,,,,,
Yaumah ko d Najmah tafito saudah tace basai tayi girkin ranaba,,dakin sauda kawai t gyara,,t koma nata dakin,,,sai da tayi sallar la'asar tafito t shiga kitchen,, gimbiyar tanan kwance tana chat har zuwa lokacin kayan baccine a jikinta,,da kyar mah ta iyah tashi t hada la'asar d azahar suma Babu nutsuwa Dan hankalinta Yana kan group,,,,,
Misalin,,karfe 5:30 Su Ammy sukayi sallamah a falon gidan saudah dake kwance,,hankalinta akan chat Koji batayi bah sai d suka kara wata sannan taji amsawa tayi tare d cewa kushigo mana,,,su Ammy tagani,,zaune ta tashi tana cewa Aa yau su Ammy ne agidan namu, sannunku dazuwa,,,
Yww,,munsameku lpia lpia kalau,to Alhmdullh,,nan su Maryam suka gaisheta,,ta amsa tana cewa ya makaranta, Alhmdullh,,,sukace dg nan duk kowa yayi shiru Sabi da Babu shakuwa Sam a tsakaninsu,,tin d itama ba wani zuwa yakeyiba hk suma,,, Najmah ta kwalawa kira,,da sauri ta fito dg kitchen,,tana Aunty gani,,yww maza ki kawowa su Ammy ruwa lemo,,to ta amsa Tare da gaishe d Ammi,,amsawa tayi cikin sakin fiska,, sannan t kalli su Halima fiskarta dauke d murmushi tace sannunku tagwaye,dry sukayi tare d cewa yww ykk lpia kalau,,
Kitchen ta koma ta kawo musu ruwa d lemo,,,ta ajieye,,Ammy ta zubawa,t mika mata,, sannan tace Yan tagwaye Kuma ga naku,,to mungode,,itadai matar gidan batace komaiba,,hankalinta n kan chat dinta,,, Najmah nagamawa t koma kitchen Dan t karasa girki,,,,
Ganin zaman shirun yayi yawa ys Ammy cewa tomu Bari mokoma dama hanyace t biyo damu nace bari muzo muga lpianku,,to Ammy ku gaida gida mun gode,,,,
Suna kokarin bude kofa Najibullah na sako kai,,tini Autocin Ammy suka sa tsalle suna yaya oyoyo,,,cike da matsanancin farinciki,yace Aa yau Ammy ce a gidan namu amman,ko kifadan zakuzo da ban dawoba d shikenan,,
To ban d abinka tin d mun gaisa d matar gidan ai shikenan ko,,Aa Ammy Nima ai sai kujira nazo yanzu dai kumokoma ciki,,HK suka koma ,har kasa y gashe da Ammy Autoci suka gaishesa,,,kundai ci Abinci ko ,,Aa kundai Sha ruwa d lemo, cewar,Halima,,in d sauda take y kallah yaga Sam hankalinta Naga wayanta,,ransa yakai kololuwar baci amman ya danne,,, Najmah y kwalawa kira,,da sauri ta fito tana lah yaya ka dawo sannu d dawowa,,yww Najmah,,ya girkin kin gama eh nagama,,to maza ki kawowa su Ammy,,to tace tare d komawa kitchen din,,Ammy tace,,kai,,mufa tafi zamuyi basai munciba,,,cike d shagwaba yace Kai Ammy,,kizo har gidana ,, amman kiki cin abinci gaskiya Aa,,ni sai kunci,,,,Babu Yan d Ammi t iyah Dole tayi shiru,,,,,,
, Sai da ta jera komai a saman Dining,, sannan tace Yaya angama to sannu,,Ammi kitashi muje Sai muci,,,gaba daya suka koma saman dani,,,shi da kansa ya zubawa Ammy tuwon semo da miyan agusi,wacce taji nama d kifi,, Najmah ta zuba masa sannan t zubawa Autoci har tana tsokanarsu ko hurhudu Zan zuba mukune,, dariya sukayi gaba daya tare d cewa amman har dake zamu hadu mucinye hudun ko,Aa kukadai idan mah ba ku koshiba sai n kara muku,,wah lallai biyun mah mucinye,,,, gaskiya yaya wa innan basason suci Abinci kirabu dasu Najmah shi ys ai gasunan Sam Babu kwari,,cike d shagwaba Autoci sukace Ammy kin gansuko,, dry tayi tare d cewa kumfi kusa ai,,,hk sukaci abincin su cike d Raha,,,,,,,,
Comment and share please
Mmn Amatullah Ce๐ฅฐ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*NAJAWA KAINA*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
(Sanadin Son jiki)
*Story&written by Mmn Amatullah*
*Dedicated to my family*
Bismillahir'Rahamanur'Rahim...
*BABI NA 11*
Ammy ce ta dubi Najmah tana cewa toke "yata bazaki zauna muciba,, Dry Najmah tayi tare d cewa,Aa Ammy kuci Nima zanci zuwa anjima,,to shikenan,,cewar Ammy,,,
Bangaran sauda kuwa batace ko kalaba karshema tashi tayi takoma daki,,azuciyanta tana mitar duk sun cika Mata kunne,,,,
Duk abin d kefaruwa, Ammy na lura dashi zuciyarta fal tambayoyi sai dai Babu me Bata wannan amsar,, bakuma zata tambaya bah,,har sai lokacin d ya budi baki d kansa ya fada mata,,zadai tayi ta tayasa d addu'a,,,,,hk suka gama cin abincin cikin so d kaunar junansu abin sai bawa Najmah sha'awa yakeyi,,,suna gamawa Najibullah ya dubi Ammy tare d cewa,to yanzu tin d magrib tayi sai kiyi sallah sannan sai n mayar daku gida,,,Aa kabarshi kazauna ka huta kaima,,Kuma ka manta d drive miketare,,,Aa Ammy ban mantaba kawai dai ninakeso n mayar daku Dan nacema ya tafi,,,,Babu Yan d Ammy ta iyah Dole tayi hakuri,,,, rakasu yayi,har dakin d zasuyi sallah,yayi sannan y fito y nufi dakinsa,,wanka Yayi a gurguje ya fito y kintsa ya wuce masallaci,,,,,,,
Bayan Najmah ta idar d tata sallar,,fitowa tayi ta gyara in d sukaci abincin,ta Kai kitchen ta wanke tana gamawa ta nufi dakin d su Ammy suke d sallamah t shiga,,,amsa Mata sukayi,,Ammy na cewa, Najmah kike ko ,eh Ammy,,to Najma sannu d kokari mungode kwarai d dawainiya Kai Ammy Babu komai,,ki dena godemin ai sai naji kamar wani Abu nayi,,dry Autoci suka saka Tare da cewa wani Abu kikayi Mana irin Wannan tarba hk gaki faran faran ko matar gidan Albarka,,dry itama tayi tare d cewa Kai tagwaye,,itama fa Aunty akwai sakin fiska,,tana d kirki sosai,,mu bamu ganiba cewar Maryam, Aikam dai inji Halima,,, Ammy ce tace to ya isa hk,,kar n sakeji kuka sani ko,batajin dadine,,kedai Najima Allah yamiki Albarka Amin Ammy na gode,,cike d shagwaba Autoci sukace Ammy muban damu,,dry Najimah tayi tare d cewa,ban d abinku ai har daku,,ko Ammy,Kai ta daga tana murmushi,,nan suka zauna sukayi ta firarsu ,,gwanin sha'awa Kai kace dama sunsan juna,,hk Najibullah yazo y samesu shi kansa sun birgesa,,,to ka dawo zamu iyah tafiya ,,eh Ammy Bismillah,,,HK suka fito ,, Ammy tana inah matar gidan miyi sallamah,,Bari n kirawota cewar Najmah,,d sallamah t shiga dakin sauda,,amsawa tayi tare d Bata izinin shiga ,,Aunty kizo su Ammy zasu tafi,,to jeki ganinan,,,Bata jima d fitowaba saigata,, Ammy tace tomu zamu wuce to Ammy kugai da gida sai d safe to Amin,,HK suka wuce itakuma t koma daki,,,har bakin mota Najmah ta rakasu,, Autoci na cewa,,yanzu yaushe zakizo mana,,Aa nikam Babu Rana,,kin mah isa ai Dole kizo Mana,,in ba hk ba ko munzo gidan Yaya bazamu kara kulakiba cewar Halima,,Ido t zaro tare d cewa to shikenan kubari duk ran d bani d aiki me yawa Zan tambayi Aunty in tabarni ,sai n tambayi yaya kwatance sai nazo hakan yayi,,,kin fanshi kanki hakan yayi cewar Maryam,,gaba daya dry sukayi,, Ammy ta duba Tare da cewa,to Ammy sai d safe Allah ya tsare hanya,,to Amin Najmah mungodefa Allah yayi Albarka to Amin,,,Yaya Allah y tsare Amin,,Najma,,to Autoci by, Najmah t fada tana daga musu hannu,suma,hannun suke daga mata,,,,sai d suka fice dg gidan sannan takoma ciki,,,,
Kai tsaye dakinta tawuce taci abinci tayi wanka ta kwanta,,tanajin kewar gida Dan Dan zaman d tayi d su Ammy ya tina Mata d gida,,,,tanan kwance har bacci ya dauketa,,,
A hanya ne Ammy take tambayar Najibullah,ainah kuka samo yarinya Mai hankali d son mutane hk,,ko kan war matar gidance,,Aa ko daya "Yar aiki ce,,d kakartace keyin aikin to tsufa ya kamata shine ta kawo Mana Najmah,,yarinya me tsafta ganutsuwa,,,eh gaskiya, Naga alama,,to Allah ya temaka,,Amin Najibullah y amsa,,har suka karasa gida suna Dan taba fira,lokaci zuwa lokaci Kuma kaji shiru kowa d abin d yake sakawa aransa,,ko d sukaje gidan Najibullah yajima agidan suna fira kafin ya tafi amman Sam Ammy batayi masa magana akan matarsaba tabarshi ne yayi bayani Dan kansa,
Bashi y shigo gidaba sai guraran 10:30 gidan shiru alamar duk sunyi bacci shima dakinsa y shige y kintsa sannan y kwanta,,,,,
Washe gari,,kamar Yan d aka Saba Najma tayi komai d yazama acikin aikinta tayi wankanta,tanan zaune a falo,matar gidan t fito,,sanye d rigar bacci,,guri t samu t zauna Najma t gaisheta,,amsawa tayi tare d tambayar ta me ta girka,,fada Mata Najma tayi tare d cewa,,ko akawo miki nan Aunty, Aa barshi bayanzu Zan karyaba to tace tare d neman guri tazauna,,shirune y ratsa falon Babu Abin d kakeji sai karar TV,,,,
Najibullah ne yafito cikin shirinsa n zuwa office,,sannu d fitowa yaya inah kwana,, lpia kalau Najma kin tashi lpia, lafiya kalau yaya,,to masha Allah,,ko in d saudah take be kallaba ya wuce y zauna,,hk itama Bata tanka masa ba,, Najmah ce ta karasa ganan Dining din ta fara zuba masa farfesun kifini,,da coffee,,uhh lallai kamshin girkin nan d Dadi yake,,,Wai nikam Najma waya koya miki girki har HK ne,,,kanacin Abinci kamar kunnanka ze tsinke,, dry Najma tayi tare d cewa Kai yaya abincin nawane kamar ze tsinka kunne,,eh mana,,ai kin iyah girki Babu karya Dan idan za'a ce n baki maki to d kullum ๐ฏZan baki,,,waya koya miki,,innah tace kai gaskiya innarki tayi kokari Allah ya biyata,,to Amin, Najma t amsa tana dry,,au dry mah kikeyimin ,,niwa Aa yaya badakai nakeba ai ,,to dawa kike,kaina nakeyiwa dry ,,dry yayi tare d cewa to shikenan tin d kinji toro kin fanshi kanki,,hk ya dingaci Yana Santi Najma n dry,,har y gama,,ya mike,,yana cewa kingani ko Najma Sabi da dadin abincinki naji yayimin yawa dakyar nake numfashi,,to yaya ka zauna idan ,,y sassauta sai ka tafi ,,Aa idan n zauna makara zanyi ko kinaso ayiwa yayanki balalar makara a office,,Ah inah zanso,,to kingani gara n tafi ,yaragu a hanya,,maza dauko jakata ki rakani mota ko yau ba'a rakaniba ,,Aa Yaya Zan kaima ka Mana yaww yarinyar kirki maza muje,,HK suka fice suna ta firarsu suna dry,,,,
Bangaran sauda dake zaune tana chat dinta,,Sam yi tayi kamar batasan sunayiba amman,duk Rabin hankalinta Yana ga firarsu Sam ba chat din takeyiba,,wata zuciyarce tace ke karki wani damu me zeyi d wata Yar aiki yanayin hakanne kawai Dan kiji haushi,,,kumafa hk ne,,ta fada a kasan zuciyarta,,,humm kayi kagama in dai nice ta fada tana kawauda tinanin tare d cigaba d chat dinta,,,,,
Ko d Najma ta dawo kaitsaye dakinsa ta wuce ta gyara ko inah,,tsaf sannan tafito t wuce dakin sauda shima ta gyara bayan t gamane ta fito t tambayi saudah ko akwai Abin d zatayi ,,Aa tace mata tare d cewa zaki iyah zuwa ki huta to Aunty n gode,,,,,,,,