Chapter 13
NAJAWA KAINA*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
(Sanadin Son jiki)
Paid book 200
Phone number ***.
*Story& written by Mmn Amatullah*
*Dedicated to my Fam*
Bismillahir'Rahamanur'Rahim
*BABI NA 24*
Dole nasan abinyi,Dan gaskiya bazan iyah da ayyukan gidannan nikadaiba,,na gidan namumah Dan bani d Yan d zanyine Nan kuwa inah d Yan d zanyi,,,zanbi duk hanyar d zanbi da kanka zaka kawomin me aiki ta karasa maganar tana kwafa,,,,,,,,
Sosai lamarin saudah,yake bashimamaki,, lallai,sai,,yau,,ya tabbatar zaman gidansu baze ladaftar da itaba,,auren da zeyi shikadai ne ze dawo ,da itah cikin hayyacin ta,,,,,
Washe gari kam Babu Abin d tayi a gidan,,Sam Beyi mamaki bah duba ga Yan d sukayi jiya da itah,,,, be kobi ta kanta bah balle,ya tan kata ya saka Mata idone kawai tayi Yan d takeso Dan yasan wataran ko da kudi akace tayi HK baza tayiba,,,,
Ban garan saudah kuwa ta dawo da duk wani Hali nata har mah d kari,,itah a tinaninta yin hakan shine zesa ya amince ta kawo me aiki tin d a duniya Babu Abin d yafi tsana sama da kazanta,,,,,,
Biki sai gabatowa yake,,,in da zuwa yanzu saura sata biyu,tini shirye shirye sunyi nisa ta duka ban garori guda biyu musamman bangaran me gayyah me aiki,,kusan komai ya kammala,gyaran gida kadai ya rage masa,,shima Yana sane y barsa har gab da biki,,tin da bawani aiki ne na kuzo ku ganiba,,,,,,
Yau mah kamar kowanne, lokaci,HK ya dawo ya samu gidannan kamar Yan d ya tafi ya barsa ko inah kachar kachar,,,Sam beji komai bah sai mah wani tattausan murmushi daya saki,,tare d rangada sallamarsa,,, tana kwance,saman doguwar kujera tana latsa wayanta amsawa tayi Babu yabo Babu yabo Babu fallasa,, sannan ta kara d sannu,duk tana kwancen batare d ta mikeba,,,karasowa yayi,ya samu guri ya zauna a daya dg cikin kujerun,,Yana wani yamutsa fiska kamar wata mace,,,Sabi da adole ya zauna,,duban saudah yayi wacce tawani tamke fiska tana cigaba da latsa wayanta,,, murmushinsa ya kara fadadawa Tare da cewa,, uwar gida sarautar Mata agidan Najibullah ko Zan samu,Aron lokacin ki inason magana dake,,,duk ta taji dadin kirarin d Yayi Mata amman hakan besa ta nuna ba sai mah,,wani Shan kamshi,da ta karayi tare da cewa inah jinka,,,to ban d abin uwar gidana ai da kin tashi zaune ko,,,kafada a HK ai kunne keji,,ta karasa maganar tana wani kara tamke fiska Wai itah adole an bata Mata rai,,,,,
Murmushi ya karayi tare d cewa to shikenan uwar gidana,,,kwanaki kinzomin da maganar ke aiyyukan gida sunyi miki yawa kina bukatar me Aiki ko wacce zata temaka miki,,ko,,eh hi nace Kuma har yanzu inanan,,a kan bakata,,Dan gaskiya bazan iyah bah,,HK kurum,,,,to kwantar d hankalinki maganar tazo karshe,,inah ganin n yanke shawarar Zan kawomiki wacce zata ringa temaka miki,, gurin hidimar gida ke har mah wajan kulawa,dani,,,,cikin farinciki ta tashi zaune tare d cewa,, Alhmdullh,,ai amman my dear nagode,,,, murmushi yayi tare d cewa,,Aa bar saurin godiya ai yiwa kaine,,,,,sai dai fa bawai zatazone a matsayin "Yar aiki bah,,,to idan batazo a matsayin Yar aiki bah a wanne matsayi zatazo,,,, zatazone a matsayin,matar gidan,,kamar Yan d kike,,, ma'ana Ina nufin, Abokiyar zamanki,,,,, what ta fada da karfi tare d mikewa tsaye,,, please Najibullah idan ma wasa kake to ka Dena Dan banaso,,,,Kinga alamar wasa anan ko kin taba ganin nayi Miki irin Wannan wasan,,to da gaske ne aure Zan kara,,,me makon na kawo me aiki ai Kinga gara na kawo wacce zata ringa temaka miki,, amatsayin matar gidan,Kinga hakan zefi Kuma abin d kikeso kenan,,,,,,,,,
In dai akan wannan ne,wlh zanyi duk wani aiki da kaina,,kabar maganar aurennan,,,ai kin makaro maganar aure Babu fashi,,sai anyi insha Allah,,,,,to dama chan kana d ra'ayin Kara aurenka in Dan ba dama kana d ra'ayin,bah tin d nace Zan gyara ai sai ka janye,,,,, murmushi yayi tare d cewa saudah kenan,,ke da kanki kinsan bani d ra'ayin mace biyu kece Nan wacce Kika samin ra'ayin,Dan HK zuwa yanzu Baki d ikon Hana zuciyata abin d takeso,,garama kiyi hakuri ki karbi Abokiyar zamanki hannu bibbiyu,,,,to wlh baka isaba badai aureba ayi mugani amman kasaka wannan aranka Kai da kwanciyar hankali kunyi bye bye,,itama ka sheda Mata HK tashigo tana sani,,,,kiyi duk Abin d kike tinanin zakiyi aurekam Babu fashi bi'izinillah,,,,,ya fada tare d barin gurin,,,,haka kace ko to muzuba mugani ta fada da karfi tare d zubewa a kasa tana kuka,,,,,,,,,,,
Tin dg wannan ranar zamansu ya kara chanzawa,Sam Najibullah bashi d kwanciyar hankali,,mun dun ze shigo gidan to saudah sai tasan Yan d tayi ta Bata ransa kullum cikin masifa take ,,,Dan HK nema yanzu Sam baya dawowa,,gida da wuri,,HK da sassafe ya fice,,,,,,,,
Ban garan saudah Kuwa,, kawayenta sai kara zugata sukeyi,,karta kuskura taraga masa hk idan Amaryar tashigo,,karta kuskura tabarta Tasha iska tayan da da kanta zata gudu da kafafunta,,,da wannan gurguwar shawarar sauda take amfani,,wajan kara hurawa Najibullah wuta,,,,,,,
Yau biki yarage saura sati daya yau Kuma Najibullah ya tashi da kyare gyaren gidah,,,,ta ban garan Amarya aka fara,,duk d bawani gayara yake bukata me yawaba sharace kawai d sabon fenti sai Dan abin d ba'a rasaba,,,,kamar Yan d gidan yake,,,,, babban falone,,Mai dauke d dakuna uku,,acikin kowanne daki, Yana dauke d ,,2 bedroom da karamin falo da ban daki,,,,, sannan kowanne daki Yana da tazara tsakanin sah da Dan uwansa ma'ana ba'a jere suke da junaba,,,,sai wani dakin da yake a gefe da ban dakinsa amatsayin n baki,,,sai kitchen,,da Area Dining,,duk a cikin babban falon gidan,,,,,,to kamar Yan d na sauda yake 2 bedroom da karamin falo HK mah n Amarya yake,,,,,
Tin da ya fadawa saudah cewa yau masu aikin gyaran gida zasuzo ta dinga zazzaga masifa,,becemata komai ba y kyaleta sukaci gaba da aikinsu,,,kar shedai sai jinta yayi ta dauki motar ta ta fice dg gidan,,,,,,,,ko takanta bebibah,,ya cigaba d har kan gabansa,,,,,,
Abin ka da ma'aikata da yawa,,kafin yammah kaf gidan ya dauki haske,,sun fente ko inah gida sai kamshin fenti,,yake sannan yasa,,an kwashe komai na gidan,,,gobe za'a zuba sabbi,,,,,suna gama aiyikansu yayi wanka ya dauki ma kullin motarsa ya fice a gidan,,,,,,
Saudah fitar Nan da tayi Bata zame ko inaba sai gidan,,babbar kawarta,,Hannatu,,tanayin parking ta fito ta shige ciki da kukanta Hannatu na. Zaune a falo da sauri tatare ta Tare da tambayar ko lpia waya rasu,,,,cikin kuka saudah tace wlh gara mutuwa da abin d ke timkaroni,,Wai badai akan maganar aurennan bane akaine mana,,,tozauna zamah sukayi ,, Hannatu tace,,to mekuma ya faru yanzu,,, hawaye ta goge tare d cewa wlh Hannatu inacikin tashin hankali kin masan wani Abu kuwa,,yanzu HK na barosa anata gyaran gida Kinga kenan ga dukkan alamu takusa shigowa,,,,wlh idan hankalina yayi dubu to duka a tashe suke,,,,tsaya ki kwantar d hankalinki,,,Wai mah kinayin duk Abin d mukace miki,,wlh inayi kullum cikin daga masa hankali nake,, amman ko ya nuna ya damu bayayi,,,ke in takaicemiki mah,,ko kulani bayayi sannan yanxu mah ya dena dawowa gidan dawuri hk kafin n tashi a bacci ya fice,,,wlh Hannatu jinake kamar zuciyata tafito Wai dama hk kishi yake,,,,kawata me zanyi kibani shawara,,,,karki damu,,inah d mafita,,,to inah jinki,,,ki kwantar d hankalinki,, sannan maganar dagamasa hankali,, karki sake ki raga musu dg shi har itah,,, sannan,,aikin ki akanta,,ze fara tin ran da aka kawo tah,,kafin ango ya shigo keki fara shiga ki razanata,,,,ke idan ta kama da yimata dukanema kiyi kidai tabbatar d tsoronki ya shiga ranta,,,in dai kinyi shi Yan d y kamata a daren zata koma gidansu,,,idan kuma ta Yi taurinkai to karki ragamata kixamar Mata tashin hankali,,dagashi har itah ta Yan d zataga shima be iyah dakeba balle itah,,in dai Kika rike wannan,,inah me tabbatar Miki farin cikin ki ze dawo,,,Kai kawata nagode kwarai,,naji Dadi shawarar Nan Zan Kuma ai kata fiyema d Yan d Kika fadamin in dai zata koma in da tafito Dan wlh banajin Zan iyah Zama da kishiya,,karki damu saimun korata,, Allah ko kawata,,,sauda tafada tana dry suka tafa,,Nan gidan ta yini sai bayan Isha ta koma gida,,,Nan tazo ta tarar d aikin d akayi Nan bakinciki y kara rufeta,,,Kai tsaye bedroom dinta ta shiga Babu komai a ciki sai mah kamshin fenty da yakeyi tsaki tayi t fito t shiga dayan shi komai na ciki Yana nan ba acireba,,sai kayanta,n amfani d aka debo dg dayan dakin aka dawo dasu nan,,hakan yana nufin ze sake Mata kayan dayan dakin Dana falontane,,tsaki tayi tare d cewa nibaka birgeniba,,,,,chan ta hango wasu haddun akwatina masu Dan karan kyau guda biyar jere da juna,,,karasawa tayi ta Fara dubasu kowacce shake take da Kaya nagani n fada,,,mayar dasu tayi tarufe tana Jan tsaki Tare da cewa,,kayan cutaba,,,,,
Washe gari masu tsara gida sukazo,,zanso kuga Yan d aka tsara gidan ko inah yasha kyau musamman ban garan Amarya,, Najibullah yayi Mata kokari sosai,,Dan komai ya zuba mata,,ya Kuma tsaru sosai,,HK ban garan saudah itama ya gyara Mata ban garanta ,,,HK mah babban falone gidan abin sai wan da yagani,,,,komai n Alfarma,,,,ana Gama kintsa bangaran Amarya ys key yarufe ko inah Dan yasan halin saudah a yanzu Babu Abin d bazata iyah ai katawaba,,,,,,,
Biki yarage saura kwanaki uku,tana kwance cikin kojara,,a dakinta,, Najibullah ya turo kofa ya shigo bakin sa dauke d sallamah,,ko amsawa bayiba balle ya sakaran gaisuwa ko sannu d zuwa,,,guri ya samu ya zauna,,,Yana uwar gidana barka da hutawa,,Nan mah banza tayi masa,,, murmushi yayi tare d cewa uwar gidana bakya jinane ko Baki ganni bah,,,to idan n gankafa saime me zanyi maka kaga malam,Dan Allah kadena takurawa rayuwata,,akan meyene,,idan zance kakeso to katashi ka tafi gurin sakarar da zaka auro amman Ni bani d lokacin ka,,kajiko,,zemafi maka ka tashi kaficemin a daki,,,,,sosai ran Najibullah ya sosu,,sai dai bashi d zabin da ya wuce ya danne zuviyarsa,,, murmushi yayi tare d cewa tuba nakeyi uwar gidana,,Nima dama ba fira nazo muyiba n kawo miki I'V ne ko Zaki,gayyaci,, kawayenki,,da Kuma wasu "Yan kudade ko Zaki bukacesu Kinga dai abunnan ya kusa,, sannan duk Abincin d za'a ci nariga nayi order dinsa,,karki damu d Wannan,,,, tin d ya fara bayani ta kankantar d idonta tana kallonsa zuciyarta fal da masifa,,,Yana yin shiru tace ka gama,,to idan ka Gama ka kwashi tsiyarka katafi Dan bana bukata ai Abin Arziki shi akeyiwa, gayyah amman ba na tsiyaba Dan HK ,bana bukatar tarkacenka,,tana kaiwa nan ta shige bedroom tinta,,ta fada saman bed tasaki kuka mecin Rai,,,,duk d ransa yayi mugun baci d jin kalamanta,, amman hakan besa ya Bari zuciyarsa ta rin jayesaba,,,Kai kawai ya girgiza tare d cewa,, Allah ya kyauta ajiye Mata komai yayi yayi ficewarsa,,,,,,,
Tanajin ficewarsa ta fito d sauri ta daki,,katin gayyatar t fara dubawa wani kuka ta kara saki,,ganin saura kawaniki uku kachan,,Dan ko takan sunan Amarya da Ango. Batabiba itah burinta taga kwana nawa ya rage Kuma tana gani ta Yar da katin tare d lalubar wayanta ,,,ummanta takira tana kuka,,,tana dagawa tace kekuma lpia waya. Mutu,,,ummah Najibullah ne me ya samu Najibullah din Wai aure ze kara,,,mtsss akan ze kara aure shine kike wannan kukan,,,to bariji na fada Miki zemafi ki kwantar d hankalinki,,tin da kome ya faru halinkine yaja Miki,,idan kuka kikayi sanadin d Kika sake dawowa gidannan,,to kinsan meye ze biyo bayan hakan,,,sakarai wacce batasan in da yake yimata ciwobah,,,,Kuma Ni hakan da Najibullah yayi yayimin dede,,,cikin kuka tace ummah kuna nufin kunsan d maganar,,eh munsan komai Dan ya zo ya fada munkuma saka masa Albarka,,, sannan inah me Baki shawara daki nutsu idan kuma kikace zakicigaba d shashancinki to kina gani wata zatazo t kwacemiki miji,,,to zefi Miki mah ki farka dg wannan mummunan mafarkin da kikeyi,,,,idan kuma ba hk bah to yarage ya naki,,,,tana Kai wa Nan ta yanke kiran,,,,,wani saban kuka sauda ta saka me cin Rai tana kara cin Alwashin Babu ragi a tsakaninsu,,,,,,,,,,