E9
*SHU'UMA*
_'Yar mutan zazzau Naanarh M Sha'aban_
*Sadaukarwa ga Yaayana d'an baiwa đ„°*
_Wannan page d'in na ku ne Khadija Shu'uma teamđku ji dad'inkuđđâ„ïž_
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
_Ku sauke arewabooks a playstore kamar yadda ake bud'e account a wattpad haka ake bud'e shi, masu iPhone ku shiga ta website ku bud'e account, book 2 chan zamu koma posting._
Website
http://Arewabooks.com
Kuyi following d'ina.
http://arewabooks.com/u/shaabandaughter01
Book 1
E9
Adam ya kid'ime ya d'ago ya kalli mahaifinnasa jikinsa na rawa, bakinsa na karkarwa ya fara k'ok'arin magana, Baffa ya dakatar dashi da cewa "ba na buk'atar ka ce komai na gama magana, ku tashi ku je ku cigaba da shirin biki, D'alhat ya kama hannun d'an uwannasa suka fita daga bukkar jikinsu duk a sanyaye, tun da suka fito D'alhat yake faman rarrashin Adam, amman ina Adam hankalinsa gabad'aya a tashe yake, ranar wuni sukayi zuciyoyinsu a k'untace, D'alhat kuwa yafi ma Adam d'in damuwa saboda gani yake duk ta dalilinsa d'an uwansa yake cikin k'unci dan da ace bai bijiro da maganar aurensa ba, da Baffa ba zai yi wa Adam d'in auren dole ba, shawara ya yanke a zuciyarsa akan ya janye maganar aurensa dan Baffa ya hak'ura da yi wa Adam auren dole, idan yaso duk lokacin da Adam d'in yake son aure sai su yi tare, da wannan shawarar ya kwanta dan ya san lokacin Baffa ya dad'e da bacci da zuwa zai yi ya sameshi, daga D'alhat har Adam babu wanda ya iya rintsawa ranar, da sassafe D'alhat ya tashi ya tafi gurin Baffa, a tsakar gida ya sami Baffan yana zaune yana shan fura, har k'asa ya tsugunna ya gaisheshi, Baffa ya amsa fuskarsa kunshe da fara'a, zama yayi akan takalminsa, yayi shiru na d'an wasu lokaci kafin ya d'ago ya fara magana "Baffa ina so a fasa aurin aurena, ba na son yin aure yanzu" A daidai lokacin Adam ya fito daga d'aki ya ji abinda D'alhat yace, tsayawa yayi ya kasa motsawa daga inda yake, dan maganar d'an uwansa ba k'aramin dukanshi tayi ba, Baffa cike da mamaki yace "Me ka ke cewa ne? kai fa ka nuna ka na son aure yanzu kuma kace ka janye, anya ka na da hankali kuwa D'alhatu?'',"Na san duk saboda ni ka ke k'ok'arin janye aurenka, ba zan tab'a jin dad'i ace an fasa aurenka duk ta dalilina" Adam ya fad'a tare da k'arasawa inda D'alhat d'in yake zaune, "k'anina nima zan so ace anyi aurenmu tare" D'alhat ya juyo yace "Yayana nasan ba ka son auren da za ayi maka, shiyasa nima zan hak'ura da auren duk lokacin da ka ji ka na son auren ma yi tare" Adam ya zauna tare da kallon Baffa yace "Baffa Ina cike da farin cikin zab'in da ka yi min, na ji dad'i har cikin raina zamuyi aure tare da d'an uwana" Baffa yayi ta shi musu albarka, suka tashi suka shiga shirye-shiryen d'aurin aure.
Wajen k'arfe 12 na rana aka daura auren Adam da D'alhat, haka su ka cigaba da yin shagulgulan bikin, gabad'aya garin kamar ya hargitse da yin biki kamshi ne kawai yake tashi ta ko ina a fad'in garin, da daddare aka kai amare gidajensu da Baffa ya gina musu.
Haka suka cigaba da yin rayuwar sau cikin farin ciki da annashuwa, Adam ya koma makaranta ya bar Safaraâu bayan yayi mata alkâawarin duk sati zai dinga zuwa ya koma ranar litinin da asuba, sannan ta yarda amman da ta nuna sam ta kâi yarda ya tafi.
Kwanci tashi ba wuya wajen Allah, Ladidi ta fara laulayin ciki ita da Safara, da yake ita Safara cikinnata mai wahala ne duk abinda ta ci sai ta yi amanshi, dan haka Adam ya tattaro ya dawo gida da zummar idan ta ji saukâi sai ya koma, duk gari ya karade da maganar cikinsu Ladidi, wasu har lissafi suke yi sauran wata nawa su haihu, dan sun san zaâa sha shagali kâila ma har kyaututtuka mai gari zai yi saboda Ladidi ita kadâai ce âyarsa kuma yana kâaunarta sosai. Adam sai da yayi wata biyu a gida ya tabbatar Safara ta fara samun saukâi sannan ya koma makaranta.
Lokacin da cikin ya cika wata tara da âyan kwanaki aka shiga shirye-shiryen bikin haihuwarsu, A ranar wata Alhamis Ladidi ta haifi samtalelen dâanta mai kama da ubansa a gida, da yake haihuwar ta zo mata da saukâi murna wajen Adam da Dalhat abin baâa magana, wuni aka yi ranar ana kidâan garaya a garin, kamar ranar ne suna.
Washe gari wajen kâarfe 10 na safe, Safara ita ma ta haifi dâanta namiji sak kamarsa dâaya da Adam, Dalhat ya rasa inda zai sanya ransu shi da Adam, Ladidi ma tayi murna sosai da ta ji Sarafa ita ma namiji ta haifa.
Ranar suna anyi bâarin naira yara sun ci sunan kakanninsu, Dâan Dâalhat aka saka masa sunan mai gari Abubakar suna ce masa Baba, inda Dâan Adam aka saka masa sunan Baffa Nazeer ake ce masa Papa ko Baffa, yaran sun ta so cikin gata da soyayyar iyayensu, gashi kansu a hadâe, sunyi koyi da iyayensu dan komai tare ake musu, kullum yaran suna gidan mai gari sai da daddare ake dawo da su.
Lokacin da su Nazeer suka cika shekara tara Adam ya saka su a boko da arabiyya, dan yana da burin ya ga yaran sun jikâu da karatun boko da arabiyya, Dalhat yayi farin ciki sosai, dan kuwa shima yana da burin ya ga dâansa yana zuwa makarantar boko dan kuwa yana ganin amfanin da take dashi tunda ga dâansa babu abinda bai iya ba rubutu da karatun nasara duk ya iya, Abubakar suna da shekara goma su Ladidi ta sami ciki, a wannan karan ta sha bakâar wahala domin kuwa har cikin ya cika watan haihuwarsa yana wahalar da ita, ranar wata Lahadi ta haihu âyarta mace zankadâedâiya mai kama da mamanta, tun a lokacin mai gari ya rokâi Dâalhat alfarma akan ya saka sunan mahaifiyarsa âKhadijaâ Dâalhat duk da cewa ya so ya saka sunan Inna, amman tunda har mai gari da kanshi ya rokâi alfarmar nan ba zai tabâa kâi ba, dan haka ya amince kuma ya radâawa yarinyar suna Khadija, Ladidi ta ji dadâi sosai dan kuwa tana tsananin kâaunar kakarta sai kuma ta mutu a lokacin da take bukatarta sai gashi mijinta ya faranta mata rai ta ji dadâi sosai, ranar suna anyi suna an watse cike da farin ciki, mai gari ya raba kyaututtuka da dama, dan rago da shanu biyu aka yanka, lokacin da Khadija ta cika wata bakwai Adam ya kammala makarantarsa ta gaba da sakandari inda ya karanci Medicine, yana kâokâarin hadâa kayansa ya dawo kâauye wani abokinsa ya nemar masa aiki a wani babban Asibiti da ke garin Kaduna, Adam yayi murna sosai kuma ya ji dadâi, a ranar ya je gida yake sanarwa Baffa da Inna ya samu aiki, Kuma idan zai koma zai tafi da Safara idan yaso ya kama musu gida a chan, da Inna ta so ta kâi Baffa ya hanata, haka ta hakâura amman kuma da sharadâin ba za su tafi da Nazeer ba, Adam ya amince da sharadâinta, lokacin da Dâalhat ya ji zancen Adam zai koma da iyalinsa Birni ya ji ba dadâi amman da ya ji ance banda Nazeer zasu koma sai ya ji dadâi sosai dan yana son Nazeer sosai.
Haka Safara ta hadâa kayanta bayan ta je ta yi sallama da iyayenta ta biya ta yi wa Ladidi sallama washegari suka dâauki hanyar Kaduna, suna isa da yake Adam ya bugawa Abokinsa waya ya fadâa masa yana son gida na haya, amman mara tsada, a ranar ya nemo musu gida ya biya, gidan kuwa yayi kyau, Adam sai ya ba gidan yake, Safara ma ta ga kyan gidan sosai.
Bayan Shekara dâaya
Khadija ta girma sosai, dan idan kika ganta ma, aka ce miki shakararta dâaya da âyan watanni ba zaâa yarda ba, dan kuwa zaâayi tunanin shekararta uku, tun a wannan lokacin Khadija ta fara rashin ji, idan Mamanta tayi girki ta rufeshi, zata dâibi kâasa ta zuba a ciki, ko kuma idan miya ce ta dâauki gishiri duk yawanshi haka zata zuyeshi, babu irin dukan da bata sha ba gurin mahaifiyarta, amman kullum kamar tinzirata ake, bata dai na wa ko yaushe da irin tsiyar da zatayi, akwai wata rana Nazeer da Adam suna bacci, ta dâauki dakakken yaji ta jikâa a kofi ta zuba musu a fuska, sun sha azaba sosai, ita kuma ranar ta ci dukan tsiya dan kuwa mahaifiyarta da carb ita zaneta, Abbakar ma bayan sun wanke idonsu yayi mata dukan tsiya, ta sha kuka ta fita waje, gidan mai gari ta je ta kai kâararsu, har gida ya zo da ita, yana ta fadâa akan me zaâa daketa, su ka fadâa masa abinda ta yi, anan fa ya fara masifa ai ba wani abu tayi mai muni ba, da za su yi mata wannan dukan mutuwa, juyawa yayi ya koma da ita sai da tayi sati dâaya a gidan sannan ta addabeshi da kuka ita gida zata koma gurin Innarta, haka ya dawo da ita bayan ya kora musu gargadâin kar su sake dukanta.
Suna shiga gida, ta ga Nazeer yana cin abinci ta je ta zauna a cikin kwanon abincin, Inna ta fisgota ta murdâe mata kunne ta rankwasheta, âke wato kunnan kâashi ne da ke, kin na so ki zama shaidâaniya ne, kullum cikin sakani magana kike, to tunda kin zama mai kunnan kâashi ni kuma ba zan fasa dukan ki ba dan uwarkiâ juyawa tayi tana kallon Nazeer wanda ya dâaure fuska yana yi wa Khadija kallon kâiyayya tace âyi hakâuri ka ji yarona ka je ka zuba wani abin cinâ mikâewa yayi tare da cewa âto Innaâ Kullum Khadija tantirancinta kâara cigaba yake, a lokacin da Khadija ta kai shekara goma, su Abbakar suka gama makarantar gaba da sakandari, inda Nazeer ya karanci Accounting Abubakar kuma ya karanci Law, Adam ya samar musu aiki a garin Kaduna, suka koma chan anan ne Nazeer ya hadâu da abokai bâata gari suka koya masa shaye-shaye da kuma neman mata, har ya kai ga tun yanayi a bâoye iyayensa suka sani, ransu ya bâaci sosai ganin dâannasu kâwalli dâaya yana kâokâarin zama tantiri, wannan dalilin ne yasa Adam ya yanke shawarar hadâa Nazeer da Khadija aure ko zasu samu ya nutsu.
A cikin satin Adam ya je kâauye ya sanar da danginnasa, akan hadâin da yake so ayi musu, Dâalhat ya ji dadâi dan kuwa daman yana da niyyar yi wa Khadija aure dan kuwa wannan maganganun da take ja masa a gari, yana ganin idan yayi mata auren zata nutsu duk da kuwa kâarancin shekarunta, Dâalhat ya nunawa dâan uwannasa amincewarsa dâari bisa dâari, dan kuwa ce masa yayi idan da hali ma a dâaura auren a yau idan yaso gobe a kai amarya dâakinta, Adam ya ji dadâi sosai yadda dâan uwannasa ya amince da bukâatarsa, kamar yadda Dâalhat ya bukâata a ranar aka dâaura aure, da yake yanxu Adam yana samun kudâi sosai, shine babbar likita a garin Kaduna, ya gina babban gidansa, Khadija kuwa tunda ta ji an dâaura mata aure da Nazeer take fushi dan ko abinci ta kâi ci, zaune suke ita da Innarta akan taburma âwai Inna ni da wannan mugun aka hadâa ni aure, ni gaskia ba na sonshiâ Juyowa tayi tana kallonta tayi dariya âau bakya sonsa, to ka da Allah yasa ki so sa mana, kuma wallahi zan kirasa na fadâa masa idan ki ka yi abinda ba daidai ba ya ci ubanki, ya soma min ke har sai kin yi hankaliâ Khadija tace âChab ni dâin zai duka? Inna kin manta wacece ni, wallahi ni Khadija na ci dubu, tunda na addabi kowa to shima addabarsa zanyi, shi da kansa ma ai kin ji sunan da yake kirana kuma âyan gari suke kirana dashi su ma SHUâUMAâ Inna tace âyaro bai san wuta ba sai ya taka, tunda ke SHUâUMA ce to ni kuma zan sa shi ya zama SHUâUMI sai mu ga kâaryar iskanciâ Daria Khadija tayi ta shige dâakintaâ Inna ta bi ta da kallo tana yi mata adduâa Allah ya shiryeta.
Washe gari da sassafe aka hadâa kayan Khadija ta je ta yi wa kakanninta sallama mai gari har da kuka, ita ma Khadija kukan ta shiga yi, haka Adam ya kama hannunta suka tafi zuwa Tasha suna isa suka ga ana lodin motar Kaduna suka shiga, driver ya ja mota suka tafi, awa hudâu sukayi a hanya kafin suka isa garin Kaduna, suka sauka daga motar bayan ya biyashi kudâinsa, adaidaita suka nema inda ya kai su har kâofar gida.
Shiga gidan suka yi, hannun Khadija yana cikin na Adam, a babban falon gidan suka tarar da su, da yake daman sun san maganar auren Nazeer ne ya kai shi kâauye amman ba su san da Khadija zaâa hadâa shi ba, âSannu da zuwa yarinyataâ Khadija ta tafi da gudu ta rumgume Safara tana fadâin âMommyna ta birniâ Abubakar yace âke kin shakâe mata wuya karki illata mana Mummyâ dâagowa tayi ta maka masa uwar harara har da murgudâa baki, âkan uba ni za ki yi wa rashin kunya, billahillazi tattaka ki zanyi ananâ Abba yace âkul karka kuskura Abbakarâ Komar da kallonsa yayi kan Nazeer wanda ya dukâufa yana daddana waya âNazeer ga matarka nan, na ba ka amana, ba na son na ji ta kawo min kâararka, ka kula da ita, za ku fara zama a gidannan a wanchan part dâin kafin na siya muku wani gidanâ Dâagowa Nazeer yayi yana kallon Abba yace âAbba ka na nufin Khadija ce matata?â Abba yace âkwarai kumaâ Nazeer yace âAbba! Khadija fa bata da kirki wannan yarinyar SHUâUMA ce, kuma bata da wasu shekaru bata dadâe da cika shekara sha dâaya baâ Abba yace âko da shekararta Tara ne, ita na zabâa maka idan kuma ba za ka bi umarnina ba, sai ka je ka nemi wani uban amman ba ni baâ Nazeer ya kalli Khadija suka hadâa ido ta kanne masa ido dâaya tana Murmushin da ita kadâai ta san maâanarsa. Abbakar yace âAbba amman bai kamata a aurawa dâan uwana wacce baya so ba, tunda yace akwai wacce yake son aura Fanan da an barsa ya auretaâ Abba yace âai na san ya fadâa min yana da zabâinsa amman ni batayi min ba, Khadija na ga tayi min kuma ita na ga damar aura masaâ Nazeer yace âto shikenan Abbaâ yayi maganar tare da shigewa dâakinsa, Mummy tacewa ta tashi ta nuna mata part dâinta, tashi ta yi suka shiga part dâin Mummy ta nuna mata ta fito ta Barta a ciki zatayi wanka.
A cikin satin gomnati ta rabawa manyan likitoci kudâi masu tsoka a ciki kuwa har da Abba, wani babban gida ya siyawa Nazeer da Abbakar sun hadâu gidajen sosai, shima Abba ya siyi mota, da yake akwai dâan gyare-gyaren da zaâa yi wa gidan dan haka ba su koma ba, sai da aka gama, a cikin satin da za su koma aka yi bikin Abbakar da Fatima âyar abokin Abba, sun sha shagali sosai dan a Kaduna aka yi biki su mai gari sun zo.
Khadija da ta ga sun koma gida daga ita sai Nazeer ta ga irin yadda yake neman mata baya jin kunyar shigo da mata har gidan aurenta, dan haka ta shiga Shuka masa rashin mutunci kullum da irin shuâumancin da take yi masa shi da âyan matansa.
Wannan shine takaitaccen labarin Khadija da Nazeer.
Cigaba labarin....
*#Share*