BAMBANCI AƘIDA

Chapter 23

by @queennasmerh08

🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐

    ( ƙaddarar Soyayya )


Based on true life story


Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

        &

Nana M Sha'aban


*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*


_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._


*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*


WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.


BAMBANCIN AƘIDA IS NOW FREE SABODA SOYAYYAR DA KU KE MA LITTAFIN KUN CI KYAUTAR BAMBANCIN AƘIDA.


Mu Haɗu a littafanmu - *ZUCIYA* , da kuma *NAWA ƁANGAREN* Wanda a yanzu haka yana chan arewabooks ya fara sauka, ku sauke apps ɗin a playstore domin samun naku, kada ku bari a barku a baya.


*CHAPTER 23*


Dariya Abba ya shiga yi har da rik’e ciki magana yake son yi amman irin yadda Mubeen d’in yake hararar shi ne ya k’i bashi damar yayi, Mubeen d’in ya cigaba da cewa “kayi dariya da kyau, kaf ‘yammatan garin nan na fad’a maka na fi k’arfinsu wallahi” Abba yace “ hmmm dama ai kai. Sai matan Nigeria", “mtswwwww "wani dogon tsaki Mubeen yayi ya ce “ba Nigeria ba wallahi dutsi" , Abba ya ce “ka manta igiya ce ba dutsi ba ", tashi Mubeen yayi tare da cewa “haka zaka ƙare gurin tsinkar fure", dariya Abba yayi ya ce “ɗan girman kai kawai ", “girman kai dama ce mutum yayi in ya cika" Mubeen ya faɗa yana wucewa.


-----------------------------------

Wayar da ke kunnenshi ya gyara ma zama, sannan ya gaɗa kai “to Abbu, har da su Mehreen ko Shaheed kawai zan ɗauko? " Mateen ya tambaya, daga ɗayan ɓangaren Abbu yace “ a'a Shaheed kawai ai shi karatu zai yi garinku, su Mehreen kuma ba hutu suke yi ba", Mateen da duk ya ji ba daɗi ya ce “To Abbu" katse wayar Abbu yayi, yayin da Mateen ki tunanin yadda zasu yi da Ummie, dan Autanta bata haɗa shi da komai ba sai.



A ɓangaren Ummu kuwa tun da tayi waya da Abbu minti talatin da suka wuce ta kasa sukuni, ita ba za ta iya barin Shaheed ya je ko da Haɗeja ce, ballanta har Lagos, amma ya zata yi Abbu ya ci ƙarfinta. Hawaye suka biyo kuncinta, Mehreen dake zaune gefenta ta kalle ta ta ce “Haba Ummu miyasa kike tada hankalinki, ba abunda zai sa mu Shaheed a can, can ɗin ai kamar gida ne gare shi, kin san dai Yaya Mateen bazai wulaƙanta shi ba, kamar ɗa zai ɗauke shi ", runtse ido Ummu tayi sannan ta buɗe idon ta ce “ba hannun da zai je nake tsoro ba, bana so ne nayi nesa da shi", murmushi Mehreen tayi ta ce “Ummu ko ba yau ba zai nisance ki, ko ya mutu, ko ya bar gidanki kamar yaya Mateen", numfashi ta sauke ta ce “Allah ya miki albarka Mehreen", murmushi tayi ta ce “Ameen Ummuna ".



---------------------------


Salloli kawai aka sallame a masallatai Aimar ya shiga wanka ko haske bai gama fitowa ba, cikin sanyin sadiyar nan ya shirya tsaf cikin yadi fari, gidansu Zainab ya nufa, ƙofar gidansu ya tsaya, sannan ya kira ta, amma har yanzu wayarta kashe take. Kamar an jefo ta fito waje, lokacin agogo ya nuna ƙarfe 7:00, zata je siyo Ƙosai ta ci, “Zainab! "ya ambaci sunanta cikin rarraunar zuciya, Rassss! Gabanta ya faɗi jin muryar abun begenta a wannan lokacin da bata yi tsammani ba, “ki juyo nine, sallama zan miki", da ƙarfi ta juyo kamar wadda aka finciko ta ce “sallama(ban kwana) bata kamaci masoya kamar mu ba ", nan take hawaye suka ciko taf a idon Aimar yana cin wani mugun zafi, zuciyarshi kam ƙuna take yi kamar an zuba mishi garwasu a kai, cikin ƙarfin hali ya ce “Zainab na so a ce ƙaddara bata zaɓi ta mana haka ba da bazan furta kalmomin ban kwana gare ki ba, amma yanzu kiyi haƙuri alaƙarmu ta zo ƙarshe ", jiri ta fara gani, da sauri ta dafe bangon gidansu ganin zata faɗi ta ce “kayi haƙuri kar ka yiwa soyayyar mu illa", “Zainab ba ni ne nayi mata illa ba, mahaifinki ne ya datse ta ".


Yana faɗin haka ya juya zai wuce, taku huɗu kawai yayi, Zainab da ke haki kamar wadda tayi gudu ta ce “Hubbynah!", bai juyo ba, kuma bai fasa tafiya ba, da ƙarfi ta ce “Abdul-rahman! ", cak ya ji wani abu ya tsaya mishi a zuciya, dole ya tsaya, “kar ka bari ayi mana katangar ƙarfe tsakaninmu, ka sani kuma kai shaida ne, numfashina yana buguwa ne tare da taimakon soyayyarka, idan na rasa soyayyar ka Abban Khaleed bazan rayu ba", “Zaki rayu Zainab " ya faɗa ba tare da ya juyo ba. “ ina ganin Bala'in da yake tunkaro rayuwata a rashinka, kar ka juya min baya", yana jin zuciyar shi na mishi suya domin hawayen Zainab sun fi ruwan dalma zafi guri Aimar, runtse idonshi yayi gam, hawaye na kwaranyo ya ce “Hawayenki azaba ce mai tsanani gare ni, kiyi min rai Zainab ki adana min su ", numfashi ta sauke tana cije leɓenta na ƙasa tace “ka kasance dani har abada shi ne makarin hawayen a", taku ya ci gaba da yi yana cewa “kiyi haƙuri Zainab ƙaddara bata zaɓa mana kasancewa tare ba ", “Aimarrrrrr!" ta kira sunanshi da ƙarfi tana durƙushewa ƙasa, bai juyo ba kuma bai tsaya ba, haka ya wuce yana maimata kalma ɗaya “kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, Zainab kiyi haƙuri " har ya ɓace ma ganinta bata fasa kiran sunanshi ba, shi ma bai fasa cewa tayi haƙuri.



TO MASU KARATUN BAMBANCIN AƘIDA KUN GA YADDA BAMBANCIN AƘIDA YA YANKE ALAƘAR MASOYA GUDA BIYU.


MU JE ZUWA DOMIN SANIN YADDA KWAMACALAR ZATA KAYA.


Anan zamu dasa aya.......✍🏽


*#Share*


*Aminan Juna❤️🥰*