PAGE__2to3
by @abbienah
[8/7/2021, 11:42 AM] Zinariya: π _page 2_π
*SAI DAKE!*π«
_written by_
*BILLY S FARIπ*
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*π‘
ππππ
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shiga yimasa fad'a sosai akan yadena wasa da sallah kuma yadena miyagun halayensa da yakeyi bata so, tun tana yimasa fad'an da zafi zafi har takoma yimasa nasihar da zata kashe masa jiki, a zahiri kam jikin Ra'ees yayi sanyi sosai amma azuciyarsa babu abunda yakeyi sai saqawa da warwarewar wajen da yake son zuwa chasu shida abokanansa a can cikin wani qauye da ake kira ambursa, ganin yanda jikinsa yayi sanyi ne yasa momy qarqare nasiharta da cewa "Ra'ees ba son kane bana yiba kamar yanda akoda yaushe mahaifinka ke qoqarin nuna maka, kawai so nake ka zamo yaron kirki tunda kaine babba agidan nan ta yanda qannenka zasu dinga koyi dakai."
Hannunta ta d'ora saman sumarsa da tayi wani tozo daga tsakiya tana d'an janta sannan taci gaba da cewa, "kaga wannan askin na banzar na fad'a maka bana son sa ka dena yi amma kaqi, idan kabari raina ya soma b'aci akansa to da kaina zansa almakashi na ciccire maka shi gaba d'aya, don haka tun wuri kaje ka gyaresa idan kana so mu zauna lafiya dakai,"
"In Sha ALLAH momy zan gyara, kuma zanje aragemun sumar indai hakan zai faranta maki."
"To da dai yafi maka, amma ace yaro girma yakeyi sam babu hankali atattare dashi, ni da nake fatar a wannan shekarar ace ka samawa su Easha da Abbie aunty, zuwa wata shekarar sai dai a ganni da d'an jikallena a hannu."
Sinne kansa yayi qasa yana d'an murmushi had'e da sosa qeyar kansa ba tare da yace komai ba, murmushi itama tayi tare da d'auke kanta gefe tana qwallawa mai aikinta mama karime kira, cikin sauri 'yar dattijuwar matar da bazata girmewa momy ba tafito ta wata qofa dake acan gefen falon ta zube agabanta tana fad'in.
"Gani ranki shi dad'e barka da rana." ta fad'a cike da girmamawa kanta sunkuye a qasa.
"Yawwa mama karime sannu da aiki, nace aje akawowa Ra'ees abinci kin ganshi nan ko karyawa inaji beyi ba."
'Dago kai mama karime tayi tadubi Ra'ees cike da barkwanci tace,
"Ashsha na Alhaji, lafiya ka kai wannan lokaci bakasa abinci abakinka ba?."
'Dago kai yayi suka had'a idanuwa da ita ya b'alla mata wata iriyar harara da tasa bata san lokacin da tayi saurin miqewa tabar wajen tana fad'in, "To hajia angama"
Momy da tana kallon abun da yafaru tsakanin Ra'ees d'in da ita tayi murmushi har haqoranta na bayyana had'e da cewa,
"Ka ganka Ra'ees ALLAH ya shirye ka, wai har yaushe ne zaka dena yiwa mama karime haka?, fisabilillahi ina laifin wanda yakula dakai da har zaka zabgawa tsohuwar mutane harara haka?, Kadena gaskiya ni sam bana son wannan baqin halin da kakeyi"
"Yi haquri momy, ALLAH tsohuwar nan tafiye shishshigi da iyayi kuma ni bana son haka shiyasa kike ganin bama jituwa da ita"
Ra'ees ya fad'a had'e da miqewa ya nufi kan dining inda ya hango mama karime na jere masa abincin," tana ganin ya kusa qarasowa tabar wajen jiki na rawa,
Momy dake kallonsu tace
"Oh mama karime wannan rawr jiki haka na meye? ki jeki sashensa ki fiddo da breakfast d'in da aka kaimasa d'azun don yana can yanda aka kaisa"
"To hajia" mama karime tace tare da barin sashen cikin hanzari don taqi jinin walaqanci irin na Ra'ees,
Ya jima zaune a kan dining yana latsar wayarsa kafin ya bud'e kulolin ya zuba abunda yake so ya fara ci hankali kwance, baifi mintuna biyar da farawa ba ya ture abincin gefe sannan ya miqe ya nufi d'akin sa.
"Ra'ees!" Yaji momy takira sunansa tana kallon abincin daya ture dake kan dining.
"Na'am momy" ya amsa mata yana cigaba da chart da abokinsa Sk da zasuje wajen casun su atare yana mai qoqarin dawowa cikin falon.
"Har kayi me?"
"Naqoshi mom" ya amsa mata a taqaice batare data d'ago kansa ba, kin bata sake cewa dashi komai ba yasa ya juyawarsa yabar falon ita kuma taci gaba da kallon wani american film da take kallo a tashar zee cenima,
Daidai zai shiga qofar d'akinsa yaci karo da Easha tafito riqe da towel d'in da tayi masa goge goge zata shanya a saman d'an corridor d'in dake sadaka da sashen nasa dana momy,
"Thanks Easha" ya fad'a yana yatsine fuska ba tare daya kalli inda take ba balle yaji amsar da zata basa ya shige abinsa.
'Yar harararsa tayi kamar zatayi kuka don ta tsani wannan gyaran d'akin da yake sata, wani kallon jin haushi ta bisa dashi had'e da jan guntun tsaki tana fad'in.
"Yasin zama ka dena ne, wlh bari dady ya dawo ALLAH boarding school zance a maidani, haka kurum kullum mutum baya da aiki sai sakani yimasa gyaran d'aki Sai kace wata matarsa, wlh ALLAH ni nagaji bazan iya ba."
Haka tayita surutunta har ta qaraso sashen na momy tana cigaba da mitar had'e da turo baki gaba.
Inda sabo momy ta saba da jin hakan aduk lokacin da Ra'ees d'in ya sata gyaran d'aki don haka ko yanzu da takeyi sai dai ta bita da addu'ar ALLAH ya shiryata ya rabata da wahala ba tare data tanka taba.
A b'angaren Ra'ees kuwa yana shiga d'akinsa ya fad'a toilet yayo wanka da sabulayye masu matuqar qamshi da tsada, gaba d'aya sai da yabi lungu da saqo na jikinsa ya wankesa sosai kai kace wata macce ne, don in dai wajen iya gayu da qwalisa ne to dole a kirasa da lamba d'aya, kusan mintuna ashirin da biyar ya d'auka kafin ya fito saye da rigar wanka da towel riqe a hannunsa sai faman qyalli fatar jikinsa keyi, don kuwa shi ba fari bane sosai kamar 'yan uwansa haka kuma ba zaka kirasa da baqi ko wankan tarwad'a ba, gaba d'aya ya d'ara kalolin haske kad'an, yanayin hasken fatarsa mai kyaune dake matuqar d'aukar hankalin 'yan mata, wanda shiyasa akoda yaushe suke bibiyarsa shi kuma yana yarfasu son ransa,
Qarasowa yayi agaban madubin dake cikin d'akin ya goge sumar kansa data sidebars d'insa sosai sannan yabi gaba d'aya sauran jikinsa ya goge ya shafesa da dad'ad'an mayukka masu matuqar qamshi da tsada, taje sumar kansa yayi data sidebars d'insa ya shafesu da kalolin mayukkan da yake gyaransu, nan take suka fara sheqi da wani qyalli mai d'aukar hankali,
Sosai ya qurawa kansa idanuwa ta cikin madubin had'e dayin wani shaqiyin murmushi don ko ba'a fad'aba shi da kansa yasan yayi kyau sosai tun kafin ya ida shiryawa, wardrobe din kayansa ya bud'a ya ciro wasu qananan kaya riga da wando masu kyau da tsada sannan ya bud'e wani gefe duk cikin wadrobe d'in ya ciro belt da p-cap wani wajen naga ya sake jawowa inda takalummansa ke jere ya ciro taki d'aya qirar canvas, sannan ya sake bud'e wani gefen ya d'auko agogo da wani zobe mai masifar kyau duk ya ajiye akan gadon.
Ahankali ya shiga shirya kansa yana rera d'aya daga cikin waqoqin devido har ya kammala shiryawa tsaf, kallo d'aya zaka yimasa yatafi da imaninka saboda kyan daya zuba, yanda yayi masifar had'uwa kad'ai ya isa yasa kagane hutu da jin dad'i sun zauna sosai a jikinsa, wayoyinsa guda biyu qirar iPhone da Samsung dake ajiye a gefena bedside ya d'auka tare da makullan motarsa ya nufi qofar fita sashen nasa, seda ya kulle ko ina sannan ya nufi harabar gidan inda ake ajiye motoci ya fiddo d'aya daga ciki qirar BMW brown colour tasha wanki har tagaji sai wani sheqi takeyi, ba tare daya jira wani abuba yaja motar da sauri mai gadi ya hangame masa tangamemen gate d'in ya fice aguje qarar sautin sipikun da yasa music acikin motar na tashi, aguje yake gudu kan titin batare daya damu dabin qa'idojin tuqin ba har ya isa bakin qofar wani gida, oda d'aya yayi kafin ya maimaita saiga abokin nasa Sk yafito daga cikin gidan shima cikin tasa shigar irin tasa da alama dama tun d'azu shirye yake shi kad'ai yake jira, bud'e motar yayi ta gefensa ya zauna had'e da miqawa Ra'ees hannu suka kashe Yana fad'in
"Shege R 3fulS" da yake haka gaba d'aya friends d'insa ke kiransa tun a secondary school shine fa sai sunan ya bisa har yanzu suke kiransa dashi, cikin shaqiyanci yaci gaba da cewa,
"Kaga yanda kayi wani irin masifar kyau kuwa? Alqur'an ni kaina ka cijeni mutumen balle babe's d'inka"
"ALLAH Sk!" Ra'ees ya fad'a tare da bawa motar wuta yana jin wani irin feeling akansa.
"Haba R 3fulS ai kasan babu qarya tsakaninmu, dole ma yau ka kashe wasu 'yan matan da kalar had'uwarka"
Saida Ra'ees yayi murmushi sannan ya jawo wani d'an box dake jikin motar ya ciro kud'i aciki da shi kansa baisan ko nawa bane ya cillawa Sk yana fad'in, "ga tukuicin ka man kawai ka raqashe kaji dad'inka yau da 'yan matanka"
Wani ihu Sk ya saki cikin jin dad'i ya cigaba da kod'asa yana dariyar shaqiyanci. Sk wato Saleem kamal abokin Ra'ees ne tun na yarinta shiyasa yasan halinsa da yanda zai lashi arziqi sosai a qarqashinsa, duk wani iskanci da Ra'ees keyi shi yake sake ingizasa duk da dai abun haline zanen dutsi.
Hanyar qauyen ambursa suka d'auka suna tafe suna shan kid'a har suka isa, adai dai kwanar da zasu d'auke wata kyakkyawar yarinya da bazata wuce shekaru goma sha hud'u ba ta gitta masu a gaban motar sanadiyar gudun da takeyi wata tsohuwa ta biyota riqe da icce da alamu laifi tayi mata, wani irin wawan burki Ra'ees yaja had'e da runtse idanuwansa jin ya bugi wani abu ba tare daya ankara ba wanda ko shakka babu yasan bazai wuce yarinyar nan ba ko kuma tsohuwar da ke biye da ita aguje.
A fusace ya fito cikin motar bayan ya taka burki shi da Sk da ransa yayi matuqar b'aci, tsohuwarce suka gani kwance a qasa ta dafe qafarta da alama itace ta bugu sosai ita kuma yarinyar na gefe ta zaro idanuwa kamar mai jiran ar taruga da gudu,
Cike da jin haushi Ra'ees ya saki wani irin tsaki had'e da komawa cikin mota ya d'auko kud'i yazo ya jefawa tsohuwar da tun d'azu take qoqarin tashi amma ta kasa yana fad'in.
"Sk jayemun ita a gefe wlh ko na takata, qauyawan banza da wofi kawai" ya qarasa maganar had'e da juyawarsa zai shiga motar, aza hannunsa ga margin gambun motar kenan yaji cikin wata 'yar qaramar murya ana fad'in,
"Kaine banza kuma kaine wofi da bakasan kimar d'an Adam ba, taya zaka kid'emun gwaggona kuma ka kirata da baqauya har da cewa zaka takata da mota, ka takata halama anfad'a maka ita akuya ce ko saniya ko anfad'a maka cewa ita bijimi ce da zakace hakan, to aradun ALLAH baka isa ba, mu ba ruwanmu da birninka in kaji mata ciwo sai ka kaita assibiti"
Duk wud'annan maganganun da yarinyar da itace silar kad'e gwaggon tata keyi yana tsayensa yana sauraronta ba tare da ko motsawa yayi ba daga inda yake, jin wani b'acin rai yayi ya taso masa wai yau kamar shi 'yar qaramar yarinya kuma baqauya ke gaigayawa maganganu son ranta, tabbas dole ya hukuntata don ba qaramin b'acin rai ta saka saba, juyowar da zaiyi kawai sai yaga ta watso masa kud'in a fuska tana fad'in,
"Ga tsiyarka nan bama so, mu ba matsiyata bane." sannan ta nufi inda Sk ya maida gwaggon da azabar ciwon da qafar keyi mata tasa ta kasa tsaida yarinyar akan abunda takeyi, duk da kuwa tasan wanda tayiwa ba barin bashi yake ba, don tsaf ta gane yaron d'an gidan SS Sada ne.
Ganin yanda yarinyar ta watsawa Ra'ees kud'i a fuska cikin ko oho yasa Sk waro idanuwa tare da zagayowa inda yake tsaye qwayar idanuwansa sunyi jajir sun sauya daga launin farare zuwa jajaye saboda tsananin b'acin rai, riqosa Sk yayi yana fad'in,
"Sorry man, qaramar yarinya ce ita, karka biye mata ba tada hankali ko kad'an kai ka sani, pls don ALLAH ka qyalesu.." ya qarasa maganar tare da bud'e masa motar yana qoqarin turasa ciki, wata irin juyowa Ra'ees yayi a fusace idanuwansa ko gani ba yayi ya nufi inda yarinyar ke duqe tana qoqarin taimakawa 'yar dattijuwar ta tashi yasa hannu ya fincikota da qarfi tare da d'aga hannu zai wanka mata mari tayi saurin rufe idanuwanta tana fad'in.
"Wayyo ALLAH gwaggo na shiga uku"
Kamar wanda aka dakatar daga marin da yayi niyar yimata sai kawai Sk yaga ya sunkuceta ya nufi wajen motar ya bud'e boot d'in ya jefata aciki, bai wani b'ata lokaci ba ya fad'a cikin motar ya tayar aguje yabar wajen yana jin ransa nayi masa quna,
Dafe kai Sk yayi don ya tabbata ba qaramin rashin mutunci Ra'ees zai yiwa yarinyar ba tunda har ta shiga gonarsa, juyowa yayi ya kalli 'yar dattijuwar dake kuka tana fad'i,
"Wayyo ALLAH na na shiga uku da 'yar marainiyar ALLAH, don ALLAH kabashi haquri kada ya cutar da ita, batada kowa a duniya saini don ALLAH kuji tausayinta." Cikin jin haushi yace,
"Dallah tsohuwa kirufamana baki, da kunsan da hakan kuka kasa tsawatar ma yaranku akan shiga hanyar 'ya'yan manya, kuka barsu suna faman 'yar banzar rashin kunya da tsiwa agari?, To wlh ni babu abunda zan iya kawai kujira koma me zai yimata yayi tunda ku kuka jawo"
Yana kaiwa nan yaja tsaki had'e da barin wajen, fiddo wayarsa yayi cikin aljihu ya shiga kiran lambar Ra'ees gashi tana ringing amma yaqi d'agawa, ya kirasa yafi a qirga amma bai d'aga ba dole ya haqura ya nemi mashin ya haye shima yabar wajen cike da jin haushi da takaicin abunda ya faru,
Gwaggo kuwa alamu sun nuna tasamu matsala a qafa don haka kasa tashi tayi saida wani mai shago dake can gefe yana kallon duk abunda yafaru yazo ya tsince kud'in da yarinyar ta watsawa Ra'ees a fuska sannan ya kira wasu yace su kama masa gwaggo dake faman reren kuka suka kaita gidanta don ba wani nisa bane tsakaninta da wurin da abun ya faru, bayan sun kaita ne mutumen ya ajiye mata kud'ad'en gefenta yana fad'in.
"Gwaggo bari naje na kulle shagona sai na samo maki Wanda zai duba maki qafar don naga tafara kumbura"
"A'a habule! Ni ba wannan ne damuwa taba, kayiwa ALLAH kuje ku dubo mani waheedah kada yaron nan ya cutar mani da ita."
Taqare zancen hawaye na sake zubo mata a fuska, gefe wanda takira da habule d'in ya koma ya tsuguna yana girgiza kai cike da jimami kafin yace,
"Gwaggo to wlh ni dai bansan me zan iyayi ba a wannan maganar, kinfi kowa sanin yaron nan ko d'an shi waye, bazamu iya yimasa komai ba, haka kuma koda munje mun kaiwa hukuma qararsa munyi aikin banza sai daima mu sake jawowa kanmu matsala, sannan ni yanzu ta ina zan dubosa tunda kin sani banida abun hawa, wud'annan yaran dakike gani ita kanta hukumar sai yanda iyayensu keso takeyi masu, gaba d'aya jami'anta babu wanda ke iya karb'ar wani qorafi akan yaran ko mahaifansu duk da kuwa iskancin da suke zubawa acikin gari, kawai kiyi haquri muyita mata addu'a ALLAH yakareta har zuwa lokacin da zai dawo mana da ita."
"Kai jama'a wannan wane irin mulkin zalincine, wud'anne irin mutane ne su da babu komai arayuwarsu sai tsabar son kai da yaudara, ya ALLAH ka zamewa Waheed gata ka kareta daga sharrin yaron nan"
"Amin gwaggo, kiyi haquri, bari ni naje nakira maki mai gyaran ya dubaki," Yana gama fad'ar hakan ya miqe ya bar gidan zuciyarsa cike da jimamin abunda ke iya faruwa ga 'yar qanqanuwar yarinyar kuma marainiyar ALLAH"
A b'angaren Ra'ees kuwa gudu ya sosai ba tare da yasan inda zai nufa da yarinyar ba, tunaninsa d'aya shine wane hukuncin zaiyi mata wanda gobe koda ance ta sake shiga gonarsa har tayi masa rashin kunya baa zatayi ba, hanyar kalgo kusan qarshen gari ya d'auke da ita, yana jin ihuun da takeyi tana bugun margin boot d'in tunda suka taso tana bashi haquri amma yayi banza da ita, dukan bayan boot d'in take da qarfi tana fad'in "Wayyo don ALLAH ka bud'eni zafi zan mutu amma ko ajikinsa haka yaci gaba da sharara gudu da ita ba tare daya damu da hakan ba duk da tarin jami'an dake kan titin ba ko kad'an har saida yakai inda zuciyarsa ta amintar masa daya tsaya, Nan ma d'in kife kansa yayi da starring motar yana tuno yanda ta watsa masa kud'in a fuska tana fad'ar wai shine banza kuma wofi? Kalmomin da ko mahaifiyarsa bata tab'a amfani dasu ba wajen yi masa fad'a balle kuma 'yan matan dake bibiyarsa duk ajinsu, sai yau ga 'yar qaramar yarinya baqauya da ita kucaka tana jifarsa dasu, ai kuwa a fusace ya fito cikin motar yaje ya bud'e boot d'in, hannu yasa da niyar shaqo wuyanta aikuwa tsabar wahala da warin fetur d'in data shaqa yasa tayi wani zillo zata fitowa ta fad'a jikinsa, kafin kace me tuni aman da take yunqurinyi ya wanke masa fuska da jiki, a galabaice ta qwalolo idanuwa bayan tagama aman ganin aika aikar da tayi masa ajiki yayi wani irin yarfi da ita gefe ta fad'i qasa, a maimakon taji haushin hakan sai kawai ta kwashe masa da dariya ganin yanda kalar fuskarsa tayi dame dame da aman har tana riqe ciki, kan kace me tsabar qyanqyami da qazantar aman da warinsa ke addabarsa a jiki sai gashi shima ya soma yin nasa aman,
Habawa mi Waheeda zatayi banda da dariya, tun yanayi tana yimasa dariya har tagaji ta soma tausayinsa, don duk tsiwa da rashin kunyar waheeda tausayi wani b'angaren dabi'ane a rayuwarta,
Hango wani me tallar ruwa ta tayi zai wuce d'auke da kular tallar ruwansa da gudu ta cimmasa tana qwala masa kira had'e da tsaidasa ta warware gefen zanenta ta ciro naira hamsin ta miqa masa tace yabata ruwan naira ashirin, karb'ar kud'in yayi ya ajiye kular ruwan ya ciro qwara uku ya miqa mata sannan ya bata canjin naira talatin ta karb'a ta nufi inda Ra'ees ke duqe yana faman kwara aman kamar ransa zai fita.
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMUππ»*
[8/12/2021, 4:44 PM] Zinariya: π _page 3_π
*SAI DAKE!*π«
_written by_
*BILLY S FARIπ*
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*π‘
ππππ
Sai daya gama aman tsab tana tsaye gefen da yake duqe sannan ta d'auki d'aya daga cikin ruwan data siya ta miqa masa tana fad'in.
"Ungo ga ruwa na siya maka ka wanke fuskarka amma yasin sai kabiyani kud'ina don ba kyauta nasiya maka ba."
Rasa tudun dafawar da zaiyi idan yaqi karb'ar ruwan tunda baya dasu a mota yasa ya wafce ruwan a hannunta ya fasa ya shiga zubawa fuskarsa su har saida ya wanke aman dake jiki tas, ya sake miqa mata hannu alamun ta qaro masa ta d'oko d'aya tasake bashi suma ya fashesu yaci gaba da kwararawa fuskarsa har saida suka qare sannan ya bud'e idanuwansa had'e da miqewa tsaye yana jin wani irin zugi a zuciyarsa, ba tare daya kalli inda take tsaye tana kallon kyakkyawar fuskarsa ba yafara takawa zuwa bakin boot d'in motar ya rufe sannan ya zagaya da nufin shiga cikin motar tayi saurin shan gabansa had'e da cewa, "Kai malan, ina zakaje kuma baka biyani kud'ina ba? Nafad'a maka fa ba kyauta na baka abuna ba tunda kai mugune mai wulaqanta mutane, don hakan ni kawai kabani kud'ina in yaso saika tafiyarka." Ta qarasa maganar had'e da miqo masa hannu idonta cikin idanuwansa, tsaye yayi cike da mamaki yana kallon tsaurin idanuwa irin na waheeda da sam babu tsoro acikinsu, baisan meyasa tun d'azu ya kasa d'aukar qwaqqwaran mataki ko hukunci akan taba kamar yanda yaci alwashi, duk kuwa da tarin b'acin ran data had'a masa yau, asalima ji yayi zuciyarsa na qoqarin lurar dashi tsantsar kyan da ALLAH yayi mata ba tare data ankarar dashi tarin laifin data yimasa ba, duk da kasancewar waheeda qaramar yarinya kuma 'yar qauye hakan baisa tasirin kyawonta disashewa ba, wani irin kyaune da ita dake d'aukar hankalin duk wanda ke kallonta musamman idan tana a yanayin fad'a ko tsiwa, yanda take motsa lab'b'anta da yanda gefen kumatunta ke lob'awa lokacin da take dariya da kuma yanda take zaro idanuwa idan tana tsiwa abun gwanin burgewa ne, haka yaci gaba da ayyana kalar kyawon da take dashi aransa ba tare da tasanma yanayi ba har saida yaji saukar takin qafarta akan tasa dake cikin canvas tana fad'in, "Kai malan da kaifa nake magana kawani tsureni da idanuwa, to idanma kai mayene saidai kaci kanka, bani kud'ina in yaso kaci gaba da tsayinka anan."
Shafo sumar kansa yayi had'e da balla mata hararar da takusan sata fitsari sannan yasa hannu ya ingije ta gefe ya shige motarsa tare da bata wuta yabar wajen, yana hango yanda take bin motar aguje ta cikin madubi tana d'aga masa hannuwa alamun ya tsaya har ta gaji ta tsaya don kanta had'e dayin duqe tana bin motar da kallo, rage gudun yayi tare da jawo turarukkan da yake ajiyewa acikin motar ya feffeshe jikinsa dashi don har lokacin be dena jin qarnin aman ba, sake maida dubansa yayi ga madubin saboda gudun daya rage ya hangota har lokacin a tsaye ta kama kunkuru tarik'e, kallo d'aya zaka yimata kafahimci yanda ta cika ta kumbura kamar zata fashe, bai san lokacin da murmushi ya kucce masa ba had'e da tsaida motar yana dariya, Saida yayi mai isarsa sannan ya sake tada motar wani gefe na zuciyarsa na fad'a masa bai kamata yabar yarinyar mutane anan ba, koba komai ita d'in qaramar yarinyace yaci yayi mata uzuri akan abunda tayi masa,
Baya ya farayi da motar har ya isa inda take yayi kamar zai tureta amma tak'i motsawa ko kad'an saboda haushinsa da takeji, don ita bama damuwarta barinta wajen daya tashi yibane kud'inta kawai take da buqatar yabata.
A hankali yafito cikin motar fuskarsa d'aure ya tsareta da idanuwa ganin tayo kansa cike da masifa sai kace zata iya dukansa, tana qaraso ya d'auke kansa had'e da tsaida wani d'an mashin yace "ka d'auki yarinyar Nan ka kaita kauyen ambursa" sannan ya koma cikin motarsa ya d'auko naira dubu biyu yamiqa masa yana qara jaddada masa ya tabbatar ya kaita inda yace masa, sauran canjin kuma ka d'auka.
"To kabani kud'ina malan indai ba ALLAH ya isa kake so nayi maka ba" Yaji muryar waheeda tafad'a a hasale kamar zatayi kuka, juyowa yayi ya kalleta da niyar yimata magana sai kuma yafasa ya juyawarsa ya shige motarsa, a hankali ya sauke gilashin motar had'e da cewa,
"Baa zan biyaba tunda bani nasa kisiya ba" Yana gama fad'ar haka yaja motarsa yabar wajen yana dariyar yarintarta, wanda aka d'auko wani wajen akazo aka ajiye wani wajen da bai sani ba amma hakan bai damesa ba wai sai naira ashirin dashi har ya manta sharabonsa daya riqa qananan kud'i irinta.
Ita kuwa idanuwanta cike da qwalla tace,
"Mugu kawai, ALLAH ban yafe maka kud'ina ba duk ranar da muka sake had'uwa sai kabiyani"
Mai mashin d'in ne ya kalleta had'e da cewa, "Mutafi yarinya sauri nakeyi." Kafin tace wani abu sukaga wata dalleliyar mota ta tsaya wani saurayi cike da gayensa ya leqo ta gilashin da aka saukar yana cewa mai mashin d'in, "bawan ALLAH wancan da yawuce kuwa ba RA'EES ne d'an gidan SS Sada ba?"
Kasancewar babu wanda baisan Ra'ees da mahaifinsa ba acikin garin yasa mai mashin d'in shima da tund'azu zuciyarsa ke cike da wasiwasin meye ya had'a wannan qaramar yarinyar baqauya dashi da yace yakaita ambursa cewa
"E.eh..shine"
"Wannan yarinyar kuma wace ita?" Yaji saurayin dake cikin motar ya sake tambayarsa akaro na biyu,
"To yallabai ban saniba nima, kawai dai yabani kud'ine yace in kaita qauyen ambursa."
Dariyar mugunta saurayin yayi cikin ransa had'e da cewa, "Shege Ra'ees! yau zan nuna maka kad'an daga cikin shaqiyancina da kai har mahaifinka" sannan ya fiddo kud'i ya miqawa mai mashin d'in yace,
"Shikenan, ungo wannan kaje bari kawai zan kaita tunda ta hanyar zamubi, mai mashin na ganin haka ya washe baki had'e da manta ko waye Ra'ees da Jan kunnen da yayi masa na cewa ya tabbatar ya kaita inda yace, jiki na rawa ya karb'e kud'in ba tare daya tsaya tambayarsa ko waye shiba yabawa mashin d'insa iska,
Waheeda kuwa dake tsaye ta zubawa zuqeqiyar motar idanuwa tana kallo kawai sai taji an kamo hannunta, cike da tsiwa da masifa ta fisge hannun tana kallon saurayin da shigar tasa batada maraba data cikakkin 'yan iska masu lasin tace,
"Kai malan lafiya?"
"Lafiya lau yarinya, ni abokin Ra'ess ne, shiyace na kaiki gida."
"Waye Ra'ees kuma?" Tafad'a tana balla masa harara tare da qoqarin barin wajen.
"Wanda ya ajiyeki da mota mana, ko bashi bane naga kun gama magana dashi yanzu?"
"Oho! Ni ina nasan hakane sunansa, kaga ni bazan bika ba balle na shiga motarka, kuma wlhi ALLAH kafad'a masa idan bai biyani nairata ashirin ba, to bazan tab'a yafe masa ba har gaban ALLAH"
Tana gama fad'ar haka tayi gaba abunta tana mitar ina d'an mashin d'in dake tsaye Yan jiranta, kodai wannan d'an iskan abokin Resis yake ko waye ma oho, yayi masa wayo ya amshe kud'in tunda taga suna magana dashi, bata ankara ba sai taji kawai an sunkuceta had'e da toshe mata baki da hanci antura cikin motar, kafin tayi yunqurin ihu da bid'ar neman taimako har saurayin ya busa mata wani abu a fuska ta some, abokinsa dake jan motar ya tayar sukabar wajen aguje suna ihu da shewar haqarsu ta cimma ruwa,
Dariya saurayin yayi tare da d'aga cemarar dake gefensa yana duba wasu hotuna daya d'auka aciki yace, "R 3fulS yau kashiga komata kaida mahaifinka, ni Sagir Ismai'l saina nuna maku d'an halak ne ni awajen mahaifina, saina tozartaka nasaka nadamar wulaqancin da kayi mani arayuwa"
"Kayi daidai abokina, shiyasa kake burgeni akoda yaushe, dolene SS Sada ya d'au darasi shida shalelensa a hannunka" abokin nasa dake tuqa motar yafad'a yana dariya, tafiya mai d'an nisa sukayi kafin ya juyo ta baya Yana kallon yanda Ra'ees ke faman shinshinar waheeda yana lumshe idanuwa sai kace bunsuru yace
"Yanzu ina muka nufa da abokina?"
"Muje gidan gonar Abba mu huta da kawai, don yarinyar nan da gani zatayi sweet sosai duk da kaya basu zauna mata ba."
"Angama" G-boy abokin nasa yafad'a tare da bawa motar wuta, cikin mintuna goma sai gasu gidan gonar, tamkar baby haka Sagir ya d'auko Waheeda da batasan inda kanta yake ba har yanzu ya shiga cikin gidan da ita suka keta mata haddi, ta matuqar shan wahala sosai a hannunsu don ba kad'an sukayi mata ba musamman lokacinda suka ga tafara qoqarin dawowa hayyacinta sai suka sake shaqa mata abunda ya shaqa mata daga farko ta sake somewa sukaci gaba da biyan buqatarsu da ita.
Basu barta ba har saida sukaga numfashinta yasoma dena fita a gangar jikinta suka shiga d'aukarta hotuna kala kala acikin yanayi marar kyau da ban tausayi da take ciki, can misalin qarfe goma da rabi na dare lokacin gari yayi baqiqirin sanadiyar hadarin dake shirin tasowa suka kaita can cikin ambursa daidai inda sukaga ya d'aukota suka jefar da ita sannan sukabar wajen, don dama agabansu d'azu komai yafaru tsakanin Ra'ees da yarinyar lokacin sun fito wajen casun da akeyi jin ance zaije wajen saboda ko kad'an basa shiri dashi, shinefa sai sukabi bayansa ganin ya sata cikin motarsa don cimma burinsu da d'aukar fansa akansa cike da tunanin zaiyi mata wani abunne sai gashi sunga beyi mata komai ba, duk da ba haka suka soba sunyi nasarar d'aukar hotunansa da ita lokacin daya riqo wuyanta da sadda tafad'o masa ajiki da kuma lokacin da yayi jifa da ita sanadiyar aman data kwararo masa ajiki batare daya san sunyi hakanba, asalima bacin ran da take ciki alokacin bai lura da suna biyarsa a baya ba.
Daidai lokacin da suka ajiyeta habule mai shago ya tashi daga sana'arsa yana qoqarin kulle shagon, ai kuwa ya hangosu, kasancewar baiga fuskokinsu ba yasa bazai iya tantance ko suwaye ba amma d'ari bisa d'ari zuciyarsa ta gama amincewa da cewa Ra'ees ne shi da abokinsa saboda shine ya d'auketa agaban idonsa d'azu, haka kuma bai lura daba motar bace saboda duhun da gari yayi, gefe ya samu ya lab'e har saida suka bar wajen sannan ya fito ya bubbugawa wani mutum da gidansa ke laqe da shagonsa ya sanar dashi abunda ya faru d'azu da kuma wanda yagani yanzu, cike da jimami suka nufi inda aka jefar da waheeda bayan sun kunna qaramar fitilar dake hannunsu, kallo d'aya sukayi mata suka d'auke kai saboda halin da suka ganta aciki, komawa mutumen yayi cikin gidansa yaje ya taddo matansa su biyu suka zo suka d'auketa bayan sun lullub'a mata zane sun rufe mata jiki suka nufi gidan gwaggo da tun d'azu ke zaune tana kuka da bawa ALLAH cigiyar inda jikarta take sai gata taga sun shigo mata da ita tamkar gawa, qoqarin miqewa tayi tana sallalami habule mai shago yayi saurin riqeta don gudun lalacewar gyaran da akayi mata d'azu na tsagewar qashi a cinyarta da tasamu.
Banda kuka babu abunda gwaggo keyi tana tsinewa Ra'ees tare da la'antarsa shida mahaifinsa, jin zafi da rad'ad'in abubuwan da yaron keyi yasa basu hanata ba har saida tayi mai isarta ta gaji sannan suka fara bata baki, taimakon gaggawa matan suka shiga bawa waheeda ganin lumfashinta na kaiwa da komowa alamun tana raye bata mutu ba don a zatonsu ta mutu, randar dake cikin d'akin gefen gwaggo suka bud'e suka d'ebo ruwa suka shafa mata afuska har sau uku amma bata motsaba, sai akaro na hud'u da suka watsa mata ruwan da qarfi sai gashi tayi wata iriyar zabura kamar wacce tafarka bacci cikin tashin hankali tare da fashewa da kuka, kamata sukayi suka maidata kwance suma suna hawayen cike da tausayinta,
"Alhamdulillah." habule da mutumen suka fad'a tare da miqewa suka fita suna cewa gwaggo, bari suje sukira nurse Asma'u, da yake wata yarinyace ma'aikaciyar asibiti da basu jima da dawowa nan garin ba ita da mijinta, wanda yanzu duk mafi yawancin qauyen ita ke karb'arwa matansu haihuwa, ungozoma ce (midwife) data san aikinta kuma ta qware sosai acikinsa cike da tausayi da mutunta mata 'yan uwanta musamman wud'anda suka zomata da matsala, tana matuqar taimakawa matan qauyen sosai don har gidanta tana amsar haihuwa kuma tanada shagon saida magunguna anan bakin qofar gidan nata haka tana taimakawa wasunsu da kud'inta ko tayi masu aiki kyauta idan tafahimci basuda wani zarahi sosai.
A can gidanta dake gaba dasu suka nufa da yake babu 'yar jayawa tsakani suka fad'o mata abunda ke faruwa ba tare da sun b'oye mata komai ba, cikin b'acin rai ta dinga fad'a tana har had'a kayan aikinta da abubuwan da zata iya buqata sannan tace sutafi gatanan tafe bayansu itama, shagonta ta shiga ta d'auki wasu magunguna da wasu sauran kayan aikin sannan tabi bayansu cike da tausayin halin da zata riski 'yar qanqanuwar yarinyar Waheeda aciki.
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMUππ»*