KISHIYA KO BAIWA

25&26

by @realeshaa

*KISHIYA KO BAIWA???*

     _(TRUE LIFE STORY)_ 


 *NA MARUBUCIYA*

 *REAL ESHAA ~*



 *WATTPAD* _Realeshaa_



 *_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*



    *PAGE 25&26*🖌️


________________________📖Sukainat naganin fitarsa ta durkushe awajen tare da fashewa da wani matsanancin kuka me ban tausayi,shin wannan wace irin rayuwace duk wulakanci da Ahmad da matarsa ke yimata be ishesuba harse ya ha'da dacin zarafin iyayenta hakika kodashi ne autan maza bazata zauna daahiba muddin zeci zarafin iyayenta.Tana cikin wannan yanayi taji dariya da shewa akanta,kai ta'daga dan ganin wacece?!Nadiya tagani fuskarta na bayyanar da farin ciki,du'rkusawa tayi agabanta tace, hausawa sunce idan kaga mutum ze hadiyi gatari to kari'ke masa 'kota"wannan Karin maganar tasu haka yake babu shakka acikinsa!,tun kafin kishigo gidan nan nafa'da miki cewa se kin gommaci zaman prison da zaman Cikin gidana, domin babu macen data isa tashigo gidan amatsayin matar Ahmad kuma tasamu kwanciyar hankali babu wannan matar aduk fadin duniya.Duk da ire iren tarin kashedi dana miki haka kikasanya 'kafa kika shure kika maida magana ta tamkar tatsuniya,kina tunanin zakishigo muzama daya saboda 'kwa'kwalwar kifi gareki.Har yanzu baki fara kuka da danasa ni, acikin gidan naba"tunda harzu wannan lokacin baki fara shirin barin gidan da kafafunkiba.Ina so in tabbatar miki cewa kishi da ni, ba Abu bane mai sauki kamar yanda kike zato,Murmushi tayi tace hakika kinbani tausayi shiyasa zanbaki shawaran daze anfaneki ,tunfasawa tayi kafin daga bisani tace" tunkafin dare yamiki kitattara inaki inaki kibar min gidana nida 'ya'yana,tun kina da sauran karfin ki dakuma kuruciyarki domin kar 'karfin ki da kuruciyat ki sukare abanza batare da kin moraba."Sukainat takasa koda furta kalma 'dayane banda hawayen dake malala daga idanunta"Wannan hawaye bakaramin sanyi sukewa Nadiya a zuciyar taba domin barin ta bewuce taga Sukainat na wahala ba.Seda tagama ya'ba mata ba'ka'ken magana kafin tafice tana karairaya tare da 'yan wa'ke'kenta.Sosai Sukainat tayi kuka da danasa ni,wanda bata ta'ba yiba irin na wannan rana.Wannan kukan datayi shi yajanyota mata matsanancin zazzabi da ciwon kai 'kyar ta iya Jan kafarta takwanta akan gado...


Da yammaci bayan tafiyar Hjy kultum badadewa hema tazo"Kafin Hjy kultum tatafi seda tajawa Nadiya kunne kan karta ragarwa Sukainat intayimata Abu kar tabari se Ahmad yazo tadauki matakin daya dace dakanta.Sosai Nadiya taji dadin wannan magana na Hjy kultum danhaka tayita zabga mata karya da gaskiya abinda kefaruwa tare da yimata godiya kan shawaran data bata.Lokacin da hema takaraso bakaramin farin ciki Nadiya tayiba tarungume ta tayi, tace gaskiya nayi farin cikin zuwanki kawata domin ina bukatar ki"Kallon ta hema tayi,tace kai 'kawata kina sha'aninki bakyajin garin sekace kece Amaryan?:dariya Nadiya tasheke dashi tace nice mana tunda se yanda najuya kambu na acikin gidan ta'fada tana juya kananun idanunta,Dariya hema tafashe dashi tace baki da dama mutuniyar, bani insha yanda abin yafaru cikin sauki??!Zama Nadiya tagyara tace agaskiya yarinyar batada reni ko rashin kunya kamar yanda kika fada, sede matsalanta daya! batasan yanda zata min biyayya ba domin da ta iya yimin biyayya toh datasamu kan Ahmad" sede tacika taurin kai tafada tana yatsine fuska.Dariyar 'keta hema tafashe dashi tace aiduk Wanda yaci tuwo damu miya yasha waya fa'da mata muna zama dakishiya?Anma yabatun Wannan maganin hope yana aiki?Murmushi Nadiya tayi tace aikomai normal tunda nafara sanyawa acikin abincin kullum abinci cikin baci yake,arasa gane kansa da gindinsa,anma dayake yarinyar akwai shegen wayo shine tafaki idona tayi girki bansani ba"Ahmad naci yazo yana wani rawan kafa...duk de abinda yafaru seda tazayyanewa hema"aikuwa suka dinga dariyar keta cike da farin ciki hakarsu na cimma ruwa yanda suke bujata.Seda daddare mijin hema yazo yadauketa sukatafi"bayan sun sake shirya sabon manakisa ...

Koda Ahmad yadawo gida direct sashen Nadiya yanufa kasancewar ita ce da girki toilet yashiga yai wanka Kafin yafito yasanya jallabiya maroon megajeran hannu Wanda yaimatukar yimasa kyau kana yafeshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi"Koda wasa besanar da Nadiya sa'banin dayafaru tsakanin sa da Sukainat ba"se bayanda ya kammala shirin kwanciya yace da ita kar tasake baiwa suky abinci na tsawon kwanaki biyu,sannan koda wasa karki barta tashiga kichen tagirka komai harse nabada izinin hakan.koda tagama jin abinda yace se tace,haba Honey meyayi zafi haka hadda horon abinci? kasanfa Sukainat yarinya ce dole se anbita Ahankali??! Ta'fada cike da kissa.Shiru yayi yajuya mata baya batare daya bata amsa ba dan bejin ze iya magana a wannan yanayin dayake ciki.Jin haka yasa tasha jinin jikinta domin tasan tunda yajuya mata baya bazece komai ba,tsaki taja aranta tace mutum se miskilancin tsiya...

Kamar yanda Ahmad yafa'da hakan yakasance, Nadiya tahana Sukainat abinci natsawon kwanaki biyu,daman ya lafiyar kura bare tai zawo,dama kawai dama Nadiya kejira Wanda zata musgunawa Suky sekuma gashi tasamu cikin sauki yanda babu Wanda ze ga laifinta.

Atsawon kwanakin biyun nan baki daya Sukainat tarame ta lalace gawani zazzabi dake damunta duk Daren duniya bata iya bacci dashi take kwana take tashi ga horon yunwa sede tasha tea kawai,tarasa Wanda zata fa'dawa damuwarta,taji sanyi aranta,ga ba waya ahannun ta bare tasamu daman kiran mahaifanta. Ahmad yadena zuwa dakinta acikin kwanaki biyun bare tasanar dashi halin datake ciki, Nadiya kuwa tasan koda shure shuren mutuwa take bazata temaka mataba hakan yasa take zaune cikin kunci da bakin ciki.Seda tayi kwanaki biyu kafin Ahmad yasa Nadiya taci gaba dabata abinci,toh koda anbata abincin ma bata iyaci kasancewar batada cikekken lafiya,haka take wuni ko yaushe acikin dakin daga Nadiya Har 'ya'yan ta babu me shiga inda take....


****

Tun daga Wannan lokaci Sukainat tashiga rayuwar 'kunci da ba'kin ciki,duk wani aikin wahala da bauta acikin gidan itace,Nadiya tadena komai,saboda tsaban mugunta irin nata ga injin wanki anma bazata yi dashi ba sede ta tattarowa Sukainat nata dana 'ya'yan ta tayi musu haka zalika wanke wanke, moffing sharan compound din gidan,duk wani aiki me wahala itace zatayi Ahmad kuwa yagoyi bayan matarsa acewar sa aikin yakamaceta"shiyasa suke mata duk lulakancin dasuka ga dama ita da 'ya'yan ta batada ikon tankamusu tun da mai gidan yagoya musu baya.Tsakanin ta da Ahmad kuwa wani irinin zama suke mecike da ban tausayi,Sai ranan girkinta ne ze shiga dakin ta,tsakiyar dare asbah nayi zefita bakuma za tasake ganinsaba se wani ranan girkinta, wani lokacin ma batasanin shigowar sa sede taga alamar mutum ya kwana adakin...Yauma kamar ko yaushe se misalin 'karfe biyu nadare yashigo dakin nata gani yayi tanata murkususu,A'kasan 'dakin tana shesshe'kan kuka,cike da rashin damuwa ya kwanta batare daya kalletaba yayi kwanciyar sa,yakai kimanin minti talatin bacci yaki daukarsa sakamakon sheshshe'kan kukanta"mikewa yayi yana Jan tsaki cike da takaici yace Dan Allah malama ki yimin shiru kinbi kin dameni da kananun kuka idan kuma bazakiyiba nabar miki dakin,ai wannan wulakanci ne kinsani gaba da kukan munafurci jarababbiya kawai yafa'da yana binta da mugun kallo....Kasa cewa komai tayi se kukan dake kara kufce mata ga wani azabebben zazzabi dake damunta shin wai yaushe Ahmad yakoyi rashin tausayi ne?tatambayi kanta"Jin taki yin shiru yasa shi yamike afusace yayo kanta hannu yasa daniyyan janta waje,Dasauri yajanye hannunsa daga jikinta sakamakon wani zafi daya gauraye ilahirin jikinta.. Zama yayi agefenta yana binta dawani mugun kallo,saboda tsaban bakin hali da munafurci baki da lafiya shine bazaki sanarmin ba,Inkin kashe kanki iyayenki kikayiwa asara baniba danni bakya gabana jarababbiya kawai yace da ita"ko Kallon sa batayiba domin ita tasan abinda kedamunta,seda yagama jifanta da mugayen kalamai kafin yajanyo hijabi yasanya mata, sukanufi asibiti lokacin uku da Rabi yayi ko acikin motar se hantaran yake tare da ya'ba mata ba'ka'ken magana...Suna isa asibitin aka shiga bata temakon gaggawa, gwajin farko aka gano tana dauke da ciki na tsawon sati shida,Bayani Dr yashiga yimasa na yanda yakamata abata kulawa sannan kartayi aikin wahala kokuma ta'daga Abu me nauyi,saboda zejanyo matsala,sannan sakamakon binciken dasukayi sungano akwai yunwa da damuwa atare da ita dole adena yimata abinda zesata cikin damuwa domin tana bukatar kulawa na musamman.Magunguna Dr yarubuta masula Wanda zatayi amfani dasu"Godiya Ahmad yamasa sannan yawuce masallacin dake cikin asibitin kasancewar ana kiraye kirayen sallah.Bayan ya idar da sallah ne yashigo,dakin datake Zaune yasameta tajinga bayanta da bango idanunta alumshe kamar me bacci,jin kamshin tularensa yasata bude idanunta tana Kallon sa cike da So, kawar dakai gefe yayi yana Jan tsaki"jiki asanyaye tayi kasa dakanta talura ko Kallon besonyi"wata noise ce tashigo hannunta dauke da Leda me tambarin asibitin da alama maganine aciki tabaiwa Ahmad,Kallon Sukainat tayi tace madam congratulations natayi murna Allah yaraba lafiya"Ameen ta amsa tana nazarin maganan, fuskarta da yakwateccen farin ciki tace ya Ahmad, ciki ne dani??Wani mugun kallo ya watsa mata yace, adakile"yece eh",bata damu dayanayinsa na halin ko inkula daya nuna mataba sema wani farin ciki daya mamaye mata zuciya,hannunta tadaura akan cikin tashiga shafawa tanajin wani yanayi me wuyar fassarawa atare da ita Ita ce ke dauke da cikin Ahmad ajikinta?,gudan jinin Ahmad ne ke kwance acikin mahaifarta,?zata haifawa ya Ahmad dinta yara kyawawa kamarsa?,wasu hawayen farin cikine suka shiga zubo mata afuska,Dawani irin sauri tadira akan gadon tarungume sa tana hawayen farin ciki....Rai abace yasa Hannu yafinciketa daga jikinsa yanabinta dawani irin kallo Wanda shika 'dai yasan ma'anarsa...






 _VOTE_ ✅

 _COMMENTS_ 

   _AND_ 

_SHARE_






       *_ESHAA CE~_*🤙🏻

[3/23, 15:13] ESHA: