1&2
by @realeshaa
*KI YADDA DANI.*
_Kishiya Ko Baiwa_
_Return_
_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA*
_WATTPAD_
*Realeshaa*
_Like my page on Facebook_ππ»
***
*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*
_Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki Naira Dari biyu se ki turo katin MTN ta wannan number ππΌ*** tare da turomin da shedar biya ta Wannan number ***.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._
*FREE Page 1&2ποΈ*
______________________πTamkar saukan aradu aka haka kalaman sa, ya daki zuciya yo yin mu,Musamman ma ni wani irin tsuma jikina keyi tamkar mazari yayin da idanuna suka kada sukayi jawur dasu tamkar garwashi babu abinda yake yawo a kwakwalwar kaina face muryar sa dake furta kalman saki agareni Innalillahi wa'inna ilahi raji'un.shine kalmar danake furta wa acikin raina ko zanji saukin abinda ke yawo acikin zuciya ta Wanda ke barazanan tarwatsamin lissafi.Nakasa ko da dago kaina ne,addu'a kawai nake Allah yasa mafarki nakeyi ba gaskiya ba domin zuciya ta yakasa gaskata min abinda kunnuwa sukaji...
Cikin kunan zuciya dawani irin nadamar kasancewar Ahmad jininsa,Alh Ali yamike tare da kaiwa Ahmad din wani wawan mari,anma ga mamakin sa seyaji anrike hannunsa ta mau tamkar za aballa.Shiru dakin yayi tamkar babu mahalukin dake numfashi aciki. Sakamakon muryan Ahmad daya karade ciki dakin,Cikin hargagi da rashin kunya yace"Wallahi Baffa karkayi Wannan gangancin acikin rayuwar ka,nacewa zaka sanya hannunka ajikina dasunan duka!,nawuce Wannan matsayin azanyu ko wancan ranan daka marini na 'kyaleka ne kawai domin ina ganin mutunci ka,amatsayin ka na wan mahaifina anma badan Wannan ba babu dalilin daze sanya in daga maka kafa.Ayanzu muddin kace zaka sake Wannan gangancin zan baka mamaki fiye da yanda baka zato,yafadi haka asanda yake wurgi da hannun Alh Ali tamkar ze karya.Kallon kaskanci ya watsa musu daya bayan daya kafin yaci gaba dacewa.Wannan rainin wayon naku ya isheni haka kunce nasaki yarinya tunda bazan iya riketa ba,nasaketa anma hakan be ishe Ku ba,ko kuna tunanin dama bazan Iya sakin tabane shiyasa kuka dameni dacewa na saketa to ko 'yar gwal ce 'yar taku Wallahi narabu da ita.!??Hhhh yakece da dariyar renin hankali kafin yadaure fuska yace"me zanyi da Wannan yar taku irin jaraba,da rashin tarbiya,tunda na aureta nafara tsiyacewa,ashe jangwam na kwasowa kaina bansani ba,saboda bakin mugunta da zalunci kunsan 'yarku gayyar tsiyace anma kuka lika min ita,saboda kunaso in talauce mudawo Dede daku ko!!?Wallahi nayi danasanin hada iri daku.Ni ayanzu ban 'ki Wannan kaddarerren cikin yazube ba kowa yahuta,sannan magana na karshe dazanyi daku shine daga yau,babu ni babu Ku maganan ciki kuma kar wanda yace"ze tun kareni akai domin ba zanyi asaran kudina akan shiba,sannan ko yau ta haihu Ku kawo min abinda tahaifa nizan bashi tarbiyan daya ce, dan banga alamar zesamu wata cikakkiyar tarbiya agidan nan ba....Amatukar fusace Alh Ali yadago kai yace"Ahmad shin kana da hankali kuwa?kasan mekake...Cikin sauri Ahmad yadaura ya tsansa akan bakinsa, tare dacewa shitttt...Bana son jin komai daga bakin ka Baffa idan har Santa kakeyi kabari idan tahaihu takawo min 'Dana ko 'yata seka aureta ina ganin hakan zefi se in tabbatar dacewa kadamu da ita anma base ka tsaya yimin holo ba...Yana gama fadin haka yajuya yafice daga dakin batare daya sake furta komai ba....
kasa dago kai Alh Ali yayi,daga matsananciyar kunyar da Ahmad yasanya shi tun lokacin dayace ya Auri Sukainat yaji tamkar anzare masa laka ajikinsa jiyake inama 'kasa yatsage yashiga da Wannan kunyar daya shiga kamar shi Ahmad ze kalli tsaban idanunsa yace"ya auri matarsa.Hakika Ahmad yabasa mamaki, anya yana cikin hayyacinsa kuwa yatambayi kansa,?wata zuciyar ce tace"yana ciki mana kawai de yadena ganin kimarka ne shiyasa yafada maka abinda ransa keso yakuma tozar taka yatafi.Ahankali yadago jajayen idanunsa dasuka rine da matsanancin bacin rai da kunya dakuma nadamar zuwan da yayi hakika dayasan irin cin mutunci da Ahmad ze masa kenan babu shakka ba abinda ze kawo sa.Cikin raunin murya yace"Dan girman Allah Malam Ahmadu kuyafe min, Wallahi bantaba zaton irin Wannan wulakancin daga wajen Ahmad ba,anma Ahmad ya tozartani acikin mutane,yafada asanda yake hade hannayensa guda biyu waje daya alamar roko tare dayin kasa da kansa...
"Cike da dattako da kamala Malam Ahmadu yayi murmushi yace"haba Alh meye abin damuwa aciki? Dan Allah karkatashi hankalin ka akan Wannan maganan, tun farkon auren Sukainat da Ahmad haka Allah ya kadarta,dole hakan zekasance atsakaninsu,dan haka ka kwantar da hankalin ka insha Allah zamuci gaba data yasa da addu'a idan akwai Rabon kome, atsakaninsu Allah yasanyaya masa zuciya yagane kuskuren sa ya maidata dakin ta,sucigaba da hakuri da juna....
Shiru Alh Ali yayi yana jinjina hakuri da dattako irin na Wannan bawan Allah,aransa yana ayyyana koda shi dasuke ciki daya da uban Ahmad yayiwa 'yar sa haka baze ta'ba mayar masa da ita ba koda kuwa ze mayar masa da ita to se yanuna masa kuskuren sa.Wani abune ya'dar su masa arai anma yabarwa kansa harse sun huce ze zo musu da batun"Hakika bani da bakin yimuku godiya domin kun nunamin halarci,Ubangiji Allah yasaka muku da alkhairi, cewar Alh Ali" Ameen Malam Ahmadu ya amsa fuskarsa dauke da murmushi...
Ummi ya kalla da kanta ke 'kasa wanda duk bin kokkofin ka baka isa kagane halin datake ciki ba.Cikin taushin lafazi da ban hakuri Alh Ali yace"Hajiya ina mai baku hakuri abisa abinda 'dana yayi muku hakika ya shayar dani mamaki, Wanda ko amafarki bantaba zaton haka daga Ahmad ba anma rana daya yacanza yadawo wani sabon mutum awajen mu tamkar ancan za mana shi...
Kai Ummi ta jinjina datunda akafara magana batace komai ba se yanzu.cike da gamsuwa da kalamansa tace"Babu komai Alh,bawa baya taba kaucewa kaddaransa walau alkhairi ko akasin haka.Wallahi ban taba jin haushin Ahmad akan abinda yake ba hasalima tausayi yake bani domin duk inda ake Neman dan halak Ahmad yakai,sede dan Adam ajizine duk kyawawan halayyar sa dole asamu wanda yake kuskure aciki kuma Har ayau ban jin haushin Ahmad ba akan abinda yayi,Ina kuma mai rokon Allah daya sa yagane gaskiya yakuma mayar da matarsa dakinta.Ta numfasa tare da kokarin danne damuwarta tace"kuma dan Allah ina mai Neman alfarma awajen ku daku taya Ahmad da addu'ar Allah yakubutar dashi abisa siradin dayake ciki,takarashe cikin sanyin murya.
Wani irin kaunar Bayin Allah ne yaratsa wa Alh Ali zuciya,Cike da jin dadi yace"Hakika bazan taba mancewa da hallacin kuagare muba,Ina mai taya Ahmad bakin ciki daya rasa nagartattun surukai irinku domin samun irinku se antona,Mikewa yayi yace"nabarku lafiya se Allah yaha damu domin zamuci gaba dayin zumunci Ahmad ne yahada mu anma be isa yara bama na zumunci ba..Murmushi Malam Ahmadu yayi tare da mika masa hannu sukayi musabaha.ficewa Alh Ali yayi cike da jimami tare, da barwa ransa kudurin da yayi...
Wani irin kuka ne ya kufce min jin kalaman da iyayena keyi game da Ahmad,wato duk irin cin mutunci da wulakan cin daya min kana yasake ni agaban idanunsa basuji takaici ba harsuke ikirarin zan koma gidan sa akaro na uku!...Dagudu namike inajin wani irin tsanar Ahmad acikin zuciya ta, tare da takaicin iyayena dake gwada tamkar bani da mutunci da daraja awajen su ko kuwa sungaji dani oho Nide bansani ba.
"Da kallo suka bi bayanta cike da matsanancin tausayin ta hakika suna matukar tausayawa rayuwar ta,da kananun shekarunta take azab tuwa haka jiki asanyaye Ummi tamike tabi bayan ta...
Alh Ali nashiga gida yazube akan tantsama tantsaman kujerun falonsa Wanda suka gaji da haduwa,lumshe idanunsa yayi kallo daya zakayiwa fuskarsa ka tabbatar daya na cikin tsantsan damuwa da tashin hankali.Dafa kafadarsa Hjy Bilki tayi cike da kulawa tace"Lafiya kuwa Alh naga kadawo haka??Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa yabu'de jajayen idanunsa dasuka rine da tsantsar bacin rai yasauke akanta...Jiki asanyaye tazauna kusa dashi tare da debo masa ruwan sanyi tamika masa bamusu yasanya hannu yakarba roban swan water domin yana bukatar abinda ze sanyaya masa rai,seda yashanye tasss kafin yacire roban daga bakinsa yana sauke numfashi akai-akai..Seda taga ya samu nutsuwa kafin tace"meyafaru Alh naga kadawo gida acikin Wannan yanayin bayan kuma bahaka kafita ba tayi tambayar cikin hikima yanda babu takura aciki...
Murmushin takaici Alh Ali yayi kafin yace"Hjy yau nakunyata agaban mutane masu tarin karamci da alkunya,yau nashiga kunyar da tunda nake bantaba shiga ba, hakika yau Ahmad yasa nayi nadamar kasancewar sa jinina...Dasauri Hjy Bilki tasanya tafin hannunta abakinsa,kai tagirgiza masa cikin dattako tace"Karkayi masa baki idan rai yabaci bekamata hankali yagushe ba tamkar mahaifi kake agaresa dan haka addu'ar mu kawai yake bukata bawai baki...
Cike da gamsuwa da kalamanta yayi murmushi, tare da gyara zaman sa sannan ya zayyane mata duk yanda sukayi da irin tijaran da Ahmad yayi masa...Kai Hjy Bilki tagirgiza cike da mamaki dakuma takaicin abinda Ahmad din yayi,kana tace"A gaskiya Alh natausayawa yarinyar nan duka duka ma nawa take anma Har anmaida ita karamar bazarawa,toh wani shawara ka yanke akai yanzu!?Numfasawa yayi yace"na yanke hukuncin idan har iyayenta zasu amince inaso su bani ita,tadawo gabana da zama har ta haihu idan kuma tahaihu tadauki abinda tahaifa tamayarwa da ubansa sannan tacigaba da karatun ta.Inaso tadawo classy girl me aji dakuma kasaita yanda Ahmad zezo yazube gwiwoyinsa biyu akasa yana kuka yana rokonta da tasoshi,ita kuma za tajuya tatafi tabarsa awajen,yakarashe murmushi na subcewa fuskarsa...Cike da farin ciki Hjy Bilki tace"a gaskiya Alh nayi farin ciki da jin Wannan maganan Allah yasa iyayenta su amince hakika zanso ganin Wannan ranan ta'fada fuskarta cike da kayataccen murmushi... Sosai Alh Ali yayi farin ciki dayan da Hajiya Bilki ta amshi maganar duk dakuwa daman yasan bata da matsala...Gyaran murya yayi,hakan yasa ta mayar da hankalin ta kacokam kan sa.Inaso daga gobe zansanya afarayiwa Ahmad saukan alkur'ani dakuma addu'o'i domin duk abinda yake nasan ba a hayyacin sa yake ba,Kai ta jinjina cike da gamsuwa da maganar sa tace"Allah yabaka nasara akan abin da kasanya agaban ka "Ameen ya amsa.Haka sukaci ga da tattaunawar yanda zasukula da Sukainat idan tadawo gidan,dakuma yanda za adinga yiwa Ahmad addu'a har Allah yasa yadawo hayyacinsa....
_Karkumanta tun awancan mungama true life story Wannan labarin kirkirarrene koda akwai gaskiya toh kadan...Sannan Ba zanyi free page dayawa ba a page 9&10 zan tsaya kasancewar tun ana farko labarin yatafi Wannan cigaba ne babu bukatar se anyi free dayawa_
_Sannan kuyi hakuri da ganin book din yakoma na kudi hakan yafaru abisa wani dalili ne da yasanya ni mayar dashi na kudi ina fatan zaku fahimci ce ni._
*Dan Allah masoya na idan kun karanta kuyimin shearing din sa pls and pls*
_VOTE COMMENTS AND SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»