MURADIN RAI

chapter 22

by @zeety

 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 




*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋 





_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*





_this page is for you sister like no other, bazan daina miki addu'a Allah ya biya miki bukatun ki na alkhairi ya baki miji nagari *UMMUKULTHUM MUHAMMAD BIBI* Ummulele nah🥰🥰_ 





By: *ZEETY*💞 





*wattpad @Zeety-AZ* 

karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻 






22📚




Murmushi yayi sannan yace haba zeezee aiko gaisawa zamuyi tukunna, ƙara ɓata rai tayi tace banida wannan lokacin, idan abunda yakawo ka ba muhimmi bane kuma ba alkhairi aciki kaga tafiyata, take tajuya zata wuce gida. 


dasauri yace dan Allah ki tsaya ki saurareni akan case ɗin mardiyya ne, tsayawa tayi batare da ta juyo ba, tace inajinka..


Ajiyan zuciya ya sauƙe sannan yace mata banji daɗin abunda yafaru ba, saboda tunda naji nashiga damuwa, wannan dalilin yasa nakira Hasib saboda inji koyasan meyafaru saikuma ya shedamin da bakinshi cewa da hannu shi aciki, nayi recording call ɗinmu, nasan ke kaɗai ce zaki temakamin wajen dawowa da mardiyya martabarta..


Dasauri tadawo tana cewa ina voice ɗin? Wayan shi yaciro yana ƙoƙarin nemo muryan, itama duk ta ɗauki hankalin ta tasa acikin wayan, ta zaƙu taji da kunnen ta…


Babu abunda sukaji banda ganin wafce wayan da akayi a hannu shi, samari biyu akan mashin da gudu ya bisu amma tuni sunsa wuta har sun ɓacewa ganini shi sunbarshi da ƙura… 

kanshi ya rike yana cewa innalillahy, shi bama wayar bane damuwan shi, ila evidence ɗin da yake ciki… 


zeezee ganin abun tayi kamar a film, a iya sanin ta dai anguwan su babu yan kwacen waya, meyake faruwa… kallon shi kawai takeyi, yana haki yadawo yana cewa yanzu zeezee ya zamuyi?


Kallon shi tayi dakyau sannan tace ta yaya kakeson inyadda dakai, ta yaya kakeson ingane wannan abun ba plan bane…

zaiyi magana taɗaga mishi hannu tana cewa um umh, babu Abunda kaina zai ɗauka don tare nagan ku da Hasib. 

Tana kaiwa nan tawuce gida.


Shiga mota yayi ya kifa kan shi a sterin motan, har ranshi yakeson ya temaki mardiyya amma ta ina zai fara, babu me yadda dashi… yaya zaiyi yasamu abunda ya ɓace a wayanshi… haka yayi ta sakawa da warewa karshe dai bai samu mafita ba yaja motan shi yakara wuta.


Kai da gwiwa ta haɗa duk abun duniya ya isheta… kawarta ce ta dafata, tareda cewa farida kidaina wannan tunanin kitashi mu nemi mafita, ɗago jajayen idonta tayi tace iklima idan babana yaji wallahi zai iya kasheni, sai ta fashe da kuka tana cewa wayyo Allah na ni farida, gana rasa ya Abbas ga abun kunya…. Ina zansa kaina.


Rarrashin ta iklima tashiga yi amma sam takasayin shuru… ajiyan zuciya ikliman tayi sannan tace kinsan meye farida? Girgiza mata kai tayi halamun a’ah… tace mafita ɗayane, shine muje asibiti ayi flushing ɗin shi…


Zaro ido waje tayi tana girgiza kai tace gaskiya inajin tsoro kar inje in mutu..


Wayace miki zaki mutu… mata nawa akayiwa basu mutu ba, kijini idan kinason wannan abun yawuce batare da kowa yasani ba wannan shine kaɗai abunda zamuyi, saboda magani yana iyayin kamar ya zubar amma daga baya saikiga abu yafito ido farida takara zarewa… toh kisawa ranki salama gobe da sassafe sai muje…



Wayan suka mika mishi, wani shu’umin murmushi yayi yace good job. 

Sosa keya ɗayan yayi yace oga saura sallamanmu…


rafan kuɗi Hasib ya ɗauko a aljihunshi yabasu, sukayi godiya suka tafi.


Ai dama jikina yabani zaka munafurceni shiyasa nasa masumin gadin ka duk inda kashiga, yanzu dai bari inga meye kakeson nuna mata…


Gallery yashiga har ya gama gani bai samu ba… 

Cikin audio wayan yafara playing ɗaya bayan ɗaya… har ya iso conversation ɗinsu, yasha mamaki don shi baimayi tunanin call ɗinsu yayi recording ba, sai yanzu yagane ashe yayi wauta daya ansa mishi direct… gumi ya goge sannan yayi dariya yace thanks to my brain dabanyi dabaran binshi ba daya jawomin bala’I. 


Kamar yadda goggo take dakon zuwan Abbas haka mardiyya ma duk wani abunda takeyi hankalin ta yanakan kofar gida, lokaci zuwa lokaci kuma tana share hawaye, ita dakanta yanzu batasan makomar rayuwar ta ba, batasan yaushe Abban ta zai yafe mata ba.


Kamar daga sama suka jiyo sallamar shi… wani farin ciki ne ya dira a zuciyoyin su, cikin fara’a goggo tace yanzu ko nake maganan ka araina, dama kai nake jira a tsakar gida… mardiyya kam tunda suka haɗa ido ta sunkuyar da kanta, tacigaba da aikin ta, yanzu shikaɗai ne farin cikin ta, ta fahimci ganin shi yana mantar da ita duka damuwowin da take ciki, anyama kuwa yanzu tanada kamar shi a rayuwar ta, saboda shi kaidai ne ya yadda da ita, kuma shikadai ne yasadaukar danashi farin cikin domin samo mata farin ciki… tana cikin wayannan tunanin kawai sai jiyo shi yana cewa.. goggo wannan autar ki ce?


Taɓe baki tayi tace, wai jika ce… 

Murmushi yayi yace kice kanwata ce… 

A’ah raba kanka, karka haɗa kanka da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyan… 


Saurin taran ta yayi da, subhanallah haba kaka bakyau munan kalamai suna fitowa a bakin babba irinki, tunda kikace jikarki ce ai ko bakomai jinin kice, kuma hannu ka bazai ruɓe kayar ba…


Haka kawai taji kunya ya lulluɓeta, yaro jikan cikin ta yana mata nasiha wanda ita yakamata ta mishi..


Cikin yanayin borin kunya tace, hakane yarona shiyasa zama da mutane yakeda amfani kaga yanzu ka tunatar dani abunda na sha’afa akai.


Hakane kaka, nima inason zama da tsofi kodon inji labarin abubuwan da suka faru abaya, dariya tayi tace indai wannan ne kasamu.


Kuma kinsan wani abu kaka… tace a’ah yace lokuta da dama yadda muke ɗaukan mutane ba haka suke ba, ballema ace munƙi baiwa zuciyar mu daman fahimtar wani abu dangane dasu, wannan yana kara nisan ta mu da ƴan'uwan mu… 


Shuru tayi yaci gaba da cewa, kaka shifa ɗa na kowa ne, bakyau tsanar ɗan Adam saboda shi ɗan Adam halittan Allah ne me daraja, sannan tsanar musulmi abune marar kyau a musulunci balle ma kuma ace wannan mutumin jinin kane, ribar mezaka samu idan ka ki shi... 


Akwai wani hadisin da yazo, Allah ma ɗaukakin sarki ranar tashin alkiyama, zaice ina waƴanda sukaso juna sabo dani, yau zan muku inuwa a inuwa ta, ranar da babu wata inuwa sai tawa…


Kaka komeye zamuyi arayuwan nan muyi shi don Allah… muso junan mu saboda Allah, karmu bari sheɗan ya ruɗemu haka kawai yasanya mana ƙiyayyan juna a zukatan mu, kar mubari laifin wani yashafi wanda baiji ba bai gani.. duka rayuwar duniyan nan bazata amfane mu ba matukar bamuyi dace a lahira ba…


Goggo kam kuka kamar wacce akayiwa mutuwa ta fashe dashi, dasauri Abbas yabar maganan dayakeyi yadawo gaban ta yazauna yana cewa subhanallah, kiyi hakuri kaka, bankawo miki maganan nan domin nasaki kuka ba, kiyafemin..


Kanshi tashafa tana kuka tace yarona bakamin laifi ba, kuma kukan dakaga inayi wakaina nakeyiwa, nakasance tsabar izza da masifa baya barin mutane sugayamin gaskiya… nayi rashin mutane irinka a eayuwa ta, waƴanda bazasuji shakkar gayamin gaskiya ba, inama dazaka kasance ɗaya daga cikin ahalina..


A zuciyar shi yace inshaa zan kasan ce ko ba yanzu ba… murmushi yayi yace toh nidai kibar kukan nan don idan kina kuka zanji kamar ni nasaki, hawayen ta tashare tana murmushi tace nadaina jikana…


Alfarma ɗaya nakeson in rokeka…


Inajinki kaka, inason kazo kanayiwa wannan jikar tawa nasiha, ko zatafara jin tsoron Allah a al’amuran ta, mardiyya kizo maza kifara jin maganan Allah da manzon shi… 


Ni bari in shiga ciki ina zuwa, tashi tayi tabasu waje.


Kallon mardiyya yakeyi, ita kuma ta sunkuyar da kanta banda hawaye babu abunda yakebin fuskar ta, itama lokuta da dama tanason shanye kukan ta amma sai abun ya gagara… 



A hankali yace Mardiyya bakisan yadda ɗigan hawayen ki yake sosamin zuciya ba? Dagowa tayi tana kallon shi da idanunta da suka kunbura tsabar kuka, cigaba yayi da cewa, zuciya ta bazata iya jure ganin ki cikin ƙunci ba, ki temakamin kina ragewa kanki damuwa, idan ba haka ba nima zan iya samun matsala, matsala kuma wacce zata iya shafan rayuwa ta..


Sam bata gane ina waƴannan kalaman nashi suka dosa ba, hannu ta ya riƙe yace Mardiyya inasonki fiye da yadda nakeson kaina, inasonki irin soyayyan da ban taɓayiwa wani halitta ba, bazan taɓa iya rayuwa babu ke ba…. 


Zame hannun ta tayi acikin nashi duka jikinta rawa yakeyi…


Bazaki ce komai ba?


Girgiza kai takeyi cikin matsanan cin kuka tace ya Abbas idan har tausayina dakakeji shiyasa kaji ka sadaukar da rayuwar ka harma yasa kake tunanin yin rayuwa dani kayi hakuri… bazan so na zamo sanadin dakushema farin ciki a rayuwar ka ba, nasan akwai wacce kakeso, kar tausayi na yasa kayi abunda zakazo kana daka sani daga baya..


Tana kaiwa nan ta tashi da gudu zata wuce ɗaki, dasauri ya riƙo hannu ta, amma bata juyowa ba..


Zuciyar shi ya rike yace mardiyya tunda nake wata bata taɓa shiga zuciya ta ba sai ke, ba yau ko jiya nafara sonki ba… nafara sonki ne tun randa idanuna sukafara ganin ki… kullum rarrashin zuciya ta nakeyi akanki, idan kuma baki yadda ba zaki iya tambayar nabil..


Kallon shi kawai takeyi tanajin abun kamar a mafarki… idan bacci takeyi yakamata tafarka…


Takowa yayi har gaban ta yatsun shi masu taushi yasa yafara share mata hawaye, yana cewa banason ganin hawaye a wannan kyakkyawar fuskar, idan dai baso kike nima infara kuka ba, kuma gobe zanzo inshaidawa goggo komai gameda ni.. saboda bazaiyu inyita mata karya ba, yanzu zan tafi dan Allah ki kulamin dakanki, kuma kisawa ranki komai yakusa zuwa karshe... 



Mardiyya kam ko motsi takasayi har ya fita binshi takeyi da kallo tama rasa meye yakamata taji, farin ciki ne ko bakin ciki oho.


Hango ta yayi acikin gari tana zuwa gun mutane kowa na tureta, aranshi yake cewa wannan ba mardiyya ta ba, da sauri ya karisa wajen ta, yana cewa mardiyya, fuskanta ya rike yana cewa mardiyyan Abba? Meyasa meki haka? Idonta da suka canja kala taɗago tana cewa Abba na kaima kagujeni, waye zai so ni? Babu Wanda ya damu dani… Abba na mutuwa zanyi ninasan zan mutuwa zanyii…. 


Kidaina faɗan haka ina sonki mardiyya na bazaki mutu ba... 


Firgigit yatashi a baccin duk ya haɗa gumi, anty ce tace lafiya Alhaji kake mafarki a baccin rana… bakayi addu’a bako? Bai cemata komai ba yakasa daina ganin yadda mardiyya take kuka kamar ranta zai fita… 

Hmm… to saika tashi wai kayi bako ne. 

Bako kuma? 

Eh 

Baifadi sunan shi ba? 

Yace wai baka sanshi ba 

Ok, to gani nan zuwa... 


murmushi anty tayi don taji shi yanata cewa mardiyya bazaki mutu ba, wannan yana nuna tana ranshi kenan. 


Fita yayi yabashi hannu suka gaisa yanata ganin fuskar kamar yasanshi.. 

Yace Alhaji baka ganeni bako? 

Eh 

Suna na lauje… ina cikin mutanen dasuka zo nemawa Hasib auren mardiyya... 




*ZEETY DELIGHT*💖