chapter 24
by @zeety
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*
_na nemi comments kuma an suburbuɗomin shi ba wasa... nasha ruwan comments kam harna koshi😅, thanks all_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
24📚
Washegari sassafe Iklima tazo domin su tafi asibiti… tasamu farida ma ta shirya donko baccin kirki batayi ba tana Allah Allah gari yawaye… mama tasha mamakin sammakon su amma ko da ta tambaye su ce mata sukayi wata kawar su ne zatayi biki , zasuje ciro anko ne shiyasa sukayi sammako, mama kawai tajisu ne amma bata yadda ba, saboda yadda taga farida batajin daɗi kwana biyun nan ko fitowan kirki batayi shine har zataje wani cire anko…
Suna fita tasa direba ya bisu, basu tsaya ko ina ba sai wani private hospital, suna shiga, driver ya juya yana zuwa yagayawa mama ai asibiti sukaje, ce mishi tayi ta gode ya tafi, tashi tayi tafara sintiri, to ma meyasa zasu ɓoye mata don zasuje asibiti? Idan wani zasuje gaisarwa ai ba hanasu zatayi ba, idan ma ɗayarsu ce ba lafiya ai yakamata tasani, sam zuciyar ta bata yadda dasu ba don haka gyalenta ta ɗauko tace driver yakaita…
Dama already Iklima tayiwa likitan bayani, don haka suna zuwa tace mishi doctor gatanan…
tsayawa yayi yana karewa farida kallo yarinya kyakkyawa haka ta bata rayuwar ta, da sauri ya kawar da tunani da yakeyi yace mata muje ko, kallon iklima tayi idon ta ya cicciko da hawaye, ido iklima ta mata nata bishi, gaba yayi ta biyo bayan shi, wani ɗaki suka shiga a office ɗin shi, yasata ta kwanta akan gadon dake ɗakin, zuciyar ta sai bugawa takeyi rokon Allah takeyi Allah yasa karta mutu… itakam batajin zata kara yadda da wani da namiji a rayuwar ta, wanda tayi ma bata gane komai ba, banda damuwa da farga babu abunda yajawo mata, daɗi da ƙari ma ga saɓawa ubangijin ta datayi… gsky lokaci yayi dazata koma ga Allah ko zai yafe mata, ita ya Abbas ɗinma ta hakura dashi komai na duniya ya isheta… wannan tunanin duka aranta takeyi kafun a gama haɗa kayan aiki… wasu hawaye ne suka farabin gefen idonta zuwa kunnen ta…
Basu fi awa ɗaya ba likitan yafito yacewa iklima angama, amma fa da matsala tashi tayi tadefe kirjinta tace doctor wane irin matsala? Muna bukatan jini ne saboda jinin ta yazuba dayawa sakamakon fitan dole da akayiwa cikin kuma yafi wata daya…
Innalillahy kawai iklima take cewa…
Ki kwantar da hankalin ki ana samata jini shikenan komai zai daidai ta, yanzu dai kije ɗakin sayar da jini wani paper ya mika mata yace ganan blood group ɗinta ki sayo leda biyu sai insa mata anan...
Karɓa tayi da sauri tafita, tana fitowa tacikaro da mama turus taja ta tsaya… sai fiƙi fiƙi takeyi da ido… gyara tsayuwa mama tayi tace ankon a asibiti ake cirewa? Shuru tayi bata iya ansawa ba…
Kamota mama tayi sukayi gefe, tace iklima...
ɗagowa tayi takalli mama…
Kigayamin komai banason ƙarya, idan kikamin ƙarya kinsan dole zan gane… kuma idan nagane bazaku kwashe da daɗi ba a wajena…
Kuka tafarayi, sannan tace mama ki gafarce mu, munso muyi komai a sirri amma ya gagara saboda yanzu haka naji daɗin ganin ki farida tana cikin wani hali, yanzu haka ma jini ake nema akara mata…
Rike kafaɗan iklima tayi tace ashe bakuda hankali… ta yaya zaku bari ciki yazauna? Wayece muku yanzu ana yayin ciki?
Ba halinta bane ansamu matsala ne shiyasa abun yazo a haka…
Yanzu tana ina?
Tanacan ɗakin jini zanje nemowa… karɓan paper mama tayi tace zo muje
Tare sukaje lab ɗin, aka duba ba’asamu wanda zaiyi matching da jinin ta ba…
Yau tun safe ya shirya saboda ya matsu ya kawowa zeezee voice ɗin nan, yau kam ma bai nemi yaro ba shida kanshi yayi knocking megadi ya fito, yace mishi dan Allah yanason ya mishi magana da zeezee ce, take yaje yagaya mata, baifi minti biyar ba ta fito, bata sha mamakin ganin shi ba, saboda tunda taji ana sallama da ita tasan bazai wuce shi ba..
Gaisawa sukayi sannan tace yau kuma dame kake tafe?
Numfashi yasauke sannan yace haba zeezee wallahi bazan zo har gidan ku domin in munafurce ki ba, kuma inayin wannan abunne kawai saboda mardiyya, inajin tausayin ta tun kafun abun yazamo haka yanzu kuma da lamarin yaɓaci naji banida sukuni matukar ban temaka mata ba…
numfashi zeezee tasauƙe sannan tace inajinka idan har dgsk kakeyi…
Haraban wajen ya dudduba sannan yace mata idan da hali mushiga mota saboda gujewa irin abunda yafaru ranan…
Wani urin kallon data watsa mishi ne yasashi cewa to idan zaiyu ko cikin gidan ku mushiga… amma kisani ni wallahi babu mummunan nufi araina.
Better… kawai tace sannan tayi gaba ya biyota, ciki suka shiga ta rufe gate ɗin, wayan shi ya ciro ya kunna mata audio sukaji tare… da sauri ta wafce wayar tasake playing sannan tace mishi turamin dasauri…
Take ya tura mata sannan yace idan kinyi making any moves sannan kikaji kina bukatar temako na ga number na ki ƙirani compliment card ɗinshi yabata, karɓa tayi tace ta gode sosai..
Kuma inason ki kaiwa Abban mardiyya yaji dawuri tun kafun abu yayi nisa…
Wayarshi da aka kirane yasashi yanke maganan, ɗauka yayi sannan yace toh shikenan gani nan zuwa.
Sorry zan tafi anneme ni a gida zankai sister na asibiti…
Badamuwa Allah ya bata lafiya, nagode sosai, kuma zankira ka kaji duk abunda ake ciki..
Yauwa nima nagode sosai, sannan yawuce.
Yau Abbas tareda nabil sukaje, sunzo sun samu goggo tasa an haɗa mishi special breakfast… suna sallama ta washe baki, haka kawai ganin yaron yake faranta mata rai, a ahh yau kam mazajen dayawa ne kace sai ns darje in zaɓa… dariya yayi yace ai yau kam sai wanda kika zaɓa kaka…
Tabarma ta shimfiɗa musu tace ai yau nima banyi baccin safe ba saida natsaya naga an haɗawa angona abun karin kumallo..
Gaskiya godiya nakeyi sosai kaka, Allah ya saka miki da alkhairi yabaki gidan aljanna… tace Ameen yaron kirki...
Juyowa tayi tana cewa nabil kai kuma ɗan samari meye sunan ka?
Sosa kanshi yayi yace nabil… tace ohh irin sunan yaran zamani, amma dai kai naji sunanka ba wuya, wasu sunan kam kamar dama saboda kar tsofi irina su iya kiran sunan ake sawa…
Dariya sukayi dukan su.
Mardiyya takira tace takawo musu abinci… fito da abincin tafarayi saida tagama sannan tazo suka gaisa… sam yau taƙi yadda su haɗa ido da Abbas…
Goggo ne tace musu maza bismillah kuci abinci…
Ajiyar zuciya Abbas ya sauƙe sannan yace kaka inason muyi magana kafun nan…
Zaman ta ta gyara sannan tace, wane irin magana ɗan nan? Amma dai koma meyene kufara karyawa tukunna…
a ah kaka zanfi jin daɗi idan nagaya miki…
Ni kuma zanfi jin daɗi idan kunci abinci… ganin ta dage kawai ya zuba musu.
shikam baya wani iyaci, saboda hankalin shi a tashe yake baisan tayaya zata karɓi maganan ba… kuma yana tsoron kartaga ya munafurce ta, saboda ta yadda dashi sosai acikin ɗan kankanin lokaci…
Goggo ganin yadda yakecin abincin yasata gane lallai yana cikin damuwa, kuma ko meye ne abunda yakeson gaya mata ba karamin abu bane…
Duk jitayi jikinta yayi sanyi, kome yake damun yaron nan oho, itama duk saitaji tanason taji me zai gaya mata, ita da nabil kawai suke taɗi sama sama shikam baya ko sa musu baki ahaka har suka gama cin abincin…
Saida aka tattara wajen sannan goggo ta tattaro hankalin ta tace inajin ka yaro na meke tafe dakai…
Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan yace kaka bansan ta ina zan fara ba saboda bansan ta yaya zaki ɗauki abunda zan gaya miki ba…
Amma abu ɗaya nake neman alfarma agareki shine… ki yadda dani, duk abunda zangaya miki wallahi iya gaskiya ta zan gaya miki bazan taɓa miki karya ba…
Zaman ta gyara tareda kallon shi tace, karka damu tun randa nafara kallon ka naga kamala, nutsuwa,haɗi da gaskiya a tattare dakai banajin ko kaɗan zuciya ta zata yadda kai zakamin karya ba, don haka karka damu kafaɗamin koma meye ne….
Huh… kaka ai na riga dana miki ƙarya shiyasa nake tsoron karki ki yadda dani a karo na biyu..
Karyan me kamin ɗan nan?
kaka dagaske ne ina bautar ƙasa amma ba’a garin nan ba, a kano nake service kuma ba haka kawai nazo gidan nan ba, dalili ne yakawoni, wayannan sune karyan dana miki…
wane iri dalili ne yakawo ka gidan nan?
Mardiyya! Itace dalilin zuwa na…
Take taji yanason ya juya mata kwakwalwa… tace tsaya, kana nufin dama kasan mardiyya?
Kai yakaɗa mata sannan yace nasan ta sosai, nine Wanda akayi mana sharri tare wanda dalilin haka yasa Abban ta kawo ta gari nan…
Innalillahy wa innalillahy raji’un…. Toh yanzu tunda ka biyo ta har nan garin meye hakan yake nufi… kana nufin bazaku daina fasikanci ba kenan….
rintse idon shi yayi sannan yace Kaka zan miki ratsuwa kuma tsakani na da Allah na…
wallahi wallahi bamu aikata abunda ake zargin mu dashi ba, sharri ne kawai irin na maƙiya, mardiyya mutumiyar kirki ce ba ma’abociya sabon Allah bane, ko ban ba da sheda akaina ba zan iya bayarwa akan mardiyya…
Abban ta yace min har video a ka muku a hotel? Tayaya kukaje hotel tare kuma duka a sharri ?
Zangaya miki komai kuma bazan ɓoye miki komai ba…
Shikenan ina sauraron ka, amma kasani idan kamin karya duk randa gaskiya ta fito bazamu kwashe da daɗi ba…
Na yadda… nan yakwashe duka abunda yafaru yagayawa goggo… shuru tayi don jikin ta yayi sanyi kuma ta yadda dashi har ranta...
Mardiyya ta ƙwalawa kira ta fito, dama tana laɓe a kofar cikin tana jinsu… fitowa tayi hawayen fuskarta sunkasa tsayawa ta tsuguna tace gani.
Kallon ta goggo tayi tace kinji abunda yace dagaske ne hakan yafaru… kaɗa kai tayi tace dagaske ne…
Maida dubanta tayi ga Abbas tace to meyasa ita faridan zata muku haka?
Nakasa tsayawa inji dalilin ta na ɓata mana suna ne saboda ganin za’a ɗauke mardiyya a kano, inason insan halin dazata shiga kafun nan inkoma…
Hmmm….. yanzu ai dole tare zamu koma yanzu zan kira Abban ta ince ya turo mana mota…
Zeezee ko gida bata shiga ba tawuce gidan su mardiyya kuma taci sa’a Abba na nan tacewa anty wajen Abba tazo…..
Magana aka mishi yace ta kariso…
Shiga tayi ta gaishe shi, sannan yace lafiya zainab kike nema na, sunkuyar da kanta tayi tace dama Abba akan maganan mardiyya ne take ta kwashe duka abunda yafaru tsakanin ta da faisal tagaya mishi takuma kuna mishi audio nan, jiyayi ba daɗi sam bai kyautawa mardiyya ba amma bazaitaɓa barin Hasib ba sai ya fanshe ɓatawa ƴarshi suna da yayi saiya ɗaureshi… suna cikin maganan aka ce mishi lauje yazo yace ace mishi ya iso, karisowa falon yayi, ya miƙawa abba disc ɗin, miƙewa yayi yaje ya kunna DVD yasa, lokacin anty ta shigo…
Komawa yayi yazauna dukan su kowa tv yasawa ido, take akwatin television ɗin yafara nuna musu komai tundaga shigowar mardiyya ɗakin… har zuwan Abbas da duka abubuwan dasuke faɗa… jin sunan da suka ambata yasa Abba saka pulse juyowa yayi yacewa zeezee wayece farida?
Abba farida ce kawar mu tanan gidan Alhaji hanif…
kai kawai ya girgiza.. babu wanda yakara magana har suka gama gani..
Murmushi anty tayi tace Alhamdulillah, yanzu kam ai zaka yadda ko, bansan meyafaru ba, bansan yaya akayi mardiyya tashiga wannan halin ba, amma har cikin zuciya ta nasan bazata aikata haka ba…
Abba kam shuru yayi ji yakeyi yayi abun kunya ace wai bazai iya shedan ƴarshi ba… bayan shida kanshi yasan irin tarbiyar da yabata,amma ba laifin shi bane kawai yayi la’akari da yadda yaran zamani suka lalace ne, saboda tarbiyyar da zakayiwa yaro daban abunda zaije ya aikata daban..
Ko tunani bai gama ba wayar shi tafara ringing yana dubawa yaga goggo ce ɗauka yayi suka gaisa sannan yace mata gobe zai turo a ɗauki mardiyya, tace nima dama maganan dazan ma kenan, zance katuro mana mota zamuzo saboda akwai abubuwan da dakaina nakeson inma bayani gameda abunda yafaru kwanakin nan…
dama nima abunda yasa nakeson tadawo kenan saboda ansamo wasu abubuwan da suke nuna sharri aka musu…
mashaa Allah tunda kaima kagane dakanka, amma dai duk da haka tare zamuzo.
to shikenan yau driver zaizo inyaso gobe sai kuyi sammako.
Allah ya kaimu.. haka suka kashe wayan.
Zeezee ya kalla yace ki nemo mana wanda yabaki voice ɗin nan domin ya bamu address ɗin shi Hasib ɗin, yau ɗin nan basai ankai gobe ba zan haɗashi da human rights sannan zan nemo alkali a shiga kotu.
kai kuma meye ma kace sunan ka?
Sosa keyanshi yayi yace lauje.
a ah nikam kagayamin asalin sunan ka.
Dariya duka akayi yace Ismail.
Abba yace mashaa Allah ji sunan ka medadi, kaje ka ɓata sunan ka da girman ka, don dai dagani kanada iyali.
Kai ya girgiza yace ba shakka yarana biyar, yanzu haka babbar yarinya ta ma tana secondary.
Kaga irinta ai, yanzu fissabilillah wane irin tarbiya kake koya ƴaƴanka gameda abubuwan dakake aikatawa… kuma ma kana da ƴa mace, waye kake tunanin zai aureta idan akaji halin uban ta, bama wannan ba, ana haɗa baki dakai ana munafurta da lalata rayuwar ƴaƴan wasu kai baka tunanin makomar naka yaran?
Sosai jikin lauje yayi sanyi…
Cigaba Abba yayi… kadai ji tsoron Allah tun kafun lokaci yakure ma, abu nagaba kuma shine nagode sosai bisa temakon da kamana, babu abunda zance ma saidai Allah ya saka da alkhairi, kuɗi Abba ya ciro yace gawannan ayi cefane…
A ah Alhaj wallahi bazan iya karɓa ba, nasihar dakamin ma kaɗai ta isheni, kasa naji ina danasani da kaicon rayuwa irin tawa… inshaa Allah bazan karayin wannan sana’ar ba kuma ko a kotu idan kana neman temako na zanma..
Mashaa Allah naji daɗi sosai dakayi nadama, inshaa Allah, Allah bazai barka haka ba zai tallafa ma, wannan kuɗin ba biyan ka nayi ba, kyauta nabaka kayi hakuri ka karɓa kuma ko nan gaba idan kaji kanada matsala karkaji shakkan zuwa wajena… yanzu ma idan komai yalafa kazo muyi shawara inbaka jari kasamu sana’aryi saboda kujewa komawa ruwa..
Karɓa yayi saboda yadda Abba yadage, yace nagode sosai Alhaji, babu wanda yataɓamin magana akan halaye na, sannan kuma mu bama zuwa wajen wa’azi ko ƙarin karatu balle muji Allah yace annabi yace, kaine mutun na farko dakamin magana naji nadama har cikin raina, inshaa Allah zanyi kokari wajen gyara halina..
Goggo kallon Abbas tayi tace kaji yanzu Abban ta yake cemin sun samo wasu shedun da yake nuna sharri aka muku yau driver zaizo gobe muwuce zaku iya zuwa mu tafi tare..
Ajiyan zuciya Abbas ya sauƙe yace Alhamdulillah, badamuwa zamu tafi tare kaka saidai muma da mota a hannu mu, amma dai zamu zo nan sai mu tashi tare…
Yana kai ƙanwar shi asibiti akabata gado take aka samata drip, yafito kenan zaije wajen sayan magani yaci karo da iklima, yace iklima tace faisal…
Waye bashida lafiya ya tambaye ta..
Kallon mama tayi sannan tajashi gefe.. take hawaye yafarabin fuskar ta, gogewa tayi tace faisal abokinka ya cucemu, kuma Allah bazai barshi ba…
Wane aboki na?
Waye banda Hasib, goshin shi ya riƙe yace meyafaru?
Meyene bai faru ba… yayiwa farida ciki ya watsar da ita, kukane yafara cin karfinta… tace munso muyi komai a sirrance amma yagagara, gatacar yanzu tana kwance rai a hannu Allah… za’a samata jini amma mun rasa wanda zai bayar… cikin kuka tace yanzu ni damuwa ta idan farida ta mutu da hannu na aciki don ni nakawo mata shawara muzo ayi flushing… Allah ka temake ni….
Innalillahy kawai faisal yake maimaitawa, yace mata look iklima ni yanzu haka banida haɗi da Hasib… ko inda yake ban sani ba balle in mishi magana, amma zan muku temako ɗaya muje a gwada jini na idan yayi daidai sai a eba asa mata…
Take suka wuce lab aikuwa ana gwada jinin yayi matching, take aka ebi har leda biyu…
Baban ta mama ta kira ta sheda masa suna asibiti anbaiwa farida gado har anƙara mata jini…
Yace dama batada lafiya ne? kuma yaushe akafara zuwa asibiti a gidana ba tareda sani na ba?
Yanzu dai kayi hakuri yanayin jikin tane yasa muka tafi ba shiri… sai yanzu nadawo hayyaci na shiyasa ma nakira ka…
toh shikenan ina zuwa.
Yau zeezee takasa rufe bakinta Allah Allah take gobe yayi mardiyya tadawo… Allah abun godiya haka Allah yake lamarin shi..
Ya harun dayake tsaye abayanta ne yace lafiya kiketa murmushi ke kaɗai..
Juyowa tayi tareda faɗaɗa murmushin ta tace albishirin ka ya harun… yace goro.
Tace asirin wayanda sukayiwa mardiyya sharri ya tonu, gobe zata dawo…
Jiyayi kamar ta bugamar guduma a kirji, yace bangane ba… kina nufin wannan video sharri ne? tace tabbas sharri ne kamar yadda aka yaɗa wancan video haka zamu sake yaɗa muku gaskiyar lamarin kujira zuwa gobe komai zai bayyana…
Shuru yayi… ko ƙala baice mata ba ya wuce side ɗinshi…
Dariya zeezee tayi tace bakaga komai bama kanaji kana gani mardiyya zata auri MURADIN RANTAH.
(saudat da tuttu dafatan kunga read more ɗin da kuke buƙata🤣🤣🏃🏻♀️)
*ZEETY DELIGHT*💖