3&4
by @realeshaa
*KI YADDA DANI.*
_Kishiya Ko Baiwa_
_Return_
_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA*
_WATTPAD_
*Realeshaa*
_Like my page on Facebook_ππ»
***
*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*
_Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki Naira Dari biyu se ki turo da katin MTN ta wannan number ππΌ*** Tare da turo da shedar biya ta Wannan number ***.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._
*FREE Page 3&4ποΈ*
______________________πIna shiga daki nakife kaina akan cinyata ina wani irin kuka me ban tausayi tare da tausayawa rayuwa ta abisa kalubalen danake fuskanta gani nake kamar laifi nayi wa Ubangiji shiyasa yake jarabta na tahanyar mijina.Jiki asanyaye Ummi tashigo dakin,kusa dani tazauna tare da dafa kaina,cikin taushin lafazi da dum bin kaunata irin wanda duk Uwa keyiwa 'yar ta,tace".Suky kiyi hakuri da abinda yake faruwa dake azamanta kewar rayuwar auren ki, musamman ma irin na yau,dole zuciyar ki zata 'darsa miki wani Abu dan gane da yanda abubuwa suka dinga faruwa kuma bamu dauki mataki akan Ahmad ba nasan dole zuciyar ki zata dinga zargin wani abu.Tanumfasa tare da rike hannun na acikin nata cikin taushin lafazi da tausayin na tace".Kisani muna matukar kaunarki fiye da yanda kike tunani,munayi miki so irin Wanda bakya zato,sannan wannan abu, dakike ganin yana faruwa dake kaddarace Wanda tariga fata"Dan haka kiyi hakuri ki dauki kaddaran ki da hannu bib biyu,Ki kuma cigaba da addu'a, idan komawar ki gidan Ahmad shine mafi alkhairi toh Allah ya yayyafawa zuciyar sa ruwan sanyi yamayar dake dakin ki,Idan kuma babu alkhairi Allah yasauya miki da mafi alkhairi, anma ninafi sha'awar kikoma dakin mijinki kuje kureni abinda zaku haifa atare idan har hakan shine yafi alkhairi...
Kallon ta nake cike da dumbin mamakin kalamanta,yayin da wani malolon bakin ciki, yatokare min makoshi!.Shin anya Ummi susuka haifeni kuwa??domin bana tunanin ko makiyina zeyi min fatan nakoma gidan Ahmad amatsayin matarsa bare kuma ace masoyana,ko kuma iyayena Wanda nake jin sunfi kowa kaunata acikin duniyar nan,Anma wai ace su suke yimin irin Wannan addu'ar zuciya tace tasake tabbatar min dacewa tabbas basu ne asalin iyayen ki ba.Zuciyata ce kasake tabbatar min da abinda nake zargi gaskiya ce,dan gani nake tamkar basa sona ne,ko kuwa basu suka haifeni ba,yasanya su suke yimim irin wannan mummunar fatan.Akan suyi min fatan nakoma gidan Ahmad gwara su yimin fatan mutuwa inaganin shize fiyemin alkhairi da in koma Wannan ukubar...Ahankali nadago kumburarrun idanuna dasuka rine saboda kuka, sun sake luhu-luhu dasu kana kwarmin idanun sunyi baki yayin da cikin idanun sukayi jaa saboda tsananin kuka da tashin hankali da kullum nake ciki.
Akan fuskar Ummi na data tsareni da idanu nima nasauke nawa,nakai kimanin minti daya ina Kallon ta batare da dayan mu yayi kokarin janye idanunsa ba,babu abinda nake Iya hangowa acikin kwayar idanun Ummi na banda tsantsar tausayi na da kuma kaunata.Atake naji zuciya ta takarye akan zargin da zuciya ta keyi musu,anma duk da haka bana tunanin zan kasa yimata tambaya akan abinda zuciya ta kesaka min.
"Cikin rawan murya nace"Ummi.Dasauri Ummi takatseni tahanyar daga min hannu batare data bari taji abinda zance mataba.Murmushi tayi Wanda yafi kuka ciwo,kafin tace dani"Suky nasan abinda zuciyar ki take saka miki baze wuce kiyi tunanin cewa bamu bane iyayen ki, shiyasa kike ganin kaman muna nuna halin ko inkula agareki.Wanda Sam bahaka bane,duk duniya bakida iyaye ko kuma masoyan dake sonki sama damu,Dan haka kikori shedan daga zuciyar ki kada kibari yayi tasari agareki ...Hawayen fuskata nashare Wanda bansan ranan dazasu dena zuba daga fuskata ba,cikin rawan murya nace"anma Ummi meyesa kukeso in koma gidan Ahmad inde har ku kuka haifeni??bayan duk irin wulakan ci da tozarcin daya gama yimin!!?Ummi kadda ace abinda Ahmad da Nadiya kefada gaskiya ne saboda kwadayin dukiyar sa yasanya kuka Aura masani!??na karashe cikin wata raunanniyar murya me nuni da zallan gajiya da rayuwar...
Mikewa Ummi tayi cikin wani yanayi wanda ke nuni da taji zafin maganata,anma batace min komai ba sema Kallona datayi cikin kulawa tace"ki kwanta kihuta,domin kina bukatar hutu ayanzu,idan kinsamu nutsuwa zamuyi magana akan tambayar dakikayi min,Tafadi haka asanda take ficewa daga dakin.Da kallo nabita har ta ida ficewa,gyara kwanciyata nayi akan gadon duk da kasancewar yamma tayi anna haka nakishin gida ina tunanin rayuwa da haka bacci yadaukeni Wanda duk tunanin Ahmad ne ya adda beni....Washe gari ina zaune adaki bayan na idar da salatul duha ban tashi akan sallayan ba se lazimi danake dakuma istigfari,Ina rokon Ubangiji daya kawo min sassauci acikin rayuwa ta...
Sallaman Sofi'a naji suna gaisawa da Ummi,bayan sun gama gaisawa ne najiyo muryan Ummi nacewa kishiga ciki Suky na nan.Cike da farin ciki naji muryan Sofia nacewa kai anma naji dadi Wallahi, dama inaso inje gidan ta dan nayi missing dinta,kuma dana kirata se tace"tayi tafiya Ashe tadawo,shine ba tasanar dani ba,tafada asanda take daga labulen dakin bakinta dauke da sallama takarasa shigowa.Amsa wa nayi kaina akasa,ina mai cigaba dajan carbin dake hannuna,banaso indago fuskata ta fuskanci ina cikin damuwa.Cike da farin ciki Sofia takaraso kusa dani tare da rungumeni.Wasu hawaye masu zafin gaske ne suka zubomin daga idanuna,kawai nima na rukunkumeta iname fashewa da kuka cike da kewar aminiyar tawa.Dago kaina tayi cike da zolaya tace"Kai Mr Ahmad wannan kukan!!..kasa karasawa tayi ganin yanda kasan idanu na suka dafe saboda kuka ga yanda kwayar idanuna sukayi jaa.Cike datashin hankali tace"Subhanallah,meyesa meki haka Sukainat!?? Kasa bata amsa nayi sema sake rungume ta danayi inaci gaba a kuka.Batayi yunkurin hanani ba sema bubbuga bayana dataci gaba dayi alamar rarrashi,seda taga nabar kukan nakoma ajiyar zuciya alamar naji saukin abinda ke zuciya ta.Dan Allah Suky kisanar dani matsalan ki bana son ganin ki cikin wannan yanayin yana tayar min da hankali.Kallon ta nayi ina sauke Ajiyar zuciya nace"Hakika da nasan haka auren me mata yake da banyi ba,babu komai acikin auren me mata face zallan tashin hankali dakuma bautuwa.Na numfasa tare da gyara zamana kana na zayyane mata duk irin matsalolin dana dinga fuskanta agidan Ahmad har zuwa sakin da yayi min jiya agaban iyayena Wanda idan har natuna nakanji kuna da tsantsan tsanarsa a zuciya ta.Salati Sofia tayi tare da rike haba cike, da takaici dakuma tausayin aminiyarta ta tace"Bakomai Ahmad be zalin ce ki da komai ba kansa ya zalunta kuma Insha Allah seya girbi abinda ya shuka,Ta numfasa tare da fadin "Lalle Ahmad yacika,Butulu matsiyaciya kuma la'ananne,na rantse da Allah muddin Ahmad begyara rayuwar sa ba,toh bazeyi kyakykyawan karshe ba seda yaga yaraba ki da Abu mafi daraja a rayuwar ki sannan ze sakeki,dama sha'awarki yake ba son gaskiya ba!?.Shin wai me mata ke nema aduniya ne!?Wannan kishiyar taki tacika makira anma bakomai kanta tayiwa da sannu Allah zehadata da wacce zata daidaita mata rayuwa.Wallahi Suky natayi ki farin ciki narabu wa da wa'annan azzaluman Allah kuma yayi miki sauyin alkhairi.Ameen na'amsa ina tambayar ta yasu mama?,amsa min tayi dasuna lafiya"Zama tagyara tare da fuskanta ta,tace"toh yanzu ya maganan karatunki?Murmushin dayafi kuka ciwo nayi,nace"Wallahi bansani ba sede injirayi hukuncin da Abba zeyanke,kuma kinsan bazeyi na tunkare shi da maganan ayanzu ba.Kai ta girgiza cike da gamsuwa da magana ta tace"Allah yasa muji alkhairi,yakuma sa Abba ya barki mu cigaba dakaratun mu atare.Murmushi nayi nace"aikin yi min nisa yanzu,'dan harara na tayi tace"bawani nisa kwana nawa ne rata shekara daya ne fa ze zama a tsakanin mu"nace haka ne kam Allah yamana zabin Alkhairi"Ameen ta amsa tare dacewa anma Idan Har Abba ya amince da karatun ki Wani course zaki dauka?Ina Murmushi nace"Islamic studied, Allah yacika miki burin ki,Ameen na amsa.Hira muka cigaba dayi cike da kaunar junan mu wanda yasanya naji kaso kashi ashirin Na cikin damuta yaragu,se bayan sallan azahar Sofia tatafi dan seda mukaci abinci rana tukunna...
"Yau kimanin sati biyu da dawo wana gida.Alhamdulillah kula na musamman nake samu daga bangaren iyayena duk abinda zasuyi suga sun faranta min rai shi sukeyi,dan ganin sun kawar min damuwar danake ciki.Sofia da mahaifiyar ta ma ba'abarsu abaya ba wajen ganin sun faran tamin,domin kusan kullum se Sofia tazo tade be min kewa kusan yini zamuyi kasancewar sun sami hutu.Ahmad kuwa tun daga ranan da yatafi babu labarin sa domin koda wasa bekirani ba bare ya tambayi lafiyar abinda ke cikina koda ni baze tambayani ba yakamata ya tambayi ajiyar sa dake kumshe amarata.
Yanzu Abu daya ke damuna,shine tsananin wa wanda narasa yanda zanyi kusan kullum da wannan jaraban nake kwana nake tashi,kuma nasan cikin jikina ne yasanya min.Aduk sanda naji irin haka kwana nake ina kuka narasa Wanda zan sanarwa da damuwa ta ya magance min...
*******
Abangaren Ahmad kuwa,yana fita direct gidan sa yawuce yana zuwa bedroom din Sukainat yanufa ya kwanta,ji yayi wani Abu mai nauyin gaske yasake danne masa zuciyar sa fiye da nabaya,Wanda yarasa menene.Tun daga Wannan ranan yakasance cikin kunci da damuwa Wanda yafi nada.Yayin da Nadiya tasanya shi agaba da bala'i kalala kullum cikin muzan tamasa take da cin zarafinsa koda kuwa agaban Uban kowa ne.Bashida wani katabus da zeyi kullum cikin hantara da wulakan tasa take...
Yauma kamar kullum zaune yake afalon ta yazab ga tagumi dan tahana sa shiga sashen Sukainat,Kasancewar can yamar wajen zaman sa.Tunanin rayuwa yake Wanda ko kadan bayajin dadin rayuwar tasa ayanzu.
Saukan ruwan sanyi dayaji ajikinsa ne yasanya shi,dago kai Azabure yana Kallon ta rike da goran swan water, tana jifansa da kaskantaccen kallo. Aharzuke tace"Wannan wani irin rashin mutunci ne haka?Inata magana kayi min banza saboda kamaidani sakarya,sannan tun jiya nake ce maka kasanar da Wannan yar matsiyatan tazo ta kwashe kayanta inada bukatar sashen.Anma ka yimin banza saboda banida muhimmanci awajen ka,takarashe cikin kumfar baki...Kasa da kai yayi yana jin wani iri acikin ransa,cikin sanyin murya yace"Dan Allah kiyi hakuri Insha Allah zan sanar dasu suzo sukwashe anma kidan bani lokaci.Banza kallo ta watsa masa kafin tace "Wallahi nabaka nanda sati suzo su kwashe kayan su in bahaka zakuga rashin mutunci!daga kai harsu.Dan nalura da take takenka kamar so kake kadawo da ita kuma Wallahi abinda baka Isa ba kenan tanagama fadin haka tashige bedroom din ta tare da banko masa kofa.
Dafe Kai yayi yana me jin wani irin yanayi Mara dadi atare dashi,Shin yatakeso yayi da rayuwar sa ne!.Mikewa yayi yadauki key motarsa direct gidan hajiyar sa yanufa ko zeji sassaucin abinda ke damun sa,driving yake anma baki daya zuciyar sa cike take da tunani kalala...Falon nata yashiga bakinsa dauke da sallama zaune ya hangota,ta hakimce akan kujera tare da kannensa suna hira.Ganin sa yasa tawashe baki tare dacewa Ahmad Kaine!?Kai ya girgiza mata alamar eh" batare dayace komai ba.Da kallo suka bisa ganin yanayin sa kamar Mara lafiya!.Cike da kulawa tace"Ahmad lafiya kuwa naga duk karame?Kai ya girgiza cikin raunin murya da tsantsar damuwa Yace"....
_Dan Allah kutaya ni shearingππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»_
_VOTE_
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»