Zamani...

Preview

by @sakina1

"Ina kud'in mai d'inkin suke? Allah Yasa baki mantasu can ba dai!" Wata mata ta furta a d'an k'age yayin da take shan wani layin tana tuka mota, tana baro layin Family house insu, dasu ka kaima ziyara.


"Wanne kud'in? Ni ba Wanda yabani wani kud'i" Yarinyar da Akalla bazata gaza shekaru 18 ba ta fad'a, kuma kallo d'aya zakamata kasan 'yar matar da ke driving d'in ce.


"Wani irin ba Wanda yabaki kud'i? Baby kud'in da nace ki dakk'o cikin wardrobe tun muna gida, zakicemini ba Wanda yabaki kud'i? Ba ke gimbiya tabasu ba ki ajiye tunda farko?" Matar ta furta a hasale, tana parking tsakiyar titin da take kai, dama hanyar ba wani wurin wucewar motoci baneba, irin hanyoyinnanne na cikin layi masu yashi.


"Mama Nikam bani gimbiya taba ajiyar kud'in ba, ba ita ta ajiye miki da kanta ba, inaji fah kamar kafin mu fito tana cemiki kud'in basu hannuna, ita ta ajiye" ta furta, idanunta na soma fidda kwalla, Dan dagaske ita dai taji kaman da maman tace a dakk'o mata kud'in gimbiyar(mai aikinsu ce) tace ba ita taba kud'in ba, Amma ga maman tana cewa ita akaba, tana zare mata idanu tana neman marinta, in akwai abinda ke d'aga mata hankali bai wuce fad'a ba wallahi.


"Yimin Shiru da iskanci, Ina kallo fah lokacin da ta gama k'irga kud'innan ta miko miki su, Ina daga kwance kinkasasu sama a wardrobe kinka aje, sannan dan rainin hankali kicemini ba ke akabaiwa ba? Wace iriyar mantuwa ce wannan tasameki? Baby bakimin adalci ba wallahi, yanzu gani zance karb'ar d'inkin Baki fito da kud'in ba, mtsssww" Ji takeyi kamar ta rufeta da duka, wannan ai rainin wayau ne.


"Yi hakuri, wallahi Ni na manta Dani taba, yi hakuri Dan Allah" Haka mamar take da zafi kamar me, abu kad'an ya isa ya sata tai fushi.


"Irin iskancinnan ne dakikeyi ana yimiki magana, kina tafiya, kina maida mutane 'yan iska, Ina zakijini ko ki tuna da an Baki ajiyar kud'i? Tun farko in kinsan bazaki iyaba, tun danayi miki maganar zaki cemini Baki iyawa, basai da na fito karb'ar d'inkinaba zaki kawo mini wata maganar banza" Ta cigaba da fad'an tana neman number mai d'inkin, ta riga tayi dashi cewar zata biyo ta karb'a yau d'in. "Abdulrashid Dan Allah turomini account numbern ka in sa maka kud'in" ta furta yana d'aga wayar, muryarta har yanzu akwai alamun fushi cikinta.


Har suka karasa gurin mai d'inkin bata k'ara ce mata komai ba, amma dai haryanzu fushin takeyi. Ta tsaya ta karb'i d'inkin sannan suka kama hanyar komawa gida.

Wani kukane taji yazo mata tun daga k'asan zuciyarta, ta kifa kanta kan hannun kofar motar hawaye na zubar mata, bataso, batason ganin maman na fushi irin haka, amma kusan basu tab'a wayuwar gari har maraice tayi irin hakan bata faru ba, bata san menene dalilin ba, duk yanda taso ta gujewa hakan, abun sai taga kamar yafi karfinta, har takai da wuya ta kai goshin a sujada cikin sallohlinta batare da ta nemi saukin wannan al'amarin ba. Ko yanzun ma addu'ar take, "Ya Allah, kana gani kana ji, Ya Allah ka bani ikon kyautatama iyayena, kabani ikon gamawa dasu lafiya, Ya Allah Kada Ka Karb'i rayuwata sai lokacin da iyayena suke ji dani, suna fad'in muna alfahari da kasantuwar 'ya a gurinmu, Ya Allah Kasa wannan yazamana rana ta karshe da zan sake yi mata abunda zatayi fushi dani" ta k'arashe a cikin ranta, hawaye na zirara. Kilan wannan ce tata kaddarar da ZAMANI yazo musu da ita, ba Mamanta kad'ai take k'orafi akan halayyar 'ya'yan zamanin ba, A'a, tanaji iyaye dayawa cikin 'yan uwansu da abokan arziki suma suma suna kokawa kan halin yaran yanzun.


Wani lokacin ba da son ranta take yin komai ba, amma sai taga tayi shi d'in, kamar ya zama wani habit nata. Maman tana luradda ita sosai, Dan saboda k'awaye ne, bayan Mahaliccinta batada wani Wanda take kusada shi kaman mahaifiyarta, takan ce mata "Baby ki dinga rage halayyannan, ba gabana zaki tabbata ba, duk Wanda bai girmama mahaifiyarshi ba, banga ubanda zai girmama ba, ni na d'aga murya ina miki magana da karfi yanda zaki jiyoni, amma ke kina karb'amin kamar na takuraki can ciki, ki canja Hali wallahi". Da gaskene walakanta mahaifiyarta take? Walakancine mana wannan, takan ba kanta ansa hawaye na zubar mata, ya zatayi ne? Tana addu'a, tanayi wallahi, kuma sai bayan tayi mata ne takejin wani nauyi ya saukar mata. Bata kyautawa tasani!


.....................................

Alhamdulillah!

Littafin ZAMANI.., zai zo muku bada jimawa ba

Me kukeji?

Share and Comment please

Ya Allah Ka bamu Ikon Kyautatawa Iyayenmu, Amin.