57
by @shooly84
🌱 *57* 🌱
*Rimin Gado*
Lokacin dasu Yawale suka isa gida ya nuna ma Yabi abun arzik'in da aka masa, gabaki d'aya gidan suka yita jin dad'i, yaran suka yita tsalle suna cewa zasu koma birni, daren yaukam Alhaji Abdullahi yasha addu'a har saida suka gaji da amsa ameen, haka acikin darennan yaje ya nuna ma Iyatu, nan itama tayita kwararo tata addu'ar.
**************
*Kano*
Tun bayan da Jamil ya koma ya kwanta da niyar bacci tinanin Maijiddah yayi masa sallama, ya kasa bacci saidai juyi, kyakkyawar fuskar Maijiddah ta rik'a yi masa gizo, idan ya rufe ido ita yake gani haka ma koda a bud'e ita d'in dai yake gani, yana tinano yadda take yi idan ta gansa kamar taga wani aljani, yana kuma tina yadda ta hankad'asa baya lokacin daya rik'eta bayan wani irin munafukin kallo da tayi masa da kyawawan idanuwanta wanda suke farare tas kamar audiga (kad'a).
"Meyasa tinanin kowa bezoman ba sai tinanin wannan yarinyar? Ina ruwana da ita? Amma Yarinyar bata da tsoro ko kad'an inason mutun irin haka, inaso naga macen da tasan ra'ayin kanta dakuma y'ancinta wanda shine abunda yayi wuyar samu anan k'asarmu bama kamar mu hausawa"
*(Tabbas maganar Jamil haka take, al'adar bahaushe ta d'auki y'ancin mata tayi watsi dashi wanda ko a addininmu ma munada y'ancinmu muna, amma mun kasance abun wulak'antawa, abun k'ask'antawa, bama kamar a zamantakewa ta aure, tabbas mace na k'asan mijinta amma sukan manta da cewa kamar yadda sukeda hak'k'ok'i akanmu haka muma addininmu ya gindaya masu namu hak'k'ok'in akansu, zakaga wasu mazan dasu siyama matarsu sutura ko su wadata ta da ingantaccen abinci gara su dunk'ula su kaima wata can waje kud'in taje ta huta, babban burin malam bahaushe ba kamar ma a karkara shidai ya k'aro aure, wai ta ciki ma bata wadata ba ake shirin kawo wata, don Allah maza ku rik'a kiyaye hak'k'inmu dake kanku sannan duk abunda zakuyi sai ya biyo baya, wasu lokutan k'arancin kulawarku ke kaimu ga halaka, muyi biyu babu, wallahi sirrin duk wani cigaba da nasara arayuwa shine kyautata ma mahaifa da Iyali sannan sai mak'ota, y'anuwa da marasa shi)*
Haka Jamil yayita juyi har bacci b'arawo yayi awon gaba dashi.
****
Da momy ta samu y'ar uwarta tayi bacci sai ta salallab'a ta tashi ta fita, taci sa'ar ganin Kamal a parlour, suka sake gaisawa sannan tace masa don Allah Hajiya takeson gani, Kamal yaje ya fad'ama Hajiya, sai hajiya tace dashi yace ta shigo d'akin, Kamal ya dawo yace ma Momy tace ta shiga d'akin, Momy ta tambaya inane d'akin, yaje ya nuna mata sannan ya dawo parlour ya zauna ya cigaba da abunda yake.
Da sallamarta ta shiga d'akin, Hajiya Uwa tayi mata nuni da gefen gado tace ta zauna, Momy ta zauna babu k'wari domin ko fuskar Hajiya Uwa babu annuri ko kad'an.
"Nasan abubuwan da suka faru yau duk sunyi miki wani iri sannan nasan a halin yanzu zuciyarki ta kasa amincewa da wannan qaddarar, amma inaso ki sani wallahi ban tab'a jinki a matsayin kishiya ba, ko rashin fad'a miki aurenmu da marigayi yayi saida nayi masa magana nace daya fad'a ni sam babu matsala ta daga b'angarena"
Wani irin mugun kallo Hajiya Uwa ta mata sannan tace "to daman kishi ai bana wadda zata shigo bane, kishi na wadda ke ciki ne, ta yaya ma kike tsammanin kanki da samun matsala bayan kayan wata kika ara ba naki aka ara ba?"
"To koma dai menene Hajiya ina rok'onki da kiyi hak'uri komai ya wuce, mudai yanzu ba yara bane kuma zumunci ne dai Allah ya riga ya had'a kada mu gujema hakan, naji nakuma yadda abunda akayi miki ba'a kyauta ba amma kiyi hak'uri, wallahi karki tona zuciyata kiji irin dad'in danaji d'azu da naga Jamil cikin y'an uwansa, Hajiya kiyi hak'uri"
"Keba Alhaji Abdullahi bace, ke Hajiya Abu ce, wanda yayimun laifi marigayi ne bake ba, kinko ga idan har wanda ya mutu yana dawowa to tabbas amincewa daku baze yiman wuya ba, bari kiji Abu wallahi ko ganinki banason yi, saboda inai miki kallon wadda ta k'wace duk wani farinciki dana cancanta arayuwa"
"Haba Hajiya meyasa zakice haka? Ki fad'aman meye abunda kika nema kika rasa a iya zamanki da marigayi? Wane farinciki ya tab'a k'auracema muhallinki yayin da kuke tare? nina tabbata badon haka ta faru ba, nasan baki tab'a tinanin mijinki nada wata mata ba, kuma da ace wani ne yazo maki da labarin sam bazaki tab'a yadda ba domin nasan marigayi be rageki da komai ba saidai kawai wannan laifin d'aya daya b'oye miki labarina, na zata ko ji kikayi marigayi ya kashe miki wani naki bayan rasuwarsa ke me iya yafe masa ne cikin gaggawa kodon ya samu haske da rahama a k'abarinsa albarkacin kyautata miki da yayi bare kuma wannan laifin dabe kai girman da kike bashi ba, haba Hajiya kefa da Alhaji kun riga kun zama damkar Uwa d'aya Uba d'aya saboda kunyi aure tun baku da wayo, duk duniya babu wanda ze kaiki sanin Marigayi, nidai ina k'ara rok'onki da kiyi hak'uri wanda kike fushin domin shi shima baya doron duniyar muma haka watarana zamu zam babu"
"Hmmm naji Allah ya yafe mana" amsar da Hajiya Uwa ta bata kenan, amma kai daga ji kasan bata kai zuci ba.
Momy dai tace "Nagode da kika fahimceni kuma Allah ya k'ara had'a kawunan mu"
"Amin" Hajiya Uwa ta sake amsawa atak'aice.
Momy tayi mata sallama tace zataje ta kwanta, Hajiya Uwa tace "Allah ya tashe mu lafiya" bayan data fita daga d'akin, Hajiya Uwa ta wani turo baki (zund'e) alamar "kanki ake ji"
(🤣 shegiya duniya, Momy kefa abunda baki gane ba wanda ni nagane shine "dakin d'auka wani abu acikin dukiyarki kin samma Uwa da komai ya wuce, don Uwa aminiyar duniya ce, da dukiyarki take kishi bada mijin ba, koko me kuka ce readers?).
****
Yaya shine mutun na k'arshe daya shigo gida, don haka yana shigowa cikin gida ya maida k'ofa ya rufe, isowar dazeyi parlour sai ya tarar da Kamal zaune yana danna waya,
" Kamal bakayi bacci ba kenan?" Ya tambaya yana mai zagayowa cikin parlourn, ya nema wuri ya zauna.
"Aiko ban kwanta ba tukun" Kamal ya amsa.
Yaya yace "nako ji dad'in ganinka don dama inason muyi wata magana"
"To Allah yasa lafiya" inji Kamal yana mai tattaro hankalinsa zuwa garesa.
"D'azu munyi maganarka nida Baba Yawale, ko nace maganarku kaida Maijiddah y'arsa, ya fad'amin komai, yadda kukayi dakuma yadda sukayi da Baba kafin ya rasu, yace yana ganin tunda dai kun daidai kanku babu abunda ake jira kenan, shine nace zamuyi maganar dakai kafin muje can k'auye akai maganar"
"Eh hakane amma nima dama inada magana daku kaida Uwa, ina jira ne bak'i su tafi, don haka ina ganin meze hana mubar maganar zuwa gobe idan Allah yakaimu?" Cewar Kamal.
Yaya yace "to ba damuwa yau da gobe duk d'aya ne wurin Allah, Allah ya bamu aron ran, nima inaga jibi zamu wuce tare da yara"
"Ok to Allah ya kaimu"
Yaya ya amsa da "Amin"
Yayi masa saida safe ya wuce d'akinsa.
***************
Washe gari.
Da safe Kamal yaje yayima Laraba tsaye don yasan halinta tana iyayin shirmen data saba, har ta kammala kayan breakfast, ta kaima kowa, Jamil da Kamal suka k'ara zazzantawa har suka karb'i number juna yakuma bashi ta Khalil.
Sune basu bar gidanba sai bayan Azahar, bayan wani zama da Yaya ya k'ara tarasu akayi na fahimtar juna.
Gida yayi shiru kowa ya kama gabansa.
D'akin Hajiya Uwa Kamal da Yaya suka shiga domin tattaunawa, kowa ya nema wuri ya zauna.
"Lafiya naganku haka?"
"Lafiya lau wata magana nakeson na fad'a maku ne" cewar Kamal, ai sai Hajiya Uwa ta gyara zama don itafa y'an maganganun nan sun fara isarta.
"Yaya tabbas ni naje na sami Baba Yawale kan cewa ina son y'arsa kuma ban taba sonta da wasa ba, amma kai nasan bakasan abubuwan dake faruwa a gidannan ba, bani kad'ai keson Maijiddah ba itama Uwa ta sani, Khalil na matuk'ar son Maijiddah kuma wallahi akanta ze iyayin komai kaidai san halinsa sarai, and'an samu sab'ani tsakanin Uwa dasu Baba Yawale wanda shine ma ya kawo sanadiyar barinsu gidan, tun lokacin Khalil ya had'a yanasa yanasa yabi su Baba Yawale kan cewa baze iya rayuwa cikin gidannan babu Maijiddah ba, yakuma k'udiri niyyar aikata komai saboda ita, kuma maganar gaskiya Uwa batason Maijiddah ta tsaneta, sanin kanka ne dama bawai tana ganin mutuncin shi kansa Baban Maijiddar bane, to hakama y'arsa babu irin kyautatawar da batayi mana ba cikin gidannan amma Uwa bata gani, ya kamata ka bata shawara don kaine babba k'ila ta fuskance ka, to duba da irin son da Khalil ke mata yasa na janye na bar masa ita, nakuma sanar masa nabar masa Maijiddah zankuma goya masa baya ya aureta, don dama bana tinanin na dace da ita"
"Kamar ya?" Yaya ya tambaya.
"Saboda ni me laifi ne, ina rok'onku da ku yafeman sannan ku fahimci dalilina na aikata hakan, wallahi niba d'an iska bane"
Yaya ya zaro ido gami da gyara zama yace "a'a Kamal dama wayace kai d'an iska ne? Ai kowa yana shedarka a gidannan meyasa zaka ce haka?"
Nandai Kamal ya kwashe komai ya fad'a masu, muryarsa na rawa.
Wani gumi Yaya yaji yana keto masa, ya fara fifita jikinsa da hannuwansa.
"Innalillahi na shiga Uku ni d'iyar Iro me nake ji haka, na bani na lalace Kamal yarinya fa kace? Yarinya fa kace har takai shekara hud'u kuma da arniya, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Kamal baka kyautamin ba baka kyauta ma kanka ba, yanzu Auta da nake ganin shine yafita zakka a y'ay'ana be kawomin d'an shege ba sai kaine zaka kawo, garjejiyar d'iya har takai shekara hud'u, ohni y'asu ina zansa kaina" aiko ta fara kuka tana sallallami.
"Uwa dama bana saran ki yafeman ayanzu, bakamar ma yau da abubuwa sukayi miki yawa amma nasan zaki yafeman, wallahi niba d'an iska bane Uwa, burina ya cika yau saboda na sauke nauyin da yaketa addabata tsawon kusan shekaru biyar kenan, don Allah kuyi hak'uri, inason y'ata"
Kuka kawai Hajiya Uwa keyi, Yaya ya mik'e yaja Kamal suka fita, shi namiji ne yakuma fahimcesa.
Yayi masa magana irin ta masu hankali, a k'arshe Kamal ya yanke shawarar komawa china yad'anyi nisa da gida yasan Uwa zata yafe masa sannan yakuma je ya kusanci y'arsa har su dawo gida Nigeria, sai kuma Yaya ya bashi shawarar idan har yanajin ze iya zama da ita maman yarinyar to yayi mata tayin aure idan ta amince ya aureta kawai, Kamal yaji dad'in yadda yaya ya fahimcesa.
**************
*Rimin gado*
Yawale yafi k'arfin awa d'aya suna waya da Yaya, suna magana ne game da Maijiddah.
Bayan da suka gama sai ya kira Yabi d'akinsa, ya karanta mata tiryan-tiryan yadda abun yake, Yabi kam dad'i taji domin acewarta Khalil da Kamal ai duk d'aya ne sannan dama ai tana lura da alak'ar dake tsakanin Maijiddah da Khalil sun shak'u da junansu sosai, Yawale yace ta samu Maijiddah ta tambayeta idan ta amince.
******
Da yamma bayan Maijiddah ta dawo daga gidansu k'awarta asabe Yabi tasata d'aki, ta tunkareta da maganar, Maijiddah tace ita sam Allah ya kasheta batason Khalil,
"Ke kike ganin haka Maijiddah, yau duniyarnan babu babbar riba irin ka auri maisonka fiye da yadda kai kake sonsa, ni Mahaifiyarki ce wallahi bazan tab'a baki shawarar da zata cutar dake ba, ki daure kinji Maijiddah, ki daure ki auri Khalil domin ko yana matuk'ar sonki, son da yake miki ko a musulunce yayi yawa, domin an koyar damu cewa idan zamuso kar muso da yawa haka idan zamu k'i kar mu k'i da yawa"
Maganganun Yabi ya ratsa duk wani sassa na jikin Maijiddah har saida tayi kuka, a k'arshe ta samu dai ta amince, Yabi tayita sa mata albarka.
***********
Bayan sati biyu dayin hakan, aka sa ranar bikin Maijiddah da Khalil wata d'aya tal, waka tara yaga murna wurin gogana, itakam Maijiddah babu yabo babu fallasa.
Lokacin da aka sanar ma Hajiya Uwa ansa bikin Khalil da Maijiddah, tace sam bata yadda ba kuma baza'a tab'a yin bikin ba, Allah ya kiyaye d'anta ya auri wannan d'iyar, wato ita bamata da k'imar da za'a nemi izininta kenan.
****************
Yau saura sati biyu bikin su Khalil, Kamal jirginsu ya tashi na zuwa k'asar china..........