Namijin Goro

60

by @shooly84


*Akace komai yayi mafari zeyo k'arshe, to haka abun yake, yaudai Allah ya kawomu k'arshen littafin NAMIJIN GORO, godiya mai tarin yawa ga duk masoyana birni da karkara, sak'o da lungu, gabas da yamma, kudu da arewa, Y'ar Mutan Machika nayinku iya wuya, nagode da kasancewa tare dani da kukayi tun daga farkon littafinnan har ya zuwa k'arshensa, y'ar Mutan Machika nai maku Son SO, ku huta🤝🏼.*


        🌱 *60* 🌱



Koda ta zube k'asa Yabi da Maijiddah babu wanda ya tanka mata saima binta da sukayi da ido gashi sunyi tsaitsaye kamar sojoji.


"Maijiddah ki taimakeni, ki rufamun asiri yadda Allah ya rufa miki, ki ceto man rayuwar d'ana" Hajiya Uwa ce ke wannan magiyar.


Maijiddah ta harareta tace "niba Allah bace bare nayi ceto, Allah zakije ki rok'a ba dare ba rana, kiyita itigfari kina magiya don shi kad'ai ne ze iya fidda yaronki daga halin da yake ciki, hmmm ashe dama akwai abunda ze iya sauko dake k'asa? Na tabbata ba tuban k'warai bane wannan, kinayi ne saboda lafiyar d'anki, amma dai Hajiya kinyi fad'uwar toto wallahi" Maijiddah ta k'arasa maganar tana mai kawar da kanta gefe.


"Kome zaki cemun zan shanye Maijiddah, domin nasan bankyauta ba, bani da buk'atar yi maki rantsuwa game da irin tuban da nayi, nidai nasani kuma Allah ma yasani tubane na gaskiya, Maijiddah wacece ni dana isa na ja da ikon Allah? Ai ko wannan abun daya faru da y'ay'ana ishara ce a gareni, nasan k'ila baku sani ba amma rabon da nasa Kamal a idona kokuma naji muryarsa na dad'e, tunda yabar k'asar nan bansake jin d'uriyarsa ba, yanzu kuma ga Auta, don Allah ku yafe man"


"Hajiya ki tashi ki zauna" inji Yabi.


Jiki sanyaye Hajiya Uwa ta tashi ta zauna kan kujera, Yabi ma ta nema wuri ta zauna, Maijiddah ko tana a tsaye tanai ma Hajiya Uwa kallon tara saura kwata.


"Hajiya kiyi hak'uri insha Allah Khalil ze warke, ba laifin bane abun dubawa ba, mutun ya gane kuskurensa ya kuma bada hak'uri shine abun dubawa ya, tsakaninmu daku babu zancen ramuwa kokuma rik'e juna a zuciya, haka rayuwa take dama d'an hakin daka raina shike tsone maka ido, mun yafe miki muma idan da lafin da mukayi miki ki yafe ma...." Hajiya Uwa tayi saurin tarar lumfashinta tace "wallahi ni bakuyiman komai ba Yabi, baku tab'a yiman komai ba"


"Tabd'i, Innah kidai ce kin yafe mata amma ni gaskiya bandai san ko nan gaba ba amma ban yafe ba don yanzu, inkinga yadda matar nan ta kafa min karar tsana wallahi saikin tsaneta kema"


"A'a Maijiddah kamar ba musulma ba, Allah yanason mai yafiya, shida ya halicce mu ma munai masa laifi komin girmansa ya yafe mana bare mu bayinsa, kibar cewa haka babu kyau don Allah"


"Eh Maijiddah innarki gaskiya ta fad'a kiyi hak'uri! Kiyi hak'uri! Kiyi hak'uri don Allah"


"Hajiya kinci darajar haihuwa domin ko darajar y'ay'anki kika ci dakuma darajar mahaifiyata, amma da kinsha mamakin irin wulak'ancin danayi miki tanadi, don dama da biyu na buk'aci kizo nan d'in kuma inada tabbacin zakizo, amma badon wai kizo rok'ona naje ganin d'anki ba, koda ke koba ke ni me iya kulawa da Khalil ce saboda sona a jininsa yake, koda ni banason sa ya cancanci na saka masa da irin bauta dakuma alkhairan da yayiman arayuwa"


"Kina ma sonsa ai, insha Allahu nasan kina sonsa, ai Auta d'an uwanki ne kuma kuna shiri sosai" inji Uwa.


Maijiddah ta wurga mata wani irin kallo tadai ce "hmm"


******************


Haka Maijiddah tayita zuwa kullun tana ganin Khalil a asibiti kuma takan dad'e idan taje can, yayita haukarsa tana kallonsa, idan yayi abun dariya ta kwashe da dariya idan kuma yayi na ban tausai tayita kuka, yanajin dad'in kasancewarta a kusa dashi, domin tunda ya ganeta ma idan ba ita ko Yawale suka bashi abinci ba bayaci saiko Yaya wasu lokutan.


Zaman be yiyuwa hakanan ga su Yaya dasu Hadiza, saboda kowanne acikinsu yanada Iyali, gashi kuma yara suna karatu, hakan yasa Yaya yace to yanzu ya za'ai da Uwa? Ko zata shirya ne ta koma cikin Y'an uwa rimin gado?, tace ita sam a'a bazata yi nisa da yaronta ba, daga bisani dai suka yanke shawarar a d'auko wata da wani cikin y'an Uwa suzo su zauna tare da ita don bazasu barta daga ita sai me aiki da megadi a wannan gidan ba, suka shirya gabaki d'ayansu suka koma gida, saidai Yaya da yake yawan zuwa akai-akai duba Khalil.


Allah sarki rayuwa haka abun yake, yanzu su Yawale su suka zame ma su Hajiya Uwa komai, Yawale yadda kasan shine baban Khalil, kullun dai cikin kyautata masu yake baya gajiya.


*****


Kasuwancin Yawale yanata albarka abun ba'a cewa komai sai hamdala, sunata y'ar rarrakawa da rayuwarsu, ga kuma makarantar boko data islamiya dayasa k'annen Maijiddah bayan rok'onsa da Maijiddah tayita yi saboda ita kam taga illar rashin ilimin boko.


*****


Hajiya Uwa ta aiki d'an uwanta Amadu da sukazo zama da ita banki, ya ciro mata dubu d'ari biyu da hamsin, kud'in adashe ne zata zuba da sukeyi da wasu manyan mata abokanta, aiko yayi sakaci Allah yaba Rabilu ikon k'yallo ido yaga kud'innan.


Da daddare Laraba wutar maitarta ta ciyota tanata dube-dube taga idan babu kowa taje d'akin Rabilu sai taji an rufe mata baki ta baya, an jata zuwa d'akinta, ya maida k'ofa ya rufe, tana ganin Rabilu ne ta sauke wata iriyar ajiyar zuciya tace "haba don Allah ni wallahi har ka bani tsoro, na bayar kasheni ma kawai za'ayi kwanana ya k'are, meya kawo ka d'akina?"


"Kefa wani lokacin bakya d'aukar haske, ai daga yanzu ni zan rik'a zuwa nan zefi mana sauk'i, amma kinga d'akina akwai matsala, ga wannan Amadun da yazo yadda kasan sabon megadi, ni har nayi bacci yananan yana zagaye kamar me kafi, amma kinga idan na samu na shigo nan fita bazemin wuya ba, iyaka ko anganni nace kirana kikayi na kashe miki tsak'a ko wani abu, canko sai kiga Amadun nan baya gaban gate baya harabar gida, idan nayi k'wak'k'waran motsi a d'akina sai yaji kuma kinga ke akwaiki akwai surutu idan....kingane dai"


Laraba tad'an kai masa duka cikin wasa tace "kajisa sai kace kaima bakayi, idan ka fara wayyo balarabiya ta, wayyo ni, wayyo wayoo" harsai na toshe maka baki.


Laraba ta matso kusa dashi tana wata iriyar kwarkwasa tana hankad'o k'irji irin na y'an duniya, ta cafko shi tana k'ok'arin cire masa riga ya dakatar da ita,

"Kinga ba wannan ba, abunda yasa nazo nan saboda na saki aikin daze amfane mu nida ke"


Laraba ta linke hannuwa tana kallonsa, ya cigaba da cewa, "mak'udan kud'i ne acikin gidannan a d'akin hajiya, don haka kisan yadda zakiyi ki kwaso mana shi mu kamu kanmu mu had'a da wanda muka tara, koya kika ce?"


"To tsaya, yanzu idan na satosu shikenan se mu tafi ko?" Laraba ta tambaya.


"Eh sai mu tafi amma sai munyi mata sallama, muce mata dama munga munason juna ne muka yanke shawarar yin aure mubar aiki, sai mu tafi muyi auren mu"


"Lallai ma Rabilun nan to idan ta gane anyi mata sata fa?"


"To aidai bata isa ta jefemu kai tsaye ba sai an kamamu da abunda tace mun sata kokuma sai ansamu shedu, nikam kina d'aukowa zan had'a da sauran na fitar dasu daga cikin gidannan, ta yadda ma ko anzo bincike baza'a Kama mu dasu ba"


Rabilu yayima Laraba fanfo, aiko taje ta sad'ad'a ta binciko kud'innan, itako Hajiya tanata bacci, lokacin da tazo fitowa daga d'akin ashe y'ar Uwar Hajiya Uwa ta ganta, sai ta lab'e kamar bata gani ba, da niyar idan gari ya waye ta fad'a ma Hajiya.


Aiko Laraba ta koma d'aki ta kaima Rabilu kud'innan, jikinsa har kyarma yake ya karb'a yana niyar fita tace "ya zaka tafi ka barni cikin tsananin buk'ata, tunda dai an gama me wuyar ai kawai ka tsaya mu danna bishasha, ta rik'a shafasa har zuwa wandonsa"


Rabilu dai yaga abunda ya fita mahimmanci a wurinsa duk ya rud'e, sai yayi mata wayo yace ta bari yaje ya fita ya b'oyo kud'in ze dawo, batayi gardama ba tace to, ya fita cikin sand'a, itako ta wani baje kan gado hada d'ebe zani tana jiran kwartonta ya dawo.


A hankali ya bud'e k'ofar cikin gidan ya fita, yaci sa'a Amadu baya harabar gidan, aiko ya shiga d'akinsa ya had'a kayansa tas bebar komai ba, ya had'a da kaf kayan satar nan da kuma kud'in da suka sato yanzu ya fece (gudu).


Laraba dai taji shiru-shiru, babu Rabilu ba alamarsa, taji kamar ta mutu, tace ai zezo ya sameta ne, itama idan yazo mata da buk'ata saidai yaci Uwarsa, batasan gogon ya arce ba.


Washe gari da safe bayan da Uwa ta duba kud'inta sama da k'asa bata gansu ba, Y'ar uwarta ta fad'a mata komai, Hajiya Uwa ta rik'a maka ma Laraba kira, Laraba ta fito babu shiri, ta zube gabanta tana fad'in "Hajiya gani"


"Gakin Ubanwa? Shegiya munafuka ina kud'ina da kika d'auka?"


"Innalillahi kud'i kuma Hajiya, wallahi ban d'auki kud'inki ba, wane irin kud'i kuma Hajiya?"


Hajiya da wannan mata suka taru suka yita bugun Laraba sai gashi ta fad'i yadda akai, akaje d'akin Rabilu aka tarar babu komai ya kwashe kayansa, Laraba ta ringa ihu tana fad'in Rabilu ya cuceta ya yaudareta, Hajiya Uwa tace "gara da kikasan cewa ke ya cuta bani ba don billahillazi sai kin biyani kaf abubuwan da kikasan kin sata muguwa kawai azzaluma"


"Hajiya ki rufamin asiri ta ina zan iya nemo wannan mak'udan kud'in?"


"Ta gidan uwarda kika sata"


***************


Bayan watanni shida.


Aka sa ranar bikin Mariya, ta samu miji acan D'anbatta amna kano zasu zauna saboda nan yake aiki, yanada halinsa d'an dai-dai kuma d'an boko ne yana teaching.


Da Maijiddah taji labari, taji dad'i sosai da sosai saboda k'awarta zata dawo kusa da ita.


A b'angaren Kasuwancin Yawale kam, acikin y'an watannin nan har ya siya mota, gashi gidansa ana cin dad'i dai-dai gwargwado, su Yabi duk sun canza kamar ba'a tab'a zaman k'auye ba.


Khalil jiki nanan jiya iyau, abun mamaki y'an iskan abokansa su sharlo tunda suka je dubasa sau biyu farko-farkon faruwar abun basu sake zuwa ba, (dama abokin banza aisai kanada shi ko kanada lafiya kake nasu, amma da zarar ka kwanta dakai da babu duk d'aya ne a wurinsu).


Su Jamil sukan zo garin kano duba jikin Khalil har suyi sati sannan su koma Funtua, shikam harya fara gajiya da k'asar so yake ma ya koma UK.


*******************


*Bayan shekara biyu*


Mariya ta haifi d'anta namiji wanda yaci sunan mahaifinta, yanzu haka yana da shekara d'aya da wata d'aya yaron, dayake ba gida ta koma ba lokacin data haihu, anan gidan nata akayi suna, su Maijiddah da Yabi sunje sunsha suna sun kuma yi mata sha tara ta arzik'i, tun bayan sunan Mariya Yabi suke ta mutunci da mahaifiyar Mariyar.


Yawale fa arzik'i yaci Uban nada ina fad'a maku masu karatu, yanzu har gangarmemiyar mota ya siya me d'auko masa kaya, gashi ya kama katafaren shago a kasuwar kwari, ga noma yanata yi abunsa, Maijiddah ma dake babu abunda take a gida sai ta siyo keken d'inki, da farko babu me kawo mata sabon d'inki saidai gyara, yanzu ko d'inkuna take sosai don kaf y'an anguwar nan ita suke ba d'inkunansu, ya zamana bata komai daga d'inki sai zuwa islamiya sai zuwa wurin Khalil.


Ushe ma tayi aure anan rimin gadon dai, amma wannan wanda take aure yana kyautata mata balaifi.


Khalil fa readers saidai kuyi hak'uri don yananan yadda yake, y'an uwansa har sun fara fidda rai da samun lafiyarsa.


Kamal ma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu, (ohni Indo shin kodai Kamal ya mutu ne?)

Bama ni kad'ai ke wannan tambayar ba su kansu y'an uwansa abunda suke zargi kenan.


********************


Kunsan Iyaye bakamar ma mata, babban burinsu suga y'ay'ansu sunyi aure sun aje masu y'an jikoki agabansu, to abunda ke faruwa kenan a gidan Yawale, tun Yawale baya goyon bayan Yabi a wannan maganar yanzu shima har ya fara, so suke Maijiddah tayi aure, itakuma tace jiran Khalil take.


Da suna sauraronta suyi shiru amma yanzu fa basu yadda, hardai Yabi kullun cikin bata baki take, tana nuna mata darajar y'a mace d'akin mijinta, gashinan duk sa'ointa na k'auye yaransu 3-4, na birnin ma duk sunyi aure, bayan nazari da Maijiddah tayi sai ta fahimci cewa, gaskiya iyayenta ke fad'a mata amma fa sam bata tinanin zata tab'a yin auren soyayya tunda har bata auri yayanta Kamal ba, shi yanzu ma b'ajin d'uriyarsa, yana lafiya baya kafiya Allah kad'ai yabarma kansa sani, sai ta yanke shawarar neman Fahad don k'ila yana saran aurenta har yanzu.

Take ta fara kiran layinsa, dama tanada number sa haryanzu bata goge ba, batayi tinanin zata shiga ba ma, ganin irin tsawon lokacin da aka d'auka, sai gashi ta shiga, muryar babbar mace taji, da alama hausa bata isheta ba, Maijiddah ta gaisheta sannan ta tambayeta Fahad, matar tace itace mahaifiyar Fahad, Allah yayi masa rasuwa kimanin watanni uku kenan, ta aje layin kan waya ne saboda mutanensa da zasu yita kira, Maijiddah tayi mata gaisuwa tace ita frnd d'insa ce dama ta kira su gaisa ne, ga mamakin Maijiddah sai ji tayi tace "Maijiddah ko?"

"Eh" Maijiddah ta amsa atak'aice.


Tace Allah sarki.


Da suka gama wayar ta kashe ta fara matsanancin kuka, yanzu shikenan Fahad ya rasu?


****************


Lokacin da Yawale ya k'ara tunkarar Maijiddah da maganar aure sai tace masa "Baba na fahimceku kuma nima bak'in auren nayi ba, saidai duk samarin dake zuwa wurina basu kwantamin ba sam, bana tinanin zan tab'a kawo maku wani da sunan zab'i na, sauran wanda nake tinani shima babu shi, don haka wallahi baba na baka zab'i, ka zab'amin wanda duk kake ganin ya dace dani wanda hankalinka ya kwanta dashi, ni kuma na maka alk'awarin duk wanda ka zab'amin zan zauna dashi zan kuma yi masa biyayya gwargwadon iyawa ta"


Yawale yace, "to naji Maijiddah Allah yayi miki albarka" Maijiddah ta amsa da Amin.


Bayan sun gama magana da Maijiddah Yawale yaje ya kira Yaya ya fad'a masa komai, dayake ya d'auki Yaya tamkar babban d'ansa, don shima Yayan da kansa yace ma Yawale be kamata a zubama Maijiddah ido ba, tunda dai dukkan alamu sun nuna cewar Khalil baze warke ba, nandai suka yi shawara da juna.


Bayan sati d'aya.


Yawale ya tara Yabi da Maijiddah ya fad'a masu cewar yaba Jamil Maijiddah sannan Jamil d'inma baya k'asar amma sati me zuwa ze dawo, sunsa ranar biki nanda sati biyu, a gigice Maijiddah ta d'ago tace "Baba wane irin Jamil kuma?"


"Jamil dai d'an uwanki, nida Yaya muka yanke wannan shawarar saboda kince kin bani zab'i, to ni kuma shine na zab'a maki shi"


"Haba Baba ai na zata mun rufe babin zuri'ar Baba Abdullahi, yaza'ai na auri Jamil? Mutunen da bansan komai game dashi ba shima besanni ba ganina kawai yake, idan lallai so kake nayi auren zumunci ai ga y'an uwa nan cike da k'asa, ka zab'a man wani mana don Allah Baba ku canza wata shawarar" inji Maijiddah ta fad'i haka cikin b'acin rai.


"Maijiddah k'addararki a gidan Alhaji Abdullahi take, kiyi hak'uri ki karb'eta hannu biyu, domin ni na riga na basu, karki so kiga yadda Hajiya Abu tayi farinciki dajin hakan, tace tun rana ta farko data fara ganinki kika kwanta mata arai takuma yaba da hankalinki"


"To shikuma wanda kuka ba Maijiddahr fa?" Yabi ta tambaya.


"Da yardarsa muka sa bikinsu Yabi, yace yanasonta kuma yanaso ya aureta" Yawale ya amsa.


Maijiddah ta tashi ta shiga d'aki ta rik'a kuka, data gama ta shirya taje gidan Mariya ta fad'a mata yadda sukayi da baban nata, Mariya tayita bata hak'uri tana k'arfafa mata guiwa.


********************


Aure akai kamar bikin mutuwa, koda yake ba'ace haka ba, tunda sudai mutane sunsha shagalinsu, amarya da ango ne dai ko inda junansu suke basu jeba, rabon ma dasu ga junansu ai anfi k'arfin shekara.


Nan cikin garin kano suka tare, Momy kamar ta had'iye Maijiddah, sai sa mata albarka take, ita kanta karkuso kuga kyautar da tayima Maijiddahr, gwalagwalai ne abun ba'a cewa komai, lefen Maijiddah da suka yi mata ko akwatina ashirin da d'aya, gidan Maijiddah ya fitinu (ke duniya muna sonki zamu barki).


Jamil baki har kunne, dama tun ganin farko da yayi mata sonta yayi tsalle yasoki zuciyarsa, badai yadda ya iya ne saboda d'an uwansa ya rigasa (oh akace matar mutun kabarinsa ashe duk wannan yak'in Jamil suke ma shi).


Da aka kai amarya kowa ya watse Jamil ya shiga d'akin, fuskarta ya tarar a lullub'e da mayafi, yanajin sautin kukanta k'asa-k'asa, yaje ya bud'e mayafin ya kalleta tasha ado, ya k'ura mata ido, kunsan abunka da bature sai kawai ransa ya basa tanada buk'atar Hug don wani irin matsanancin kuka takeyi, irin na cikin zuciyarnan, ya matsa ya rungumo ta jikinsa yana shafa bayanta yace "dnt worry evrytn wl b ok i promise, i wl tek kia of u, i wl mek u d mst happiest woman on earth , i won't force u 2do anything u dnt wanna do, dat i promise u *JIDDAH*.


***************


Bayan bikinsu sai ya zamana tare suke zuwa duba Khalil, idan bayanan kuma taje ita kad'ai dayake ya siya mata mota yakuma d'aukar mata driver.


Hajiya Uwa har kuka tayi lokacin da aka d'aura auren Jamil da Maijiddah saboda wani takaici taji da tsananin danasani gakuma tausayin d'anta da taji, da tayi hak'uri ta ta barsu da tuni da d'anta aka d'aura.


Bayan watanni biyu da auren su Jamil Allah yayima Momy rasuwa sakamakon zazzab'i da tayi na kwana biyu kacal.


Maijiddah taji rasuwarta sosai don tana sonta ba k'arya, abunda take mata ko Yabi sai haka.


Arzik'i wurin Jamil ko yanzu ba'a magana, bayan rasuwar Mahaifiyarsa da wata d'aya, ya shirya tafiya tare da matarsa Uk da zama na har abada saidai su rik'a zuwa ganin gida, don dama shi d'an k'asa ne, acan aka haifesa.


Suka shirya suka je suka yima kowa bankwana, harda Hajiya Uwa.


Sunbar k'asar yau washe gari Kamal ya bayyana tare da matarsa da wata y'ar yarinya wadda bata wuce shekara biyu, Hajiya Uwa ta rasa kuka zatayi ko murna, ai sai ta rungume Kamal ta fara kuka tana fad'in " na zata ka mutu Kamal, ashe kana raye" ta k'ara rungumesa"


Bayan sun natsu Kamal ya k'ara bata hak'uri akan abunda ya faru sannan ya fara fad'a mata cewa wannan matarsa ce AYSHA (Grace) ta musulunta, wannan kuma y'arsa ce JIDDAH, Hajiya Uwa fuska cike da murmushi ta karb'a d'iyar tace ina d'ayar to?, yace ai Allah yayi mata rasuwa sakamakon ciwon pneumonia, shima ya tambayeta ya yaga gidan duk ya canza?.


Nanfa tahau bashi labarin abubuwan da suka faru tanayi tana kuka, da tana fad'a masa ji yayi kamar ya mutu, kasa daurewa yayi saida yayi kuka, acikin zuciyarsa yace (danasan ba Khalil ze auri Maijiddah ba dana tsaya na aureta).


Ko awa d'aya cikakka beyi ba a gidannan yaje ganin Khalil.


************


Acan UK Jamil yasa Maijiddah wata training school, ana koya masu turanci dakuma wasu sanao'i, Maijiddah ta fara koyon son Jamil domin tanajin dad'in zama dashi ba kamar yadda tayi tinani ba, yana mata soyayya ne irin tasu ta turawa, yana bata kulawa sosai da sosai, be had'a komai da matarsa ba, (marayan Allah, babu Uwa babu Uba saidai mata dole yaso ki).


In tak'aice maku dai yanzu Maijiddah na d'auke da ciki wata hud'u.


****


Wata tara na cika gam Maijiddah ta sullub'o d'anta Namiji kyakkyawa, sunga kara iya kara, ashe su turawa haka suke, ana gadon asibiti idan sunzo ganin baby suke tahowa da gift, haka kowa ze shigo da gift d'insa a hannu, yaro yaci sunan kakansa suna kiransa da ABDALLAH, soyayya tsakanin Jamil da Maijiddah gwanin ban sha'awa. *JamilunJiddahn*❤


*****************


Bayan shekara biyu da Haihuwar Maijiddah Allah yaba Khalil lafiya, ya warke tangaran kamar be tab'a hauka............... *NAMIJIN GORO*


*Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, daya bani ikon kammala wannan littafi nawa, kurakuren dake ciki ubangiji Allah ka yafeman.