KI YADDA DANI

5&6

by @realeshaa

*KI YADDA DANI.*

_Kishiya Ko Baiwa_ 

   _Return_



 _Na Marubuciya_ 

 *REAL ESHAA*


_WATTPAD_ 

*Realeshaa* 


 _Like my page on Facebook_πŸ‘‡πŸ»

***


 *_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*



 _Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki dari biyu zaki turo da katin MTN ta wannan number πŸ‘‰πŸΌ*** tare da turo shedar biya ta Wannan number ***.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._



 *FREE Page 5&6πŸ–ŠοΈ* 


______________________πŸ“–Cikin raunin murya da tsantsar damuwa dake addabar zuciyar sa yace".Hajiya ni kaina bansan ainihin abinda ke damuna ba,Iya abinda nasani kawai shine tun daga ranan dana saki Sukainat nake cikin 'dimuwa gakuma tashin hankali da rudun dake sake karuwa kullum yake hanani bacci.yakarashe hawaye nataruwa akormin idanunsa.Wani mugun kallo Hajiya kultum tawatsa mai kafin tace"Ban fahimci inda maganar ka tadosa ba!,ka yimin da yaren da zan gane,dan naga sewani kumbiya kumbiya kake tafada babu walwala atare da ita ganin kamar so yake yace" zedawo da Matar sa,Abinda baze taba faruwa ba kenan sede bayan ranta.

"Cikin sanyin murya da ganin yanda batawa bawa kalaman sa muhimman ciba,yace"Hajiya kiyiwa kalamaina kyakykyawar fahimtar,Ina cikin tashin hankali mara misaltuwa wanda nikaina bansan tayan da zan misalta miki,ki fahimce niba.Ya numfasa tare dacewa kitayani da Addu'ar Allah yaya yemin abinda ke addabar zuciyata yakuma kawomin sassauci acikin rayuwa ta Dan inaji kamar wani gagarimin Abu ze faru dani anan gaba!.Baki ta tabe,cikin rashin bawa zancen sa muhimmanci tace"Bana son munafurci da kumbiya kumbiya,In ma so kake kadawo da wancan la'anan niyar yarinyar! yasa kake wani kame-kame toh gwara tun wuri ma kacire ta, aranka tun dare bemaka ba,Dan Wallahi ko mutuwa zakayi bazaka dawo da ita gidan kaba.In kuwa kace bazaka bi umarni naba to Wallahi sena 'daga maka nono idan yaso,kaje can ka lalace kowa ma ya huta...


Cikin sauri kanwar sa mai suna Samira tace"Haba Hajiya Wannan wace irin magana ne haka kikeyi?ai Wannan maganan Sam bedace yafito abakin kiba tsakanin ki da Yaya Addu'a ne domin,tsakanin mace da miji se Allah duk abinda zakiyi yakamata kiyi tunani akai Yaya fa 'danki ne kinsan kuma addu'ar iyaye karbabbe ne awajen Ubangiji, domin babu hijabi tsanin addu'ar iyaye akan ya'yan su awajen Ubangiji. Ta numfasa tare dacewa yanzu dakike cewa bakiso takoma,idan kuma akwai rabon koma wafa mekike zaton zefaru anan? ga... karasawa maganan tayi sakamakon wani bahagon mari da Hajiya kultum ta kwasheta dashi,nunata da 'dan yatsa tayi tana huci tace"Bakinki ya biki shegiya me bakar zuciya Wanda takwaso halayyar dangin ubanta.Idan bakin ki baze fadi alkhairi ba toh kiyi shiru dan Wallahi muddin ina numfashi Wannan shegiyar yarinyar bazata dawo gidan Ahmad ba me za'ayi da dangin jaraba irin Allah wadai!!.


Rai amatukar bace samira tamike tare dacewa tace"Hajiya gaskiya dayace kuma daga kinta se bata,bawai ina muku baki bane anma kugiji ranan nadama ranan daza kuje kudur kusa gwiwoyinku akasa kuna neman gafarar ta,data yafemuku,Domin Allah ba azzalumin bawan sa bane sede bawan daya zalunci kansa"Cikin tsawa Hajiya kultum yanuna kanta da yatsa tace"Samira ni mahaifiyar ki kike fadawa irin Wannan maganan akan wata banza kucaka Yar matsiyata!.Hannu Samira tasanya tashare hawayen ta kasancewar ta mutum me saurin kuka"cikin raunin murya tace Hajiya Allah yahuci zuciyar ki ni ban fada miki haka da niyyan bata miki ba,sedan gyara muku kuskuren dakuke shirin taf kawa akaro na biyu.


"Tana gama fadin haka tafice daga gidan batare databi takan zagin da Hajiya Kultum suke mata ba.Hawayen takaici take sharewa,aranta na maijin tsanar halayyar mahaifiyar ta,hakika tana guje musu ranan nadama ranan dazasu so sune kuka da idanunsu anma babu mai sauraron su." Kanta takife ajikin stearing din motar ta tana wani irin kuka me ban tausayi...


Ahmad kuwa cikin wani irin yanayi na tsananin tashin hankali yamike tare dayiwa hajiyar tasa sallama.Da harara tarakasa kafin tace"kaji dashi magulmaci inde ina raye to Wallahi babu kai babu Wannan shegiyar yarinyar mai kama da 'Yar aljanu"Dariyar mugunta Murja tafashe dashi wacce kebima Ahmad, cikin halin ko inkuka tace"Hajiya nima wlh INA bayanka kada kibari Wannan shegiyar yarinyar tadawo"Kwafa Hajiya kultum tayi tace "aisede bayan ba raina zata koma gidan sa....


****

Alhamdulillah yau kimanin wata na guda agidan mu,iyayena na Iya bakin kokarin su wajen ganin sungusar min da damuta,domin insamu nutsuwa.Ganin yanda suke nunamin kulawa ne yasa na kwantar da hankali na tare da kokarin danne damuwata na abinda Al'ummah ke fada akaina.Babban abinda yafi daga min hankali yanda makwaf ta keshigowa yawon tsegumi,akan zamana agida tamkar akansu nake."Wasu ma basa Iya hakuri,idan suka shigo sesun yaba mana magana nida Ummi na kancewa kwadayi mabudin wahala,dama duk abinda ba'ayi atsarin gaskiya ba toh baze daure ba" Aduk sanda suka fadi haka Ummina kanyi Murmushin takaici batare data tanka musuba,haka zasuyita yada magana se sungaji dankansu sutafi.


Wannan dalilin yasa nakan zauna adaki naci kuka har nagode wa Allah,hakika da akwai inda zanje toh dana bar gidan mu domin gujewa iyayena kananun maganan ganun dasuke fuskanta akaina.Kana babu abinda yafi min ciwo araina kamar Idan natuna Ahmad yarabani da Abu mafi muhimmanci arayuta,yarabani da martabata,nakanji takaici Mara misaltuwa da kananun shekaruna yamaidani karamar bazarawa,aduk sanda tunanin haka yafado min arai nakanji kuna acikin zuciya ta tamkar ana hura min wuta...


***

Wayarsa dake kan beside drawer yadauka yasanya a aljihun babban rigansa.Murmushi ne yasubu ce masa ganin yanda tazabga uban tagumi tana Kallon sa


Cike daso yace"ya'akayine Uwar gida sarautar mata??Yakarashe cikin sigar zolaya.Kwabe fuska Hajiya Bilki tayi tace"Naga kai baka wani far gaba ma sekace kana da tabbacin zasu bamu ita.zama yayi akusa da ita yarike hannayenta cikin sa.Cikin karfafa mata gwiwa yace"Insha Allah inaji ajikina zasu bamu ita kede kitayamu da addu'a. "Murmushi tayi tace"Insha Allah zantaya mu,Allah yasa kuma su amince da bukatar mu.Ameen ya amsa tare darike hannun ta sukafito compound din gidan su,daya gaji da tsaruwa daya daga cikin ha'da'd'dun motocinsa yashiga,hong yayi mai gadi ya bude masa gate,hannu tadaga masa seda taga yafice kafin takoma ciki.Akasan ranta kuwa addu'a take Allah yasa su amince da bukatar su...


Malam Ahmadu nazaune adakin sa bayan yadawo daga sallan isha" Ummi ce tashigo hannunta dauke da madaidacin faranti da food flaks akai se jug na ruwa.Kusa dashi tazauna tare dayi masa barka da dare.Amsawa yayi dayanayin damuwa afuskar sa,Cike da kulawa tace"Malam lafiya kuwa naganka cikin damuwa tun jiya nake lura dakai da alama akwai abinda ke damunka!?tafada asanda take ajiye kwanukan abincin agaban sa tare dazuba masa idanu,Alamar amsa take jira.


Numfashi yasauke kafin yace"...Ringing din wayar sace yahanasa kasa karasa abinda yayi niyyan fada...Sunan Alh Ali keyawo a screen din.Cikin kamala da dattako yadaga tare da sallama.Amsawa Alh Ali yayi daga daya bangaren fuskarsa cike da Murmushi,gaisawa sukayi cike da mutun ta juna kafin Alh Ali yadaura dacewa.Dama ina kofar gidan kane dan Allah idan baka komai inaso zamu tattauna wata magana mai muhimmanci.Dan jim Malam Ahmadu yayi aransa kuwa addu'a yake Allah yasa Ahmad ne yaturo ayi masa bikon Matar sa.Tunanin hakan dayayi seyaji sanyi aransa. Cikin fara'a yace"toh bismillah kakaraso daga ciki.godiya Alh Ali kafin yakatse layin.


Cike da farin ciki Ummi tace"Allah yasa de bikon Suky yazoyi tafada cike da farin ciki,kasancewar wayar a hands free yake taji komai. Ameen ya amsa fuskar sa nanu ni da zallan jin dadi.


Sallaman Alh Ali suka jiyo hakan yasa Ummi tagyara zamanta daga gefe,Izinin shiga Malam Ahmadu yabasa hakan yasa,cikin nutsuwa yayi sallama tare da shiga.Cikin mutunci da girmama juna suka sake gaisa wa.Bismillah Malam Ahmadu yace"dashi asanda yake bude musu kwanan abincin,lafiyayyan tuwon masa rane da miyar bushashshen kubewa se kamshin man shanu yake.Duk da Alh Ali akoshe yake hakan behanashi Ciba dan abinci yaburgeshi.Ganin haka yasa Ummi ficewa dan tabasu damar ci...



Bayan sun kammala ne Alh Ali yadubi Malam Ahmadu cikin sanyin murya da mutuntawa yace"Malam ina mai baka hakuri abisa abinda yafaru abaya,dole nasan abin zemaka ciwo,sede bayan da zamuyi kaddara tariga fata.


Murmushi Malam Ahmadu yayi yace"kamar yanda nafada maka tun farko,Wallahi banjin haushin Ahmad araina ba,koda Ahmad nada laifi itama Sukainat Na dashi, tunda sukadai suke tare ba dole bane musan meyake wakana atsakanin su se sun sanar mana dan haka ko wanne nada nasa laifin,fatana de a kullum Ubangiji Allah ya yayyafawa zuciyar sa ruwan sanyi yakuma maida Matar sa dakinta su cigaba da zaman Ibadah,tare da rainon kyautar da Allah zemusu.Zama Alh Ali yagyara cikin gamsuwa da kalamansa yace"hakane Allah Ubangiji yamana zabin alkhairi "Ameen ya rabbi Malam Ahmadu ya amsa cikin zakuwa da son jin ainihin abinda yakawo sa.

Gyaran murya Alh Ali yayi alamar magana me muhimmanci yakeson yi,ganin haka yasanya Malam Ahmadu tattara nutsuwar sa baki daya izuwa kansa.


Cikin muryan dake nuni da Neman alfarma,Alh Ali yace"Malam nazo Neman alfarma ne awajen ka Wanda nake saran insha Allah nafi karfin sa awajen ka,anma inaso akira mai dakin ka idan yaso se ayi komai agaban ta domin ita ma maganan yashafeta.Kai Malam Ahmadu ya girgiza cike da gamsuwa da kalaman sa yace" toh ba matsala,karamar wayar sa kiran burin kwaila(Itel)yadauka yakirata,tare da sanar mata tazo yana son Ganin ta...

Kamar minti uku da gama wayar segata tashigo sanye cikin katon hijab,wajen zaman data tashi nafarko nan takoma tazauna...


Cikin taushin lafazi Alh Ali yace"Kamar yanda nafara fada maka Malam.Alfarma nazo nema agareku toh hakanne.

Ina so kutaimaka kubani Sukainat rikon ta yakoma hannuna domin inganta rayuwar ta,ina so tadawo mace mai yanci wacce duniya zatayi alfahari da ita sannan Al'ummah annabi suyita sanya mata albarka,kana tazamto jagora acikin mutane.

Ya numfasa tare dacewa badan komai nake son yin hakan ba sedan ganin rayuwar ta tayi kyau da inganci bana fatan Sukainat takoma gidan Ahmad ayanzu!.Inaso koda zata koma gidan sa anan gaba to yazamto yasan mutunci ta da darajanta,inaso inga Ahmad yazuba gwiwoyinsa biyu akasa yana mai rokon Sukainat dataya fe masa,kana kuma yazo yanemi yafiyar ku abisa rashin kyauta ta muku dayayi"Inaso da zaran tahaihu taci gaba da karatun ta domin cika burinta,nason yin karatu mai zurfi.Banaso yazamto mun tauye mata hakkinta bayan kuma munada hanyar temakon ta domin inganta rayuwar ta....


Shiru dakin yayi tamkar babu mahulukin dake numfashi aciki,bayan sun gama sauraron bayanin sa kowanne da abinda kesakawa a zuciyar sa,hakika basuyi tsammanin Wannan alfarma zenema awajen suba shin tayama yake tunanin hakan zefaru!Malam Ahmadu yatambayi kansa cikin tsananin jimami.


Zazzafar ajiyar zuciya Malam Ahmadu yayi asanda yake cewa"Alh duk munji jawabin ka,Mun kuma yi matukar farin abisa nuna kulawar ka ga ahakina.Ban San da bakin da zan iya gode da maka ba abisa wannan karamci daka, mana hakika baza mutaba mancewa da alkhairin ka agare mu ba,sede muyi fatan Ubangiji Allah yabar zumunci.Cikin yanayin jin nauyi yace"anma sede kayi hakuri Alh domin baza mu Iya baka Suky ba!!,zaman Sukainat agaban mu shiyafi alkhauri,domin darajar 'ya mace da martaban sa shine gidan mahaifanta.Ya muskuta tare dacewa,shin idan Har muka baku rikon Sukainat yakoma hannunku,wani irin tunani mutane zasuyi!!asanda sukaji cewa mijinta yasaketa,sannan kuma takoma gidan wan mahaifin mijinta dazama?!,wani irin kallo kake zaton zasuyi mana awannan gaban!?.


Ya numfasa kana yaci gaba dacewa zasuyi mana kallon kwa'dayayyu masu son abin duniya dakuma rashin wadatar zuci.Hakika mun gode da Wannan halarcin naka baza mutaba mancewa da Kai acikin rayuwar muba domin ka bamu gudun mawan daya dace.Sannan Zamu kasance masu yimaka fatan alkhairi duniya da lahira...Ummi kuwa shiru tayi kanta nakasa takasa koda dagawa ne.


Hankif Alh Ali yaciro a aljihun sa yashiga goge zufar dake tsattsafo wa agoshinsa kamar babu fanka adakin,saboda tsaban tashin hankali,Sam beyi zaton zasuki amincewa ba jiyayi jikinsa yayi sanyi,hakika samun kamilin mutum irin Malam Ahmadu zeyiwa wuya awannan zamanin jiyayi duk wani karfin gwiwa da karsashin daya zo dashi sungudu.Anma dake Jarumine mekuma jajurcewa akan duk wani abu dayayi niyayya,se ya aro Jarumta cike da karfin gwiwa yace".....




 _VOTE COMMENTS AND SHARE_



     *_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»