SILAR FYAƊE

7&8

by @rabiattu0444

*🍀SILAR FYAƊE🍀*

      Free Book 




     NA💋

UMMU MAHER(MISS GREEN💚)


Wattpad user name

  Rabiatu333






       7🟦8



"Wata rana Umma ta aiki ni gidan Baba Na sidi sai akai rashin sa a ranar anyi ruwa kamar da bakin Ƙwarya,har Mama Khaltum tace in ƙwana na ce mata ai ban tambayi Mama ba,babu yadda bata yi dani ba nace ni tafiya zanyi haka na biyo hanya ga dare ga komai haka na fito ina ta tsare motoci amman babu wacce ta tsaya.


 Na yi tagumi kamar zanyi kuka wata ƙyaƙyawar mota ce naga ta shawo ƙwanar titin,banji tsoro ba haka na tashi naje tsakiyar titi,ina tsayar da motar da hannuna,baiyi niyyar tsayawa ba amman sai da na tsayar dashi,sauke glass ɗin ya yi,kansa a ƙasa bai kalleni ba ya ce"come in".



da sauri na shiga ina ta raba idanuwa,ban kalli mai motar ba shima bai kalleni ba,da alama bashi da lafiya don naji yana ta numfarfashi ni kuwa tsoro na ya ƙara ƙaruwa sosai jin wani baƙon al'amari yana ta ziyarta ta,shima a nashi ɓangaren haka wannan abin ya dinga faruwa.




In ta ƙaice miki a wannan dare ne abubuwa da dama suka dinga faruwa,na samu kaina a mai ƙin hanashi duk abinda ya ke son faruwa,tun abin yana tafiya gentle gentle har dai ya yi tsanani,ban san me ya faru dani ba?ban taɓa jin tsananin feelings ba sai aranar,a wannan dare komai ya faru kuka na ya tsananta sosai.


 Shima hankalinsa ya tashi sosai da sosai,don ina jin gunjin kukan da ya ke yana cewa Allah ka sani ban taɓa zina ba,ban taɓa kusantar ta ba sai yau ya Allah idan mafarki na ke ka farkar dani ya Allah.


 A matuƙar hargitse na fito daga cikin motar ina ji yana ta yimin magana don shima har fitowa ya yi,amman na fizge hannunsa na tsayar da wata adaidaita kamar ƴan party ya ɗebo,akayi sa a unguwarmu ɗaya don haka muka tafi.



Ina dawowa Baba yana kiciniyar kulle gida don sun san tunda na kai yanzu to sai gobe zan dawo,mamaki Baba ya yi na ganina amman bai ce komai ba ya matsamin na wuce,kai tsaye ban ɗaki na wuce ina kuka haka na cire sutura ta,kamar a mafarki haka na ke ganin komai yana dawomin,to me ya faru dani haka na bada kaina ga wani wanin ma ban sanshi ba.


 Kaca kaca siket ɗina ya yi da jini ina kallonsa na saka wani ihu a banɗaki,Baba da ya ke a tsakar gida hankalinsa ya tashi yana tambaya ta lafiya,shiru na yi ina rufe baki nan ina kuka don tabbas na cigaba da kukan to kaina xan tonawa asiri.


Don wannan abin ba dole ya yi min ba,ban san me ya shiga brain ɗina ba,Rabiatu me addini me kishin musulunci,me girman kai awajen wasu saboda kamun kai to me ya sakani aikata haka kuma?.



 Ina fitowa ina ɗingishi na hango Baba da Mama suna tsaye cirko2 suna kallo na na sunkuyar da kaina zan shige ɗaki,Mama ta daka min tsawa ta ce"aiken ne sai yanzu?Kuma me ya samu ƙafarki ki ke ɗingishi"?.


wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riskeni,gaba na yana dukan uku uku na buɗe bakina daƙer na ce faɗuwa na yi Mama,ba tare da ta ƙara cewa koma ba ta shiga ɗaki ita da Baba.cen kuma ta fito a lokacin ina zaune na yi tagumi da hannu bibbiyu ga ƙasa na kamar zai tsage saboda tsananin zafi.



 "Rabiatu ina saƙo na"?.



sai alokacin na hau dube dube don sai yanzu na tuno na barshi a motar wannan azzalumin mutumin.






Anan zan tsaya saboda matsalar chagi.





*Miss green ce🍀*