Huɗu
by @pinkylady
Masu complain sun kasa gane inda labarin ya nufa, kuna son rikita kanku ne. Pages d'inmu na farko guda ukku kowace zaman kanta ta ke..Ku karanta kowace ba tare da kun had'ata da 'yar uwarta ba. Misali:da kun karanta chapter 1 idan kuka zo 2 karku yi tunanin ta farkon, haka idan kuka zo chapter 3 kar ku tuna 2. Daga nan zaku ci gaba da gane 'yanuwansu a sauran masu zuwa..Shikenan zaku fahimci labarin. Nagode da k'auna😍
~~~~~~
Katsina
ƙarfe ɗaya ta fito, ba ta ga su Rafiq ba tasan basu kai ga fitowa ba ne sai ta nufi masallaci kawai kamar yadda ta ke yi duk in ta rigasu fitowa in ta gama sallar sai ta kirasu su je cin abinci idan kuma lecture kowa ta ƙare sai su tafi gida.
Ta na jin yadda idanuwan mutane ke yawo a kanta duk sai ta ji ta wayam kamar an balle mata wani gini da ta ke jingine da shi. Za ta iya cewa hakan ma, ƴayyunta ai kamar katanga ce a gare ta. Ta ƙara ɗaga ƙafa ta shige masallacin ta na sauke ajiyar zuciya duk da a cikin matan ma ba tsira tai da kallon ba. Za ai ta kallon ta ne ana magana ƙasa-ƙasa. Ba komai ke saka hakan ba sai yadda ta zamo ƴar gata ga yayyunta da yadda su ke nuna ɓacin ransu ƙarara idan a ka so shiga lamurranta.
Cikin rashin sa'a ta tadda ba ruwa masallacin sai pure water ake saye ana alwalla. Dole ta koma wajen ta siyo sannan ta koma cikin gajiya da kallon ƙurillar da wasu ƴammata ke mata tun shigowarta ta farko.
Sai da ta zo wanke fuska ne ta ji ɗayar na faɗin
"Wallahi sak!.."
ba ta ida ba ƙawarsu da suke jira ta jawo ta cikin ɓacin rai.
"Haba ku dai kun faɗo da yawa. Yanzu kawai sai yarinya ta juyo ta ga kun mata gwale? mtsw"
ta ja tsaki ta ja su suka fice suna mai da yadda akai. Ta dai ida alwallar ta tai sallah, ta na cikin salla ne ta ji ƙarar wayarta sai bayan ta gama ta ga Rayyan ne ta kira shi. Kiran na shiga ya katse ya sake kiranta sannan ya faɗa mata su na gaban masallacin idan ta gama.
Cafeteria su ka nufa suka ci abinci sannan suka rako ta ajinsu. Rayyan ya ce
"Yau za ki rigamu gamawa ko?"
ta gyaɗa kai.
"To ki dai zauna a nan harmu gama kinji?"
ta ƙara gyaɗa kai ta na shiga. Kullum magamar da suke maimaita mata kenan idan dai zata rigasu gama lecture. Ba ta taɓa kawo tunanin in sun ida makarantar ya zasuyi da ita ba tun da yanzu suna aji huɗu ne ita ta na biyu.
Malamin da ya shigo awanshi ɗaya da rabi mai makon biyun da zai yi ya fice. Shiyasa zaman jiran da ta ke masu ya ƙaru duk kusan kowa ma ya tafi sai walanda ba a rasa ba mazauna hostel da har lokacin suke ajin suna ƙara bitar karatunsu. Babu mai ko kallonta a cikin su duk ta gaji da zaman ga laptop ɗin ta ma babu charge sai ta yanke shawarar fita waje ta sha iska kafin su rafiq ɗin su gama.
Ta ɗau jikkarta ta miƙe. Karo ta ci da mutun ya na shirin shigowa ita kuma zata fita, gyalen kanta ya zame daga fuskarta ya koma cen tsakiyar kai. Idanun su suka haɗu.
"Sorry"
ya ce mata. Ta gyaɗa kai yayin da ta ke gyara zwman gyalenta walanda suka lura kuma sukai mata ƙuri da ido.
Sarai ya gane ta tunda ya na yawan zagayowa department ɗin nasu wurin budurwar shi Naja. Ya zagaye ta ya wuce, ita kuma ta fita.
Ɗaya da ga cikin kujerun suminti na SUG ta samu ta zauna. Ba daɗewa ta ga dawowarshi ya wuce da waya kare a nunnan shi sai sauri ya ke zubawa. Akan idon ta ya buɗe wata mota da ta ga tsawuwarta ya shiga suka bar wurin. Haka tai ta zama ta na kallon shige da ficen mutane ta na nazari a cikin kanta.
"Mai kake zuwa yi a nan ne? ranar ma a nan dept ɗin na ɗauke ka"
cewar Nadeem ya na ta da motar.
"Na'am" zayyan ya ce ba dan ya na da tabbacin zai maimaita mashi tambayar ba, sai yadda tambayar ta zo mashi a bazata ne.
Kamar yadda ya tsammatan kuwa banza Nadeem yai mashi kamar ba shi yai tambayar ba ya ci gaba da tuƙin shi hankali kwance.
"Ehmm..gaisawa kawai mukai sharp-sharp"
ya faɗi dan ba zai iya yi mashi ƙarya ba, kuma ya na jin nauyin ya ce mashi wurin budurwa ya zo.
"Kasan makaranta kake ko?"
ya faɗi ba tare da ya kalle shi ba balle ya ga kan da ya gyaɗa mashi. Ya ci gaba
"Ka maida hankali ga karatun ka kawai ka barta ta ji da nata. Ai kasan gidan su ba?"
kunya ta kama zayyan, ya murmusa ya ce
"Inshaa Allah"
bai kuma cewa komai ba, zayyan ma ya ja bakinshi yai shiru.
***
Huɗu da kwata su rafiq su ka ɗauki Radhiya su ka tafi gida su na jera mata sannu tamkar wacce ta yi aikin nauyi.
"Babu inda zaki sai kin ci abin ci"
ta tsinci muryar ammin ta na gab da shigewa ɗakinta. Ta juyo ta na kwaɓe fuska ba haka ta so ba.
"Ammi mun ci abinci da su yaaya. Yanzun ban jin yunwa"
"Ok. In kinyi sallah ki fito nan, ban son baccin nan na marece"
Ta gyada kanta.
Ta na gama sallar kuwa ta watsa ruwa ta fito falon. Ta dai so ta dan runtsa amma tasan ta na kwanciya ammi zata zo ta tashe ta. Ita kan ta ba jin dad'in baccin marecen ta ke ba, amma wani abu ne da ya riga ya zame mata jiki ga duk yadda ta so daurewa in dai ita kafai ce sai ta yi shi.
Sai da ta saka laptop din ta caji sannan ta fita. Su duka suna falon ana ta fira har Abba.
"Radhiya wannan k'ashin wuyan fa da ya fito ko duk bokon ce"
Cewar Rafiq ya na gimtse dariya. Ta harare shi sannan ta kalli gefen da Abban ya ke fuska a dame kamar mai shirin kuka.
"kai ko dai makaho ne Rafiq..Yanzu fisabilillahi ina ka ga wani k'ashi a wuyanta in ba neman tsokana ba. Idan ma bokon ce ai ka fita shan zafi tunda niyyar kammalawa kake, ji yadda kan ka yai k'urmeme a saman wuya.."
Bai ida ba kowa ya kwashe da dariya Rayyan har da k'warewa, ban da Rafiq da ya fara tsokar da ya had'e rai kamar ba shine ya fara ba.
Ammi ta tungure mashi k'eya ta ce
"sakar mana wannan fuskar da ka had'e, maganinka kenan da ba ka jin dad'i in baka tsokane ta ba"
"bayan kuma kasan yarinya 'yar babanta ce ba"
Radhiya ta amshe ta na dariyar k'eta.
"1-0 yarinya" ya fad'i.
Duk su ka sa dariya kuma sannan suka mik'e saboda kiraye kirayen sallar da aka fara.
****
Ta shigo d'akinta bayan firar dare da su ka gama kowa ya tafi ya kwanta. Mai makon ta kwantar kamar yadda ake ce mata ta kwanta ta huta sai ta jawo system d'in ta ta lalubo films din da aka saka mata da ta b'oye abun ta gudun wani ya gani. Kusan kala hud'u aka da mata duk korean ne.
'Decendant of the sun' da ta fara cin karo da shi ta shiga. Sai kuma ta tuno da Aysha da su naja suka fad'a mata bata lafiya.
Ta jawo wayar ta da niyyar kiranta sai kuma ta kalli agogo tara har da rabi, wata k'ila tai bacci. Sai ta bari da safe sai ta kira tun da babu makaranta ma Ko ta gwada tambayar Abba ko zai yadda akai ta? Ba ta sa ka rai ba amman zata gwada ta aje wayar ta ja laptop d'in ta mak'ala earpiece sannan ta danna play.
Episode biyu tai niyyar kallo ta kwanta amma duk yadda ta so ta datse kallon zuwa asuba sai abin ya gagara, sai ta ji ta na son ta ga abin da za a yi a gaba. A haka har d'aya saura, baccin ya ci k'arfin idanun ta saboda rashin sabo. A dole dai ta aje ta kwanta ta na tunanin ba k'aramin barin ta a baya akai ba ashe. Maganin ta kuwa ba ta ma tuna da batun shi ba ta hau baccin ta.
****** *****
Ya na zaune a falo da laptop a gaban shi ya na duba sabbin kayan da zai yi order na electronics. K'arar kyatawar agogon d'akin ta bango ya sa shi d'agowa ya duba. Goma cif na dare ya lumshe manyan idon shi da suka fi yanayi da mai jin bacci, ya bud'e su a hankali.
Yunwa ya ke ji. Rabon shi da Abinci tun safe, da rana bai samu ci ba saboda baccin da yayi na ramuwar jiya da ya kusan kwana idon shi biyu. Ya kai duban shi ga takeaway d'in shi da yai masu shi da Zayyan ba yan ya d'akko shi makaranta. Ya tabbatar da ya huce yanzu sai ya mik'e ya d'auke shi ya ida sakawa fridge kawai, ya san zayyan yai bacci bale ya saka ya d'umama mashi. Ya zari makullan motarshi ya fita ko Allah zai sa ka ya samo wani abu waje.
Ya bud'e motar kenan zai shiga ya hango giftawar abu ta cikin flowers d'in wurin. Sai ya kunna sauran k'wayayen wajen ya na d'an lek'a wurin da tunanin zai samo maganin jab'a dan yafi tunanin ita ce. Jiya ma zayyan ya fad'a mashi ya ga jab'a.
Ya gama lek'awa bai gabta ba sai ya juya kawai da nufin tafiya, idon shi ya kai ga wutsiyar maciji ya na k'ok'arin b'oyewa a flowers d'in. Kan shi ya sara yai saurin dafa kan ya na jin jiri na niyar kayar da shi.
' ka guji zaman wurin nan Nadeem. sam-sam ruhinka baya son macizai, dole in saka maganinsu a wurin '
Muryar Baba ta shigo cikin kan shi. Da sauri ya juya ya bar wurin.
Duk halin da ya ke ciki bai hana kewar baban ta lullub'e zucciyarshi ba. Da dafe bango ya koma cikin gida, makullan ma a nan ya barsu yashe a k'asa.
Tsawon lokaci ya na ajiyar zucciya tare da addu'o'in neman tsari sannan ya d'an ji dama. Gefe d'aya cukun shi ya cugaba da k'ugi, abin cin da ya aje fridge shi ya d'akko a dole tun da ba iya dafa wani abu yai ba. Aranshi ya na tunanin dole zai kawo d'anabin da zasu iya ci a irin lokaci kamar haka.
Bai ci sosai ba saboda rashin zafin, ya sha malt kawai ya kwanta. Aikin da bai ida ba kenan.
******* ******** *****
Kano
Horn kawai ta ke dannawa mutanen da su ka shige gaban ta da sukai daddab'a a wuri d'aya. Wasu da ababen hawansu suke tsayen wasu kuma sun faka sun fita. Babu alamar sun san tsayuwarta wurin bale hon d'in da ta ke faman yi.
Cikin k'ufula ta fito da ga motar ba tare da ta kashe ba, haka ba ta ko tsaya rufewa ba. Tasan dai tatsunniyar gizo ba ta wuce ta k'ok'i, ta kutsa cikin mutanen gabanta ta isa wurin da yawa idon mutanen ya baro da ga abin da su kewa dafifin kallo da d'auke-d'auken hotuna sun maido gareta. Da yawa sun santa ko dan hotunan ta da suka gama karad'e duk wata kafa ta yanar gizo Da mujallu ga masu bin karatun jarida Na fashion.
Yarinyar jiya ce. Ya kamata kuma ace ta dad'e da tashi tunda ta shafe ciwon da zai galabautar da itan.
"wai wace irin annoba ce haka ke damun garin nan ne? Wallahi sak yadda kaga yarinyar nan a kwance haka ta faru da yarinyar da na ke baka labari satukan baya. Kuma an tabbatar mini ba ita ce ta farko ba, yanzu ga wata"
Cewar wani dattijo ga na kusa da shi da yake nuna alamar tare suke, da kuma sauran jama'ar wurin da ke maida yadda akai.
Kallo d'aya taiwa yarinyar ta fahimci sumul ta ke, kawai hadda gajiyar wahala ya ha na ta farfad'owa. Ta juya ta nufi motarta da niyyar yi masu Horn d'in da za su matsa su bata wuri tun kafin ta ida rasa d'an guntun hak'urin da ya rage mata.
"Ta tashi!"
Ta tsinkayo muryar wani.
Yarinyar ta mik'e ta na binsu da ido cike da mamakin me ta ke a nan.
"sannu baiwar Allah"
Dattijon ya fad'i. Ba ta ansaba tunda ba tasan sannun ko ta miye ba. Tai saurin mik'ewa duk kunya ta kama ta tana zaton banke ta akai, hakan ne ma. Ta ba kanta tabbaci.
"wai mai ya same ki?"
"sace ki akai?"
"mai ki ke ji?"
Tambayoyin da mutanen wurin ke jefo mata kenan kowa na son jin ainahin abin da ya same ta, ya damu na yad'awa.
Da sauri ta dinga wuce su, so ta ke tabar wurin. Su kuma suka bita cike da mamaki wasu na kyautata zatin Aljanu gareta har mafi yawa na k'aryata zancen dattijon nan suna ganin neman sin adani ne kawai.
"Baiwar Allah! Dan Allah ki rage mini hanya banke ni a kai"
Cak! Farrah ta tsaya jin abun da yarinyar ta ce. Ta juyo ta kalleta sai ta mata murmushi ita ma yarinyar tai mata.
"Ok" ta ce. Ta bud'e mata mota ta shiga.
"ina kika nufa?"
Farrah ta tambaye ta ganin ta dafe kai da alama ciwo ya ke. Ta kuma san zaman ta kusa da ita ne bayan abun da ya faru, dan dai kawai yarinyar ba za ta iya tunawa ba ne.
"Gadar d'an hassan"
Ta fad'i batare da ta d'ago ba. Farrah tai murmushi ta ja motar sakamakon watsewar da mutanen sukai.
Har k'ofar gidansu ta aje ta tare da taimakon kwatancenta.
"Na gode" ta fad'i kafin ta fita.
Ta ja motarta zuwa FMA abunta.
****** ****** ******