2
by @shooly84
✍🏻
...Rumanah🕊️
(Zabin Iyaye)
©️Aisha Machika
Page~2
A zato na zan ga ya shafa mashi mari ko ya kama bala'i dan gaba ɗaya yanayin fuskar shi ya canza launi, amma sai ya yi mana ba zata, ya ce Saraki dube ni da kyau, kasan dawa kake magana ko?
Bai yadda ya kalle shi ba yace na sani Baba, ok ka sani rainin hankali ne ko?
Ba haka bane Baba kayi haƙuri ya ce kanshi a ƙasa, ka mance dokata ne Saraki? Baba ya ce cikin kwantar da murya, ban mance ba Baba, daman ina nufin idan na auri wannan ɗin daga baya sai na auri taka zabin, iyayenta aure zasu yi mata, sun ce na fito inda gaske nake ko kuma a aura mata wani.
Sai ga hawaye na zarya kan fuskarshi, ni da Baban muka yi ƙuri muna kallonshi cikin mamaki, can Baba ya ce daina bata hawayenka Saraki, dan yarda kake so ɗin ba zai yiwu ba, tunda a bun ya zama haka ma, bari kaji na riga na zaba maka matar aure yau saura sati biyu ayi, sannan kada ka mance kuma zabina babu saki tsakaninku, daga yau na kulle maganar Hairatu har abada a tsakanin mu.
Shiru Saraki ya yi na wani lokacin kanshi a ƙasa, shi kuma Baba ƙafa ɗaya ya ɗauka ya ɗora kan ɗayar yaci gaba da kallonshi, can yace toh Baba wacece ka samo manin?
Wani murmushi Baba ya yi, cikin jin daɗi ya ce sunanta JAMILA ɗiyar Alhaji Ibarahim Ningi ce, na zaro ido sosai cikin tsoro dan jin wacce Baba ya kira, tashin hankali waye bai san iyalan gidan Ibarahim Ningi ba, ƴa'ƴanshi sam basu da mutumci basu ganin mutumcin mutane.
Saboda tsabar gata da suka samu daga wajen uban, bai haɗa ɗiyanshi da komai ba, ya sakar masu kuɗi kowa yanayin abinda yake so, ba wanda ake kwaba mawa, komi sukayi dai dai ne, Ibrahim Ningi mutum ne mai mutunci da taimakon talakawa, abokin Baba Saraki ne na kasuwanci, sannan mutum ne mara zama cikin iyalanshi yau yana wannan ƙasa, gobe yana wanccan, dan haka gaba ɗaya sai ya sakar ma matanshi tarbiyar ƴa'ƴanshi.
Tabbas Baba Sarki baisan halin jama'ar gidan ba, idan ya sani ba zai taba marmarin haɗa zuri'a da dangin bala'i da masifa ba, balle har ya ba kamili kuma miskilin mara son maganar ɗanshi ba, kada kaji komai Saraki ubanta mutumin kirki ne itama yarinyar na yaba da halayenta har nayi maka sha'awarta ta zama matarka.
Saraki bai yadda ya sake cewa komai ba ya miƙe yana ma Baba sallama ya fice, domin shima tabbas ba zai rasa sanin su waye iyalan gidan Ibrahim Ningi ba.
Na tausaya ma Yaya Saraki ƙwarai dan haka na samu kaina da fidda mashi hawaye, shi kaɗai ne ya yi rashin sa'ar mace, dan sauran gasu can hankalinsu kwance daga mai yara biyar sai uku, aunty Maimunatu ma mijinta ambasado ne a ƙasar Malasia, ita ma aunty khadijat tana chadi mijinta munista ne, toh muma Allah ya bamu danshin su Amin.
_________________________________________
Ina cikin zana SSCE ne aka yi bikin Yaya Saraki da Jamila, wacce naji ƴan gidansu na kira da Jamee, ..uhm...tun wajen bikin na gane cewa Yaya Saraki tashi ce ta sameshi, a yadda na fahimta ma kamar ita kanta Jamilar ba son shi ta ke ba, ita ma dole aka yi mata, bata kunyarshi balle shakka idanunta atsaye suke tana jiran ace mata kule ta maida da cas.
Tun da akayi bikin ban sake ko marmarin zuwa gidan shi ba, domin ganin take-taken Jamila ba mai son dangin miji bace da hayaniya, nasan ba shiryawa zamuyi da ita ba dan bana ɗaukar rashin mutunci ko wulaƙanci, yanzun nan ajimu da mutum, dan nima masifaffiya ce amma haƙuri yafi zama tare dani, idan na so kuma ina juyewa miskilar gaske, na iya zama da kowane irin mutane duk ta yadda ka bullo ta hakan zan bullo maka nima.
Wata uku da auren Saraki na kammala makaranta ta, Baba Sarki ya biya mana zuwa hajji dani da aunty Salimat da shi kanshi Baban, ita ma aunty Salimat ɗin ta kammala karatun ta na (mass communication), munje mun sauke farali muna dawowa aka sanya ranar bikinta da Abu-ƙasim Gwadabe, yaro matashi mai tashen kuɗi ɗan shekaru 33 a duniya.
Admission ya fito na ci sa'a sun bani course ɗin da nake so wato (madicine) da murna da komai naje na nuna ma Baba, ya tayani murna ga khaleepha ma ya samu low a A.B.U Zaria.
Bayan kwana biyu ina zaune gaban Baba Sarki sakamakon kirana da ya yi, toh Rumanah nayi tunani da nazari naga ba ƙaramin nisa bane daga nan zuwa B.U.K, walaha zaki rinƙa sha ta zuwa da komowa, dan haka na yanke shawarar zaki koma gidan ɗan'uwanki Saraki domin can yafi kusa da makarantar, amma ki tabba duk weekend kina nan gidan inba da wani dalili mai ƙarfi ba ya hana zuwan.
Na sake yin ƙasa da kai zuciyata na ci gaba da bugu, wannan wace irin rayuwa ce mukeyi wannan gida, ace baka da ta cewa sai bin Zabin Iyaye koda yaushe, Allah ya gani bana son zuwa gidan Saraki, wane irin zama zamuyi dasu gaba ɗayansu daga shi har matar tashi?
Dan Allah Ummu ki kula da kanki, rayuwar jami'a ba irin ta secondary bace, yanzu kina da ƴancin kanki, gashi maza da mata ne a haɗe, kinsan dai halina sarai ko yayunku maza ban bari sun rabeku ba balle wasu kartin banza.
Ki kula da kanki ki kare mutuncin kanki, dan wallahi duk lokacin dana gane kin canza hali nida ke ne, shi ma gidan Sarakin sai kin kula, dan shi ba zama yaci ka yi daga ke sai matarshi, dan haka ki kula kada inji wata fitina kowansu ki bashi girmanshi. Banda samari inma kinyi kinsan makomar hakan, karatunki zai zo ƙarshe sannan nayi maki aure, idan kunne yaji toh...kina jina? Na ɗaga kai yace yawwa toh Allah ya yi maku albarka jeki fara shiri gobe Sarakin zai zo ya tafi da ke.
Ɗaki na shiga idona cike da hawaye sai dai ban yarda sun fito ba, aunty Salima ta kalleni ta ce wai ya kuka yi da Baban, na kwashe yadda mukai na faɗi mata, ta ce toh shi ne abun kuka da bacin rai Rumanah? Ba gidan yayanki za ki ba, tsoro na ɗaya aunty matarshi, kinsan hali na da nata, na tabbata ba zaman arziki zamuyi ba.
Dafani ta yi, haƙuri zaki yi Rumanah, ki bita a hankali in kuma ta nuna maki wani abu toh dole ki sake matakin zama da ita, yanzu kenan ni kaɗai za'a bari sai Iyalle, ɗan murmushi nayi kema saura kwana ashirin da ɗaya ki gudu gidan Abu-ƙasim kafin nan ga Iyalle da Amir sannan nima Baba ya ce duk weekend tayi mani anan gidan.
Akwatuna uku na cika da sutura sauran na barsu nan gida, bayan sallar isha ina kwance barin cinyar Iyalle aunty Salima na zaune gefenmu, labari muke cikin farin ciki daga baya Iyalle ta maida shi nasiha tare da nuna mani halin Baba Sarki.
Rumanah ki ƙara kula da kyau dan Allah kada kiyi ma kanki asarar karatunki, jikina ya yi sanyi sosai da nasiharta inda na yi mata alƙawura masu dama, ta ce gobe kafin ki wuce ki tuna mani zan baki zuma.
Da daddare ba wani baccin kirki nayi ba duk dan tunanin zama da Jamila Ibrahim Ningi.
Washe gari Saraki bai zo ba sai wajen la'asar, shima yana sashin Baba Sarki har kusan awa biyu sannan ya fito ya ce in fito muje, muka yi sallama da mutan gidan Baba ya miƙo man dubu ashirin wai na riƙe dan kada ya ɗora ma Saraki nauyi, na amsa ina godiya muka fice gidan ina danne kukan dake son ƙwace mani.
Follow me on Arewabooks@Shooly84